Allah ya sauwaka nayi na shareta ina jiran tazo tai min magana kan fitan da nayi dasu din amma sai naji shiru kwanan mu shidda ran na bakwai tunda safe muka bar garin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , , , ,

72
A wahale muka isa don gaba daya na ragwabe a motar da kyat naga an kai don tun ina jurewa har yakai bana iya jurewa sai dai daddy yana ganin kamar gajiye ne kawai ke damuna.
Tun shiga na daki ban fito ba na watsa ruwa a jikina na kwanta ranan ko wurin daddy ban samu zuwa ba a dakina na kwana.
Washegari har ya fita na kasa tashi sai bayan fitan shi ne kawata tazo gidan tai treatment din na har na danji sauki.
Ban samu kaina ba sai yamma jikin ya dan sake min na fito falo wurin mutane sai dai duk da haka a kwance nake.
Dadi ya dawo daga office mukai mai sannu da zuwa sai su Aisha suka mike ina kokarin mikewa zaune ne naji yace dani wai ke duk gajiyan hanya ne haka ko kuma kewan antyn ki ne ke damun ki ?
Murmushi nayi nace ai anty na wanan karon ba mu kwasa da dadi ba da ita don ta fada min magana na fada mata sai daga baya abin ke min ciwo da na biye mata har muka kai ga haka da ita.
Yace abinda kuke son kai gayi ke nan ni na kasa fahintar may nene matsalan ku ga wanan halin da kuka tsiro yi.
Shiru nayi har ya gama fadan shi ya bar falin inda ni dai banga laifina ba don duk yadda ake ai nayi wa anty halarci.
Satin mu daya da dawo daddy ya shirya yabar kasan zuwa Spain don wani businesses da suke hassashen yi na karafuna a can.
Tun da daddy ya tafi na samu sakewa a gidan don dama a takure nake dashi don ina jin kunyan yadda zai gane cewa akwai ciki a jikina tun kan na yaye goyona.
Tun tafiyan daddy ba mai jin motsin kowa tsakanina da su anty nace a raina watan sai idan yana gatin me dama matsala yake yanzu da bai kasan shiru babu ruwan wani da wani.
Sannu a hankali nake bussines dina inda nake saro kayan da zasu shiga na tura dasu kano wurin Zarah da mai kayan harka da yake mata na shiga wurin ta nan danan zakaji tace min a karo wasu sun shige ta turo min da kudina.
Rana wirin yawon shige shigen, Hindatu sai gata gidan mai kayan harka wata kawar ta takaita wurin ta bayan sun dada ta wurin iya hada mace.
Ta shiga Mai gyaran harka tagane ta amma ita ba san ta sanni ba na ta sake tana fada mata komai akaina tace.
Wallahi wata hatsabibiyar kishiya muka samu gata yarinyar karama kuma yar kauye ce amma shigowan ta gidan gaba daya ta kwace muna miji.
So nake yadda ake yabaki din nan ki hadani don Allah yadda mai gidan zai rikice akaina ya bar wacan gajar yarinyar yaji ba kowa a gaban shi sai ni cikin mu hudu.
Wallahi ni ban ki ace duk sufice su barni da gani sai shi ba a rayuwan mu na tsani kishiya a rayuwa na gashi kuma Allah ya bani su har mu hudu ne kuma ina son mijina don ban iya rabuwa dashi.
Sai da maigyaran harka ta gama saurarenta tace ai ba haka yakamata kice ba kedai kawai abaki abinda idan kuna tare yaji ba wata bayan ke.
Tace haka nake so ashe dai ke yar hannu ce sosai kinga daga haka ai zan samu kanshi ya tunkudo waccan shigiyar data koma Abuja da zama ta dawo gida ni in dane.
Yarinya kamar hatsabibiya ba duk abinda nayi mata tankar taki nake zubawa akan ta shigiya ko gezau sai naga kamar aiki zaici amma kwana biyu sai abu ya koma fiye da farko.
Tace da ita su bata kwana biyu su dawo idan ta gama mata hadi duk da kudin da ta tsala masu amma haka hindatu ta lale ta biyata kudin ta kai tsaye.
Suna fita wayana dake gefe na yai kara na daga da kyat don a kwance nake tun safe da yake yau ban fita aikin sai da dare.
Ina dauka muka gaisa tace Rahama kin san may nace a, a tace wallahi yanzu wanan kishiyar taki tazo guna yau.
Nan dai take fada min yadda sukayi da irin zagin da ta dinga min sai dariya nake nace kai Allah na gode ma wallahi Allah ka kara rufa min asiri dama nan suna yawan jifana duk kan su Allah ne dai ke kareni wallahi don ba imani ne dasu ba akan mijin su.
Tace ni dai yanzu na bata kwana biyu ta dawo idan kuma ta dawo zan mayar mata da kudin ta ne don ba zan iya mata komai ba.
Nace a, a hajiya kadai ki haka don Allah kefa akasuwa kike don haka na rokeki da duk abinda kika san na amfanine tsakanin miji da mata ki bata ni a gareni babu komai wallahi ai zaman lafiya zai sa a tsakanin su Allah kuma yasa ta gane gaskiya.
Waiko kina da hankali kuwa Rahama kishiya har kike fadin nabawa abin amfani taji dadi da miji ko may ?
Nace yo hajiya sai may jikinta daban nawa daban ai bashine zaisa tafini ba kema ai zakiji tsoron Allah ya tambaye ki akan yi mata kissa da kikayi idan baki bata mai kyau ba.
Tace kai lalai ma Rahama halinki daban ne wallahi da zasu gane natabbatar ba karamin zaman lafiya zakuyi dasu ba amma kishi ya rufe masu idanuwan su.
Mun dan kai wani lokaci da ita muna hira daga karshe mukai sallama da ita tabarni ina tunanen irin hakin na kushiyoyina naga maganan maigyaran harka gaskiya ne datace na kar mikewa na nemi tsarin jikina da na yarona.
Haka na wuni da zancen lafazin hindatu akaina nasan Allah ne ke tsare ni bawai iyawa na ko wani abin ba da na keyi.
Sai dare na shirya nai masu sallama nafice zuwa asibiti inda zanyi night duty dina tun shigana na shiga na shiga aiyukana na manta da zancen wata hindatu can a raina don aiki da yai muna yawa a gany don matsalan mata da yai yawa yanzu.
Sosai nake kula da kaina ban wasa da duk abinda zai kawo min kuzari ajikina na masu ciki tunda na sani ba sai wani ya fada min ba.
Ranan na shiga wurin aikin mu nan nasamu sauran likitoci mata yan uwa na suna hiran aka rayuwan duniya kowa tana fadin nata matsalolin.
Ina sauraren su banyi magana ba sai da sukaji ni bance kala ba sai wata hadiza ke cewa dani ke kan doctor Rahama kin huta ke kadai ce a gun mijin ki kin huta da matsalan rayuwa.
Murmushi kawai nai mata nace a ganin ki ke nan doctor hadiza ni jinku kawai nake don nafi ku matsala idan da zakuji sai kice ashe ke naki dan mali ne.
Tace kajiki da wani zance matar dake zaune daga ita sai mijinta ke har may kika sani akan halin wani zaman takewa haka ?
Nace doctor hadiza nice ta hudu a gun mijin mu ba yadda kike tunane bane din a lokaci daya suke hada baki wurin cewa what nace hakane namike ina tattara takatdin dana gama dubawa na wata mace da aka kawo a cikin dare ciki ne idan ta samu sai yaki zama a jikin ta har sai yafita asamu lafiya.
Nafice duk suka bini da kallon mamaki dayar tace kai ina ban yarda ba wallahi ta dai fadi ne kawai don muce itama din ai tana da nata matsalan.
Amma mai kishiyoyi ne zata zauna haka ko yaushe hankali a kwance bata cikin wani damuwa ko kadan.
Basu yarda ba nima ban kara masu bayani komai ba muka bar zancen a haka a tsakanin mu bandai masu bayani ba.
Sai kuma kamar sati uku na shigo na samu abokiyar aikina tana waya cikin tashin hankali sai na fahinci da mahaifiyar ta take wayan.
Tana fada mata rikicin da suke da mijin ta da kushiyar ta har takai gayin kuka nasan uwar tace ta nemi tsarin jikin ta ne sai naji tace mama nida ke nan a ina zan samu wanan ?
Sai dai ke ki sama min don Allah dai mama daga ni har yaran da zaran Nafisa ta shigo garin nan bamu da sauran kwamciyan hankali har sai ta bar garin nan zamu zauna lafiya dashi.
Har ta karasa wayan bata daina kukan da takeyi ba nai ajiyan zuciya nace da ita kiyi hakkuri hakana don Allah.
Shi alamarin namiji sai idan kana sakawa a ranka ne zai damay ka tunda har kin san inda matsalar take maku da zaran matar shi ta shigo gari ki rungumi yaran ki kifita zancen su har lokacin da ta tafi ya dawo maku.
Idan yaga kina damuwa da alamarin maimakon kiga sauki sai dai kiga ma yana kara tula maki haushe ga hakan yadda ranki zai kara baci ga banza.
Mafita dai daya ke nan mama ta fada maki shine kidai tsare jikin ki dana yaran ki don kariya daga duk wani manufa nata akanki.
Don idan kin fahinta sai kiga bayin kan shi bane hakan shuumanci ne irin namu na mata take kara ingiza shi akai don ranki ya dinga baci kawai idan tazo garin.
Tace doctor Rahama don baki da kishiya ce yasa kike fadin haka wallahi a yanzu nayi dana sanin auren Abdul a rayuwa na.
Haba dai don Allah kice astangafurullah mutun da kuka haihu har biyu dashi zaki tsaya fadin haka kuma akan shi.
Tace doctor kishiya fa ba abin yarda bace walkahi nasani nace mata don ma sai nace ni nafiki sani don ni nan da kike ganina kishiya tai sanadiyar aure da mijin mu na zama ta hudu amma kuma yanzu nice babban makiyiyyarta a duniya don halin kishi kawai.
Da sauri ta dago kai tana kallona a cikin mamaki nace kwarai kuwa nan nafara bata labarina har zuwa wanda hajiyan harka ta jiyo min din ga hindatu.
Nisawa tayi bayan tagama saurare na tace amma kan matsalar ki yafi nawa gaskiya ni ina zan iya zama cikin mata uku na zama ta hudu ai sai su caza min kaina dayan ma yaya na gama da ita balle har na zama ta hudu.
Nan dai muka yanke shawara tare zamu tura wa mahaifiyanta kudi ta taimaka muna yadda tace daga kasan bargu na kayanji.

********* ********* *********
Ranan dai nace bari na kira anty mu gaisa don kwana biyu ban kira ba bata kirani ba kuma dama dai nice mai kira din ba ita ba.
Ga mamakina sai bata dade ba ta dauki wayan na fara gaida ita tare da tambayanta lafiyan yaranta.
Mun dauki lokaci muna dan hira wanda duk akan yaran ta ne mukayi shi normal ba wani matsala a ranan haka yasa bayan mun gama wayan naiwa Allah godiya kan hakan.
Tun wanan lokacin nakan dan kira wayan ta mu gaisa tunda ta rage yawan daure min da takeyi a baya gashi har zata tambayi lafiyan baba wani lokacin abinda a baya batayi.
Abinda ban sani ba yanzu ta fahinci zama dani ba karamin rana ne gareta ba don barina yasa ta fahinci cewa ni ba kishi nake da ita ba sai taimako amma ta biyewa son zuciya tana musguna min haka.
Gashi tsakanin su duk da miji baigida kullun da irin matsalan da zai bullo a tsakanin su sai iyayye sunzo sun shiga ga maganan.
Don raini dama sun riga da sun raina tako tun baya wanda ba komai yaja mata haka ba sai son kai da suka fahinci tun farko tana dashi ashe ?
Ga gori dan abu kadan zasu rufe idon su suyi mata gori akaina kuma su zageta fes shikuma mijin dake goya mata baya yanzu yafita zancen ta .
Shiyasa taga ta shirya da Rahama kila zai kawo mata saukin zaman doya da manjan da ke tsakanin su tunda dama shine matsalan nasu.
Haka yasa take kokatin ganin ta taushi zuciyar ta akan kishina da take ji a zuciyar ta ko za,ta samu sauki a rayunta.
Ban dai yarda na sake sosai da ita ba kamar baya don bana fada mata komai na sirin daya shafe ni yadda muke da ita a baya can.
Koda yaran ne suka bulstiye mata zata kirani ta fada min nai masu magana kuma suji tundai ma Amira dake yawan dauko mata magana a gidan yanzu.
Nakan wa yarinyar magans maikama da Nasiha a cikin hikima kuma ta fahinci magana na ta bar abinda takeyi din.
Cikin jikina ya girma yanzu sosai don har ya fito watan shi bakwai da kwanaki haka nake ta fama dashi ni kadai nake kunshe da abina ba wanda ya san da shi bani ma fatan wani yazo daga fannin daddy har ya fahici hakan.
Shima muna waya dashi amma ban taba sanar dashi komai ba akancikin don haka baisan dashi ba tare dani sai dai nasan ranan da zai gani da akwai rikici kan gaskiya ban damu ba an dai riga da anyi din ko.
Ya bugo waya zai dawo cikin wani sati don watan shi uku acan da kwanaki kenan baya kasan sai da yaga komai da suke so ya kammalu masu shine zai dawo gida.
Naso bashi sakon kayan baby amma kuma may zance dashi ga hakan sai kawai nashiru sai yazo ya ganewa idon shi zai san yadda yayi ai da hakan.
Anty da kanta ke kokarin sanar dashi shiryawan mu da ni da ita sai dai idan tai magana a waya yayi murmushi don yasan tuban mata na mazuru ne dan abu kadan zai sa ta koma wa halinta tunda ya fahinci abin a jini yake muna.
Sai dai ya fahinci tunda muke ni baitaba jin nai mai wani korafi mara dadi akan kowacen su ba bani kuma sukan su gaban shi koda kuwa sun bata min rai na.

********* ********* *********
Da yamma ya dawo ya iso gida da biyar da wani abu lokacin ina daki ina kara shirya duk da dogon riga ne a jikina light blue na daura dan kwalin shi a kaina sai cikin daya turo a jikin rigan yai tsiri dashi.
Nafito da fara, a na don na manta da baisan da zancen cikin ba ni da murna na samu yaran gidan suna taron shi nace daga kofan da nake fitowa din da daddy oyoyo.
Ido ya zuba min bai iya karba oyoyon danai mashi ba a lokacin sai idon da ya zuba min har na karso inda yake tsaye sagale da corth din rigan shi a kafadan shi.
Da hannu ya daga yace dani dakata Rahama da sauri naja wuri daya na tsaya kamar yadda yace min din.
Kallona yake cikin mamaki idon shi akan cikin nawa, yace Rahama ciki ne dake komay nake gani haka ajukin ki ne wai ?
Murmushi nayi nace kai wallahi har naji tsoro na dauka wani abune wallahi, ina karsowa inda yake a tsaye sai su Aisha suka fara sulalewa falon.
Ya kara kallo na yace yaushe har kikai ciki a gidan nan har ya girma haka ban sani ba Rahama ?
Nace daddy wani ciki kuma kai mutum bai kiba sai kace ciki kuma humm naji yace kawai tare da kara bina da kallon mamaki ?
Boye min kuma kikeyi ko may Rahama da har ciki zai zauna a jikin ki yakai haka ni uban cikin ban sani ba saboda may zaki boye min wanan irin maganan da ba karami ba haka.
Na rugumay shi ina sauke ajiyan zuciyan ganin shi ya dan dafa bayana tare da kai hannun shi ga cikin take kuwa dan cikin yai wani bul bul daga cikin riga.
Yace tabbas kuwa cikine dake Rahama, don gashi naji motsin shi yanzu ai.
Na sake shi ina fadin daddy sannu da hanya yaya aiki yaya jama, a kuma da sanyi ?
Yana dai tsaye yana kallona daga inda yake bai motsa ba yace abin ya daure min kai wallahi yadda har mace zatai ciki yai girma haka ace wai ban sani ba don may zakiyi min hakane wai ?
Zama nayi don banda jimirin tsayuwa mai yawa yanzu da kyat na kai zaune ya kara kallona a cikin mamaki.
Ganin baida niyar zama nace ka zauna mana daddy ka huta tukun kafin muyi wani magana dakai ko.
Yace dani barni a nan tunda banda wani amfani a gunki har zaki iya boye min alherin da ubangiji yai min haka banyi mai godiya ba.
Nace afuwa yallabai tuba nake nayi kuskure amma may zan fada ma tunda lokacin da zaka gani yayi ko .
Kallon mamaki ya sake min daga haka bai sake magana ba sai ya fara tafiya zuwa part din shi ran shi a bace mai.
Bin bayan shi nayi da kallo daga gurin da nake zaune na sauke ajiyan zuciya bayan naga shigewan shi ciki.
Ban iya tashi ba don tashi wuya yake min sai da na dauki lokaci mai tsawo na mike
Showing 294001 words to 297000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99 Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153