a ne yakeyi taka maimai kike gani yake wanda ke kawo mashi kudi ?
Nace yafi sayen dabbobi yana sayarwa sai kuma sanan kayan masarufi suma yana dan tabawa wani lokaci.
Yace na dabbobin yafi aminci ai don shi sanan irin kayan abinci hanya ce wani lokaci na halaka ga bawa mutane ne basu ganewa.
Sai na tuna da wa, azin wani malami da na saurara a wayan anty kan masu tauye maauni irin azaban da Allah ya tanadarwa yin hakan.
Har yagama cin abincin shi bai kara magana ba sai ruwan da ya kara tsiyayyawa ya kora na mike na kwashe kayan na mayar part dina na rufo.
Koda na dawo yana kallon national new a wani tasha na zauna nima ina kallon abinda yake kallo ba tare dana fahinci komai ba sai naji na sake hamma.
Baiyi minti daya ba naji ya dauki remote ya kashe tv ya nufi gurin Ac din falon ya kashe har wutan dauka na yayi cak a hannaye shi sai cikin master bed room din shi.
Yana ajeni ya shiga wanka nima ban kwanta ba na dan mike tsaye na kara gyara shiri na.
Na koma na kwanta yafito yana tsaye yana shafa turare nabi fadadar bayan shi da kallo.
Har ya gama yazo gareni tankar dai ranan ya fara sani na a ya mace don sai da na raina kaina matuka a gun daddy.
Allah Allah nake gari ya waye na bar dakin don bazan iya kare jurewa ba don na kasa sabawa da matsin irin nashi haka.
Nake mamaki ko hakan ke sa anty na da duk tai girki sai jikin ta ya dan motsa mata tayi ciwo ne ?
Washe gari bai barni na fito ba wajajen tara na safe na samu fitowa daga gurin shi.
Haka ya jawo min sabon tsana daga matan shi don har anty sai da naga dan sauyi a fuskan ta dana shiga gaishe ta.
Amma bata dade ba ta sake don dana dawo tambayan ko tana da abinda za, a ai mata kafin mu dora girki take ce min cikin wasa.
Ke aikin may zaki yi ku zauna ki kula da mijin ki kibar gajiye tai muna aiki kada kuma anjima kice ke bazaki iya ba.
Kunya naji na fice daga dakin naje na dama mata kunnun magani na kuma zauna saida na fifita mata shi don yai sanyi taji dadin sha.
Tana falo zaune na tunkaro ta da magani tana gani ta bata rai tana fadin Rama yanzu baki manta da dama maganin nan ba so kike muyi fada ko ?
Nace ai newa mama alkawari zan dinga dama maki shi duk lokacin dama shi yayi da kyat na samu tasha tana bata rai ina mata sannu har ta shanye na dauki cup din na fita dashi daga falon.
Na dawo na samu daddy ya shigo suna zaune tare nai mashi sannu da dawowa.
Yace yau ina son shiga da kaunar ki gurin su Alhaji mu gaisa tun kafin nai tafiya naso mu tafi ban samu lokaci ba.
Tace hakan na dakyau ai yace daga can har gurin Abba zan shiga da ita su gaisa tace amma ba don zaku biya ta gida ba da sai ince zan je naga Abba nima.
Yace may zai hana don zamu bi ta gida ne ba zaki ba ko may tace ba hakana bane kasan yaune zaka fara shiga da Rama gurin su shiyasa bazan biku ba kawai.
Inda nake ya juyo ba wani sakin fuska a tare dashi yake ce min ki shirya karfe hudu zamu fita.
Daga haka ya fice ina mamakin shi cikin raina kamar bashi bane da safe yai ta jagwalgwalani har tsawon wani lokaci.
Sai da ya jima da fita nake cewa da anty may za, awa Abba dashi da Alhaji ?
Tace kije kiyi abinda ya dace idan kin gama ai maci ko don nasan baki wasa da alamarin Abba ai Rama nace ba dole ba anty mahaifi ba wasa ba ai.
Tai murmushin jin dadi yadda nake mata kara da mahaifin ta na mike na shiga kitchen.
Cake kamar kullun na hada masu sai miyan dana shiryawa Hajiyan daddy kafin wani lokaci komai ya dauki kamshi na sa a kula na shirya komai yadda ya dace na kuma gasa kaji nai peppeying din su.
Na idar da sallah na shirya cikin wani lace light blue mai kyau da tsada na kawo after dress fari mai duwatsu na aza sama tare da rolling din dakwalin shi a saman kaina.
Na juyo zuwa falon anty sai kamshi ke tashi a jikina takalmi masu tsini na saka a kafana.
Ban dade da zama ba ya shigo dakin shigan kananan kaya yayi kayan sun matukar karban jikin shi sajen fuskan shi da ke kara mai kyau ya kwata lub lub a fuskana shi, fuskan shi yai matukar kyaun gani.
Ya dan duka yana wasa da jinior yana cewa yaron baba ka fa isa shiga school haka na.
Anty tace daya huta da gorin Rama kullun zasu fita sai tace dashi No school bye suna mashi sheri.
Ya dan dago yana kallon inda nake yana cewa kyaleta kaji mai suna kaima zaka fara fita kamar kowa wanan school din da aka bude sabo zan kai ka.
Ban san yaya akayi ba yau nai magana sai cewa nayi daddy amma har dasu Nasir za, a mayar can ko ?
Kafin ya bani amsa anty ce tace si dai zauna inda suke don kada akai min dana shi kadai zakice wai wani Nasir can .
Nace haba anty Nasir fa soja ne ba wasa gare shi don kar ya shigo da bindiga kiji tsoro wata rana.
Sai naga ta canza fuska tace kaiyya Rama da Allah zai gwada min haka danafi kowa farin cikin ganin haka ga rayuwa na sai dai Allah kawai.
Cikin bata rai naji yace da ita zaki fara ke nan ko may ya kawo wanan irin maganan ku ba zaki daina ba ko ?
Ya juya inda nake a fusace yana cewa dani ke kin shirya mu tafi ne ?
A sanyaye nace eh sai dai bazan iya fita na bar anty na cikin wanan yanayin ba gaskiya ya juya ya bar falon da sauri tace kira gajiye ta fita maki da kayan har lokacin magana take cikin sanyin murya.
Bayan na kira gajiye maimakon na fita tunda ana jirana a waje sai na dawo na zauna a hannun kujeran da take zaune akai na dan kwanto da kaina ga jikin ta sai naji ta rugumay ni.
Cikin hawaye nace anty ban san magana na zai soshi zuciyar ki ba a wanan lokacin da ban yi shi ba wallahi .
Itama dai hawayen takeyi tace dani Rama ai fatan alheri kikai mashi nice dai nake ganin da shawan son ganin hakan a gareni amma hakan da wuya gare ni.
Anty don Allah dai ki daina fadar hakana ciwo fa ba mutuwa bane yin haka kamar shigewa Allah gabane.
Tace babu komai Rama ai na bari ku gaida su hajiya idan kunje ina gaida Abba don Allah kinji.
Ina shirin tashi daddy ya dawo falon yana cewa yaya baki fito bane kallon yanayin mu yayi kowa na sharan kwalla a fuskan shi.
Ko da muka fito mun samu Hindatu suna shan iska ita da wata kawarta sai hanne mai aikin ta dake dauke da abu zata kawo masu inda suke.
Daddy yana gaba ina nin shi a baya sai dai mutum zai dauka ko jerowa mukayi gashi nai matukar kyau damu.
Kawar Hindatu ke cewa da ita kai kai kai kardai nace wanan ce armaryan taku hindatu ?
Ta tabe bakin ta cikon dan dago kai ta dan kalle mu sai kuma ta kawar da kanta gare mu tace itace fa kinganta nan sai wani rawan kafa yake akan ta.
Wanan ai ba bakauya nace ku kuna may kuka bari ya kwaso maku wanan zankadediyar yarinyar haka a gida.
Nifa na dauka irin yan kauyen nan ne da naji kina ta wai wata yar kauye gaja da ita ashe yarinya sunan muna kauye ne kaiwa wallahi.
Wanan idan har bakiyi da gaske ba wallahi tana kwace maki miji kina ji kina gani ke ni har sai da naji wani abu fa jita fa don Allah ji yadda suka dace dashi.
Don Allah kubura ki bar maganan nan don zafi nake ji a raina na tsani naji ana koda yarinyar nan wallahi.
Har muka shiga mota maganan mu sukeyi inda daddy ya bude min gefen mai zaman banza na shiga yadawo ya bude gefen shi ya shiga yaja muka fice gidan.
Sai da muka dan yi nisa da gida har lokacin rai na a cunkushe yake min sai naga ya ciro handkici a wani guri ya miko min yace ki share fuskan ki don bazan fita dake haka ba azaci ko dole nai maki kibiyoni.
Karba nayi na dan goge fuskana ba tare da ya kalloni ba fuskan shi na a titi yace kamata yayi ace kina kara mata kwarin gwiwa ba wai kina biye mata kuna karaya ba haka.
Nace daddy ban iya ganin anty tana irin haka na jure ganin ta ban san har yau may ke damun anty ba take irin wanan kalamin haka.
Bata da lafiya ne a jikin ta shine take ganin kamar zata iya rasa rayuwan ta ta wanan sanadin ta manta da Allah shine mai kashewa da rayawa a duk lokacin da yaso.
Rahama idan zaki taimake ni kan anty ki zan fi kowa farinciki da hakan duk da dama kina yi amma zan so ki kara taimaka min gurin kawar mata da mumunan akidar yarda da tayi da maganan likitoci gurin fadakar da ita cewa shi ciwo Allah na iya kawo saukin shi idan ya tashi yin ikon shi don ba ko wani magana ne likita zai fada ya zama gaskiya ba.
Nace insha Allahu daddy zan yi yadda kace dani yace nagode da hakan .
Mun isa gidan su mun samu Alhajin shi yana gida a lokacin dama ya kwatanci hakane don mu samay shi a gida.
Suna falo zaune da hajiya da Aisha da anty kubura yar wajen mama laraba da sun zo gaida su don atare suka taso kuma ko yanzu komai a tare suke abin su.
Anty Aisha ce ta hango mu tafe tun daga nesa, tace ga yaya nan kamar da amaryan shi.
Hajiya tace hauka yake da zai kwaso wanan yar matsiyata ya kawo muna gida shi dai da yaga yana iya hada jini da jinin matsaiyata sai yaje yai tayi ai.
Ko da ta gama maganan ta a cikin kunnawan mu munji komai don muna tsakiyan falon bamu kai ga zama ba.
Alhaji karami ina kuma zaka shigo min gida da wanan yar matsiyatar mai farar kafar tsiya daga shigan ta gida har an fara neman kashe matan gida ana zuba masu guba ga abunci.
Cak naja na tsaya guri daya naji kafana bai daguwa daga inda nake tsaye a bayan shi.
Duban uwar yayi da mamaki ya kara duban ta yace haba hajiya matata ce fa kikewa wanan kalamin haka ba dadi.
Cikin matsanacin bacin rai yake mata magana tace eh nagani matarka ce kuwa yar gidan matsiyanta da aka cinna maka ko ?
Ta juyo gare ni tana cewa wai ke shin ko manyace bamu sani ba yarinya haka da bakin nacin tsiya kamar bakar mayya dake kin nace don bakin jaraba sai da kika shigo gidan shi dasunan wai mata gare shi ?
Wallahi tir da halin naci irin naku na yan kauye da son kwadayin duniya ke kinga arziki adole kin nace saida kikayi wa uwar dakin ki asirin data amince dake.
Itama din ai wata shasha ne da kamar ki shine take son mayar min da da kamarta har kana wani ce min wai matatace fa har ina matar take nan ?
Daga baya muka ji ana fadin idan ba matar shi bace farkan shi ce ko ?
Kinga kuma idan naci ne ai sai ince ke tabiyo ko don ke ma ai yar tallakawan ne kika aure ni da arzikina ko ?
Kai samu wuri ku zauna kabar yar mutane a tsaye haka baku bata gurin zama ba.
Nan na zube a kasa saman carpet tare da dukar da kaina ga tsoro da bacin rai sun cika min zuciya na fam.
Anty Aisha da kubura suna ce wa dani zo nan ki zauna ga guri mana zaki zauna a kasa.
Eh zata zauna a sama mana tunda nida ita duk yan gidan tallakawa ne an fada mata taji yau kuma da vaku sani ba kunji na auri karuna mai kudin duniya.
Wanan kuma yanzu ya saura gare ki inji Alhaji dake kokarin dogara sandar hannun shi yana son ya zauna a daya daga cikin kujerun falon.
Sai da ya zauna na juya gare shi ina cewa Abba ina wuni ?
Yace an wuni lafiya ya ta ince dai duk lafiya kuke gidan yaya sauran abokan zaman naki da yaran ku ?
Na amsa kaina a kasa da duk suna lafiya Abba.
Yace masha Allahu sai ai ta hakkuri kinji a zauna lafiya da kowa ke karama ce a cikin biyayya ga babba yana da matukar rana Allah yai maku Albarka nace Amin Abba.
Na juya gurin hajiya nace Mama ina wuni kaina yana kasa cikin kunya da ladabi.
Tace ke ban son makirci irin naku idan zaki kirani da hajiya da kowa ke kirana ki kirani wai harda wani shake murya wai mama ina wuni tana kwaikwayona?
Da ban wuni ba zaki ganni a yanzu shiru nayi kaina a kasa na kasa dagawa na kallesu.
Wanan dai ba girman ki bane wallahi kin gama da Saade yanzu kuma kin fado ga ita wanan din ?
Yo da ita da Saade duk ba barayin na tsunta bane may ya raba danbe da kokuwa ?
Daddy kan shi na sade ya dafe goshin shi da hannuwan shi yana sauraren irin cin mutuncin da mahaifiyar shi ke min wanda ya kasa fahintar wanan halin da takewa matan shi haka?
Saboda haka yasa hindatu ta daina zuwa gaida su idan yazo gidan da matarshi hajiya tai murmushi sai idan yazo da Zulfa ne zakaga fara,anta.
Muryan Alhajin su ne ya katse shi yana cewa dashi sai na samu an kawo min maganin da na da sako na dade ina bada sakon shi ba, a samo min shi.
Daddy ta dan sauke ajiyan zuciya yace eh Alhaji sai dana tura can kasan larabawa aka samomin shi don yana da wuyan samu anan dakai da Saade na sa a sawowa ai.
Yace Allah yasa mu amfana da shi yace amin Alhaji suka dan taba hira da mahaifin shi can hajiya ta juyo inda yake tana cewa dashi may ake ciki batun kwayan da aka sakawa Zulfa?
Yace iya bincike na na kasa gane gaskiyan maganan don matar ta rantse ba itace ta zuba wani abu ga abin shan ba.
Yanzu sai akayi yaya yace hajiya laifin da baka kama mutum da hannun shi yana aikatawa ba wuyan sha ani gare shi har ga Allah.
Don haka ina nan ina bincike a hankali don ina son in fahinci wani abu a tsanake.
Tace wai kai wani irin mutum ne mai bakin sanyin halin tsiya haka a cuce ka kace baka ramawa ita hindatun tsoran ta kakejine dabaza kafito fili kai mata magana ba ?
Haka akayi munaji muna gani yarinyar hanifa ta mutu aka cewafata ruwa an rasa yadda tayi tafada ruwan nan sai gawanta.
Yace hajiya wanan duk zargine tunda ba wai mun gani bane da idon mu amma ai in halin sune za, a gane gaskiya komai dadewan shi.
Baba yace ki barshi yayi yadda yake so ai iyalin shi ne shike zama dadu kuma shi yasan halin su yake zama dasu ai.
Nan dai suka kara dan tattaunawa kan maganan baba ne yace ya kamata ya mayar da hankali ga irin rayuwan da akeyi a gidan kada kishi ya koma hauka kuma har ana kadhin kai.
Ya amsa da insha Allahu Alhaji inayi sai dai na kara don ba mutunci ne dasu ba su buyun nan.
Hajiya tace su biyun kuma suna da mutunci ke nan ko?
Yace ba haka nake nufi ba hajita sanin kowa ne irin hakkurin da nake dasu waya sani ko wurin yawon ta ta sha wani abu tunda suna fita sau goma albarka nace zan dauki mataki akan su kince ba haka ba.
Alhaji yace ai kinji irin ta ban san may yasa kikewa yaron nan haka ba da iyalin shi kin hanashi yin yadda ya dace da gidan shi.
Tace amma ai ban hana shi aure ba ko tun yanayi har yakai ga daukowa mutane mugun iri a gida.
Alhajine ta kawar da zancen cikin cewa yaushe ne tafiyan naka ne nan suka buge akan hiran tafiyan sai canya juyo inda nake ina duke kamar mai sauraren wa,azi yace muje ko Rahama don akwai inda zamu tafi.
Nace bari na dauko tsaraban su mama a mota yace ok na tashi na fita sai ga ni na dawo da kuloli niki niki har biyu na anjewa baba nashi na cake da nai masu tare da Abba mahaifin anty sai ita kuma hajiya
Showing 186001 words to 189000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63 Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153