yace wanan yarinyar ta gama daure ni ta ko ina bai dade zaune ba ya mike ya bar gidan.
Dama ina jiran called din shi kan maganan yai ta kira har sau uku yana katsewa ban dauka ba har muka isa bai kara kirana ba.
Ranan momday na fara fita aiki ban samu matsalan komai ba nayi clearing din komai yadda ya dace nayi kafin na fara aikin da na dawo.
Yaran kuma na kaisu makarantan da yafi ko wani kyau da kulawa na saka su a nan nike zuwa na kaisu na kwaso su.
Ban hurda da kowa ba ruwa na da kuma kowa don gujewa zargi ko surutun mutane a kaina komai namu yana tafiya normal .
Ranan mun dawo gida na kwaso yaran na shiga dakina nai wanka na fito falo ina saye da dogon riga iri mai hula baya din nan sai harkokin su sukeyi ina kallon wani program a tv.
Nocking din kofa akeyi Jinior ne ya tafiya bude naji yace la ga daddy kano yazo sai naji gabana ya fadi ras.
Ya shigo rike da Jinior a hannun shi nan yaran suka shiga yi mashi sannu da zuwa suna gaidashi yana amsa masu tare da kiran sunayen su.
Haidar ne da Abdul suka nufo ni suka fada a jikina dama haka sukeyi in sunga wanda basu sani ba yazo balle sunji ance daddy don in sunyi laifi sai muce sai mun kai su wurin daddy ai sai suyi ta kuka don ba waye sukayi da uban ba sosai.
Sannu da zuwa nai mashi tare da bashi wuri ya zauna nake cewa dashi a she muna da bako bamu sani ba yace ban fada maki ina tafe bane ina son ku ganni ne kwatsan irin hakan.
Mun gaisa muyi mai yaya hanya sai yaran suka shiga watsewa daya bayan daya suka barni dashi a falon.
Ya kira suna da cewa Rahama gashi yau na sake dawowa gare ki da kokon bara na da fatan shine zai zamo zuwa na na karshe a wurin ki kaan wanan zancen don ina son muyi magana ta fahinta dake please ?
Shiyasa ma kika ga nazo nan din ni kadai batare da kowa ba a cikin masu maganan har shi uban aikin.
Shiru nayi ina sauraren shi a lokacin yace don Allah Rahama kada ki boye min komai ki fada min tsakanin ki da aboki na yau dai na sani da kuma shawaran da kika yanke tsakanin ku a yanzu.
Tun da na fara magana sai umm, umm yake fadi yanq kada kan shi yana nisawa har na kai karshen magana na.
Yace to sannu Rahama da hakkuri shi musulmi bai gajiya da hakkuri sai ki kara yanzu idan aka hada ku ukun a gida daya zaki amince ki zauna ki koma a karkashin shi ki daina daukan nauyin kan ki da nayara dakike yi kike nuna muna kin kai kin isa ke ma.
Nai murmushi nace ni bance nakai ba ko na isa kawai dai ina kare mutuncina daga wullakancin ku da kuke ganin abin ku zai rufe min ido na dauki wullakanci ku akaina.
Wallahi yaya bashir bazan kara jure wullakancin da daddy yake min a baya ba yanzu ku sani ina zaune sai dai kishiya ra ban abu ko na gani tana min sallo dashi ni ko idan za ai min sai kowa yaji don ina diyar tallaka ko mai son miji.
Yai dariya yace kiyi hakkuri insha Allahu duk wanan ya wuce sai dai ina son ki kama bakin ki ki sa muna ido don Allah kuma zan rokeki wani abu kafin komai ya kammala yadda muke so ki daure ba don ni ba don Allah zakiyi Rahama ki bar nan ki koma dakin ki da yaran ki kafin komai yazo daidai.
Nace har zuwa yaushe komai zaizo daidai din kake nufi ?
Yace insha Allahu ba za, a dauki lokaci ba nan da dan lokaci idan mun samu wurin da yai muna kyau a nan din zaku koma ciki hakan yayi maki ko ?
Zaki kuma koma dakin ki don Allah ki bar nan din da kuke zaune don dai ki san mutumi ba zai taba zuwa nan ba wurin ki da sunan aure.
Nace kada yazo mana ba sai yasha zaman shi ba in sha nawa in baizo nan ba ai yana iya zuwa wurin wata ba kunya yadawo yara na kallon shi.
Wani irin dariya ya kwashe dashi yace kai Rahama yaushe kika koma hakane wai kodai har da karatun kishi kika koyo ne can ?
Nace dama aina iya ina dai binku sannu ne don biyayya kuma yanzu naga kamar kuna ganin tsoron ku nake ji ban iya daukan wa kaina incin hakan ?
Yace musan kin iya ai har kin wuce wuri tunda har da yaran mun kin hana muga abin sai labe labe kika barmu dashi kawai.
Daga karshe muka juya kan hiran karatuna yake cewa gaskiya na godewa Allah abin kamar a mafalki wallahi Allah.
Nace a ro ai baku so hakan ba dani ku yace haka dai kikace ko mu wuce ace muna mijin doctor ai dadin mune ko.
Da zai tafi ya kawo alheri yabawa yaran nace haba harda wani guzuri kuma yace ai wanan ba komai bane ni dai naji dadin mutuntanin da kikayi ai.
Yanzu yaushe ne zaku koma can din ku bar nan don na sani kafin natafi in ma da hali ki gobe ne sai nazo na kai ku da kaina kafin na wuce ai ?
Nace kai haba dai kamar wacce ta matsu sai na shirya may be nan da wata ko fiya da hakan dai .
Yace a, a don Allah k bar wanan zancen mana ko so kike abokina ya samu hawa jini ai wanan horon ya isa hakana don Allah.
Nace horon may kuma sai kace wanda baida wasu matan a tare dashi dai don Allah barni har na shirya a tsanake please ?
Ya daure fuska yace to naji amma insha Allahu nan da Saturday mai zuwa zan zo na kaiku gidan da kaina nace da sauri a, a ni bani hurda da Saturday ai don nasan aibun yin abu a wanan ranan sai dai Laraba mai zuwa na sama ko Friday din ta.
Yace yadda kikace hakan za, a yi rankishi dade aiko hakan ma mun gode sosai wallahi don zan tafi da kwarin gwiwa ai.
Nace amma fa ia sani gidan nan zamana yakeyi ba zan sake shi ba muddin naga baiyi yadda mukai alkawari da kai ba wallahi wallahi sai dai ku wayi gari na dawo nan din kuma bazan taba kara yarda da ku ba har abada.
Yace insha Allahu ma zaki samay mu da cika alkawari da yardan ubangiji kada ki damu yi muna dai fatan alheri mu samu mu fita daga tarkon ku na mata tunda haka Allah ya nufe mu da gani a kan ku.
Har bakin mota na raka shi ya wuce yana min godiya na koma ciki na zauna sai lokacin hiran mu dashi ke dawo min a raina nai mamaki yadda na amince mai da bukatan shi haka ?
Ina fa jin tsoron kada sai na koma daddy yace bai san da zancen ba yazo ya karya alkawari sai gabana ya fadi dam a lokaci guda.
Na dauki waya nai dialing din nomban shi kira daya biyu gana uku ya dauka ina jin yana magana yace hello nace yaya Bashir sai kaga na kira ka kuma yace eh wallahi ko kinyi mantuwa ne dai ?
Nace kamar ka sani nace wallahi yaya Bashir kada na koma gidan daddy da zama yazo yace baisan da zancen hada mu wuri daya ba daga baya.
Na rantse da Allah idan yai min haka sai nayi inpiching din ku a kotu daga kai harshi daga baya kada kuce ban fada maku ba.
Yace subbahanallahi Rahama may ya kawo wanan zancen kuma haka kodai kina shawara da watace ban sani ba ?
Nace aini ba haka nake ba banda yawan kawaye haka kuma ban sharing din matsalana da kowa sai idan naso na dai kirane kada na koma yaga na koma yace zai min wullakanci kan hakan ba zan dauka ba.
Yace kada kiji komai kwantar da hankalinki ashe daddy yana kusa suna tare yana jin may nacewa Bashir din ya kada kan shi kawai.
Sai da muka gama wayan yace Bashir yanzu na gane dalilin wasu maza da basu yarda mace tai ilimin zamani bayan secondary.
Wai yau Rahamane ta zare haka don Allah yarinyar da ko yatsa aka sa mata a baki bata ciza shi idan ba taso ba amma jita yanzu don Allah.
Yace nima abin har tsoro yake bani ai sai da mukai wanan maganan da ita bashir din yace wallahi ba komai bane sannin ciwon kan ta tayi yanzu kawai duk shi ya jawo hakan ba komai.
Sai dai gaskiya sai kayi da gaske don akwai magana babba idan sun hadu a wuri daya dadin abin kasan halin kayan naka ka iya zama dakowan su ko.
Amma dai ayi a sannu ayi adalci don Allah a tsakani kaga wanan daukan wacce bata girki ka fita da ita don Allah a daina tunda suna da motan su kowa taje gashin kan ta don ba kowa fa zai iya hakkurin abinda yarinyar nan kai mata ba.
Yace ni may ne mata illa kishi data saka a ranta kuma duk haka suke ai da bakin kishin junan su yace dashi ai dai ba a taba ji ba sai yau din nan ko ?
Nan dai suka tattauna daga karshe suka shiga gari don yin wani harka daya shafe su can.

********* ********* *********
Ban fadawa yaran batun tashin mu ba gidan sai ana saura kwana biyu mu koma can muna falo dasu mun barbaje nace dasu.
Tau yau dai saura kwana biyu mubar gidan nan dai sai duk sukayo min ido caaa akaina sai Aisha ce tace dani anty ina zamu koma kuma bayan nan din , ?
Na bisu da ido nace daddy yace bai yarda da zaman mu nan ba dole mu koma gida mu zauna can wirin shi.
Har suna hada baki wurin cewa inda mama ihisan take nace can din kuwa kai kai inji Nasir yace wallahi ni haka bai min dadi ba nace ina ruwan ka kai da kake namiji baka zama gida kuma kwana nawa ya rage maku ku tafi ku barmu nan din.
Kowa ya dinga fadan albarkacin bakin shi nasan dan freedom din da muka samu yanzu akwai matsala idan ance za ai muna abinda akayi a baya zama ba sakata ba wali a can din.
Basu so ba haka dai na kwantar masu da hankali muka shirya ba komai muka dauka ba don wacin gadi zamuje yi mugani ga watauna ba san mu dai shiga din ba agani.
Dogon motar su na wurin aiki ya turo muna ta kwashe mu da kayan mu zuwa gidan ni da yarana da yan matana ras har su uku don ko wace ta girma yanzu.
Mun shiga da sallaman mu babu kowa a falon sai tv dake faman aiki a wurin kawai shi kadai.
Ban tsaya ba muka wuce part din mu a rufe yake na dauko ke daga bag dina nabawa Aisha ta bude muna suka fara shiga da kayan da mukazo dasu ciki.
Jin motsi yasa ihisan fitowa tare da yar aikin su sai taga muna suka juta da sauri suna fadawa hindatu din tace wa Rahama fa a gidan nan yai daidai Aisha ta fito falon tana jin su.
Ta koma tana fada min nace tasan abinda tayi kila kada na dawo yar iska wacce bata tsoron Allah ga alamarinta.
Aiko kamar ai aiko mata da sakon kayan ta har muka gama shiga da kayan mu ciki ba wanda ya leko falon cikin su.
Dama munzo da abincin mu da zasu ci don haka bamu damu da rashin girka muna komai ba.
Sai bayan wani lokaci daddy ya dawo gidan ina zaune na idar da sallah la, asar naji shi da yaran sukan Haidar da Abdul sukayo daki da gudun su da suka gan shi.
Ina may nene wai haka ya bude labulen dakin ya shigo yana cewa ikon Allah daddy kuma kuke tsoro.
Daga yaron nayi ina kwashe salaya na nace dashi sannu da dawowa fuska a daure yace yauwa kun dawo lafiya.
Alhamdullahi na bashi amsa dashi ya nufo yaran suna kokarin shige min a jikina basu son ya dauke su wai .
Yai murmushi ta re da kadan kanshi yace baku sanni ba ko maman ku ta hana ku sani na ko ?
Ni dai banyi magana ba na bude wardrobe na ciro wani dogon riga nawa Abdul ya rike min kafafuna nace kai tsaya dan Allah ni kada ka kadani kasa kaji.
Ya zo ya duka har inda muke ta dauku yaron ya fara kuka zai fita dashi shiko haudar duk yabini ya make shima nace kubi daddy ya sayo maku ice cream ba zaku sha ba yaran suka kada kai nace to kuje gun daddy ya sawo maku biscuit da sweet yanzu zaku dawo da big bros zaku tafi cewa Nasir sai suka yarda suka bishi.
Bai jima ba ya fice dasu har jinior da Nasir din suka fita tare yan matan suka dawo guna suka zauna muna hira.
Sai gab da magariba suka dawo gidan hindatu na falo taga shigowan shi dasu tace bissimillahi diyan gwal sun dawo ke nan bamu da hutu yanzu gidan nan balle aiyi lokacin mu.
Tace ashe kin gane ke nan farin cikin rayuwa na sun dawo duhu ya yaye min banda lokavin kowa yanzu sai su.
Aiko tace dawa Allah ya hadata bashi ba kuma don may zai fada mata hakan ai wullakanci ne ba sai ya fadi ba kowa ya sani ai.
Aikin banza may ye bamu sani ba mu dama ai mun ssn komai shiyasa aka dawo aka lake wani gurin har a gama shirya maka don a samu a mallake mu wallahi duk abinda mutum ya dauko ya kare a kansa.
Munafuncin banza da wofi sai da aka gama ta zubar da bin dangin miji a na rokon su sannan aka dawo muna mu Allah ma dai ya cece mu da ciwo wallahi.
Yace cikin wani tsawa ke hindatu ya isheni haka duk kika kara bude baki kika zagar min mata na ki kikai mata sheri yanzu zan dauki mataji a kan ka.
Eh lalsi shirin ki na kyau wallahi Rahama amma mu zuba dake a gani wallahi sai anga wanda zai raina kan shi.
Ina daki ina jin ta nace ohoni Rahama na dawowa turke na mai cabo dada an fara ke nan kuma amma zan daga mata kafa na iya gudun ta dai.
Shi oan shi yai mamakin yadda na kyale ban tan ka ta ba a lokacin don har lokacin ma ni bata sani a idon ta ba haukan ta dai take kwasa.
Ina jin komai na na dake a dakin bayan sunyi sallah ya fito da yaran suna zaune falo haidar na kuka jinior ya taba mai biscuit din shi sai ga wayan Raliya ya shigo mashi a lokacin.
Ya dauki wayan tana jin kukan yaron tace kana inane haka nake jin kuka yaro kuma ?
Yace ina gida zaune daidai fitowa na daga daki in gaidashi tace gidan ka fa ya sake cewa eh a gida nake zaune mana.
Tace wake kuka yace Haudar ne da Junior ke rikici haidar sun dawo ne ko may sai raji murya ina cewa kai Jinior baban kwabo ne fa naka zaka sha na kanin ka kuma kyale bros sai na dauko nashi ai kasha kaima.
Tace dashi eh lalai na yarda kuwa ashe akwai munafunci ban sani ba haka sai yace muna funcin may sai ta kashe wayan ta.
Kallon wayan yayi yai tsuki tare da murmushi yana girgiza kan shi kawai na fahinci komai amma sai nai kamar banji ba naci gaba da magana da yaran na bar wurin ban sake magana ba.
Tsaye yake yana waya yace Bashir maganan ka gaskiya wallahi na fara fahintar komai a yau din nan da dawowan Rahama gidan nan.
Nan dai yake fada mai komai da yafaru tsakanin shi da Hindatu da Raliya din yace bashir kaji min matan nan yadda taita rokona kan na yarda muyi aure zata kawo min kwanciyan hankali a gidana.
Yanzu gashi na fahinci shigowan ta ma yafi tayar min da hankali fiye da baya can don ko tsakanin ta da sauran babu kauna kullun cikin makirci take wa abokan zama.
Bashir tace kafara ganewa ke nan yanzu sa masu ido da a tsakanin su da kan su zasu fahinci komai akanin kaga am fara shiryawa ai mata ba a shiga tsakanin su sam barsu suyi tayi da kan su.
Ban karbi girki ba sai washe gari nayi girki ba zance komai ba don nasan mai karatu zatace dama ahi nake so eh ko shi din ne ai mutum nake mai jini a jika dole ne nima naso mijina dan yaushe rabo.
Bayan komai ya kammala ya dan rugumoni yana cewa Rahama na amsa a dakile yace na rokeki daga wanan karon kada ki kara nisan ta kanki gareni.
Dariya ma maganan shi tabani nace nina nisanta kaina gareka ko kai kanisan ta damu don kawai baka dauke mu da daraja ba kayi mun haka don ran matan ka yai dadi.
Showing 369001 words to 372000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124 Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153