ki dai daure ki sha magani.
Nafita na dauko goran ruwa nadawo dashi nasan inda ledan maganin yake na dauko na kawo mata tasha ina tsaye na kawar da kayan.
Falo na koma nasamu yaran sunyi barci na kwashe su zuwa cikin dakin kwanan mu sai mama dake zaune daga gefe daya tana tasbihi.
Dakin anty na koma yadda na samay ta ta bani tausayi a hankali na zauna tare da dan fara tausa mata kafa a hankali sai naji ta sauke ajiyan zuciya tana cewa wai nagode Ramana Allah yai maki albarka kinji.
Dama baban su Amira nake samu yadan yi min hakan yanzu ko bani kadai bace, baida lokacin min hakan sai gashi Allah ya kawo min ke a rayuwana.
Nace Allah dai ya baki lafiya Anty ki koma kamar kowa tace ai matsalan cikin nan dake jikina ne yanzu shine damuwa na .
Insha Allahu lafiya zaki haife shi babu matsalan komai, tace to Allah yasa Ramana nace Amin.
Ina nan gurin ban dade da fara mata hakan ba naji barci ya dauke ta ban daina abinda nake mata ba duk da na soma jin barcin nima.
Naji anturo kofan dakin dake a saye na juya don a zatona ko mama Altine ce ta shigo dakin sai naga maigidan nata ne ya shigo dakin .
Saye yake cikin farar jallabiya ta maza mai dan gajeren hannu iya damtsen hannuwan mutum.
Ina ganin shi nai saurin kokarin mikewa nabar dakin yace min a hankali ki zauna abinki tayi barci ne ?
Eh tasamu barci yanzu ya dan kai hannun shi saman wuyanta a hankali sai ta bude idanuwan ta.
Dan murmushi ta sauke tana cewa bakai barci ba ashe yace yanzu na gama kallon ball shine nazo na dubaki.
Gashi kuma na tayar dake daga barcinki, tace ai yanzu ne ma barcin ya dan dauke ni dan nasamu Rama na dan tausa min kafana.
Sune ke damuwa na da mugun tauna wallahi yace da safe in Allah ya kaimu lafiya dole mu je asibiti a duba lafiyan ki ai.
Ba tace komai ba sai lumshe idanuwan ta da tayi yana tsaye ya kura mata ido na dan lokaci yake cewa ita dawa ke kwana a dakin nan.
A hankali nace dashi da mama suke kwana yace ki kwana da su yau don naga alaman tana jin jikin bata dai son fadi ne kawai.
No taje gun yaran ai ba damuwa nasha magani da zan kwanta Rama tabani nasha ba wani matsala.
Yace shike nan sai da safe Allah ya sauwaka ya juya yafita daga dakin ina zaune gar lokacin ina dan mata tausa a kafan.
Naji ta koma barcin ta na mike na koma daki nai shirin kwanciya sai dai hankalina bai kwanta ba na koma dakin nata.
Har lokacin tana barci ne mama ma ta shigo dakin na fita na rufe part din namu tare da kashe duk wani kayan wuta dake aiki a falon.
Nai ma mama sai da safe na koma na kwanta sai barci na dan samu barci sosai sai zuwa biyu na dare na falka.
Mikewa nayi na kewaya ban dakin bayan nafito ne nace bari na leka dakin nata nagani.
Ina shiga dakin mamane nagani zaune bakin gado kusa da kan anty da sauri na karasa gurin su.
Jin motsina yasa mama juyowa gareni tace kin falka ne Rahama nace eh mama jikin ne kuma, tace ai tun dazu bamuyi barci ba wallahi.
Kai kai kai take fadi da sauri na karasa ina fadin sannu anty ta daga min kai a hankali alaman amsawa take min.
Da sauri na fita na dauko cup a kitchen din mu tare da goran ruwa na dawo dakin zama nayi a kasa na zuba ruwan a cup din sai na dago shi daidai saitin bakina.
Na fara da bissimillahi bissimillahi, bissimillahi, lahaula walla kuwati, inni billahi aliyyal azzeem kafa bakwai, sai li, ilafi qurrashen kafa uku na karanta falaki da nas uku uku na karanto suratul ikilas kafa uku na tofa a ruwan.
Na mike zuwa inda take nake cewa anty mike kisha ko kadan ne mama take cewa may ye kuma wanan Rahama nace addu,ane na tofa mata a ruwan tasha.
Dariya mama ta dan yi tace kai wanan yarinyar da bakin rigima kike wallahi kece zaki tofa addua asha.
Hannu anty ta miko min tace wassh mama bari na sha don Allah ta dan mike zaune na bata da hannu na tasha nace ki dan raga kadan a shafa maki a jikin ki.
Ta rage tare da komawa ta kwanta na shafa mata sauran ajikin ta har zuwa cikin ta na shafe ta dashi inajin abin cikin cikin yana motsawa.
Da ita da cikin suka ban tausayi sai naji tayi ajiyan zuciya mai dan karfi nace da ita sannu anty a tausa kafan ne tace baki gaji ba da kije ki kwanta kawai kinji nagode ma da wanan din.
Na dai fara tausa mata kafan nara har zuwa guiwan ta tace na ja mata hannayen ta ma.
Ina ja ina tofa mata Ya fattahu, Ya salam, Ya Arrahaman, sai naji tana dan numfashi daidai alaman ta samu barci ke nan a lokacin.
Mama har ta samu ta dan kishingide a gefe barci ya dauke ta a lokacin ina nan zaune ban daina mata adduan da nakeyi ba .
Har karfe hudu da rabi sai barci ya dan dauke ni nima a furin na kifa kaina kusa da kafan ta ina zaune.
Biyar da yan mintina ta falka taganni a hakan yadda nake kwance tausayina ne ya kamata a gurin.
A hankali take kiran sunana na falka zubur ina cewa anty kin tashi nw tace eh ina son in dan kewaya ne bandaki ga lokacin sallah ma yayi.
Na gyara inda zata mike ta yunkura da kyat ta tashi zaune harta dan sako kafanta zata mike sai kuma naga ta koma ta zauna can ta mike da kyat ina tsaye ina kallon ta da kyat take cira kafa tana tafiya zuwa ban dakin.
Naji tace Rama zo ki kamani jiri nake ji sosai na zo da sauri na kamata zuwa bandakin sai da naga ta zauna saman toilet na fito daga waje sai da taga ta doro alwala sai tace nazo na kamata.
Har lokacin da alama tana jin jirin nakaita bakin gado ta dan zauna na shimfida na shimfida mata salaya ta zauna a zaune tai sallah ranan duk kokarin da take dashi gurin yin sallah a tsaye ga halin da take ciki.
Nima alwala nayo nan na zo nai sallah ina addua naji tace Rama don Allah ki rufe ni sanyi nake ji jiikin ta rawa sosai a lokacin.
Da sauri na dauko bargo na rufeta dashi sai sharking jikinta ke faman yi duk na rude na rasa abinyi a lokacin.
Can dabara ya fado min a raina da sauri na nufi inda wayan ta yake na fara duba lamban mijin ta.
Naga ta rubuta mai Heart Beat na danna kira duk da babban waya ne gareta amma na gane yadda zan kira dashi.
Kira daya na biyu naji an daga wayan da sauri yake cewa heart beat yaya dai sai dana daure nake cewa daddy nine anty ce jikin ba dadi bata samu barci ba tun dare.
Yace subbahanallahi Rahama shine baku kirani ba muje asibiti nace harta dan samu sauki ne da farko shiyasa ban kira ba.
Naji ya kashe wayan nashi nakoma inda take kwance a kasa saman salaya tana rawan sanyi cikin bargo.
Baifi minti shidda ba ya fado dakin a rikice dashi idanuwan shi a kansa yana kallonta da saurin shi ya karasa gurin da take ya dan yaye bargon a hankali.
Idon ta yana rufe ya kai hannayen shi yana dan taba jikin ta naga ya mike zubur da sauri yacewa shiryata mu tafi asibiti yanzu da ita.
Na mike jikina min rawa na sauri dauko wata doguwar riga na samu ta mike da kyat tasaka na kamata zuwa hanyan waje duk nauyin ta a kaina yake sai gashi da saurin shi ya kama min ita muka fice daga gidan ban ko tsaya kallon inda mama tashiga ba ashe tana bandaki.
Nan dai muka kama hanya sai asibiti take aka karbe ta sai dakin likita aka shiga dubanta an fada muna cewa, tana fama da rashin lafiyan masu ciki yashigo mata kuma.
Gado aka bata za, a kara mata ruwa da allurori idan ma har da bukata harda niji zaa saka mata likita ya fadi.
Hankalin mijinta yai matukar tashi yake cewa ai mata duk wani abinda ya dace a taimaka mata dashi don Allah.
Dakin da za, a kwantar da ita aka kaimu nan dai aka fara mata duk abinda ya dace muna waje zaune cikin damuwa dagani har mijin nata kowa hankalin shi a tashe yake lokacin.
Ba adauki lokaci ba barci mai karfi ya dauke ta sai lokacin aka bari muka shiga gurinta tana barci sai dai kana gani kasan tana cikin wahala sosai.
Lokacin ne yaran suka fado min a raina na sauke ajiyan zuciya nake cewa ina son nakoma na shirya yara a gida saina sanar da mama halin da ake ciki.
Nan ya dan dago kanshi daga inda yake zaune yana dan buga kafanshi a cikin damuwa yace zaki gane gidane idan kin fita nace insha Allahu zan gane.
Bussimillah yace dani tare da mayar da hankalinshi gareta na fice daga dakin na nufi hanyan fita daga asibitin.
Tafiya nakeyi a cikin damuwa yanayina yake ina tafe babu abin hawa a lokacin sosai duk wanda nagani a cike yake da mutane can naji anata faman horn a bayana ban juyaba don ban zaci da ni akewa horm sai da naji horn din ya matsa ne na dan daga kaina mijin anty ne na gani yana min horn din yace shigo na saukeki nima zan shirya ne.
A tare muka dawo gidan muna tafe ina kallon hanyan don in gane kada na bata idan zan dawo asibitin, ina shiga gida na samu mama a cikin damuwa tana ganina take cewa ina kuka shiga nafito ban samay ku ba nace cikin wani yanayi mama asibiti aka kai anty an bata gado tana can kwance nake mata bayanin komai.
Na nufi gurin yaran da sauri na samu sun falka sai dai suna kwance da sauri na shirya su nai masu indomie kawai ranan sun dan makara zuwa makaranta.
Na shiryawa Anty breakfast koda ta tashi tana son cin abinci abinci mai sauki na hada mata jeloup da vegetables sai anta da nai amfani dashi a cikin wani littafi na karanta yadda ake hada shi don mara lafiya na zuba ruwa a flask da sauran abubuwan bukata da za, a nema acan.
Nafito na hadu da zulfa tana shigowa main falon na gidan nai mata ina kwana ta amsa a dakile ta wucce abinta.
Allah ya taimake ni don droup na dauka sai asibitin mijin na waje yana magana a waya ya hangoni tafe da kaya.
Waya yake amma yadan kalloni na wuce shi tare da dan dukawa nagaidashi na shige ciki.
Har lokacin tana barci mai nauyi ga drip din da aka samata da allurai acikin sa ya canza launin ruwan.
Mama na zaune saman kujera na shiga da sallama tadago tana cewa kin dawo Rahama na amsa da ehmama ina aje kayan a gefe tana ganin nazo da carpet da filo don zama tace Allah dai yai maki albarka Rahama don zama saman kujeran ba dadi.
Na karasa bakin gadon ina cewa har yanzu bata falkaba ne ?
Bata falkaba likitan yacs abarta ta samu barci don shima cikin lafiyan ne haka, wanan yar dai Allah ya tausaya mata yabata lafiya amna tana wahala wallahi.

****** ********* ******

Zuwan Jatau gidan mu gurin biko yafi a kirga wanan lokacin ganin mama ba zata sauki ba yanemi sulhu gareta.
Kudin data yanka mai dole ya fitar yaba da shine suka dan hada ma Lawisa kayan aiki da dan gado madaidaici da sauran abubuwa.
Sai dai Lawisa takafe bazata koma ba gidan nan dai sani Allah sani Annabi aka samu suka shawo kanta aka mayar da ita gidan da kuka dakomai bafon ransu yaso hakan ba har mama din.
Zuwa wanan lokacin hankalin baba ya dan dawo gareshi don ya fahinci rashina da mahaifiyana a gidan ba karamin kuskure yayi ba.
Don gidan gaba daya ya sauya ba dadi gare shi ga cin mutunci ga mama kaman an kara mata hakan ne bata tunanen mutuwa ko kadan a rayuwan ta.
Haka yasa ya nemi aminin shi suje ai mai bikon Inna ko zata dawo dakinta.
Amma inna tace har abada tagama zama a gidan shi don ita yanzu hankalinta a kwance yake mata.
Duk yadda yaso Inna taki daawowa gidan hankalinshi yai matukar tashi ga gida ba dadi ko ga diyanshi agaban shi yaro sai yai abin fitsara ba su dauke shi komaiba garesu.
Lawisa na komawa matan gidan suka hade mata kai kan sai an raba girki ta fara tace ita baza tayi ba tace da Jatau ai Rahama da tai aure a gidan garbati marigayi bata girki da matan shi don su suna da iyali sai itace za, ace ta shiga cikin manyan mata tai girki.
Jatau dai ya fahinci tana da kaifi irin na uwarta na ya fara shiga da fice yana neman magani ya kafeta a gidan.
Yai nasara cikin kwana biyu aiki ya haukanta sai gata tafara yin komai na gidan tukunyane babba duk ranan girkin mace ita zata tukeshi da tuwo.
Ba wani cima na kwarai a gidan dare da rana tuwone miyan kadi dasafe ma sai mutum ya danyi dabara neman na karyawa don dimamay akeci sai rana za, a girka abinci kowa yaci.
Wani lokaci ma idan yan tsiyan nashi na akai sai dare za, a girka abinda za, aci a gidan irin dai mugun rayuwan mutanen kauye.
Cikin dan kankanin lokaci tafara fita hayacinta ta ramay tayi baki sosai da ita ga matan gidan da ita babu dadin zama ko kadan.
Komai sai su ware ta ai mata wullakanci ba matan ba ba yaran su ba gashi ita ba sana, a sai zaman baza ga Jatau bai kwantuwa ko kadan amma akwai shi da auki kwana da mace kamar ba tsoho ba.
Har gudun ranan girkinta yazo rakeyi don bakin kwazaba irin nashi bai da sauki gurin yin harka da mace gashi gidan shi mata basu fita kasafai sai tsawon wani lokaci.
Abindai babu dadi gashi sam yanzu bata son abinda zai fitar da ita gidan duk da bakin wahalan da take sha aikin gida kamar zai kasheta.
Sai Rukaiyyane kan da tafi gurinta wani lokaci ta dan taimaka mata da abinda ke hannun ta don ta samu na tabawa don mijin baya kwantuwa.
Idan ta koshi sosai sai ranan girkinta amma idan kishiyoyinta suka tuka dan kadan ake zuba mata a kwano ace abincine bai kaiba kowa haka yasamu.
Ranan da abin ya isheta ta dauki abincin ta nufi gurin wace ta raba ta gwanmace ko kashe ta zasuyi yau sai tai magana kan hakan.
Tana zuwa tace maman Abu wanan abincin da aka zuba min aiko loma uku bazai kai ba dubifa yawan shi ki gani.
Matar ta dago kai ra kalleta sama da kasa tace tunda uwarki ta tuka min ba sai kisa na cika maki kwano ba tunda kinfi kowa agidan ne.
Wani irin takaici ne ya kama lawisa jin harda zagin uwarta daga magana kan abinci iya hakkuri dai tayi shi a gidan nan duk irin cin fuskan da ake mata tana daurewa don magani na aiki a kanta lokacin.
Cikin zafin zuciya tace wallahi ba dai uwata ba sai dai na wanda ya zaga cikin mamaki matar ra wawuro ido waje tana kallon Lawisa da mamaki.
Tace lalai ma yarinya baki san wuta ba sai kin taka kina nufin uwata ke nan komay ?
Tace ni dai wanda ya zageni dashi nake ai tana yowa kan Lawisa ita kuma tasa kafa tai shuri da abincin da miyan da matar ta cika kwanon ta dashi nata dana diyan ta abincin ya zube a kasa .
Haushi yakama matar cikin wata bakar zuciya jikake kiff takaiwa lawisa duka da karfi Allah.
Tabita ta hada ta tukwanen dake gurin da kyat Lawisa ta iya mikewa matar ta kara kai mata duka cikin zafin rai da hasala jin zafin da lawisa tayi yasa itama tai kokarin ramawa ai nan dambe ya kaure masu.
Abinka da sabon jini lawisa tafi hanne karfi sai ga hanne a kasa tabita ta taushe ta akasa .
Kafin mutanen gidan su fito duk sun sha wiyan junan su a gurin yaran Hanne na ganin haka sukayo kan Lawisa suka taya uwar su fada.
Sun dake ta sosai sai da suka barta kwance a kasa suna fadin shegiya gobe ki kara cewa zakiyi fada da uwar mu ki gani.
Da kyat lawisa ta daga daga kwace cikin karfin hali rake cewa wallahi ko gobe aka zuba min abinci kamar nazo bara bazan kyale ba.
To mu zuba dake mugani mara mutunci kawai in ma ba abin baba ba wazai kwashe ki haka ragowan kwararo dake kawai tace oho nadai ji haka ubanku ke zaune dani kuna jin haushi na.
Dariya da shewa suka saka mata suna fadin andaiji kunya wallahi an kare da auren tsoho.
Haka taja kafata zuwa daki ga yunwa na damunta babu abinda zataci a dakin gashi gurin rashin hakkurinta ta zubar da dan abincin da aka bata.
Showing 75001 words to 78000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26 Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153