Su sancewa baka damu dani ba, dani da babu duk daya muke a gare ka don kawai ran su yai dadi su san ka wulllakan tani.
Yace bar wanan maganan ke bazaki gane bane ko nai maki bayani sai kiga ai da gangan nai maki hakan.
Nai murmushi nace ni yanzu aikai nake saurare naji hukuncin da zaka yanke wanda zai kawo fahinta a tsakanin mu kowa ya zauna a matsayin shi.
Yace na fahince ki na kuma gane komai yanzu da kike nufi da fatan zaku kara hakkuri da junan ku nace ita Zulfa sai zuwa yaushe ne zata dawo nan garin.
Yace sai na shirya nace amma daddy baka ganin ana shiga hakkin ta da yawa duk yaran mu suna nan suna samun ingantaccen karatu ita ko tana can an barsu da nata yaran.
Ji nayi ya numfasa yace zan shiryawa dawowan nata nan da yan kwanaki kadan insha Allahu zata dawo amma kin san dole a kwai tsarin daki da zamuyi don nan din dakuna shidda ne kawai a gidan ke kina da biyu hindatu biyu sai nawa dana su Nasirda suke a ciki.
Nace hakane yace amma ba matsala ita Ihisan sai ta dawo dakin da yaran ki ke ciki su zauna tare ko ta koma dakin uwarta da zama sai ta zauna a dayan har mu samu daki araina nace anzo wurin.
Nan inda mukayi a nan muka bar zancen sai ko ga Zulfa a cikin bazata tazo ni dai na dawo aikin dare na samay ta a gidan.
Har dakin da take na shiga nai mata sannu da zuwa na dawo dakina ina cire lab coth dina sai gata a dakin nawa tashigo.
Nace a, baku hutaba kun taso tace ina naga hutawa Rahama matar gida tace bani zama a kusa da ita nai murmushi nace haba dai hakan ko zai yuyu.
Yanzu bari nazo nace da Aisha dake ciro min kaya a wardrobe Aisha yanzun keda su Amira ku koma dakin can na yar aikin maman Ihisan sai ku gyara wa anty wanan da kuke a cikin sa.
Nagama magana sai ga daddy ya dawo daga gun aikin shi yana tambaya suna ina nace magani yaki nema ke nan.
Sun gaisa da ita yake cewa kin kai kaya ki dakin ko tace mai dakin tace bata san da wanan zancen ba a falo ma ta barni zaune tun dazun yanzu da zanyi sallah kagin Rahama ta dawo ne yar aikita tace na shiga nan nayi.
Ya juta zai fita nace dashi da har nace su Aisha su gyara mata wanan da suke a ciki ai su sai su zauna ina ya tambaya cikin fada da dan harara nace su zauna da ihisan din a can .
Yace ba haka na tsara ba babu kuma wanda zai canza min tsari na kan hakan yaran ki su zauna nan kusa dake kina ganin su yafi.
Nan dai suka fice a tare ya ga su Aisha sun fara fitar da kaya su yace su maidashi ciki kawai a wancan zata zauna.
Shi da kan shi ya shiga dakin ya samu mai aikita a ciki yace mata ke koma gun uwar dakin ko ta mai dake dakunan dake baya nan matana zata zauna ta mike tana cewa tau Alhaji.
Ta shiga gun Hindatu ta fada mata sai go gata tafito da saurin ta tana fadin banga wanda zai min wanan ba ni da wurina ace za, a ai min kutse yace gidan ki ko gidana ?
Tace gidan kane amma may zai hana ka kaita can inda Rahama ta zauna do sun fi kusa ai da ita yanzu nagani.
Yace bake zaki tsara min yadda za yi da gidana ba ya juya gun Zulfa ce ga dakin ki nan zaki zauna gobe a shirya yaran su fara shiga school da yan uwan su.
Daga haka ya wuce ance ga kofa aiko ta shiga bakin ta inda take shiga ba nan take fita ba zagi gori ba wanda mu ukun bamu sha ba a ranan gun ta.
Nan dai dole aka dawo da tsari sai dai abinda ke daure min kai shine duk wani abinda ke gudana gidan yana kunnen Raliya tasan komai kamar tana zaune a gidan.
Sai kuma nazo na fahinci cewa yanzu idan zatazo garin sai ranan da zanyi girki tayi na farko na kyale ta sai gashi tayi na biyu again shine na nuna ban yarda bada hakan.
Don ta shigo garin kamar yadda ta saba sai gashi ya dawo ya samay ni a kitchen muna hada abincin dare ya dan tsaya a wurin yaran can ya wuce dakin shi sai ya aiko z kirani naje na samay shi yayi wanka ya sauya kayan jikin shi ko.
Ina karasowa yake cewa har kun gama ne nace da dan saura ya juyo da kyau ya fuskance ni nasan yana da magana sai na fuskance shi nima.
Yace tau gashi kuma yau Raliya tazo garin kuma kinga dole a can zan kwana gunta ke nan tunda tazo ba nan ba.
Nace ok ta shigo ashe yace eh wallahi nima nafito meeting ne na samu called din ta take fada min wai ta shigo.
Nace to sannun ta da zuwa yanzu akwai magana ne yace eh nace abinci kada ksa dani a can zan kwana .
Ba dai yau ba ko don yanzu after six ra shigo sannan kuma ai ba gaskiya bane tace sai ranan girkina zata dinga shigowa garin nan wancan karon tai min haka na kyale ta to wanan karon ban yarda ba kuma idan kaje ba yafe maku zanyi ba ta bari idan na gama wunina sai ta dauka kaga girkin sai yazo muna daidai ke nan tana fira zulfa ta dauka kuma.
Tsaye yayi tana ksllona tare da sauraren magana ina ganin kamar zaiyi magana na juya na fice daga dakin ban tsaya sauraren shi ba.
Na koma naci gaba da aikina a kitchen can naji fitan shi yara na mashi sai ya dawo ya fice daga gidan.
Sai bayan na gama ne na koma daki don har na gama raina yana a bace ina jiran inga gobe in an matakin dauka a gare su.
Muna daki hayya hayya da yaran sai ga Nasir ya shigo bayan ishai yana fadin Mummy dadi yana kira a falo nace daddy fa yaron yace eh.
Na mike na nufi falon yana zaune fuskan shi babu alaman annuri a cikin sa nai mai sannu da dawowa yake cewa banga abinci bane nace ya kiraki nace na zata ba nan din zakaci bane ai.
Yace don Allah dauko muna abinci muci kafin yaran nan suyi barci don tun dawowan mu tare yake zama da yaran shi maza suci abinci tare da shi sai idan baya garin ne.
Na juyo naje na hado mai abinci na kawo masu suka zauna sukaci na shige ciki abina na barshi nan tare dasu suna ci ana hira.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , ,

91

Muna barci da safe dashi a daki wayan shi yai kara ya mika hannu ya dauki wayan yana dauka daga inda nake kwance ina jin muryan ta.
Fada take sosai dashi wai har ita zaiwa wullakanci don ya raina mata wayo saboda ya gyara wa matan shi rai.
Akan wanan shegiyar mai kama da kwara zaka wullakantani ka barni kaje gunta don ta fini ko may ?
Yace ashe kin san inda nake ke nan dama kika zo don ita ma ki wullakan ta tako ?
Sai ta kashe wayan yaja tsuki daga inda nake kwance na gyara kwanciya na tare da dauka hannu na kai saman jikin shi na dan rungumoshi kadan sai ya sauke ajiyan zuciya.
Yace ashe ba barci kike yi ba ke nan nace kun dai tayar dani da wayan ku yanzu yace baku barin fitina ku ai.
Ban san wai may ke kawo wanan son rigiman ba haka a tsakankanin ko yaushe kowa da nata kallan son fitinar ga yar uwar zaman ta.
Banyi magana ba sai sauke ajiyan zuciyan da nayi kawai tare da lumshe idanuwa na ko dai ba komai na daukar wa kaina incin wanan son tozarcin da Raliya take son yi min din.
Ban fito ba sai wani lokaci don Aisha da Amira suna gida suna iya taimaka min da komai yadda ya dace.
Koda na fito Aisha ta kamala har ta sallami yara sun tafi school tana wanke kayan miyan da zatai abincin rana dashi.
Sun shigo wurina muna gaisawa dasu ina zaune ina shafa mai muna hiran rigiman yan makaranta haidar da Abdul da dan wurin anty zulfa wai sun gaji basu zuwa school ranan.
Sai ga Zulfa tashigo dakin daidai ina saka kaya a jikina tace kin tashi nace eh ina kwana anty tace Alhamdullahi.
Yau fa mutanen ki an sha rigima dasu a gidan nan wai ba zasu school ba sun gaji da kyat muka samu suka wuce.
Nace yanzu nake tambayan Aisha su take fada min yadda kuka kwasa dasu ai tun ba aje ko ina ba an fara haka kuma ?
Tace ashe kuma mutumiyar ki ta shigo gari ne nace wake nan fa tace Raliya mana tsohuwar banza nima a waje na ganta tazo gun mutumiyar ta suna magana.
Nace ashe har yanzu suna tare ne ke nan haba ina mamaki yadda komai na gidan nan yake a kunnen ta dama.
Matsalar su ne wanan ban dai bin kowa da sheri tace ai sunji kunya dana gansu amma sai nai kamar ma ban gan su ba na wuce abina.
Wai ma kin san wani abune maman haidar don haka take kirana kotace dani maman yara don har yaranta a gun mu suke sakewa su wala in suna gida komai tare muke masu tun zuwan su garin.
Don yanzu gaba daya Zulfa ta sake dani sai dai ni sese da sese nake da ita ban yarda na sake kamar yadda ita ta sake dani ba sosai.
Tace ina mamakin wanan zaman nasu Raliya bata san halin hindatu bane tukun aini na dade da dawowa rakiyar karya da zalunci tun tuni shiyasa take jin haushina kamar ta shake ni take ji.
Nace anty ba ke kadaiba ai ita kowa haka take dashi in ba yarta ba a gidan nan shiyasa ban yarda taiwa yara na horon da bataiwa yarta.
Tace in anyi magana tace wai ita kadai ke gare ta ai dole ta so ta tunda ita take gani.
Nace muma din da muke ganin wasu ai babu wanda bamu so a cikin su balle tace haka tace aike sha kundum din ta .
Don lokacin da nazo baya ta gama haukan ta don zuwa na ta mayar dani wawiya wai shine ranan kina wurin aiki take son yin gulmanki dani batasan yanzu ba da bane.
Wai yanzu kwana biyu za a ganki da ciki don baki da guri sai ki vika gida da yara kifi kowa samun gado don ko wandin kika shaka sai kinyi ciki ke kamar kinfi kowa iya kwana da miji ne.
Dariya nayi nace ita gado ya dama ko ita da zata samu haihuwan irin haka ai yi zatayi har tafi kowa tace balle maganan ta daya biyu zancen gado ne ita.
Nace ita ya dama wanan sai ta kasheshi ta kwashi gadon ai tunda shine burin ta ko yaushe.
Tace waya san gawan fari tsakanin mi da mai dukiyan wanan Allah kadai ya sani yau ina Saade ta huta da wanan rigima nan mu kullun da baida ranan karewa.
Take naji wani daci a raina nace Allah sarki anty ita dai ta dabance wallahi duk irin abubuwan nan bai damay ta ba dama a rayuwan ta barta dai da son diyan ta shine nata.
Tace ai basu da kaico sai dai ace uwa uwace kawai don may suka rasa wanda baki masu yanzu wa zai iya wanan abinda kike sai an tona a halin yanzu kan.
Murmushi nai mata kawai na kara shirina duk muna hiran take cewa ita wanan mara tunane da akai mata shigo shigo ba zurfi ai sata ta dafa mata a bayan ki data zauna gunta.
Da sauri na juyo nace wa Amira tace ita mana cewa tayi idan tazo da kudi wai Amira tana diba kuma in tayi miya sai Amira ta kwashe nama ta cinye.
Nace Allah sarki ba dai Amira bz kan da dai ta tsaya ga cewa tana sa rashin kunya da zan yarda amma ba sata ba kan.
Tace aiko sun hadu da uban don ya haukace mata sosai a lokacin ya kwashi yar shi ya mayarwa Hajiyan shi itama hajiyan tai masifa sosai a lokacin .
Nace niko banji wanan labarin ba tace ina zakiji kuna can waje lokacin ke sheri iri iri fa ta lakawa yarinyar harda cewa tayi tana kawo maza a gida idan ta fita.
Nai salati nace ashe abin wanan matar na gaske ne ita bata san daddy akan dan shi baida wasa ba da kowa tace aiko sun hadu dashi don da kyat ta samu ya sauko suka shirya dashi.
Ai lokacin ne ta dawo nan dakin marigayiya da zama don yace bai yarda da zaman ta inda take ba don maza na shiga gunta.
Nace matsalar su ce don bai shafe mu ba wa yan nan idan ka biyewa halinsu sai ka zauna kullun baka da aiki sai cin naman su kana rage masu nauyi.
Shiyasa kikaga banda lokacin irin wanan suraitan a rayuwa na aikin gaba na ya damay ni na fadi hakane don ta bar zancen don naga bata da niyar barin maganan su.
Har na shirya muka fito tare da ita falo inda na fara taya Aisha aiki da na sama tanayi ban dauki lokaci ba na dawo muka zauna sai suma yaran sukazo suka zauna inda muke.
Amirace take muna hiran film din data kalla muna ta dariya saiga daddy ya fito cikin shirin shi zama yayi ya karya yana yi yana sauraren hiran mu da mukeyi ana dariya.
Mamaki yaji sosai a ranshi yau a gidan shine aka zauna haka ana hira harda dariya ba wani fiti a tsakani.
Yadaga ido daga inda yake yakai idon shi ga dakin Hindatu dakin ya na a rufe kamar bata cikin gidan.
Sai da ya gama ya mike yana goge bakin shi da tissue yake zo inda muke yana cewa ita waban bata ciki ne ko tafita ne ?
Sai mukai shiru ba wanda yai magana daga cikin mu sai ya sake maimata tambayan nashi da cewa hindatu ta fita ne ko may ?
Sai zulfa tace dashi ina ga tana daga ciki don banji motsin fitan ta ba dakin nata ya nufa ya tura ya shiga tana daga kwance a saman gadon ta.
Ta dan dago kai taga mai shigowa dakin sai ta mayar da kanta a saman filon da take kwance ya karoso yana fadin lafiya ke kika dawo daki kika kwanta yan uwan ki na falo suna hira ?
Gyara kwanciyar ta tayi tana fadin tau wani sabon magana ke nan kuma wani hira yanzu aka dauko yi a gidan banda labari ni ?
Yace wai ke may yasa baki son zaman lafiya kin fi bukatan ko dayau ai fitina dake ne wai daga tambaya zaki jero min wasu maganganu can ?
Banga zan iya hiran kulla makirci ba ne shiyasa na dawo daki don nasan ko ina ba a kai indon wanan hadin kan ne da naga anayi a gidan nan.
Wsnan ke kika sani don ke ko yaushe baki kaunan zaman salama sai na tashin hankali da anyi ance kawai in bashi ba kowa na waje ke kin dawo nan ki ware kan ki ke kadai kin fita sun kore ki ne ?
Ta dab dago a nakashe tace kora fa acikin su kaga wacce nake shayi ne ban dai iyawa ne don ban iya makirci ba ni.
Murmushi yayi don jin may tace ya juya zai fita sai tace kirikiri Raliya tazo garin nan akai mata wullakanci ta koma don wata.
Yace wullakanci?
Wa yai mata wullakanci din ?
Tace kaida matar ka yar so mana yace ban san da maganan ba sai yanzu a bakin ki naji dai.
Tace amma ai kasan tazo garin nan ka barta ka dawo gun matarka ka kwana don kada ran ta ya baci ko ?
Yace oho ashe tazo ne dama ita don ta bata mata rai ita ma ban sani ba sai ki bari ranan girkin ki zance ta dawo daidai lokacin da take zuwa sai ke da ba a so ki barmata naki girki ko ?
Tace da sauri ban gane na barmata ba akan may zan bar mata fina tayi ko may ?
Yace oho ashe ita tafi tane da zata bar mata girkin nata ko yaushe taga dama tazo garin.
Sai dai ita ba, amma ni kan ko tasha giyan wake ne ai bata min haka ban din bata ga wuri ba kai ya girgiza ga shi dai a sannu abubuwa suna baiyyana mashi yana gani da idon shi.
Wanda a baya baidamu da ya bincika ko ya luraba yasan may yin hakan da takeyi yake nufi shi kawai mata tazo gari dole a wurin ta zai kwana ke nan bai damu da ya hankalta da hakkin wata yake dannewa ba a ranan .
Showing 372001 words to 375000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125 Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153