nata.
Sai ga yarinyar ta shigo da wani matsatsen wando duk surar jikin ta a waje ina kallon daddy ya kawar da kan shi data shigo falon.
Kudi ya mikawa kowar mu yace mu aikawa iyayyen mu dashi su sai abin sallah nace mun gode Allah ya kara budi ta hanyan alheri sai kowa ya shiga godiya.
Ban son dogon zama irin haka don ba a watsewa lafiya karshe ina ganin ya gama na mike na barsu nan na shige abina.
Ina shiga Amira tace humm umm mummy kinga wani wando da yarinyar shiyan nan ta saka tashigo falon ga daddy a zaune kanta ko dan kwali babu.
Nace nata kallar wayewan ke na Amira fitar da tsiraici in kinga haka ba a kwabe su da yin hakan bane tun farko.
Tace to ai mummy indai wando mu ba a gwada muna wanduna a gidan nan nace iyakar ku kuwa shiyan nan ba dashi.
Tai dariya tace kai mummy ai na sani ni mamakin yadda ta shiga falo hakana ga daddy zaune nake ji ai.
Ashe bayan fitana da zadu watse sai yace ta tsaya maganan wanan shigar na diyar ta yai mata .
Sai tace to may ye kuma a cikin hakan naga a gida suke zaune ba fita tayi haka ba waje dashi nifa yara na sun saba da free life ban faye son takurawa yaro ba a rayuwana.
Yace to nan gida nane idan baki son nina takura masu wallahi ki tsawata masu ga abinda sukaga yan uwan su ba suyi min.
Don ba zan yarda a kawo min gurbataccen akida ba a gidana ina zaune lafiya da yara na tace dashi wani sabon fitina dai kake so dani kawai.
Naga dai da yardan ka nazo da yaran nan don tun farko sai dana fada ma ba zan barsu a kano ba na dawo nan na zauna fakon diyan wasu nawa na can zube.
Gwamma duk abinda sukeyi suna gabana yafi min sauki kace ka yarda nazo dadu da aina kowa ne shine yanzu zaka zo min da magana don yarinya tasa wando kawai.
Yace ok so kike ajimu kan yaran nan ke nan tunda har na fada maki ban son hakana ke wata irin uwa ce da batasan abinda ya dace ba da yaran nan.
Haka ahi wanan yaron nagan shi a kofan gidan makwabta ni bani son iyalina suna jaye jaye ina zaune kalau cikin rufin asirina.
Tace kuma dai shima najin ke nan sai nayi ta kullen shi a gida tana koyon akidar mata ba fita ko may don ka gan shi kofan wani gida gidan ya shiga ne ?
Shiru yayi don kada zancen yai masu nisa don ya fahinci akan yaran ta zasu fara samun matsala da kowa a gidan.
Zulfa ta samay ni muna hira da Amira ina zaune ina mata kalaba a kanta take cewa dani wai Rahama baki fahinci matar nan bako ?
Nace wake nan anty tace Raliya mana tsohuwar banza nace kuma dai amma azuciyana cewa nayi ai tafi nan ma.
Tace ita fa by all means ta zama uwar gida tana leading din mu take so wai ita a dole tafimu shekaru take nufi ai tasan yara ne mu ta aure shi ta zauna da mu.
Nace anty nifa kwata kwata bata gabana wallahi don ni halinta bai min ba bamu zuwa daidai in ba don daddy na yawan taka mata burki ba da kullun sai anji bakin mu da ita a gidan nan.
To ya riga yace bai son fitina kinga shiyasa ni ba ruwana da tsabganta daga ita ko har yaran ta ma basu gabana.
Tace yau ai naga fitsara kinga yadda yarinyar ta shigo muna haka kerere da ita da wani matsatsen wando can abu ko gaba babu ciki.
Dariya maganan ta ya bani sai kuma tace ke ko fa uwar haka take a bushe wallahi ko nono bata dashi sai bussashen kirji haka ta tashi ina kiranta da yar kadangaruwa.
Dariya muka kwashe da shi gaba dayan mu falon tace bakiga munafukar nata ba yanzu ta fara dawowa rakiyan ta taga babu ci ga harkan.
Da ta dauka karyan arzikin da ake mata ko gaskiya ne shine ta wani shishige mata don ta dauka zata zo da wani kadarine a gidan tafi kowa.
Sai gashi taga a binda ba ta zata ba a wurinta mai shine zai tsaya fadan kayan masarufi a gaban kowa haka ?
Su dai suka sani kan su ake ji ai dama irin haka ga haka ake karewa wanda ka shigo kuna shiri da shi dashi za, a fara jin kan ku a gidan.
Gara ma ka zauna da kowa da zuciya daya idan kishin yazo ayi shi in angama akoma daidai yafi don shi kishi dole mace tayi shi ko wacece kuwa.
********* ********* *********
Wani wayewa jinkai duk Raliya tazo muna dashi amma sai taga ashe kowan mu da take gani da nashi iyawan a gidan.
Haka mukai azumin mu mukan fita zuwa sauraren tafsir ni da yara da anty Zulfa da bata bin mu amma daga baya ta tsiri bin mu muna zuwa tare.
Idan kuma ina da aiki ita ke zuwa da yaran su sauraro su dawo ranan mun tafi tare da zamu dawo muka tsaya mukai sayayya a wani shago na kayan kwallaman yara don daddy yai tafiya a lokacin mu kadai ne a gida yasu yasun mu.
Tun a bakin get muke jiyo hayaniyar su anty tace ba lafiya dajin wanan fitinan mun fiti muka karasa shiga muke jin harsunan su yana tashi sosai.
Naso na wuce amma sai naga ihisan a waje zaune tace mummy ku shiga kuyi masu magana ko zasu daina don Allah.
Yarinyar ta ban tausayi muna shiga naga daga uwar har yaran suna zagin hindatu itama tana mayarwa.
Nace subbahanallahi may ya kawo haka kukuma waya saka bakin ku ga maganan su na manya.
Sai wanan fitsararar mimin tace wallahi duk wanda yace zai zagi uwar mu a gidan nan bamu kyale shi.
Ku bar ganin don munzo kuce wai zaku wullakanta muna uwa muna kallon ku tun dai ke wai ke a dole ga star a gidan ko ke kikai mata bazan kyale ki ba.
Nace wa kike nufi ni ko wa tace ke Rahama dake nake nace tarkasa nifa kikace tace kwarai kuwa take na tuna da kauye ai batai aune ba tako biyu nayi sai gani a gaban ta ji kake kayau kayau nai mata mari biyu masu kyau a fuskan ta.
Sai data duka don wahalan da tasha ta dago idon da ya cika da hawaye tace kika mare ni wallahi sai na kashe ki yau a gidan nan.
Nace bissimillah gani gaki yarinya karyan iskanci kikeyi baki san Rahama kuwa sai kin shiga track dina zaki raina kan ki.
Daga magana zakiyi min rashin kunya zagina na ta fara ta uwa ta uba sai babban nasu tace dani don Allah anty kiyi hakkuri ke Mimi wai baki kyalewa ne hakana.
Nace idan bata kyalewa barta ai nine maganin ta nace ke har kin isa ki zageni ai ban san an kawo muna kushiyoyi ba a gidan sai yau da kika fada.
Uwar tace don Allah don annabi doctor kiyi hakkuri sai ko ga yarana sun shigo part din Aisha tace ke wallahi ku kama kan ku ko yanzu jikin yarinya yai tsami in kina iskancin ki ki san inda zakiyi shi.
Nace Aisha maza ku bar nan ku koma inda kuka fito maza ku koma ciki ba bata lokaci yaran suka juya suna fadin wallahi da yau anyi karamin yaki a gidan nan kuwa.
Hindatu tace kun gani kunga inda akasan darajan babba magana daya tai masu sunjuya amma ku da baku san komai ba sai fitsara don wullakanci.
Raliya sai faman hakkuri take bani tana kuma zagin yarinyar haka yasa na juya na wuce banyi magana ba.
Bayan an sha ruwa muna zaune falon mu sai gata tare da yarinyar sun shigo muka gaisa take cewa dani doctor na zo da mimi ne ta baki hakkuri don Allah tayi kuskure na saka bakinta ga harkan mu harta fada maki bakaken magan ganu irin haka na.
Zulfa tace wuribta samu ai yanzu tasan kwaruru ba tsaran wake bane in ba rashin kunya ba ta yaya zaka bude baki ka zagi babba wanda ba sa,an yin ka ba.
Uwar ta bani tausayi kuma dai ko ba komai ta nuna yadda ya kamata tace ban san may yakai yaran nan ga maganan mu ba.
Shara dai ne da kazanta ba dama a gyara wuri an bata shine nai magana ya zama muna na rigima yanzu in deen yaji wanan magana aini tawa ta samay ni daga ni har su a gidan nan.
Sai naji ta bani tausayi sosai nace bama zai ji ba ai tunda anyi ya wuce ta dai bar fadawa babba maganan da yai mata dadi tunda ba haka taga anayi ba a gidan.
Tace ai gata bayan marin da kikai mata sai dana kara mata wani don banga abinda ya kaita sa baki ba ga maganan manya ?
Na juya wurin ta nace da yarinyar wa sunan ki tace dani cikin fushi don har lokacin ranta yana a bace da Fatima .
Nace suna mai kyau haka ai sunan ki nada kyau ki daina haka kin ji ba a son mace tana dabian rashin kunya don wata rana aure zakiyi ke ma kuma ki zama uwa idan an maki haka yaya zakiji.
Ki daina kinji banji dadin yadda kikayi ba shiyasa har na taba lafiyan jikin ki batare da nai niyyan yin hakan ba .
Uwar tace wallahi ni kin min daidai haka nake so mutum ya nuna maka gaskiya komai dacin ta idan tazo ba wai yai ma aikin fanin ido ba.
Yaro na kowa ne ai idan ka yi alheri wa dan wani wata rana kaima baka san wanda zaiwa naka ba haka duniya ya gada dama.
Tace don Allah dai doctor kiyi hakkuri da abinda yarinyar nan tai maki insha Allahu ha zata sake ba da yardan Allah.
Don nasan idan maigidan yaji abinda ya faru ba karamin fitina zamu kwasa ba dashi akan hakan.
Murmushi nayi nace indai don wanan ne kada kiji komai ba zai taba jin wanan maganan ba don zanyi warning din duk wani wanda nasan zai iya fada mai zancen.
Godiya ta fara yi min duk tausayin ta ya kamani uwa ke nan ance da kuka mai jawa uwar shi jifa, yau shi nake gani diyan ta sun ja mata zubar da aji tana bi tana rokon ai masu hakkuri don Allah sherin shedan ne ba komai ba .
Na yiwa kowa kashedi ajan maganan sun ja bakin su sunyi shiru sai wani laddabib ya shigo tsakani na dasu da kowa a gidan.
Har daddy ya dawo ba wanda yai mai hiran sabanin da aja samu sai ma zirga zirgan hidimar sallah da ake ra kokarin yi don mu a zaton mu a nan zamuyi sallah sai gashi a cikin dan iankanin lokaci yace ina sam ai gida zamu koma muyi sallah can din.
Gashi sallah da kwana biyu ina da wanin aikin da zan yiwa wata mace mai lalarurar matsalan ciwon ciki dake yawan samun ta.
Duk na fada mai amma yace ina shi wanan bai shafe shi ba idan baije gida yai sallah da iyayyen shi ba su wa nake son su kula mai da yan tsofin shi a can.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,
94
Daddy yaso muyi tafiyan a tare dashi sai dai hakan baiyi ba don ni tare da yara na mukai shirya tafiyan da motana inda sani ne zai jamu har zuwa can.
Bayan mun fito ne sai anty tace mu zata bi don ba zaitai tafiyan da za ai fitina akan shi ba.
Don haka da ita muka tafi mota uku mukai tafiyan dashi don itama Raliya motar ta yaranta suka shiga.
Mun isa lafiya zuwa la,asar kowa ta shiga part dinta tana gyara don kuran da yayi saboda rashin mu a gidan.
Gajiye ne da mijin ta zaune a gidan tashigo ta taya mu gyara da girka muna abinda zamuci idan ansha ruwa don tun muna hanya nai mata waya.
Kafin magariba mun gyara ko ina sai shirin shan ruwa da mukeyi ina dakina zaune ina lazumi sai ga Amira ta shigo take cewa dani.
Suna son su ci abinci nace kira min Aisha kuzo tare sai gasu nace idan abincin yana da yawa ku diba kubawa sauran mutanen gida.
Suka fita kamar yadda nace hakan sukayi sun kaiwa kowa abincin don tayi muna shi a wadace kamar yadda nace tayi din.
Sauran sun karba amma sai Raliya tace adawo min dashi suma sun girka nasu ai ban dauki hakan komai ba a raina.
Tunda safe helen ta tashi ta gyara muna ko ina na part din har zuwa corridors din daya raba nawa da na Anty na na da tai mopping din wurin yadda ya dace.
Ban fito ba sai sha daya a falona na samu Sani da ya kawo mu zaune da yara suna kallo.
Baysn mun gaisa ne nake tambayan shi zancen tafiyan shi yace dani ai anan zaiyi sallah tare da mu don idan ya koma in mun tashi tafiya kuma fa ?
Nace aiko mun gode da hakan don ni ina ga kwana uku zanyi dama mu koma don ina da aiki dana koma da zanyi.
Zama nayi inda yaran suka fara baibaye ni kowa da korafin shi nace ina Nasir ya shiga Amira tace ta nagani yana daki a kwance bai tashi ba.
Nace Jinior duba min shi ka gani idan yana ciki sai yace naga sun fita saman mashin da wanan yaton matar can .
Gabana yai mugun faduwa sosai don sam bana son halakarshi da wannan yaron ko kadan don yaron bai min ba gaskiya.
Ba wai naki yaron bane don yana dan kishiyana a, a don dai tarbiyan shi ne bana son kasancewar su a tare don kada na saka ido yazo ya ture min ginan da nai shekaru ina azawa akan yaran.
Ina zaune a falon basu dawo ba sai zuwa karafe sha biyu da wani abu yaron shigo gidan.
Yashigo yana wani rangajin gajiya don azumi ya kamoshi sosai a lokacin.
Yana zama ina fadin Nasir ina kafito ya dan bata rai yace mummy mun shiga gari ne nace kai dawa ?
Sai ya dago ido ya kalleni yace dani da Awal muka fita nace dashi waye hakana kuma ?
Yaushe ka samu aboki Awal ban sani ba kuma sai yai dariya yace ba wani bane sai yaron amaryan daddy din nan.
Nasir kafita da wanan yaton mara tarbiya yaushe ka fara yawo ban sani ba har ka fara hurda da wanda baka sani ba ?
Ssi yai shiru fada sosai nai mashi har Sani dake zaune ya saka bakin shi yace gaskiya nima yaron haka nake ganin shi kamar baida kwabo wallahi don bai ganin kowa da daraja ko kadan.
Mun dai mai fada yana wani kumbure kumbure shiya tayar min da hankali don ba halin shi bane yin hakan idan an mai fada.
Bayan la asar sai ga yaron har part din mu yazo wai Nasir yazo su fita sai Nasir din yace ka tafi kawai ba zan tafi ba.
Ina jin shi yana lalashin shi da su fita din amma Nasir din yace ba zai tafi ba ya juya yafice nace kagani ko har ka fara jawo muna shi yana shigo muna nan.
Yace cikin wani murya mummy nifa bani na kirashi nan din ba fa nace Nasir ni kakewa magana haka ?
Daga haka ban kara magana ba nai shiru na kyale shi shima shiru yayi yaci gaba da kallon film din Annabi musa da akeyi a wani tasha.
Ban kula shi ba har wani lokaci na fita batun shi shima yana ta cika yana batsewa Haidar na zuwa kusa dashi ya buge yaron .
Hakkuri nabawa yaron najashi a jikina sai dai a raina nasan sabon aiki ya samay ni ke nan kuma kan yaron.
Yaushe ne har suka fara wanan halakan da yaron nan ban sani ba ni kuma kowa bai fada min ba sai yau da na gani da idona.
Daddy ya shigo part din namu ya samu haidar yana kuka yake tambayan may ya samay shine wai yake kuka ?
Nasir ne ya dake shi don kawai an mai fada ya fita yawo da wanan yaron Awal shine yake fushi daga yaron yaje gun shi ya dake shi.
Haba Nasir may yai maka kuma ka dake shi kai ina kaje ne har akai ma fada yace daddy kawai mun fitane akan babur din shi muka zagaya gari da abokan shi.
To mummy ka tace bata son yawo idan zaka fita ka dinga fada mata zaka fita ina ganin shine bata ji ma dadi ba ka fita ba a san inda ka tafi ba.
Nace daddy ni dai yawon shi da yaron ne bai mun ba kawai bana son yana yawo da yaron da bamu san halin shi ba daga sama.
May ya faru da yaron da baki son hurdan su ba maza bane namiji sai
Showing 384001 words to 387000 words out of 456145 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129 Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153