cin fuskan ba haka da anty ke min.
Daddy ya shigo gaida mama ya samu mama na fada da anty din, yake cewa mama gaya mata dai na rasa inda halin Saade ya boye har ta amince wanan yarinyar ta kai ta ga wanan zubar da mutunci.
Da sauri anty ta dakatar dashi tace kaga idan zakai maganan ka kayi amma ka daina sako Falmata a zancen ka kadai hanata shigo maka gida kan matarka ko kuma ta bari ba sai ka barta hakana ba.
Nan suka fara sa insa a gaban mama din dashi hankalin mama yai matukar tashi tana jin yadda anty ke mugun aiban ta ni abin ba dadi ko kadan.
Da kyat anty ta samu ta sashi ya fita tun fitan shi bara sake magana da anty ba ta mike zuwa dakin da take sauka a ciki.
Ina shiga daki na kuka na zauna nayi sai da na gaji na share hawaye na ni kadai a dakin don nasan tunda har mama tai magana anty bataji ba abin yayi nisa ke nan.
Tun da safe sai ga mama har part dina inda ta samu na shirya zan fita ina saye da lapcoat a jikina da cup din tea ina dan kurbawa Gajiye da Fatima suna zaune suna kallo don har sun gama duk abinda zasuyi ko.
Muna ganin ta shigo ne duk muka mike muna gaida ita ta zauna sai mukai shiru na dan wani lokaci.
Can ta ambaci sunana tace Rahama abinda nake so dake shine kici gaba da hakkuri don shi ramin karya kurare ne bai dorewa don na fahinci an riga da an zuga Saade don haka ni yanzu sai dai ke da kuke tare a nan na kara baki hakkuri kawai.
Nace mama babu komai dama haka zama ya gada zo mu zauna zo mu saba watarana kai da mai shi.
Tace jiya abinda tayi a gaban minin ku banji dadin shi ba ko kadan ni tsorona kada wanan shuumar ta cuta mata ta inda ba a sani ba.
Gashi ta kawo mata wanan munafukar ta zauna da ita a gidgida Allah kadai yasan irin abinda suke gunguma mata a tsakanin su.
Gajiye tace nima abinda nake tsoro ke nan wallahi amma ita hajiya taki ganewa nace insha Allahu zan saka ido don ni ba zan yarda na biye mata ba haka.
Nan dai mukai sallama da mama din bata kara kwana ba ta bargarin ko anty din ta saduda amma ko a jikin ta don ta shiga tarko ko .

********* ********* *********
Falmata tagama duk shirin da take son yi a kan anty don haka ta shirya fara aiwatar da nufin ta gareta.
Ina dawowa daga school da yamma don yau ban tsaya an karasa dani ba don bana jin dadi tun safe .
A daidai kofan mu naga mai Napep ya sauke yar aikin anty tafito da wani irin katon jarka irin na mangyada ko manja din nan.
Da kyat ta ciciba zuwa cikin gidan ina mamaki ko may ye a cikin jarkan haka ta dauko mai nauyi ta dai shige dashi wurin su kai tsaye.
Ban shiga ba don na rage shiga yanzu sai da dare bayan na gama magariba kafin ishai na dan lekata don jikina ya dan sake min lokacin.
Ina shiga na samu matar ta tsiya wanan abinda ta shigo gidan dashi da yamma ta mikawa anty shi.
Ta amsa zata fara sha na shigo falon nakai kallo na ga abin bakikirin da shi haka ta kurba tana bata fuska na gaida ita naga bata ji dadin shigowa na ba na gan ta a hakan.
Ni dai na gaida ita na juya abina ina mamaki ko may ye wanan abin da anty ke kinkima ma cikin ta oho ?
Muna samun hutu daddy yai tafiya dani sai da mukai wata daya da sati biyu muka dawo nayi kyau sosai gashi da mun dawo bukin Gajiye da Fatima za, ayi shi.
A lokaci duk wanda yasan ciki zai gane ina dauke da ciki a jikina sai dai su matan gidan gaba daya idon su ya rufe basu gane ba.
Sai ranan da mama Laraba ta shigo ta zo akan maganan auren son shi ya kirata tazo maigidan don bai abu har yanzu bada ita ba.
A falin na samay su zaune suna hira na shigo gaida ita tana ganina tace a, a ikon Allah abu ko yayi kyau sosai wallahi ashe na dade rabon da na ganki sarakuwa na ashe abin arziki ya samu haka har ya nuna ban sani ba ?
Da sauri gaba dayan su suka mayar da hankalin su a kaina cikine zaune a jikina kuwa dagwas dashi dan wata shidda da kwana ki har ya dan turo dayake na farko ne a gare ni baiyi wani girma ba sosai.
Gaba daya falon yai shiru na durkusa har kasa ina gaida mama tace a, a haba tashi tashi kina wanan matsayin inake ina durkusa kada ki haiho min da igiya a wuya.
Daddy yai murmushi yace fada mata dai mama don Rama bata jin magana wallahi haka nake fama da ita kan kula da kan ta.
Nai dan murmushi na dago na dan sakar mai harara irin na masoya nace kai daddy duk wanan kokarin da nake kuma sai an kai kara na gun mama kuma ?
Yace wani kokari kin dai ji abinda mama tace don Allah ki kula Rahama ni ina maganin hutu zan daukar maki ki daina shiga asibiti har ki haihu.
Humm, umm inji Hindatu lalai abu yazo ga masuyi ke nan shi cikin ma har wani abin ado ne dashi kuma ashe.
Zulfa tace ai ba ayi ba yanzu za, ayi ashe mugani ashe an samu karuwa ake faman boyon shi gare mu to Allah ya ingata.
Amin inji daddy da mama ni dai kaina yana kasa Anty na daki a nade don jikin ta ya dawo ba dadi yanzu amma haka take nukurkusa dashi.
Daga bakin yar aikin ta da sukai gulma da hanne ta samu labarin cikin jikina sai ga mama kuma da zata tafi ta shigo tana mata murna ashe an samu alheri ne Allah ya raba mu lafiya.
Amin kawai tace wa mama din don jin maganan take kamar zata shude a lokacin ranta ta rasa may ke mata dadi.
Ranan kan gidan kamar an aiki masu da mugin labari ko wani part zancen cikin suke suna mamakin yadda basu gane ba sai da mama tazo sukaji a bakin ta.
Bukin saura sati uku ayi shi jikin anty ya tsanan ta mata ina shiga gaida ita duk da ba fuska a gareta amma haka nake shiga gaida ita na dan zauna na dan lokaci.
Gashi ina son na taimaka mata amma babu daman yin haka a gare ni ganin bata da lafiya yasa mai aikinta yin abinda taga dama sosai ta fito da kalar ta a fili.
Yaran basu da shakat ko su walla su da gidan uban su yakai har ta fara dukan yaran da sun danyi ba daidai ba.
Haka yasa na rufe ido ranan da na samu ta daki Amira uwar na kwance babu daman magana nan na rufe ido nai mata tas nace idan ba zaki iya hakkuri dasu ba sai ki tafi.
Har nagama na zaci anty zatace don may nai mata haka amma sai banji tace dani komai ba naja yaran nai masu wanka nabasu abinci a part dina sukaci sai barci.
Zakaji tana kiran saliha saliha amma sai ta kyale ta hakana har tagaji ta barta tace bata zuwa ita tagaji wallahi.
Haka muka wuce muka barta a cikin matsala muka nufi kauye wurin buki satin mu daya amma ina buga mata waya akai akai naji lafiyan jikin ta.
Na samu na shawo kan mama Altine taje ta duba anty bata ki ba ta shirya muka zo tare yadda muka barta daga ita har yaran mun samu abin ma karuwa yayi sosai.
Sai da nai kuka yadda na samu yaran sun lalace na samo wata yar aiki diyar lami kawar mama altine da Innata.
Gajiye a cikin gidan zata zauna a boys quarters inda akaba su tace basai na dauko mai aiki ba zata kula dani haka na amma dole na nemo wata da zamu zauna dindindin a part din tare dani.
Mama Altine sai kuka take cikin tashin hankali dole aka je asibiti da ita ba laifi ta dan samu sauki kwana biyu.
Yanzu muna dan samun saukin a zaman mu gashi cikina ya gama fitowa fili sosai kowa kuma yasan da akwai shi.
Bayan kaman sati uku har na walwale ga jigilan bukin da nasha ina barci cikin dare naji ana buga kofan mu sosai da karfi.
Na yunkura na tashi da kyat kaina babu ko dan kwali na fito dasauri muka hade da Aisha da na dauko take cewa anty tun dazun ake buga muna kofa da karfi haka.
Sai da na tambaya da waye naji muryan mama Altine ne na bude da sauri nace mama lafiya dai ko ?
Tace ina fa lafiya Rahama jikin antyn naki ne ya tashi wallahi abin ba dadi ita kuma wanan shedaniyar nayi ta da ita tace wai bazata fito ba dare yayi gashi ni kadai ne a shiyan sai ita.
Da sauri na kwasa sai dakin yadda na samu anty zaka dauka ma ta mutu ne wallahi na fashe da kukan tashin hankali sosai.
Na kamo ta ban ko damu da nauyin da nayi ba na fara bata taimakon gagawa wanda ko asibiti muka tafi shi za, a fara bata a can din.
Allah ya taimake ni ta nisa da karfi na rugomay ta ajikina ina wani irin kuka mai tsuma rai sosai.
Can dabara ya fado min nace mama ta miko min wayan anty dake aje gefe na kira maigidan yana ganin kiran karfe biyu da mintuna ya dauka a cikin tashin hankali nake fada mai halinda take ciki.
Ai ko minti biyu bai dauka ba sai gashi dakin yana ganin ta yace yaushe abin yai tsanani haka mama tace wallahi lafiya muka kwanta da ita don har ta sha magananin ta fa kafin mu kwanta din.
Asibiti aka nufa cikin daren nan dole da ita take aka bata gado naso na bisu amma daddy ya rufe idon shi ya hana ni yaran na tayar muka nufi dakin mu da su hakana.
Na rufe dakin anty na wuce da keys din wuri na ranan dai haka gari ya waye muna tunda safe har na shirya da abin karyawa na nufi asibitin da take.
A cikin tashin hankali muka samay su sai bincike ake a kanta daga karshe zuwa karfe daya likitocin suka gano wani magani take sha yai mata wanan illar haka ajikin ta sosai don har ya fara bata mata kayan cikin ta ko.
Maganin da take sha likitoci ke son suyi bincike akai an kwaso sin duba amma duk basu da wani illa sai abin ya daurewa mutane kai sosai.
Can anata magana mama tace akwai wani wanda naga wanan yar aikin natsiyaya mata safe da yamma koshi za, a duba a gani ne.
Cikin mamaki daddy yace wani irin magani ne wanan nace lalai nima naga tana yawan shan shi don nasha ganin ta dashi da dadewa.
Daddu yace a je a dauko tare muka tafi mun samu Saliha tana kwance ta kure volume din tv tana kallon raye raye.
Cikin fada daddy yace what noses is this a gida na wanan abin ke faruwa haka kuma mai shiya na kwance rai a hannun Allah ke kina nan kina holewar ki.
Part din na shiga dubawa inda Allah ya taimakeni na hango jarkan maganin can an boye shi cikin wani lungu na tsiyaya a wani gora Saliha na kallo na zamu fita take cewa dani Rahama bani key din dakin hajiya zan gyara ne.
Nace abar gyaran sai ta dawo ayi amma ba yanzu ba kan muka fice daga gidan da maganin muna hanya daddy sai kallon maganin yake yana mamaki shi.
Yace yaya ma za, ayi mutum mai hankali ya dirkawa cikin shi wanan mugun abin haka ne wai ?
Nace ni kwata kwata ban yarda da wanan maganin ba ma daddy wallahi amma dai bari a bincika a gani kawai.
Sun shiga dashi a cikin dakin bincike mun kuma samu taji dama numfashin ta ya dawo normal yanzu ko.
Nan dai muka zauna likitoci na shigowa duba ta akai akai bayan fitan babban likita ne nace mama kinji waban matar wai na bata dan makulin dakin anty zatai gyara a ciki .
Mama tace injin baki bata ba dai nace gasu a jakkana ai nifa mama ban yarda da mutanen na ba don zasu iya cuta mata gaskiya tace Allah dai ya kyauta ke dai Rahama.
Doctors suka taru inda suka kira maigidan tare ya shiga dani mun samay su a zaune bayan gaisawa ne suke tambayan wanan maganin da aka kawo daga ina aka bata shi ne wai ?
Yace bai sani ba sai babban likita yace to a gaskiya masu binciken mu sun yi bincike sosai a kan shi sun gano cewa an hada sanadarai ne masu matukar cutar da dan adam a cikin sa..
Don haka maganin ya cutar da ita fiye da tsanmanin kowa don ma anyi mamakin yadda mutum zai sha shi ya kai har war hakan nan bai mutum ba.
Dole sai an binciko mai hada shi kafin ya cutawa sauran al,umma daga baya don yanzu Allah kadai yasan wanda aka cutawa dashi hakana.
An bar maganan ga sai an nemo wanda ya bata shi dole kafin ai wani abu akai da haka aka mike kowa ya fice office din.
Muna fita nace daddy Saliha itace ta farko da zamu fara tuhuma don ita ce ke daukowa tasan inda ake karbo shi dole.
Nasan kuma zata iya gudu idan ta fahinci akwai matsala da sauri yace bari ya bugawa maigadi waya ya tsare ta karta gudu.
Sunyi magana da mai gadi yace yanzu kuwa yaga wanan matar da ka hana zuwa tazo sunyi magana ta shiga gida sai ya hango ta tafe da sauri yace gata nan zata fito da kaya Alhaji yace tsare ta har in zo yanzu.
Bamu bata loiaci ba ya dauke ni police station ya tsaya yai reporting aka bashi yan sanda da mota muka nufi gidan.
Kafin saliha ta karaso get din yasa sakata da key ya rufe ya kada aljihun shi tana zuwa tace dashi bude min na fita yace ba ko gidan nan ba.
Wayan ta yai kara ta dauka take cewa gata nan bakin get maigadi ya rufe kofan da ita ai a ciki ta wayan akace da ita ke bazakiyi yadda zaki fito ba ki mashi masifa dole ya bude maki ai.
Tun daga nesa muka hango wata bakar kamri a kofab gidan sai dai maishi na hango motar daddy yaja tashi motar yai gaba abinsa.
Tare da yan sanda muka shigo Saliha na ganin an bude kofan ta yunkura zata fice aka cafketa.
Ciki na wuce ban bisu ba nasa mai gadi ya dauko min jakkar data cika taf da kayan anty ta sace zata gudu dasu.
Gajiye ce ta zazzage duk kayan ne masu muhinmanci ta kwasa na anty zata gudu da su dama.
Tun nan nasan akwai magana kaddara bai kiran mutum yace baya zuwa ke nan don anty takimu tace mu muggaine ta jawo muggan gaskiya a jikin ta sun cuta mata.
Falon yai kaca kaca duk ta bincike mata kaya dagani kuma ba ranan bane tafara diban kayan uwar dakin nata.
Da farko Saliha taso tasa taurin kai, taki fadin inda take daukowa Anty maganin sai da ta taji matsi ne take fadin ai wurin wani maimagani ne take zuwa karban mata maganin.
Yan sanda sun tabaye ta wakai anty gurin ta nuna ita bata sani ba ita dai ana turata ta karbo ne.
Tana cikin handcuffs aka tasa ta a gaba sai gidan wani mutum shi kadai ne a gidan bai ma tare da mace yaso ya musa amma daya ji matsin yan sanda tambaya na fito mashi ta ko ina take ya amsa da lalai wirin shi take karba mai maganin anyi ciniki akan dubu dari biyu da hamsin da ita.
Inda yace da farko shi yaso ya taimaka mata ne sai daga baya wacce ta kawota ta dawo daga baya da wani bukata ta nun ka mai kudi masu yawa tace tana son ya dinga saka guba da zaiwa matar illa a cikin ruwan sanyi yace shi da farko yaso yaki amma daga baya da ya fahinci matar yar duniyace dole ya amince yake mata yadda take so don in ma baiyi ba wani zatakaiwa yai mata aikin.
An tambaye shi damay damay yake hadawa aciki ya lissafo wasu itatuwa masu cutawa yace sai yake dan zuba kayan yaji don ya kawar da kamshin iccen garesu.
Tambaya sosai akai mai inda yai masu bayani yadda suka gamsu yake cewa shi gidan matar ne bai sani ba sai dai yya masu kwatancen ta da motar ta tare da basu lambar wayan ta.
Shima aka hada dashi aka rufe tare da saliha da tai bayani kan irin cutar uwar dakin nasu da suka dade sunayi wacce wata matace ta sata akan yin haka din gareta.
Don ta sha ji matar na cewa sai taga bayan Saade don da ita zata fara kawar da sauran
Showing 264001 words to 267000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89 Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153