tsaye kai da kada min alaman kada na soma na tanka mata.
Har muka gama aiki da Inna tana zaune sai maga take sakewa ita da diyan ta a tsakar gida.
Bayan sallah na samu guri a dakin mu na shige ban fito ba har lokacin da naji shigowan baba gida.
Ya zauna don cin abincin dare Inna na gurin shi don itace da girki.
Sai murya wani yaro naji yai sallama ya gaidasu yace wai ana sallama da Rahama .
Gabana yai wani irin mugun faduwa daga inda nake zaune a dakin mu naji baba yana cewa waye ?
Yaron yace ina ganin kamar Alhaji garbati ne da wani a wajen.
Baba yace kace su jira gata nan fitowa daga inda yake zaune, yake cewa ke Rahama kina dai jin ana sallama dake ko ?
Na jawo hijjab dina dake gefe na nasaka tare da yan silifas dina da anty ta saya min nafice daga gidan.
Suna zaune a gidin iccen durumin dake kofan gidan mu inda wani lokaci samari ne ke zama suna hiran dare idan sun dawo daga gurin neman kudinsu.
Su biyu ne bazan iya sheda dayan ba tunda akwai duhu a lokacin sosai.
Sai kamshi turare suke irin na yan kauye mai hawa kai ya saka mutum ciwon kai a lokaci daya.
Na karso inda suke zaune tare da sallama suka wani amsa min kamar wasu kananan yara dasu.
Tare da cewa barka da fitowa hajiya Rahama insha Allahu kila badi dake za, a sauke farali indai kin amince.
Dan gajeren murmushi nayi bayan na fahinci mai magana baba sallah ne dan uwan mama.
Nace baba ina wunin ku ?
Yauwa barka dai Rahama .
Kin wuni lafiya dai ko ?
Na ansa a fili a gajarce da lafiya kalau.
Amma azuciyata cewa nayi ina fa na wuni lafiya bayan bakin cikin da kukajawa rayuwana ?
Baba salla ne ya fara magana yace ba sai mungabatar maki da kan mu ba dai tunda naga alaman babaki da Lauratu sun gudanar da komai yadda ya kama ?
Na dan kai durkushe a gaban su cikin ladabi nace haka ne kan.
Yace yauwa ashe bazamu samu matsala ba ke nan yadda muke tsanmani ?
Malama Rahama ga abokina nan kuma amina na yaganki ya yaba da tarbiyan ki shiyasa yaji yana son kasan cewan ki daya daga cikin iyalin shi.
Don haka yanzu yakike gani ?.
Nace kamar ya fa ?
A yadda nai magana tankar ban fahince su ba nayi.
Sai shi baba sallah din yace kamar na amincewa da shi amin nawa ga bukatan shi a gare ki ?
Nai wani gajeren murmyshi da har ya baiyyana sukajini a fili danayi shi.
Nace lah ni na Isa na ketare maganan mahaifina aida ban fito duya ta gari ba mai tarbiya ga iyayyen ta ba ?
Nace ai babu komai sai dai Allah ya tabbatar da abinda yafi zama alheri ga rayuwan mu.
Sun nuna sunji dadin magana na yadda suke fadin to Alhamdullahi alama ya nuna ke diyace mai tarbiya tun yanzu.
Sai lokacin shi garbatin yai magana da cewa na ji dadi kwarai Rahama da kika amince da bukatana haka da sauri don ban taba zaton hakan ba a gare ki.
Nace to yaya zanyi tunda umurni ne daga mahaifana ai dole nayi biyayya garesu.
Ai ko ban amince don ra, ayina ba dole ne na amice don biyayya ga mahaifa na tunda sune masu iko dani bani ce keda ikon kaina ba.
Cikun wani jin dadi garbatin yake cewa.
Duk da umurni ne iyayyen ki akaina naji matukar dadi da amincewan ki haka ba tare da wani matsala ba.
Insha Allahu kada kiji komai zakiji dadin zama da iyalina don zan kafa masu doka akanki don ke karamace sosai a cikin su.
Sukace zasu tafi sai na kara jinsu dama sunzo ne su tabbatar da idon su halin da ake ciki.
Kuma Alhamdullahi a yadda suka samu taro a gurina sunji dadi kuma sun gode.
Yanzu dai kinga mu ba yara bane don haka bazamu dinga zuwa ko yaushe ba don gujewa idanun jama, a akan mu.
Kindai sai komai a kauyen nan yanzu ana ganin mu labari sai yasha banban kuma.
Bakar Leda ne baba sallah yake miko min yana cewa fa wanan dan tsaraban rano ne da muka shiga dazun mukazo maki dashi.
Na girgiza kaina tare da cewa da kubarshi aiko haka ma nagode kwarai.
Haba haba ayi haka kuma diya ta ki karba kawai wanan ai ba komai bane idan mun samu hadin kanki yadda muke so ?
Nace kada muyu haka daku baba idan ina karban kayan maza Innata fada take min .
Da alama sun gamsu da bayani na yadda naga sunyi sun fahinci dai a karkashin controling din iyayyena nake ba kamar sauran yaran da suka sani ba .
Baba sallah ne yace duk da gaka dai diyata ki daure ki karba zan wa mahaufin ki bayani yadda zai gamsu.
Kinsan kin karban kayan mosoyi wani alama ne na kiyayya kuma.
Haka dai na daure na karba tare da masu godiya na juya nashiga gida raina a bace .



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, ,


IDAN KIN BIYA KI KA BAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YAR UWA, , , ,

5
A haka na juya zuwa cikin gida jiki a sabule min ina dauke da ledan da suka bani a hannu na.
Har lokacin Inna suna gurin zaune da babana nazo na wuce su zuwa cikin dakin mu.
Tafe nake ina tunane a zuciyata sam bana cikin natsuwa ko kadan a lokacin zuciya bata kwanta ba da wanan hadin da ake son yi min.
Sam garbati bai min ba gashi dai dattijo a gurina na ni yar sha biyar tsoho kutuf nake ganin shi,
Koma da ace lokacin kuruciyar shi yake nidai bai mun ba don bakine wulluk kakaura dashi sai dai ba can kwarai ba.
Ga fuskan shi duk ya bar gemu a ciki baje baje wai shi sunnan kauye babu dai wani abin armashi a cikin sa ko kadan.
Sai dai ban da wani zabi ga gakan tunda ba zan iya bijirewa hukuncin mahaifina ba akaina.
Duk da har lokacin ba wai ma na fahinci may ye zaman aure ba tunda a gidan mu ba wani zaman auren dadi naga anayi ba ma balle na koya.
Nasan irin rayuwan da inna ta tayi na zaman bakin cikin rayuwa ni ma dai din shi zan je naitayi gidan nawa auren ke nan.
Ban da wani zabi a hakan don ban isa na bijirewa zabin mahaifina ba haka zan ta kokarin tursawa zuciya na kaunan shi koda kuwa zuciyan nawa na barazanan kamuwa sa ciwo ne.
Ganin yanayin da na dawo gidan yasa bayan na dan shiga da yan mintoci Inna ta mike daga inda take zaune ta biyo ni dakin mu.
Nan ta samay ni nayi zaune nayi tagumi ga ledan da nashigo dashi na tasa a gabana.
Tocilan hannun ta ta haska ledan da shi sabulai ne sai clean manya biyu sai turare fesawa na passition da turmi zani guda biyu sai kudi wai kudin dinki dubu uku.
Baki Inna ta ta rike tana cewa kai anya Alhaji garbati bai dauko hanyan riya ba ga alamarin nan kuwa ?
Yanzu ace duk yawan iyalinshi zai iya binsu da makamancin kayan nan haka ne ?
Gaskiya ni ban son abinda tun ba, aje ko ina ba zai shafa maki bakin jini akai .
Duk wani abinda zaiyi a gidan nan tamfar a kunnen iyalin shi ne don dai yaya tana hurda da sabuwa da can baya.
Daukan ledan tayi wai zata kai wa babana da mama dake waje da sauri na tura hannu ciki na kwashe kudin don nasan idan ankaisu mamace zata kwashe su da wani dadin bakin ta.
Inna dai bata ce min komai ba ta juya ta fice daga dakin ina jin su baba yana cewa kai kaya haka kamar za, a kai lefe ?
Mama sai faman binciken ledan take da sauri nasan kudi ne take nema a ciki gashi ta wani tsuke fuskan ta tamau da ganin kayan.
Can taja tsuki tare da tura kayan a gaban babana tana fadin kaiyya sai dai tsiyan abin duk wanan gatan tsoho ne.
Da yaro ne shine za ai farin ciki da nuna rawan kai amma tsoho ga karamin yaro may za, a gane ciki haka.
A, a lauratu inji babana kon san da haka kikace nai maki alfarma na bada ita gare shi tunda da dan uwanki akazo neman ta ?
Idan kin san haka ne may yasa kika sakani gaba saida na furta na bada ita yanzu zaki zo min da wanan sabon zance kuma ?
A, a ni yanzu may nace kuma ai gaskiya na fada yanzu ba ga abin arziki ya fara sauka maka ba har kuna murna.
Cikin mamaki yace murna kuma kamar yaya lauratu akan wanan kayan ne zanyi murna da rayuwan da yata zata shiga ?
Nifa don ki na yarda naba Rahama ga wanan mutumin may naci nasa da zanji nauyi shi a baya ?
Ashe ke nan ke da wata manufa kika sa na bada Rahama gare shi ke nan ?
Manufar may kuma malam banda abin arzikin da na hada ni idan bashi din ba akwai wanda ka taba jin yazo ya sallama akanta ne a gidan nan bayan duk ta gama zubar da mutuncinta ga samarin gari.
Daga inda nake ina sauraren su na hade wasu yawun bakinciki a raina tare da hawayen da yazubo min.
Koma may zan tarar a gidan gara na tafi na huta da kullin sherin mama da yaranta hakana nida inna ta akaina.
Jin hayaniyar tasu zai yi karfi ne yasa na fito waje inda suke don mama ba komai bane hassada ta nuna min karara .
Tayi min hakane don ta jefa rayuwana dana mahaifiyata a kunci ne kawai.
Basuyi aune ba sai ganina sukayi a waje durkushe a gaban su ina cewa baba don Allah kabar wanan magana haka.
Indon nice na yarda da kaddaran da Allah ya kawo min na auren garbati bazan bari kayi kunya ba a kaina insha Allahu.
Tausayi na bashi yai shiru tare da yi min wani irin kallo na ban tausayi yagane manufata bazan bari yai magana biyu ba yace eh yadawo yace kuma a, a daga baya.
Yace shike nan Rahama Ubangiji ya tsare mun ke a duk halin da zaki riski kan ki a gidan shi nace amin baba na share kwallan da suka zubo min na mike na koma dakin mu.
Ina jin mama bayan sun gama hayaniya ta juya dakin ta bata dade ba ta rufo kofan ta hakan ya nuna ranan bazata yarda na kwana a dakin ta ba ke nan.
Inajin Innata bata shigo daki ba da taga haka dakin da suke aje shirgin su har bunun dakin ya zabbace ta gefe daya don wahala ta dan gyara min gefe daya tace na kwana a can ko naje gidan mai kuli na kwana.
Nace dare yayi Inna bari kawai na koma can na kwanta yanzu mama ta rufe gidan ta nasani.
Baba tana ganin haka ya nufi dakin mama ya na bugawa tace daga ciki wai lafiya kake dukan min kofa haka kuma may kuma zan maka ?
Yace ki bude Rahama ta shigo ta kwanta tace ai kaba uwar ta daki ka bani don haka ku kwanta tare da ita mana tunda ta zama yar gwal matar Alhaji yanzu.
Dole ya juya ya barta zuciyar shi na tir da Allah waddai da halin mace ba haguwa irin ta.
Sai ta kaika ta baro kuma ta tsira ma sabon fitina dama wanda ya kaucewa Allah dole ya fuskanci kalubali irin haka a rayuwan shi.
Hakana na kwana dakin ga sauro ga beraye suna ta hawa min jikina ba dadi ko kadan dakin don yawan shirgin kayan aikin su dake cikin dakin.
Kwana biyun girkin Inna haka tayi shi a cikin kunci a gidan rai a bace mata duk nabi na damu ga bacin ran da mahaifiya ta take ciki ga zancen auren da ake son yi min na dole.
Haka nake zaune a takure ga mama ta saka mu gaba da gori ita da diyan ta duk mun kasa sukuni a tare da mu.
Na dai yanke shawara zuwa yamma na shiga gurin mama altine ko zan dan sarara a tare da ni.
Nan samu mama tana dan aikace aikacen marance na shigo da sallama na na karbi tsintsiyan da take shara a hannun ta na karasa mata sharan.
Na dawo gurin da take zaune tana gyara geron da zatayi birbisco dashi na abincin dare na karba ina gyara mata.
Kallon yanayi na tayi abinka da babban mace ta fahinci babu dadin rai a tare da ni lokacin.
Take cewa lafiya kuwa yar gidan anty na gan ki yau wata iri dake haka ?
Maimakon nayi magana sai hawaye ne suka biyo baya tace subbahanallahi may ke faruwa ne Rahama ?
Sai da nayi kuka mai isata nake cewa mama baki ji kaddaran daya fada akaina bane halan innata bata samu shigowa ta fada maki komai ba ?
Tace Asiya ta kwana biyu bata shigo gidan nan ba gaskiya may ya faru.
Ina kuka nw nake labarta mata komai da ya faru a gidan mu akaina cikin kuka tace waye shi wanda aka baki din ne ?
Nace Garbati cikin rike kirjin ta tace wani garbatin ba dai Alhaji garbatin dan bida ba dana sani ?
Nace a sanyaye shi mama.
Tace subbahanallahi yanzu shi mahaifinki da ranshi da lafiyan shi zau dauki ya kamar ki ya mika wanan gidan na sa, an nin kakan nin ki ko may ?
Nan ta haufada tana cewa idan Salihu bai yi hankali ba sai Lauratu ta kona shi tun a cikin duniyan nan wallahi ko.
Fada sosai mama tayi tare da kara kwantar min da hankali take cewa zan tafi gurin anty ki ance min ita ma bata jin dadi ga abokan zaman ta ba kirki ne dasu ba.
Kin san kishin yan birni ba irin namu ne ba na kauye kishi suke suna hadawa da yahudanci aciki.
Rayuwan ne na kowa tasa ta fishe shi akeyi wai suna ganin su wayewa ne a gare su.
Inbashi ba dan uwan ka baida lafiya ina zaka kawar da kai gareshi haka kana tsabagan gaban ka.
Nace mama Anty na bata da lafiya ne ?.
Tace ina fa taga lafiya tunda tazo din nan take fada min wai bata da lafiya ajikin ta har zasu tafi kasan waje da maigidan a dubata.
Allah yaba anty na lafiya nace tace amin Rahama ita nake gani ta tuna min da mahaifiyar ta don dan uwan ta shi namijine baidamu damu ba kamar yadda ita take kula mu.
Na sake cewa mama dama anty tana da abokan zama ne tace tana dasu mana har biyu ma.
Ai anyi aurenta ba a kokai shekara ba uwar mijin tasa ya auro yar uwarta shima mahaifin shi wai akwai yar abokin shi da yake son hada shi dashi tun farko shima yasa ya auri yarinyar.
Zoki ga irin yadda suka saka min yarinya a gaba da fitina suna ganin itace bare a cikin su sai abinda suka ga dama suke mata a gidan .
Allah dai yasa shi mijin yana son abin shi haka yasa basu samu yadda suke so ba akanta.
Yanzu ga ciwo yazo ya sakata agaba haka wama yasani ko ije ne aikai mata ya hanata jin dafin rayuwan ta.
Nace mama ije kuma may nene ije ?
Tace baka ji maganan ba keda zaki shiga kishi cikin tsofon mata Rahama baki san ije ba kuma sai may.
Nan tashiga yi min irin kissan ije da dalilin da ke sa aiwa mutum asiri idan anga hankalin miji nagareshi da yaran shi.
Nan nai mutuwan zaune nace na shiga uku mama koma don ai min ne yasa mama ta tura baba ya kaini wanan gidan akashe ni kowa ya huta dani kamar yadda take fadi.
Har na dawo gida duk yadda mama taso ta fahintar dani hakan bai samu ba daga gare don na kasa fahintar dongon sharfin da take min akan ije wai shirin kishiya .
Ko da na dawo gida na samu ranan har baba ya dawo daga kasuwa ko suna zaune da mama yake tambayana daga ina nace na shiga gurin mama altine ne na taya ta aiki .
Bai yi magana ba sai bina da yayi da harara har na shige dakin mu ban dade da shiga ba Inna ta kamala abinda takeyi sai ji kawai nayi ta rufo kofan dakin ta garam.
Nace ashe yau akwai tsiya a gidan nan ke nan don Inna zata rama abinda akai min ne kwana biyu na barina na kwana dakin shirgi ni kadai sai bera ye.
Lawisa ce tashigo gidan daga gurin hira ta fara zuwa dakin mu don ta kwanta taji shi a kargamay.
Ina jin ta lokacin data juya zuwa inda iyayyenta suke tana fadin wai Asiya ta rufe kofan ta don haka suke kiran Inna da sunan ta gazatsau ba sayawa.
Mama tace kamar yaya ta rufe kofan ta a ina take son ku kwana yau din ?
Nace a raina jifa mama da son kai ta manta abinda tai min ni .
Ban dai ji baba ya tanka masu ba har lokacin tasowa mama tayi
Showing 15001 words to 18000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6 Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153