barci a jikin ta na shiga da sallama na dakin ta juyo tana fadin baki kwanta ba ashe nace eh nazo yi maki sai da safe ne.
Tace dani gashi ko kamar kina sauri da naso muyi magana dake ne, nace cikin mamaki sauri kuma anty ?
Na karasa bakin kujeran dakin na zauna tace na sani ko mijin ki na can yana jiran ki ne ?
Haba dai anty kuma tace dazun yake ce min na tambaye ki kan gajiye da yaran nan ya dai min magana kamar akwai matsala ko ?
Shiru nayi na dan lokaci can dai nace eh to ba matsala dan zan saka ido sosai nima ban so kiji hakan ba gaskiya don ba dadi.
Yaran dai ne a cikin hiran suke fadin kamar tana dan masu mugun hali a bayan idon mutane.
Nan dai na fada mata abinda suka ce a falon ranta yai mugun baci take cewa akan may zata dinga dukan min diya nimay na ragata dashi a gidan nan ?
Idan da kece kike dukan su wallahi Rama raina bazai taba baci ba kona digo don nasan harga Allah da zuciya daya kike dasu ke ban kara tabbatar da hakan ba ma sai yanzu.
Dakike yawan kusanta su da mahaifin su har yana jin korafin diyan shi, wanda ni da can baya bayi hakan ba saboda gudun zuciya.
Nace Anty don Allah kiyi hakkuri zan saka mata ido akan su sosai dama naso daukan mataki a hakan ba sai kin sani ba kada ranki ya baci haka ?
Amma don Allah kiyi hakuri don mutum yau abin tsoro don kinga babu wanda zai taba tsanmanin hakan da take masu ai.
Amma kamar jinior zata dinga duka kan snocks da sauran ko wanka tace shine ai nima nagani Rama ?
Shekaran ki nawa dasu amma wallahi har yau banga wani abinda ba daidai ba akan yaran nan daga gare ki.
Yi hakkuri anty zan mata magana insha Allahu ta yadda ba zata gane su suka fada ba don kada ta canza masu sallo.
Tace idan ta gaji ne ta tafi mana nace yi hakkuri anty insha Allahu bazata sake ba da yardan Allah.
Tace gaskiya kina da hikima wallahi da baki haka ba saita ta cuta masu ba,a sani nace hakane.
Kudin da nashigo dasu a hannu nake mika mata tace na may ye wanan kuma ?
Nace kudin da daddy ya bamu ne anty, .
Ni may zanyi da su kuma ta fada ?
Anty ki aje wurin ki ki muna lalura dashi tunda ta fara fada sai yanzu naga murmushin ta tace cikin murmushi kai Rama akwaiki da shirmay wallahi.
Ke matar shi ne ni matar shi ne yabaki yabani shine ni zan aje a guna ?
Nace anty ni may kika ragani dashi har may zan saye dasu don Allah anty ki karba ki barsu a gurin ki don Allah dai ?
Kallona take cikin mamaki gashi sai hada ta da Allah nakeyi akan ta karba dai.
Ta mika hannu ta karba sai ta kirga dibu goma ta miko min tace karbi wanan don shan mai a mota, kada ki zauna ba kudi a hannun ki.
Nace akwai dubu biyun da kika bani ai last week suna nan ban kashe ba tace to ki kara da wanan din.
Na karba da godiya tace kai Rama ho, sai da safe nace Allah bamu alheri anty.
Na wuce ina tunane a raina gaskiya Gajiye bata kyauta ba anty mace ce saliha gashi son diyan ta ya rinjayi zuciyar ta kullun maganan ta shi tausayin su take ji ko Allah zai barta ta rayu da yaran ta.
Ina shiga yana tattara kayan shi zai shige dakin shi na karba nashige mai dasu ciki.
Ina gyaran su ya shigo dakin bathroom ya fada yai wanka ya fito yai shirin kwanciya.
Mun kwanta nake cewa daddy na so fada ma motan nan yanzu tana bani matsala sosai yace yaya baki min magana ba sai yanzu da tafiya yazo min sai dai ki dauki nawa ki amfani dashi mugani kada ki kara shiga mota ba lafiya bana son haka.
Yana gyara kwanciya yace ki dauki farar CRV din nan dake aje kiyi amfani dashi.
Ga keys din su can cikin drower na fada maki kada ki sake shiga motar nan kuma tunda tana da matsala nace insha Allahu daddy yace sai ki shirya kin san yau na sallama zaki min don zanyi wata hudu ban ji laushin wanan jikin danake bukatan shi ba a tare dani.
Murmushi nayi nace ai da wani jikin zaka daddy ba kai kadai ba fa zaka tafiyan.
Yace bayan kin min zaben raguwa may zan gane ga tafiyan sai maneji kawai ai.
Nace daddy ai gara kaje da ita saboda cikin ta ina ga bai zauna ba a jikin ta har yanzu don kaga ko yaushe jikin ta ba dadi gareta.
Yace haka nagani nima shiyasa ai na amince da tafiya da ita in bashi ba may zai kaini daukan mai ciki yawo da ita nagane may banda gaiyan barci.
Daga haka ya jawoni zuwa jikin shi ya fara shafana yadda yake so saida ya jagwalgwalani son ranshi ya gaji ya barni hakana.
Da safe ma bai barni na na huta ba bayan ya dawo sallah sai da ya kara biyan bukatan shi a kaina ko yaushe ji yake kamar ko yaushe sabuwa, nake gare shi.
Sai four na fita girki na na dawo dakina don yinin ranan daddy na gida manne dani bai fita ba.
Ina shirin zuwa dakin anty wayana dake gefe ke ruri alamar kira ya shigo min lokacin.
Bakon nomba ne na dauka muryan mace naji muka gaisa gashi nasan muryan amma na kasa gane ko wacece.
Tace dani Rahama kina waya da Zulfa ne yanzu nasa farida ta turo min nombaki.
Nace a raina Farida kan ta zama munafuka idan ana neman nombana itace mai bawa mutane ke nan .
Don haka taimin tabawa mahaukacin sojan nan layi na ya dinga damuna lokacin.
Yanzu kuma ta dauka taba kishiya na wanda na san da magana haka kawai zata kirani ta waya kai tsaye muna gida daya da ita.
Muryan Zulfa ya katse min fadan zucin da na keyi da Farida lokacin.
Tace nakiraki ne nai maki magana don Allah kiyi hakkuri abubuwan dake faruwa a tsakanin mu nasan kina kokari dani sosai sai dai kin san ala,mari na kishi.
Yanzu mama ne tace na kiraki kan wanan karamcin da kikai min shiyasa na kiraki din.
Nace a rai na ji yar rainin wayo watau badon mamanta tace ta kirani ba ita bazata iya kirana ba ke nan.
Sai nace ai babu komai duk mai tausayi ai yasan ciwo yasan kuma lalurar mai ciki tace ke kika san haka ita wanan da bata da tausayi ai tana nan tana hauka kan tafiyan wai bata yarda ba.
Nace to Allah ya kyauta nagode Allah ya kai ku lafiya ya kuma bada sa,an tafiya tace amin na kashe wayan kafin ma ta kashe ita.
Nabi wayan da kallon mamaki akarshe ma cillan da wayan nayi saman kujra na ci gaba da gyaran dakina kawai ina mita a raina.
Bayan na gama na rufo na nufi dakin anty don sai dare zan dawo ke nan idan na tafi.
Anty na daki ni da gajiye ne a falo nake cewa da ita, yaran nan sun kusa dawowa yanzu.
Tace wallahi su dawo su cika mutane da surutu da yimini yimini basu bari mutum ya huta wallahi.
Nace haba Gajiye don may muke nan ni dake ba don mu taimaka ma wanan baiwar Allah ba.
Don haka yaran ta sune farin cikin mu muma batawa yaran ta kamar bata mata raine gare mu.
Matar nan bata rage mu da komai ba a duniya ta dauke mu tankar yan uwanta na jini yadda take kyautata min tun farko yasa bana yarda ko kadan na saba mata.
Mussanman ma akan yaranta da take jin su kamar rayuwan ta tun zamana dasu ban taba daga hannu na daki yaron ta ba haka kuma banta yiwa yaron ta koda jan idone a bayan ta.
Don nasan idan nayi ji zatayi komai dadewa a wurin su shi yaro na kowa ne ai kahaifeshi baka san iya wanda zai amfana dashi ba a duniya.
Wallahi gajiye bani fatan daidai da rana daya ko a gabanta ko bayan ta na kuntatawa dan ta don ita bata kuntata muna ba.
Yanzu dubi fa ba dangin iya babu na baba amma ko yaushe zancen auren ki da maigadi take tana tausaya ma zaman ki hakan nan.
Yo gajiye may muke dashi mu da zamu saka mata dashi banda muso jinin ta tsakani da Allah.
Kai nifa ko ba dan anty ba bani fatan in cutawa dan kowa bayan idon uwar shi a duniyan nan.
Balle wanan salihar matar mai mutunci da karamci irin haka mu may zamu iya saka mata dashi a duniyan nan bayan haka ?
Tunda na fara magana jikin ta yai mugun sanyi sosai naga nadama karara a udon ta tace dani .
Wallahi Rahama kin min maganan da yai min tasiri yau a zuciya na maganan ki dutse bamu ko da abinda zamu saka mata bayan hakan.
Nace yaran kan ai yanzu muka fara son su tunda sune farin cikin rayuwan ta ko yaushe.
Tace masu iya magana ko sunce idan so na Allah kaso da kaso uwar shi da zuciya daya.
Daga haka muka dauko zancen auren ta da take son yi ina kara bata dan shawara daidai iyawa na.
Ranan talata su daddy suka bar garin shi da zulfa da dare bsshir ya kaisu airport.
Hindatu bata san ina amfani da motar maigidan ba sai ranan na dawo yar aikin ta ce ta ganni kuma nasan itace ta tsegunta mata hakan.
Muna zaune falo da dare dariya muke kwasa wai Jinior na gwada muna tafiyan wani makwabcin su.
Sai ganin an bankado kofa mukayi tabi mu da kallon daya bayan daya muma ita din muke kallo .
Ta juya inda anty take tana cewa Saa kin san lokacin da wanan mai isar yar kauyen ta dauki motar maigidan ta fita dashi ko may ?
Mota ?
Wace mota ke nan fa nace ai da kiyi dani amma ba da yar uwata ba nida na shiga motar har ya damay ki ?
Tace ke har wani matsayi ko mukami ke gareki da zaki dauki mota maishi bai nan ?
Nace malama banda lokacin ki amma idan kin damu sai ki kira maishi ki fada mai babu ruwan anty cikin wanan magana.
Sati biyu na baki gashi ko cika baiyi ba kinga caji da idon ki idan zaki daina gori da hassadawa mutane ki daina shine saukin ki kawai.
O yanzu na gane may kike nufi dayin hakan wallahi wallahi zaki san ba hindu ake tabawa a zauna lafiya ba.
Don ni kowa yaci tuwo dani miya yasha sai na mayar dake abin tausayi a gidan nan keda wanda kike kwadayin sai hange da ido.
Nace saukin abin dai kuma bakece Allah wanan Allah kadai yakai can ga bawan shi amma bake mutum yar uwata ba.
Mu zuba wallahi ni da ke banza yar kauye kawai zan gwada maki na fiki sanin hanya nake sherin na yan kauye ne.
Sai kin bar gidan nan da kafan nan naki da kika shigowa mutane yar cin amana kawai.
Ke ko kunyan kanki bakya ji kinzo kin asirce mata da mijin ta ki aure mata miji don sheri kullun kina mane da ita da yaran ta kina cusa masu mugun abu suna ci.
To ni wallahi nafi karfin ki ke har boka da malam kika sani zaki gane kuren ki wallahi.
Anty tace hindatu may ye zafi hakane don mota zaku tsaya kuna wannan tayar da jijiyan wuyan haka har kuna sabon Allah akai.
Ai ba mai iya yiwa wani wani abu sai Allah shi ganin bayan mutum ai ba alheri bane.
Dallah rufa min baki almunahuhu kawai wa zakiwa wa, azi bayan duk sherin kece mai kullawa kina wani lafewa a daki kullun wai ke baki da lafiya .
Haka zaki kare a nakashe cikin daki kina kulla kilibibi a zauna makira bamza kawai.
Tai tsuki tare da juyawa da karfi zata bar dakin nace an dai yi hasara anji kuya haka za, a kare ga hassada da kyashi a rai.
Anty ai ta godewa Allah don kaffara take don kowa yasan ciwo kaffara ne keko fa sai bakin hasaada da kishin tsiya dake cinki baki iya komai damu wallahi ta Allah ba taki ba.
Ta juyo tana fadin haka kikace muzuba mugani shege ka fasa ni daku muna fukai kawai.
Gaki munafuka yar hassada da bakin ciki tafi haka zaki kare wazaki zo kina zare wa ido nan kowa kika aje ke ?
Tana fita anty tace wai sannu Rama ashe ke ma kin iya wanan irin haukan na su ai zakuyi daidai.
Ta zaci iri nane da suka raina su kwaso sharan su su yaba min duk lokacin da suka ga daman hakan.
Nace anty ni yanzu nai alkawari bazan kara ragawa wanan mara mutuncin ba wallahi tunda ana bata girma ita bata sani ba.
Tace ya isa hakana kyale ta basu da aiki sai gadara da jahilci ai kun hadu yan bana kun saje ke nan.
Nace haka wai fa dayar abokiyar sherin nata ranan sai ga waya ta bugo min nan na fadawa anty yadda mukayi da ita.
Tace ji rashin wayo harda fadin wai uwar ta ce tace ta bugo maki waya watau ba kashin kanta ra bugo ba saida aka sata ke nan.
Nace ita, dai ta sani ni duk bugu daya na dauke su dukkan su ai bazan yarda da shiri da kowa ba na sheri.
Anty tace ita Zulfa tana da dan dama sosai bisaga hindatu don ita hindatu gani take duk tafi mu a gidan.
Hakama ake fadi yadda ake ganin tana karya da rawan kai yanzu ko taga wata tashigo kin san dole haukan ya karu mata.
Nace sai tayi ni banda lokacin ta Allah dai ya baki lafiya anty mutum harda ciwo yake gori ?
Anty tace ni ko makiyina bana fatan yai ciwon nan balle wani nawa su da basu san halin da nake ciki ba yazama masu abin gori gare su.
Allah dai ya baki lafiya anty ki koma kamar kowa gajiye tace Amin wallahi mutum ya dinga kirari kamar shi ya halicci kan shi don kishi.
Muka gaji dayi dole muka kyale ta sai dai maganganun ta sun tsaya min a rai sosai tunda ta fadi nasan zata iya abinda tai niyya akaina din.

********* ********* *********
Munje school bayan mun fito daga lectures ne Zarah ke cewa sai naga yau gaki nan wani iri dake nai ajiyan zuciya nace bari kawai Zarah.
Alamarin matan daddy ne abin ba dadi wallahi sai nake fada mata duk yadda al, amarin yake muna.
Take cewa dani ke yanzu wani mataki kika daukar ma lafazin ta ke nan ?
Nace wani ko mataki zan daukar Zarah idan naga abin go no go na bar masu mijin su ban iyawa wallahi sai dai anty tayi hakkuri dani kawai.
Rahama kina hauka ne da zakice wai kibar masu mijin su, tabdi jam ai wallahi basu isa ba sai dai ai ta tafkawa din.
In sun sani ai kowa ma ya sani ina dai duniyan ce din kowa tashi ta fishe shi.
Na kalleta da mamaki nace saboda may kikace haka zarah ?
Tace saboda ko mijin kowa ne ba don su, su kadai aka hallice shi ba ai.
Ko bake ba haka zasuyi ga kowa ma don haline zanen dutse zafin kishi da hauka ke cin su ita anty Allah ya bata hakkuri ke nan.
Bafa bata son mijin ta bane ta sadaukar maki dashi wallahi tana son abinta kuma duk yadda akayi wani abin nacin ta na kishi akan ki daurewa kawai takeyi bata nunawa a fili.
Nace kai haba Zarah ina gaskiya wanan kan ba gsskiya bane.
Tace kika dai ce amma wallahi tana kishin ki kice ni zarah bukar na fada maki wanan magana wata rana zaki tuna.
Nace ko dai tana kishina tunda bata nuna min ba nima bazan taba nuna mata ba.
Yana da kyau hakan amma kiyi raka tsantsan don watan watarana wallahi wurin boye mata wani abinki.
Nace naji kawai nifa duk na antyna mai sauki ne zarah bisa ga na wanan matan da ke ikirarin halakani.
Tace wanan sai Allah ai kema ba zama zakiyi hakana ba yanzu wa ya saura da wanan in ba don Allah na tare dake ba ai da yanzu sai buzunki kila.
Nace ni Zarah yaya zan yi ne dasu ni wallahi dai na shiga uku aure babu kwancitan hankali haka ?
Yaya ko zaki in banda kema tashi tsaye zakiyi kamar yadda suke tsaye kyam akan zaman gidan ko yaushe wake kwanci irin ki yanzu.
Nace nikan in dai sai naje gurin boka ko malam wallahi sai dai na bar masu gidan su Allah ko.
Tace ke don Allah an daina yayin boka
Showing 204001 words to 207000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69 Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153