matsalar babba ne haka ba sai yanzu dana fahinci abin kamar ba mai karewa bane muna tunda yana iya amfani da yan uwa na ashe nice dai muke da wanan matsala din tsakanin mu.
Haka naci kuka na da tunanena nafito na koma na kwanta ban farka ba ga dan barcin dana samu sai bakwai na safe ashe hindatu nace ta kasa ta tsare taga fitowana daga dakin don haka take min wanan dabian kullun nake da girki.
Haka na daure na ci gaba da alamura na kamar kullun sai dai daddy yazo karyawa da safe sai naga ya kura min ido ban yarda mun hada ido dashi ba sai naji yace Rahama na amsa a sanyaye ban dago na kalle shi ba.
Naci gaba da abinda nakeyi yai shiru yana nazari na nazo wucewa ya riko hannuwa na abinda yasa ni dagowa na kalleshi ke nan yace dani.
Sai naga idon ki kamar kin yi kuka a daren jiya ko?
Ban tanka mashi ba sai kokarin wucewa da nake son ya sake ni nayi kawai nake da hannuna dake rike da nashi din.
Tambaya na ya sake yi na sunkuyar da kai na kasa wani irin abu nakeji a zuciyana kuka kawai nake da bukatan yi a lokacin ko zanji sanyi.
Ya sake ni ban tsaya ba na shige dakina na rufo yakai minti talatin sai gashi dakin ya shigo yazo ya tsaya kaina ya dan jima a tsaye ba tare da yai magana ba.
Sai zuwa can yace nasan kina cutuwa Rahama nima abin ya fara fin karfina don ni kadai nasan halin da nake ciki a zuciyana.
Nace ni bashi ke damuna ba gida nake son zuwa kawai na kwana biyu ko zan huta sai naji yai murmushi yace cikin wata murya Rahama kina nufin kije gida ki fada masu matsalar da muke ciki ko may ?
Muryan shi ya ban matukat tausayi a yadda yai magana yace kina ganin idan sunji wanan matsalar da muke ciki zasu barki ki zauna dani ne haka Rahama ?
Ban sake magana ba sai kukan da nakeyi shima din bai min magana ba yana dai tsaye a wurin kawai can naji ya sa kai ya fice daga dakin a gurin Aisha nake jin wai daddy ya fita.
Mikewa nayi na shiga bandaki nai wanka tare da dauro alwala na sallah raka,a biyu nakai kuka na ga Allah.
Nan na zauna naci gaba da lazumi da jero adduoi sai tunanen abubuwa da dama dayazo min a raina na zamantakewa na a gidan daddy wanda a kullun da irin matsalar da nake fuskan ta a gidan.
Nake tunane shin haka sauran mata masu kishiya suke zaune a gidanjesu dama ake ganin kamar wani dadi mace ke ji idan anga tafito tana tunkaho a waje.
Ni kan gaskiya da muguwar rawa gwanma kin tashi da a illanta min rayuwana kan kishi gara kowa ya kama gaban shi a huta hakana.
Don in anci gaba da haka watarana inaji ina gani akan rayuwana za, a koma wama ya sani ko ana hakan nice dai ban gane hakan gare ni.
Da kyat na iya tashi na shirya na fito don duba girkin da Aisha ta riga ta dora muna ba laifi na samu taimin shi yadda nake so sai dan abinda baza, a rasa ba kawai nayi.
*** *** ***
Tun bayan fitan shi daga gidan abin duniya ya damu zuciyar shi ya rasa wa zai fadawa wanan magana sai bashir ya fado mashi a rai don ya fishi sanin irin matsalolin hakan nan.
Sun gaisa sunyi komai yace Bashir wallahi akwai matsala bashir din yace subbahanallahi matsala kuma Gentle yace wallahi babba kuwa.
Nan dai yake koro mai komai har yagama yi mai bayani Bashir din ya nisa yace lalai babban matsala ne wanan.
Yace sai dai gaskiya ko ka yarda ko kada ka yarda zan fada ma gaskiya wanan abin sihiri ne wanda mata keyi a tsakanin su.
Sai dai banyi tsanmanin yanzu wayewar kai din nan ashe an saura yin irin shi abune mai wuyan sha, ani sosai don dole sai ka nemi makarun shi.
Yace a ina zan nema Bashir kafa san ni ba wai na iya irin abubuwan nan bane a rayuwana asalima naki jinin alamari da sihiri shiyasa ma ban yarda da shi ba ni.
Yace to shike nan tunda baka yarda ba Allah ya sauwaka ko yace kamar ya ban yarda ba ai magana nake fada ma yanzu kan ai dole na yarda tunda ya faru dani.
Sunyi magana yace idan ta shigo kano akwai inda zasu tafi tare dashi aji ko may yakawo hakan sukai sallama ya kashe wayan.
Monday tunda safe na shirya don zuwa inda ake neman mu wurin interview din da za, ayi ban tafi da haidar ba gida na barshi gun Aisha na dauki mota na fita.
Koda na isa na samu wa yanda aka neme mu tare sun hallara a wurin ko na shiga don gaisawa da mutanen arzikin mu.
Ban dade da zuwa ba aka kirani na shiga ba wani tambaya sosai akai min ba don sun riga da sun san mu dama don haka bamu sha wani wuya ba sun dai karbi takardun mu kawai.
Sai bayan mun dawo ne Aisha ke fada min ai akan fitina daddy sunyi fada da maman Ihisan nan dai ta labarta min komai.
Sai da na huta nafito falon don bata ma san dawowa na ba gidan sai ganina tayi falo zaune muna kallo.
Sai naji tace an dawo ta zubar dama an saba ana mazuru ana shaho may zai sa a iya zama gida tunda an riga da ansaba hurda da wasu maza.
Take naji raina ya baci sosai sai dai Allah ya taimake ni ban tankata ba tunda na gane hassada ne abin nata ba komai ba.
Sati biyu sai ga shi anturo muzo mu karbi appointment letter din mu ya fito ban bata lokaci ba na tafi na karbo inda sabon wata zamu fara aiki dasu din .
Wanan dalilin yasa na matsawa daddy kan son zuwa gida na dubo su yaso ya hana amma da na matsa yace mu shirya idan zai shiga ya sauke mu.
Take na fara shirin tafiya tsaraba sosai na hada tunda safe muka kama hanyan kano tare da shi.
Banzo da yaran ba don suna school dagani sai Aisha da baba da haidar mukazo kawai anty tai mamakin ganin mu don bata san zan shigo ba.
Duk da halin da nake ciki amma ita a idon ta taga na mata kyau ne sosai na sake na zama wata classic lady dani.
Ban dade ba a gurin ta na fita zuwa part dina inda na samu duk yayi kura dayake dare ne inda zamu kwanta muka dan gyara tunda safe muka shiga gyaran wuri da taimakon gajiye muka gyara ya zama neat.
Nan take min hira wai yanzu ai anty ta karaya sosai tana son janta a dawo irin da can baya amma ita gaskiya tana tsoron hakana don wanda ya zarge ka a baya bayan yasan halinka amma ya rufe ido yai ma sheri ita bazata zauna da ita ba.
Tace takan dai dan taimaka mata wani lokaci can ba, a rasa ba sai da nai kwana biyu a kano na shirya muka wuce gida.
Mun isa da wuri don haka kafin wani lokaci akasan da zuwan mu nan yan uwa da abokan arziki suka dinga shigowa taron mu sai dai naje washe gari Allah yaiwa Jatau mijin Suwaiba na rasuwa muka tashi da wanan tashin hankalin kuma a gare mu.
Koda naje gidan abin ba dadi ruwa ma babu shi a gidan ko kadan nasa akira masu ruwa suka cika duk wani kayan dake gidan take na bada kudi aka sayo masu abinci sai dai suwaiba ke cewa dani ai rabawa akeyi kowa yai nasa nace ba matsala tabar masu sai a kawo mata nata.
Ban samu zama ba don kwana uku a gidanta muke wuni sai dare nake dawowa gida don haka ban samu kebewa da Innata ba.
Sai ranan da aika sadakan uku bandawo ba saida na wadata Suwaiba da duk wani abin bukata suma kishiyoyin nata nai masu nasu irin alherin gwargwadon hali na dawo gida ban kai dare baranan gidan .
Da dare muna zaune muna hira da Aisha uwarta ta kirata bayan fitan ta ne Inba ta ke cewa dani wai niko yarinya lafiya kuke kuwa don naji ance wanan hatsabibiyar kishiyar taki takoma can inda kike da zama yanzu ?
Nace a sanyaye lafiya muke inna sai dai dan abinda ba a rasa ba can kuma ba kullun bane tace to Allah ya kyauta a daita hakkuri da jama, a don Allah.
Nace insha Allahu Inna sai na boye mata don ban san yadda zan iya fada mata komai dake faruwa ba a tsakanina da daddy din.
Sai wurin Attu ne da naje cikin hikima irin nasu na manya take tambaya na na sake jiki sosai ina fada mata matsalar dake damuwar mu tsakani na da daddy din.
Take naji yar tsohuwar ta saka min salalami tana tafa hannayen ta tace yar nan tun yaushe hakan ke faruwa na fada mata tace to kin fadawa uwar ki da kikazo nace haba attu ko nasha giyar wake yaya zan iya fadawa inna wanan maganan kuma.
Ko ke dai daurowa tayi da har na koma bazaki ji shi ba a bakina ba tace ki koma ina cikin wanan irin laluran haka na ai banga ta zama ba .
Dole ne na bazama wurin masana a walwale maki wanan sihirin don idan ba walwale shi ba ku ba zaman lafiya ko zaman aure a tsakanin ku tunda akwai cutawa ga hakan.
Wunin da banyi ba ke nan don Attu ta fita tabar mu don haka na wuce uguwar mu na gaida mama Altine da matan babana.
Gidan mama Altine na fara shiga duk da mun hadu a gidan Suwaiba da ita amma tana ganina ta shiga ina taka saka dani ta shimfida tabar muka zauna ni da yaran ta kawo ruwan randan kasan ta mai tsabta muka sha.
Tace Rahama har na fara zargin ko don irin halin da uwar dakin naki ta tsiro dashi yasa kike ja baya dani kuma yanzu.
Nace ni kan yaya zanyi na gujeki mama aisai butulu ke mantawa da uwar shi irin halarcin da kikai min duniya ko uwata data haifeni ai ya tsaya nan.
Tace to na gode Rahama nan muka shiga hira tace zata dafawa yaran abinci suci nace barsu mama kada ki wahalar da kanki mama kinga abincin su nan biscuit tace yaran birni ke nan.
Mun sha hira da mama amma ko ta dauki halin da anty take min sai na kawar da zancen nace da ita ai yanzu an daina dama rudin shedan ne kawai.
Sai bayan la,asar na bar gidan na shiga gidan mu tsatsaye na gaidasu mama tsufa ya taso mata kanta yai wani farin gashi gashi a dankare mata ba gyara hakoranta na gaba sun zube.
Tabani tausayi sosai nace da ita idan na koma zan sa ai mata hakoran roba tunda dai batai tsufan da zata rasa hakora ba haka na san dai daya ya fadi wurin fadan su da amaryan ta a baya amma sauran biyun fa ?
Nakawo alheri nai masu nace zan dawo don in gana da babana naga jikin nashi yadda yake yanzu.
Sai gap da magariba nakoma gida inda na samu har Attu tazo nema har sau biyu ban dawo ba sai ta bar sako da magariba zata dawo mu fita.
Na samu yaran sunyi barci koda tazo ban zauna ba muka fice tare zuwa inda zamu nida ita sai kanina Audi da ya raka mu zuwa unguwar da zamu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , , , , ,
81
Kusan wuri uku Attu ta tafi dani duk maganan su daya ne kamar hadin baki kishiya ce tai min aiki ta yadda mijina ba zai iya saduwa dani ba.
Sai in an karya wanan abin da tai min wasu suyi misalin kamannin mai shi wani kuma yace daga cikin kishiyoyina ne sukai muna aikin.
Dama irin abubuwan da ake kullawa akaina da diyan da na haifa bayan na dawo gida sai barci ya gagare ni wasu kwallan bakin ciki da tausayin kaina suka zubo min.
May wa yan nan yaran sukayi da har za, a saka dasu cikin harkan mu haka su dai tsaya a kaina nida nai karanbanin shiga rayuwan mijin su.
Ina kwance wurin ashe inna batai barci ba sai naji tace dani yarinya kada ki sa damuwa a ranki abu ya zamo maki biyu fa don kinga shi harka kishi dama idan baka hadu da mai imani ba da tsoron Allah haka ne yake kasan cewa dama.
Nace ina niba kaina nake jiwa ba sai yaran nan da suna su ya shigo ciki duk da bawai na yarda da hakan bane har cikin raina amma nasan zasu iya don har yau babu daya daga cikin su data taba kallon dana da sunan so ko tace zata dauke shi.
Suma din hakan sukeyi idan suna goyo ba mai yarda kishiya ta taba danta kinga wanan ba zai damay ni ba amma ace an hada da asiri shine illar ai.
Tace wanan aiba bakon abu bane dama ba yau aka fara yin shi ba a duniya magana daya anan shine kafin ku koma sai a samu tsari abawa yaran dake ma sai kusha.
Gabana naji ya soma faduwa abinda ban so ban kauna naki jinin naji aikin sihiri yau gashi ya hau kaina in har ina son kaina da lafiya dole ne kuma nayi din don rigar zamani ne muke ciki dole ka nema kasaka kaima a zauna lafiya.
Bandaiyi wa kowa sheri da yardan ubangiji haka kuma ina fatan duk wace ta nufe ni dashi ya koma kanta.
Sai naji Innata tace dani aiki godewa Allah da yake kare ki in bashiba dama shiga irin wanan wurin kai tsaye ai kasada ne babba sai mutum ya shirya yakan shiga.
Amma ke in ma don Attu da ta dan kaiki kafin tarewan ki ba ai haka zaki shiga masu kara zube amma kinga da yake Allah yana son ki sai yake kare ki daga kaidin su.
Nace yanzu ni inna gaskiya hankalina ya daga sosai in da zai sauwaka min da zaifi min sauki wallahi a zauna lafiya.
Tace akul na karajin wanan mugun shawaran a bakin ki akwai may yine in ba Allah ba da sukeyi ba Allah ne ke tsare muna ke ba.
Kedai ki dage ga ibadan ki roki ubangijin ki sauki ga komai Allah yana tare da bayin sa ko yaushe suma din masu yi Allah ya shirye su su daina su gane gaskiya nace Amin .
Satin mu daya yadda aka bani sai ga daddy da kan shi wanan karon yazo dauka na nasan ba komai yasa yazo ba yazo yaji ko na fada a gida halin da muke ciki.
Amma sai yaga an tare shi da mutunci ba wanda ya nuna mai yasan da wani abu muna batun fitowa ne ya so ganawa da maigari.
Bai boye mai komai ba na halin da muke ciki maigari ya nuna bai san maganan ba don ban fada masu komai ba.
Yace ai baba Rahama yarinyace mai kaifin tunane da sanin ya kamata duk tsawon lokacin nan ban tsanmani ta fadawa wani wanan matsalan ba.
Maigari yace hakan yana da kyau boye sirin ka ga jama, a don yanzu duniya ba abin yarda bane sam.
Yanzu gashi kazo a makare da akwai inda zamu dan tafi dakai nan gaba damu ne kadan a kwa wurin wani amin na da zamu mutumin masunci ne yana da wanan makarin ina ganin insha Allahu.
Ni dai muna jiran ace mu fito sai mukaji wai sun fita da baba maigari haka yasa na samu daman fita da sauri naje naga Suwaiba da Rukaiyya inda muka dawo tare da ita Rukaiyya din don taga tshin mu.
Sun kai awa uku suka dawo saida sukai sallah akace mu fito mu wuce nai sallama da mutane yan uwa da abokan arziki muka kama hanya zuwa
********* ********* *********
Mun iso kano bayan sallah la, asar nayi mamaki kwarai dana samu anty ta aje muna abinci don tasan da zuwan mu lokacin .
Har part dina ta bayar da abincin aka kawo muna saida mukai sallah muka zauna mukaci abincin na hada dan tsaraban da zan basu na aika masu dashi suka aiko min da godiya.
Sai da nai sallah magariba da ishai na shiga wurin anty mu gaisa take cewa dani ai har tana batun zuwa gaida mu ashe na taso sai naji nauyi da kunya ya rufe ni don ba haka na saba yi mata ba idan na dawo da baya.
Nace mun dawo Abba baya jin dadin jikin shi ne yana fama da zawayin hakaro tace kai haban nawa banawa bana yana son aci naman layya dashi ke nan ashe.
Na zauna tana tambayana mutanen gida nace suna lafiya tace miko min baban nawa na ganshi injin dai kina kula min
Showing 330001 words to 333000 words out of 456145 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111 Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153