za ai magana da ita.
Tana jin haka tafito waje da sauri ta saba hijjab din ta zuwa waje don amsa kiran don tasa daga wajen mu ne kiran .
Tana dauka taji muryana ina cewa inna ta, kuna lafiya tai murmushi ta kawar da kunya tana cewa kwana biyu ina kuka shige ne ke da maman ki?
Nan muka shiga gaisawa tana tambayana labari inda nake nan na shiga labarta mata irin kulawan da anty ke bani da kuma makarantan da ta sakani yanzu ina zuwa.
Tace yarinya babu zancen aure gare ki ke nan ko may babakin ba zai yi fada akan hakan ba kike gani ko may ?
Nace Inna kwantar da hankalim ki zan shigo zan mai bayani yadda zai fahince ni insha Allahu.
Sai naji tace yaushe ne zaki zo garin ne ?
Nace sai munyi hutu Inna nan da wata daya da kwanaki insha Allahu anty tace zamu shigo.
Sai naji tayi shiru nake cewa inna ko akwai wani abin ne dama ?
Tace tau dama dai naso in fada maki ne cewa zan yi aure jibi insha Allahu ranan jumma, an nan mai zuwa.
Aure inna gidan baba zaki koma ko ?
Tace a, a wani dai zan aura yarinya ai na fada maki bazan taba komawa wanan gidan ba har abada zaman da akayi ya isa tunda shi baida tacewa a cikin iyalin shi sai abinda mace ta sashi yi yake yi.
Inna ta wa zaki aura yanzu na tambaya cikin kaguwa da son jin sabon mijin da zata aura din indai ba kuma wani wahalan zata kara fadawa ciki ba again.
Tace ba wani bane yarinya sai maigari da ya aiko Liman cewa yana so na da aure ni kuma naga banda zabi a kan hakan sai dai na yarda kawai.
Shiru nayi ina sauraren ta har tagama bayanin ta tare da tambaya na ko may na gani a takaice na bata amsa da cewa Allah yasa haka shine alheri cikin rashin dadin rai gare ni.
Tace idan hakan bai maki ba ai sai a fasa ko nace haba inna ni na isa na hanaki ra, ayin ki kawai dai ni tausayin babana ne kawai nake ji.
Hmm inna tace tace kawai dai na fahince ki yarinya kina kishin mahaifinki ne dana rabu dashi ko ?
Na basar da maganan ta nace sai ki kwashi kayan na da suke aje ke nan idan da gyara sai a gyara maki kiyi amfani dasu gaba daya.
Tace idan na kwasa kika tashi aure ke kuma fa yaya za, ayi nace Allah ya zai rufa asiri inna kedai yanzu fara amfani da wanan tunda nasan baki shiyawa aure ba a yanzu zuwa yayi maki a bazata kawai.
Tace to na gode Allah ya rufa asiri duniya da lahira don Allah yarinya ki kula da rayuwan ki a can kada kiyi watsi da tarbiyan ki da kike dashi a nan duk inda kike ki kama mutuncin kan ki .
Nace da ita insha Allahu inna zanyi kamar yadda kike so inna take cewa dani in gayar mata da mama da anty nayi mata kuma godiya akan na nace zasuki Inna Allah ya bada zaman lafiya.
Mukai sallama ta mayar da wayan gurin maishi nikuma na shiga wani yanayin tunane nake tuna wani irin zama inna zatayi kuma a gidan maigari idan ta shiga don gidan shima yana da dan jama, a sosai a ciki.
Nan dai anty ta fahinci tunda nai wayan nan banda sukuni a tare dani tun lokacin.
Batai min magana ba sai da dare take tambayana may ke faruwa taga tunda yamma jikina yai sanyi danai waya ko ance ne na dawo gida ?
Nai murmushi nace ba haka na bane anty wai inna ce zatai aure jibi nan take fada min tace ikon Allah Rama inna zatai aure kuma ?
Nace fuska a cushe wai haka tace dani da muke wayan, to ke shi kikewa fushi haka Rama ko may , ?
Nace anty ni naso ace Inna ta koma gidsn mune wallahi da ta koma tayi hakkuri tunda ta saba da halinsu.
Amma inda zata ai bata san halinsu ba can gasu da yara su ma a gidan kuma manya dasu.
Wa zata aura ne yanzu nace wsi maigari zata aura tace duk da ban taba jin wani abin asha ba a kan shi tun tasowa na.
To aike rama wannan abin alheri ne zata auri maigari dungurun gun kai haba anty don yana mai gari halin shi dana iyalin shi fa a cikin gida.
Muryan mamane ke cewa wazai auri maigari kuma Rahama nace wai Inna ta ne zata auri maigarin mu jibin nan mama.
Kaikai aiko wanan abin yayi dadi wallahi wani hani ga bawa akace baiwa yanzu Asiya maigari zata aura kaji hukunci Allah kuma ko daga shi har iyalin shi nasan insha Allahu zaman su zaiyi dadi ba irin wancan zaman wahalan da tayi ba a gidan ku na zama karkashin kishiya ko yaushe ba miji ba.
Nan dai take kawo halin iyalin maigari wanda jin hakan ya dan sa hankalina ya dan kwanta sosai ga yadda na shiga damuwa da farko.
Ranan Jumma,a sai ji kawai mutane sukayi a massalaci ana sanarwa a dakata za, a daura wa maigari aure yanzu.
Kowa yai mamaki don basu da labarin maigari na neman aure a garin sai da aka fara gabatarwa ne mutane suka fahinci da Inna ne aka daura mashi aure kaji auren manya ba sai ansan da nema ba sai dai aji daurin aure kawai.
Take labari ya karade gari mama na gyaran dawan da zatai madu abincin dare sai ga larai kawar ta tazo da labarin .
Nan suka shiga gulma akai suna fafin dama kwadai yasa ta watsar da auren ta don taje hangen nisa gashi ta fada gidan mai gari ai taje su kulu matan maigari sunan nan ta samay su.
Lairai tace amma dai kin san taci aba dai ko a hankan gidan maigari fa akwai hutu lauranta kuma akwai ci da sha ba kamar ku nan ba.
Sheri kuma zakiyi min inji mama tace ai ba sheri bane sai gaskiya ina zaki taba hada auren maigari dana gidan ku laurantu kuma ko acan fa amarya take.
Gashi duk matan shi sun girmay mata ga shekaru kinga ko yanzu amarya take shatafa kuma ta bar maki sudaden mijin ki ki jika kisha ke kadai yadda kike so.
Larai nagane dai magana kika zo sola min ba wai gulma ya kawo ki ba tace ai babu soka magana anan sai gaskiya ke dama maigarin kika cuna ma Lawisa ai da yafi mata auren wanan tsohon da takeyi sai aukin susuka kawai kamar bajimi.
Ran mama duk a hasale yake dama basu haduwa gulman su basuyi fada ba tsakanin su haka dai suka rabu baram baram.
Da dare da baba ya dawo mama ta tare shi da zancen auren inna da maigari.
Ran baba yai matukar baci da jin wanan labarin yace amma ko maigari bai kyauta min ba yanzu haka zai min na saki matana ina kokarin mayar da ita sai ya aure ta.
Nan dai mama taita zuga shi wai sai ya kwace diyan shi kada ya yarda aje agola dasu gidan wani yace ai haka za, ayi bazan yarda aje min da yarana yawon agolan gidan masu gari ba.
Mama tace ita dai Rahama ka barta can gurin yawon duniya ke nan kuma ko ?
Kamar yaya yawon duniya kuma shi akace maki tanayi a can inda take yanzu ne ?
Idan ba yawon duniya taje yi ba gidan yan uwanka take ko na uwar ta da zata je ta share guri ta zauna can ba labarin komai tare dasu.
Shiru baba yayi yashiga nazarin maganganun da mama ke zuga shi akai bai sake tanka mata ba don ran shi yai kololuwan baci sosai a lokacin.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA HAKKIN AMANA YANA KAN KI YAR UWA DON AMANA NE ALLAH NA GANIN KI YAR UWA, , ,

24
Monday mun koma makaranta bayan an gama shagalin buki na watsar da zancen auren Inna da na saka a raina har yaso ya damay ni sosai.
Banda kawa ko daya ni kadai ce ke al, amari na don babu wacce na sani a school din balle na je na daukowa kaina wahala.
Idan ban class ina massalaci naje yin sallah sai kuma idan anzo daukana da yamma zan koma gida.
Da zaran na dawo banda wani time sai zancen aikin gida girki da gyaran shiyan mu.
Sai ma wani lokaci kowa yayi barci an barni ina aiki ni kadai don gudun kada na makara washefgari ke sa sai na rarage aiyukana nake kwantawa.
Gashi yanzu na san gari wani lokaci ni anty take aike gurin yan uwanta ko abokan ta ban ta samun matsala da kowa nata ba sai mutun daya daga cikin sisters din ta da tace dani don Allah idan mijinta yana gida anty ta daina aiko ni.
A gabana ta fadawa anty hakan sai naji anty tayi dariya tace ina da gaskiya na sister in bake ba wa zai aje wanan zukekiyar budurwa haka a gidan shi mijin shi na gani kullun ya kyaleta.
Don dai daddy su Amira ba irin mijina bane aida yanzu ya fara kai mata hari bada sanin ki ba na dauka zanga canji kan wanan maganan da sister tayi a kaina amma sai naga anty ko a jikin ta ita.
Haka yasa naiwa kaina kiyamallaini idan daddy yana gari bana yarda mu hadu dashi ta ko ina ina part din mu kumshe sai ko idan nafito zuwa school anty bata taba hankalta da hakan da nakeyi ba don ita zuciyar ta fes yake akaina.
Wasa, wasa sai da Zulfa ta kwashe wata daya agidan su mama Zulai ta ga abin bana wasa bane ta nemi sulhu da kanta don da farko takafe sai daddy yaje biko da kan shi ta fada mai son ranta Zulfa zata dawo dakin ta.
Sai taga sam diyar ta bata gaban shi idan sun tambaya sai dai taji ai yazo ya tafi ko ace ai baya ma kasan sam ga baki daya.
Wanan karon ma basu kasan shida Hindatu sun tafi kasashen turawa don sun kai sati da tafiya gaba daya yaran suna gurin mu a gida.
Hindatu bataso barin yarta hannun anty ba amma daddy ya kafe ga haka shine ra, ayin shi sai dai idan zata fasa tafiyan ne ga baki daya dole ba yadda zatayi ta bar yarinyar a hannun anty.
Mama zulai ta je gidan hajiyan su daddy inda hajiyan ta kira yan uwasu kaf suka hadu a gidan ta sannan aka aika kiran mama Laraba.
Tana zuwa ta fahinci zance ne akan yaransu zasu aiwatar a lokacin, da farko mama zulai ta soma yabawa mama Laraba magana masu zafi sai da hajiyan ta tsawata mata.
Take cewa idan har sulhu kikazo nema ki bari ai magana na fahinta a tsakanin ku don wanan abin da kuka dauko hanya ne na koyawa yaran mu wani mugun akida a tsakanin su.
Aure dai ne Allah ya hada a tsakanin yaran mu sai hakkuri da junan mu yanzu kada ku bari shedan ya rude ku mu bata zumuncin mu.
Gaskiya wanan karon hajiya ta turza don bata tsamaci jin haka ba daga hajiya din.
Dole ta sasauta kalamin ta ga yar uwarta nan mama Laraba take cewa Zulai ni banda abincewa don ko a haka alhamdullahi don zumunci yai min rana banda da namiji babba kuma banda arziki amma dan yar uwana ya gwada min ni wata abuce mai daraja a cikin ku.
Ban sa Alhaji karami ya kori yarki a gidan auren ta ba asalima ni baiji wanan magana daga bakina ba don dashi da Hindatu duk diya nane.
Yadda zan dauki Alhajin haka zan dauki hindatu a matsayi ya a gare ni idan naga tayi abinda ba daidai ba na fada mata ta gyara don goben ta.
Cin mutuncin da kukai min keda yar ki daga gyara kayan ka bai taba damuna ba a raina don ni na tsaya a matsayin da Allah ya tsayar dani a cikin na bandashi.
Kuma na dade ina bin shi Alhaji karami yayi hakkuri ya dawo da matar shi dakin shi a wuce gurin wanan dalilin yasa yanzu ma ya daina zuwa gurina ya kuma ko daina kirana ga waya yadda yake min kullun.
Don haka idan har kuna zargina akan wanan zancen kun dai dauki Alhakina ne kawai shi Alhaji karami baya manta mafari ne shiya sa yai min wanan gatan da kuke gani kamar asiri ne mashi na jaye shi dafa alaka da kowance daga cikin ku don har wasun ku na cewa na asirce ce shi harda ita yaya ina kokarin rabawa da dan ta.
Wanda abin ko kusa ba hakana bane shakuwan dake tsakani na dashine tun yana dan karamin shi yakai mu ga haka yanzu ada ai bai wanka ya bushe yana gurina kuma kowan ku ta sani anan.
Sai yanzu ne da ya zama wani abu kuma zan mai asiri na jaye shi daga mahaifan shi komay ?
Muryan mijin hajuya ne baban daddy ya leko falin yana cewa yin haka ma babban kuskure ne gare ku gaba dayan ku nan wa ya gwada wa Alhaji shi dan shi a baya kamar yadda laraba ta gwada mai.
Laraba zata iyayiwa Alhaji laru da kudin ta ba tare da mu nan mun sani ba sai daga baya mu samu labarin hakan a furin shi ko a wani wajen sai yanzu da Allah ya maidashi mutum ne kuke son ku nuna mata bata isa ba da danta.
Kinyi kuskure Zulai gurin nuna son kanki dakikayi wa yar uwarki idan dashi ba jarumin maza bane yai maki haka kina ganin diyan ki kaf akwai wanda zai kara kallon daya daga cikin ku nan da daraja a idon shi.
Sai sauran uwayen dake zaune suka ce hakane fa Alhaji gaskiya anyi babban kuskure sai dai Allah ya kyauta kawai za, a ce a gyara gaba.
Alhaji yace uhum haka nake sin ji don fa abinda kukayi ba abin alheri ba ne don takai har yarki ta fara kyamatar shigan ku gidan dan ku duk kun san da hahakan.
Nan sauran suka shiga fadin albarkacin bakin su akan haka mama zulai ta kwatakes ba bakin magana don babu gaskiya.
Karshe dai Alhajin su dady ne ya shirya tsakanin tare da kara fahintar dasu karfin zumunci da kuma sakaci da zumunci sukai godiya aka fahinci juna yasa akakira Zulfa dake dakin hajiya tana sauraren su tun farko ta roki iyayyen nata gafara kamar yadda mijin ta yake bukata haka akayi ta tsugunba tsakiyan su tace tasan tayi kuskure don Allah a yafe mata sukai mata dan nasiha tai godiya tamike tabarsu a gurin.
Sai lokacin Alhaji yace tau yanzu laraba aiki ya rage naki don kin san halin dakin da tauri tsiya sai kikirashi don yaji da kunnuwan shi gaku a hade an sulhunta asamu yarinyan nan ta koma dakin ta hakana.
Shiya kira daddy da wayan shi ya na ganin kiran Alhajin ya dauka lokacin suna tare da hindatu kwance saman gado tana dan shafan shi a hankali kiran yashigo mai.
Da sauri ya daga yana mai gaida mahaifin nashi cikin ladabi nan yake ce mai bani ke magana da kai ba uwar ka ce Laraba da yan uwan ta gasu ya mikawa mama laraba wayan takarba da sallama.
Saida ta tambaye shi uaya suke can yace Alhamdullahi tace ya gaida hindatu din nan take cewa Alhaji karami zancen matarka zulfame gamu nan gaba dayan mu mun hadu a gidan yaya kan maganan don Allah muna mai baka hakkuri komai ya wuce tsakani ka maida matar ka dakin ta hakana don Allah.
Yace mama idan fa zulfa da mama basu baki hakkuri ba kan cin zarafin da sukai maki wallahi bazan hakkura ba.
Tace haba dana komai ya wuce nace ma gamuna gaba dayan mu yaya da Alhaji sun sulhunta komai a tsakanin mu ai.
Yace to shike nan ta karbi makullin ta a hannun Saade zan fada mata inda na aje mata su ta koma kafin na dawo.
Mama Zulai bataso ace diyar ta takoma ba haka zikau sai yazo yaje inda suke amma jin amsan shi yasa tasan ba inda zai tafi ya gama maganan shi ke nan .
Mama tai mashi godiya tare da mai nasiha ya tai hakkuri da iyalin shi don mata sai hakkuri komai girman su sukai sallama ya kashe wayan kowa najin yadda sukayi ko banza mama lataba ta kara wankuwa a zukatan masu zargin ta a cikin su.
Nan Alhajin su daddy yace gobe yake so mama zulai ta mayar da zulfa dakinta don yau yamma yayi shiyasa ba zau ce ta koma yau din ba gidan ta.
Akai sallama bayan yai wa kowan su alheri suka watse kowa ta kama gaban ta cikin jin dadin samun sulhu a tsakanin su yanzu.
Hindatu dake kwance a gefen mijinta tana jin komai ranta ya baci don dai ita bataso dawowan Zulfa ba don zaman kishi ke nan bataki ace anbarta daga ita sai shi ba agidan duk sauran su watse ba.
Balle wanan yanayin jin dadin da suke ciki a tafiyan da sukayi ji take dama a kullun su kasance a haka tsakanin su dayafi mata
Showing 87001 words to 90000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30 Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153