shirya tare da daukan abincin daddy na kai falon na jera na koma ciki don na tsawata wa yaran da kada suyi fada kin san yara ba a raba su da fada a tsakanin su.
Ban jima ba na dawo falon tun kan na karasa na hango kafanta kwance a saman dogon kujera shi kuma yana zaune a kasa yana dubar wayan shi.
Mamakine ya kama ni haka dai na daure na shiga gun shi don dama bayan gani da ido naji sauran na korafin hakan da ita.
Ban zauna ba sai na shige bedroom har na gama abinda nake a ciki na kwanta daddy bai shigo dakin ba kuma ina jin muryan ta.
Can har na fara barci naji shigowan shi dakin yana fadin kwanciya kikayi ashe ban tankashi ba naji ya shiga bathroom don yai wanka.
Tsam na mike zaune na hado komai nawa na bar mashi part din na koma wurina na saka sakata na rufe har dakina saida na saka sakata a cikin shi na kwanta a gefen diyana dake kwance.
Da safe ina shafa mai sai gashi ya shigo dakin yana saye daga shi sai jallabiya a jikin shi.
Fuskan shi babu walwala a cikin sa yake cewa dani a wani dalili jiya kika bar wueina kika dawo nan bada sani na ba ?
Nace au tambayana ma kakeyi daddy ai na ga banice dakai ba shiyasa nabarwa mai girki wuri taci gaba da aikin ta.
Yake cewa dani wanan wani irin magana ce haka kuma wacece mai girkin ban sani ba ?
Nace wacce tazo debe ma kewa kasan ni ban iya ba wallahi daddy in dai don ka muzantani akan wanan yarinyar ne ba zan kara lamunta ba a gidan nan anyi na farko anyi na karshe.
Bana shiga hakkin kowa daga cikin matan ka don haka bana son wata ta shiga min itama.
Yo itama ta san yin hakan waye ba zai ita ba idan yaso don haka ta kama kan ta dani tun kan mu karasa saka kafan wando daya da ita a gidan nan.
Yace yanzu dan zaman da tayi shine matsala kuma bata fada kowa da zai debe mata kewa tare da ita shiyasa take shigowa guna.
Auto hakane ashe to shike nan ba hira ba har kwanan ma ku dinga yi a tare indai don ta Rahama ne na yafe aje akarata can.
Dama na dade da sanin cewa baki damu dani ba Rahama ba sai kin fada ba ai nace ban damu ba kuma ba zan taba damuwa da abinda bai damu da nawa damuwan ba.
Yanzu dai muje ki hada min ruwan wanka nace ai sai dai ita data fini muhinmanci ta karasa wanan duty din amma ba dai ni Rahama ba kuma wallahi.
Yace kina son ki zarga min sheri ne ko may Rahama kike shirin yi ga maganar ki ?
Wallahi ba sheri ga wanan maganan ni ba zan dauki a wullakan tani a kan wata ba tunda ban wa kowa haka ba ina iya kokarina wurin tsare doka ga kowa a gidan nan.
Don may zaka zauna karamar yarinya tana son juya ka ka fada ga halaka da saboda tana takama ta iya yin kissa da kisisina watake zaton bai iya hakan ba ne.
Don haka kaje dana zauna ka dinga wullakantani a gabanta gara na yafe na san ban jiba ban gani ba ku karata can kaida ita yafi mun sauki.
Kara dan step yayi daga inda yake tare da fadin hummm sam ni ban dauki wanan abin a wani abuba a rayuwa na amma kowan ku yai min wanan korafin kan hakan .
Duk macen da tasan darajan kan ta ai zata gujewa shiga hakkin wanj kada itama ai mata hakan watarana.
Ba komai bane ka nuna mata cewa ita din tafimu daraja da kima a gunka shiyasa take ganin tafi kowa ne a gidan nan.
Da sauri ya dan kallo inda nake ranshi ya baci yace Niimar ce tafiku daraja da kima a gurina komay ?
Tafimu mana tunda a gabana kuma gaban ta ka shanya ni a daki kana zaune tare da ita kada ka taso ranta ya baci.
Murmushi yayi yace kaiyya ita din har ita waye da zata ce tafiku a guna nace ita matar ka mana kuma amaryan da kake diban karfin kurciya a gare ta.
Tsuki yaja ya juya rai a bace yana fadin wanan maganan ke kika san shi ni nasan abinda nakeyi kada ki maidani wani wanda bai san abinda yakeyi ba mana.
Bishin nayi da kallon haushi naci gaba da shirina har na gama na fice tare da yara da nake kaisu wani nursery mai kyau da tsada.
Ban dawo ba sai uku na rana naje gidan Fati na dauko yaran muka tsaya hanya nai masu sayayya su da yan uwansu na doso gida.
Tun a haraban gidan nasa daddy yana gida ban tsaya bin ta nasu ba na kwaso kayan tare da kamo hannun yara na zamu shiga gida.
Sai gashi fitowa daga ciki bin mu yayi da kallo don bai masan yaran sun fara zuwa makaranta ba sai ranan.
Don duk yan uwansu ba a saka su ba tukun niko don fita aiki gashi Aisha bata nan yanzu yasa nakaisu karatu da wuri.
Yaran suka nufe shi nai mai sannu na shige da ledojin dana shigo dasu a hannuna zuwa part dina.
Ina daki naji shigowan shi da yaran wurina wanka nake son shiga don har na fara tubewa suka shigo.
Yaushe ne yaran nan suka fara zuwa makaranta ban sani ba Rahama ?
Yanzu kece mai bugun gaban kan ki a gidan nan kike nufi ko may don ban san may kike son dauka na ba.
Ba wai makaranta na saka su ba saboda Aisha tayi aure isan na fita kuma kada su shiga damuwa yasa nake kaisu day care na wata yar shuwa data bude wurin ana bada kulawa ga yara sosai.
Alright don banda hakki yasa ba a fada min ba aka kai min yara can ko nace dashi kayi hakkuri kawai batare da na sake wani magana ba kuma.
Amma dai kin san yin haka zai kawowa sauran iyayyen yaran zargi ko wani abu ko ?
Nace daddy yanzu shike nan kuma banda right din yiwa yara na komai sai na hada da na wasu komay ?
Nifa wanan irin matsalolin sun fara isata daddy kowa yasan ina aiki yaran kuma suna son kula shiyasa na daure nakaisu can don su samu kulawa a wurin.
Sai yaron yake ja mai hannu yana fadin daddy mun yi karatu alifun ba un da kuma cake muka ci.
Yana fadi yana jan hannun uban nashi ya dan kai kallon shi ga yaron sai yaja su suka fita daga dakin .
Wankana na shiga na fito na tayar da sallah ina gamawa na shirya na fito falo abinci na nema don ina jin yunwa a lokacin.
Na zauna na fara ci ke nan yaran suka dawo sai dai su biyu suka shigo wanan karon.
Zasu zauna nace su bari nai masu wanka don manyan basu dawo ba a lokacin mama ce kawai muke bari a gida helen ta koma kauyen zatai aure itama.
Wanka nai masu na shirya su muka zauna cin abincin tare da su na dan fahinci tun bayan bukin Aisha akwai dan matsala agida namu don kowa yaja baya da dan uwan shi.
Hakan bai wani damuna ba don dama na saba zama a hakan don shirin dama na iya baki ne kawai akeyin sa baikai zuciya ba .
Muna gap da gama cin abincin ne daddy ya shigo falon ya sauya tufafin jikin shi wanan karon duk wanan sintiin da yake na fahince shi na lalashine kawai kan matsalan dake tsakanin mu dashi.
Ban sake fuska ba sai naji yace dani may ye na ganki kuma rai a bace haka dake ?
Nace batare da na dago ba may kuwa zai bata min rai yace har yanzu a kan wanan maganan kikewa fushi haka ko may ?
Wani takaici naji a raina watau shi bai dauki maganan a bakin komai ba ke nan a gunshi.
Takaici duk ya kamani nace fushin may zanyi aini nagama magana ta don na sallama mata kai kuje kuyi tayi can.
Murmushi yayi yace dani Rahama dago kai ki kalleni mu gani idan kin salama wa watani da gaske ?
Ban dago ba ya sake cewa dani dago kanki mana mu hada ido idan da gaske kike zan gani ai.
Kin dagowa nayi don ma ba zan iya ba din don nauyi da kunya ba zai barni ba naji ya sake cewa dani maganan taki iya baki ne ke nan.
Nace don Allah daddy mu bar wanan zancen tunda munyi shi tun safe mun gama banga dalilin dawo da zancen ba kuma.
Shiru yayi nasan kallona yake a lokacin ya dan sauke ajiyan zuciya tare da kara takowa zuwa inda nake naji yace dani Rahama ina son ki sani daga yau bana son irin wanan maganan daga bakin ki a gidan nan.
Laifi akai maki kuma kin fada ya wuce don haka ki tabbatar da zancen ya wuce ke nan ke ma wurin ki.
Bana son ki na bari wani na fahintar halinda muke ciki don a kulun so ake aga wani dan baraka a tsakanin mu.
Nace nasan da hakan amma dole ne na kwaci yancina a gare ka don ina gudun ai mun dariya zai sa na ki fadar ra, ayina ko may ?
Tsaye yayi yana min kallon mamaki na dago kai muka hada ido ya sakar min murmushi na shuumanci.
Nunani yayi da yatsa yana fadin ban taba sanin son da ake min ya kai haka ba sai yau din nan.
Na dan kara kallon shi nace so fa so fa kace yace cikin daga giran shi yes so mana gashi kinga akan yarinya karama kina wanan haukan haka .
Nace ba wai hauka bane ai yarinyar ne da son wuce wuri na fahinci bata da wayo tare da ita ban so shiga shirginta ba amma naga tana son ja danine a gidan nan.
Yace amma shine ke zaki biye mata ku zama daya ko yaushe nace aida ace na biye mata da tuni ta raina kan ta ko a gidan nan.
To naji bani son dai kiyi abinda zai kai ga zubar da mutuncin ki akan ta ki barni da ita ni da na dauko ta ni nasan halin kowan ku kuma.
Don haka wanan maganan abarshi nace an barshi ya wuce sai dai idan an sake baza ai mai kyau ba kan .
Yai min sai ya dawo ya fice sai da yara suka dawo na samu kaina na nufi part din daddy din ina tsaka ga aiki kamar ance na leka window sai na hango zulfa da Niima a tsaye suna ta faman magana a tsigar munafunci murmushi nayi tare da fadin kaico a fili.
Tun wanan ranan na kara kama kaina da wani hafin kai na kishiya bana shiga harkan kowa a gidan nima na kuma lura da cewa ita Niima ta daina wanan tsagerancin da takeyi yanzu ko tanayi ba dai ranan girkina ba kan.
Duk wani kumbiya kumbiyar su na gaiyar tsiya bai damuna don hassada ga mai rabo taki ne gareshi.
Hindatuce nake ga kamar ba a gama sakata cikin shirin ba sosai don itama ta mayar da kan ta gun sana,ar ta.
Wanan halin ba wani bakon alamari bane a gidajen mu tun fil, azal haka ake a gidajen hausawa masu tara mata.
Da zaran anga kamar namiji ya doshi wani wuri ko yana dan tausayawa wata sai kiga saura suna hafin kan karya wanda ko su a tsakanin su ba wani son juna.
Sai a ware dayan ace tunda miji na kulata ko tafi samu a rayuwa a barta a gefe daya wai ala dole sai ta zama borar gida da karfi da yaji.
Sai dai abinda bamu sani ba warw ta a gefe dayan ne zai kara mata kwarjini da fada gun miji.
Nikan a wuri na sai ma hakan yafi mun sauki don babu komai ga wanan irin hadin kan sai makirci da gulma kawai.
Fahintar hakan yasa na gane ni din ke nan wata abune a gidan don haka maganan daddy gaskiya ne bari wasu su fahinci matsalan mu babban jin dadin kowan su ne.
Haka yasa banda lokacin kowan su idan mun hadu dai sai a gaisa a wasance a wurin a wuce .
Mun kai har zamuyi kwanaki mai dan tsawo bamu hadu ba a tsakanin mu sai ma zaman hakan ya fi mun dadi yanzu.
Ranan daddy ya kirani a waya na samay shi a falon shi da safe na saka dogon riga tare da dan gyara fuskana na nufi wurin shi.
Yana zaune ya baza wasu takardu a gaban shi nai mai sannu da aiki ya amsa ba tare da ya dago kan shi ba.
Zama nayi daga gefen shi a kasa bayan na zauna ne ya miko min wasu takardu da akai banding a wuri daya.
Na fara bin takardun da kallo sai na lura takarda ne na shedan wasu aiyuka a ciki.
Sai naji yace ki duba da kyau ki gani takardun yaran kine na gadon su da uwarsu ta bar masu an juya su har sukai haka shine naga ya kamata yanzu na sanar dasu su san komai a kai.
Kwandala ban taba tabawa ba daga ciki tun uwarsu na a raye har zuwa yanzu.
Zan so naji ra, ayin su idan za, a rabane tun yanzu don ita Amira dake shirin aure idan kuma za, a barshi a hakane aita juta masu har nan gaba idan sun kara tasawa gashi nan dai.
Kara bin takardun nayi da kallo na fahinci ba karamin kudi bane a ciki da kaddarori na yaran da suka gada a wurin mahaifiyar su.
Nace Allahu akbar Allah mai hikima da basira buwayi gagara musali Allah mai yin yadda yaso da bayin shi.
Ar, razaku mai azurta bayinsa a yadda yaso ga dukiya haka ga yaran nan amma kuma ya dauke mahaifiyan su a tare dasu.
Ya Allah kabamu ikon tsayawa akan gadkitan ka mu gudanar da rayuwan mu a cikin sauki da kamala kowa da tashi irin kaddaran rayuwa da yake zuwa mashi.
Samun mutum mai gaskiya da adalci irin ka daddy sai an tona a wanan zamanin wanan ba karamin baiwa bane mutum ya rike amana irin haka da wuyan samu a wanan zamanin.
Yace Rahama ba zan taba mantawa da Saade ba a rayuwa don saade mutum ce ta fada a duniya a sanadin ta na samu abubuwan alheri da dama a rayuwana.
Saade ta tafi ne amma tabar min alherin ta a duniya wanda ke kan ki kina daga cikin wanan alherin da ta bar mun.
Dole ne na tausayawa yaranta na kuma godewa Allah da ya rufa min asiri ya hada ni dake kika rike mun su amana tanakar kece mahaifiyar su kika hana su su san maraicin uwa a tare da su.
Rahama yadda kika tausa zuciyar ki ka rike min yara nan shine dalilin da har gobe bana kaunar naji ko naga na sabawa rayuwan ki don kin min abinda ba kowame zai iya wanan ba.
Ban taba ganin banbanci riko ba tsakanin su da diyan ki saima nace kin fi kaunarsu akan diyan ki in ba zuwan su yan biyu ba wanda suma nasan son Saaden ne dani ya jawo kike masu shi.
Don haka banda ma bakin godiya a gareki bani kaidai nai yaki ga hakan ba harda ke da kike bani gudun mawar kan yadda naga kina rikon su haka.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , ,

105
Ban san irin bakin da zanyi magana dashi ba kan wanan abin da daddy yai muna yai muna mana don kamar ni yaiwa hakan.
Ya zama dole na samu daya daga cikin shakikan su na dangin mahaifiyar su bayan mama Altine na fada mata komai sai naga ya kamata kuma na samu wasu don su sani .
Matsala daya ne yanzu shine yan uwan na marigayi tun rasuwan mahaifin nasu kan gidan ya karasa watse masu kowa tashi ta fishe shi suke.
Ko sisi baka sayen su yanzu duk sun wullakanta dan abinda aka bar masu na gado a wurin su.
Karshe dai naga Sadiya ya dace na gani don ita tana da dama mijin ta kuma na da dan abin hannun shi ai.
Tunda ba wai dukiyan za a danka maasu a hannun su ba kawai dai su sani ne cewa ga halin da ake ciki da dukiytan yaran don fita daga zargi.
Labarin dukiyan da sauran matan daddy sukaji ya tayar masu da hankali don sunce basu yarda ba da zancen shi dai wani hadin kaine mukayi a tsakanin mu da daddy don a fitar da wani kaso daga dukiyan shi a inganta rayuwan yaran su kadai don ni na riga da na inhanta na yarana ba sai sun jira want gadon mahaifin su can ba.
Tun Ana kumbiya kumbiya maganar har zancen ya Kai kunnen daddy yaji don yar rashin kunyar matarshi ce to fito mai da zancen gaban shi.
Abin
Showing 429001 words to 432000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144 Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153