a gabana na fahinci yana nufin na bude nagani ne ai kuwa na mike na jawo kayan kaya ne ciki da gani tsaraba ne muka samu a ciki.
Lafaya ne da kuma atamfofi irin na matan Sudan masu kyau da tsada sai kayan yaran shi suma zubin na yaran sudan ne.
Nai mamaki kwarai don daddy ba ma, abucin yo muna tsarabq bane idan ya tafi tafiya na fahinci hakane tun ban shiga gidan da sunan aure ba a gareshi.
Don dan dama idan yai tafiya da mace zai bata kudi yace tai tsaraba idan taga dama amma shi baya sayowa ko da yara tsaraba idan yai tafiya.
Sai na fahinci duk yadda akayi akwai matsala ne gayin haka a gareshi haka yasa ya daina sayo kayan tsaraba a bangaren shi don kwanciyan hankalin shi.
Nace ai mu sun goga muna tsiya yau sai gashi zamana a nan tare dashi ya sayo muna tsaraba sai abin yabani mamaki sosai.
Kayan sun min kyau jira jake ya gama waya naji ba asin kan kayan nan dai na diga daga kayan ina yaba kyawon su a raina don har baba sai da ya samu tsaraban har hula da takalma da su falmara irin na yayan larabawan sudan din.
Yana gama wayan kuma aka sake kiran shi ashe Zulface tana mashi sannu da dawowa har take tambayan shi yaushe zai shigo kano ne ?
Yace da ita sai na huta ko akwai matsala ne tace ai ba a rasa ba don so nike kazo sai a zauna tsakani da matan ka fada masu motar daka aje don zuwa makarantar yara na kowa da kowa ne bai na diyan su ba kawai don sai a wuce abar min ya ba a dauke ta ba.
Yace haba Zulfa har yaushe na dawo da za, a tare ni da wani korafi haka tace na sani abin ne ya soma isa na wallahi shiyasa nai magana.
Yace to sai ajirani nazo naji matsala may yake kawo hakan ne kuma sukai sallama ba tare daya fada mata ranan da zai shigo ba din.
Ya kashe yana cewa kai bisimillahi zasu soma ke nan ace mata ba zaman lafiya kullun da sabon fitinan da za, a tsiro ma a gida don bakin fitinar tsiya.
Lokacin nai magana nace daddy ai kaji abinda ta fada tunda ko kaji tai magana akwai abinda akayi mata ne kan hakan.
Yakamata a duba agani inda matsalan yake don a gyara fitina ba dadi wallahi ni dai yanzu Allah ya rufa min asiri na dan ketare wanan tunkuna kagin mu koma kuma a dasa inda aka tsaya a baya.
Yace ku koma ina kina ganin akwai inda zaki koma ne kuma can sai dai idan ni na bar garin nan da zama ko zaku koma can yanzu yadda na san dadin zama da mace una zan iya zama kuma ni kadai.
Nace to amma daddy kasan hakan ba mai yuyuwa bane tunda bani kadai bace muna da yawa dole ne kuma a raba zuwa nan din watarana don bazan tabbata nan ni kadai ba.
Yace a naki tsarin ke nan amma ni kan ai nasan abinda zai min kyau ba sai wani ya tsara min ga yadda zan yi ba agidana.
Kawar da zancen nayi ta hanyan tambayan shi cewa daddy naga kaya gasu da kyau kuma sosai yace bakece da zan tafi kikace sai kunga tsaraban Niger ba ?
Naso na sayo maki sarka sai dai ance na bari idan na tafi Dubai anfi samun na kwarai a can .
Godiya nafara yi sai kuma nake cewa kayan sun hau a yadda muke idan kowan mu ya cire guda guda ina ga uku zasu saura.
Yace ban yo tsaraba da wani ba amma idan kinga zaki basu ba laifi ga hakan duk fitina da akayi ke kika jawo shi.
Nace ba matsala ai hakki ne akan ka dadi nan na zaba na ware namu yana dai kallona nace Amira ma ya kamata ace ta samu a ciki tunda sun hau.
Yanzu aigaki gasu sauran biyun yace sai ke ki dauka don dama ni ake na sayo su duk don ban son zancen na wance yafi kyau da haske nace ba komai ba dai ka sayo ba ladan ka naga Allah ai.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON ONLINE NOVEL NE, , , , , , ,
70
Satin daddy uku da dawowa daga sudan ya shirya zai tafi kano sai dai kafin lokacin sai da yasha korafi a wurin matan shi na can kan rashin zuwan shi gida da baiyi ba.
Banyi mamakin rashin ganin bai dauki wani kaya ba daga nan daga shi sai wayan shi da laptop din shi kawai ya tafi nai mai rakiya har kofan sai da naga dagawan shi na bar kofan nakoma ciki a raina sai ina jin ba dadi ba ina ruwan saboda miji dadi.
Nan ya yafi ya barmu da kewan shi nasan ko na kirashi ba zan samay shi ba a lokacin don haka naci gaba da harkokina kawai.
Kamar yadda a kwanaki yai muna zuwan bazata suma yau din dai sai ganin shi sukayi ya dawo garin kawai bai sanar dasu zuwan shi ba.
Ya samu matan duk basu gida gaba dayan su duk dako rana yayi a gurin mai gadi yake jin lokacin da kowa ya fita daga gidan.
Su dake hake da zuwan shi su mai korafi sai gashi abin ya juya su yanzu yake jiran dawowan su yaji da izinin wa suka fita daga gidan ne.
Antyna ce tafara dawowa daga unguwa wai ta tafi gidan Hannatu kawar ta ne don sun kwana biyu basu gaisa ba da ita shine yau ta dan leka ta.
Tana dosowa gidan taga motar shi a haraban gidan tace a,a shi wanan ya dawo ne babu ko sanarwa haka yai ma mutane bazata.
Nan dai ta karasa daga ciki tana mamaki sai fada takeyi tana fadin kai akwai dai muna funci a duniya shine Rama ta kasa kirana ta sanar dani don kawai kulin sheri.
Tana zama ta jawo wayan ta nan taga miscall dina har sau biyu dana kirata bata sani ba ashe wayan yana a sillent ne.
Tace muna funci may yasa tun jiya bata fada min da zuwan shi ba ai munyi waya da yamma da ita amma bata sanar dani yau zai shigo ba ai.
Kai maikishiya dai bata mutuwar Allah inji hausawa duk dai ban tsira ba ke nan daga kazafin ta din.
Kamar yadda ta dawo haka ma sauran suka dawo zuwa yamma sun tar da bako a gidan haka suka dinga shiga daya bayan daya suna gaida shi da zuwa ko wace kuma sai ya tambayeta hujjanta na fita bada izinin shi ba da sukayi.
Haka ya rufe masu baki akan korafin da suke son yi mashi kan zancen dake cin su arai kowa taja bakin ta tai shiru da hakan.
Ba fuska ga korafin da kowa ta shirya mai don gudun kada su daukowa kan su fitinan da zai jawo masu matsala a tsakanin su.
Nan dai ya zauna bai fita ba har dare sai da anty ta shirya abincin shi sai abin ya zama mata banbarakwai don bata saba kaiwa ba, bata kuma saba kwaso kayan idan ya gama ci ba.
Sai abubuwan yanzu ya koma mata sabo don jikinta baya son wahala a cikin shi saboda lalabashi takeyi da tayi abu mai wahala yanzu zata kwanta ne.
Wanan abin ya dan sata tuna da Rahama da yanzu tana garin itace zata kai kuma ta kwaso duk da rashin dadin ran da babu a tsakanin su bai sa ta daina taimaka mata ba itace ta gyara part din yadda ya dace amma yanzu gashi dole ita da kanta ke komai don bata farawa ta tura yar aiki tace tai mata wani abin a gurin maigidan.
Sai washe gari ya tafi gidan su, gaida mahaifan shi inda mahaifin shi ke tambayan lafityan mu har lokacin dan dattijon na fama da kan shi da jiki ga tsufa ga ciwo.
Daddy yai murmushi yace suna gaida ku Alhaji mahaifin nashi yace da alama wanan dabaran da kayi yayi tasiri a yadda jikin ka ya nuna a yanzu.
Murmushi daddy yayi ya dan shafi fuskan shi yace gaskiya ne Alhaji nima a yanzu hankalina yafi kwanciya don duk korafin da za, ai min zan iya hade shi saboda haka shine kwanciyan hankalina.
In ko ba haka ba da nufina na kara gyara wanan tsohon gidan nawa sai ita Rahama din ta koma cikin shi da zama.
Saboda may zakai haka ka raba masu gida muryan Hajiyan shi ce dake shigowa kuma maganan da suke a kunnen ta.
Tace ba a aure su aka auro su ni yanzu ba zan yarda ba su kashe min kai ga banza don duk abinda ake ciki a gidan ina da labatin shi sarai.
Har may kaiwa wanan yarinyar wanda su bakai masu shi ba ita har wani dadi taji don sun samay ta karamar yarinya kuma dai tana da biyayya ai da yar bariki ka kwaso masu duk wanan tsiyan bazasu yi shi ba haka don basuga wurin yi ba.
Yarinyar dai ta san ya kamata shi ya kawo haka inda yan zamani ne ai ba zata tsaya dubaiyyan komai ba akan su sai dai a rikice gaba daya agidan.
Kaga sunyiwa kan su ke nan idan rashin mutuncin yaran zamanin nan ai sun fi kowa iya wa don abinda yaran yanzu zasuyi sai ya daure maka kai kai babba.
Yanzun dai wanan hukuncin da ka yanke shine daidai dama sun saba cin kan su sai suyi tayi ai tunda shine aikin su.
Alhaji yace ni Saade ma tafi bani mamaki wallahi yarinya ana murna da halinki na dattako sai ki kwaso shirmay kuma ki saka a cikin harkan.
Dama halinta ne kune baku ganewa don shiru shirun mutum mugune tanayi tana nokewa kamar batayi ba.
Sun dauki lokaci yana hira da mahaifan nashi daga karshe yai masu sallama ya bar gidan tare da basu alheri irin yadda ya saba basu kullun idan ya dawo.
Gidan Bashir ya wuce daga nan don sunyi waya zasu hadu dama dashi din bashir na ganin shi yace kai mutumina anya ba wani injin Rahama ta turaka ba wanan irin fresh haka may ye sirin hakan ne wai ?
Murmushin shi yayi kawai yace da bashir din ka faye gulma wallahi kowa ya gani yai shiru sai kaine mai magana.
Ai kaima kasan ko may ye sirin shine kwanciyan hankali banda wani zullumi a yanzu da zan shigo gidana dashi.
Sai dai a tare ni ana haba haba dani kamar wani dan baby karami ba a yarda raina ya baci ko a fada min bakar magana da zai sa raina baci.
Wallahi bashir yanzu na kara fahintar halin yarinyar nan sosai dan zaman da mukayi da ita din nan mu kadai a can.
Saade bata san tayi sakaci babba ba sai da ta zubarda mutuncin ta akan yarinyar da ta yarda da imanin ta har tai shaawan hada taraiyan mu da ita sai daga baya kuma wai abin ya koma mata ciki kuma.
Banda wani matsalan da zance gashi akan wanan yarinyar don hakkirin yarinyar ya baci sosai fiye da tsanmanin ka.
Yace to dama ai abinda muke fata ke nan a samu gayin haka Alhamdullahi kuma tunda an samu din gashi a zahiri kuma mun gani ai.
Don wallahi gaba daya ka canza kayi wani fresh dakai Allah ko, daddy yace ai hindatu naga tana so magana amma bataga fuskan hakan ba sai cewa take wai indai an cuce su Allah yana gani.
Bashir may na ajewa Rahama wanda su nan ban aje masu shi ba ban taba ba yarinyar nan wani abinda ban basu ba a rayuwana yanzu haka tsaraban da tace na sayo mata na Sudan nasa matar kamal ta sayo mata saids ta raba shi tace akawo masu har Amira sai da taba daga ciki.
Yace kaga ma na manta ban basu ba balle kuma naji may za a ce akan kayan don nasan sai sunyi korafin shi kan.
A daiyi hakkuri mace ko daya ce sai hakkuri da halinta balle kai daka cika sunnan ma,aikin Allah kai hudu gaba daya.
Yace aiko nasan na cika sunna don ina ji a jikina wallahi mata halin su sai su wallahi bashir wani lokaci har nakan ji na barsu na huta gaba dayan su zaifi min alheri wallahi.
A, a kada kai haka please ai sai duniya ta zage ka ma gayin hakan don ba za, a ga laifin su ba sai naka don nasu boyewa zaiyi.
Kuma in kai haka ai dole wasu kuma zaka auro tunda ka saba zama da mata kuma duk halin su daya ne kana ganin su nan.
Nan dai sukai hira daga karshe ma suka fice zuwa unguwa basu dawo ba sai dare ta sauke bashir ya nufi gidan shi.
Nan dai ya samu an hada mai komai yai wanka ya zauna don yaci abinci Zulfa ta fara shigowa ya mika mata key yace ta kwaso mai kaya a motan shi a baya tana fita hindatu na shigowa falon.
Sun gaisa take cewa dashi yau ya fita ya shige gari haka, sai da ya dan kurbi ruwa ne yake tambayan ta idan na zauna gidan wani abu zakiyi min ne ?
Tace ko ban maka komai ai muma muna son ganin ka ko tunda an jaye muna kai sai lokacin da muka gan ka yanzu a garin nan.
Dama abinda kike so na zauna ke nan a gida kina fada min idan kin isa ai kema mace ce sai ki jayeni yadda aka jani din ko ?
Tace inda kana jayuwa min da na ja din don nafi kowa son yin haka amma muna ji muna gani ana son a fifita wacce tazo bayan mu da karfi da yaji haka ?
Kafin ya bata amsa sai ga zulfa da kaya tashigo falon ta zube su a gefen kujera kamar hafin baki sai ga anty tai sallama ta shigo itama idon ta akan kayan da ta gani a gefen shi.
Sai da ta kai zaune tafara gaida shi ya amsa mata da yaya aiki ya gida tace Alhamdullahi yace ga kayan nan naku ne sai na Amira guda daga ciki sauran na yara ne ku duba ku gani kamar da sunaye a cikin sa.
Da sauri hindatu takai hannu tafara duba kayan tai daidai da wanda aka rubutawa Zulfa a jikin ledan tace wanan Zulfa naga an rubuta mana ?
Sai taa shiga daga sauran da karfi ta dawo akan wanda aka rubutawa zulfa din ta rike tana cewa ni wanan din nake so ai.
Zulfa tace wallahi kinyi kadan don da suna na yazo ko ban so ko shi nake so balle kuma kallan yai daidai da jikina baki.
Tace wallahi baki isa ba yace miko min nan ta miko mashi yace kwaso sauran mun sauran nan ta miko mashi ya duba sunayen yana mika masu kayan.
Sina shiga hannun anty ta sheda rubuta na take ranta ya baci sai da ta bari sun gama haukan su tace da shi wai Rama ne ma ta zaba muna kayan ?
Yace eh itace tace ai a kawo maku din don natane ta aiko maku dashi take wurin yai tsit ba wanda ya sake magana kuma daga cikin su.
Sai tace yanzu Ramane kuma zata zaba muna kaya ko may hakan ke nufi wai ?
Yace amma kinji abindana fada maki ai cewa na ta ne ta aiko maku dashi ko da wani magana ne kuma bayan hakan ?
Zulfa tace aiko mun gode na dade ina son wanan kayan wallahi amma Rahama ta kyauta kuwa.
Zakai wanka ne yanzu ko sai anjima ta tambaye shi don kawar da zancen don ranta yai matukar baci ga hakan da taji.
Yace ko abinci banci ba ai kin gani kuma ita dai zulfa ta hada nata dana yarta tana fadin ai muna godiya ta fice daga falon.
Hindatu kamar bazata tashi ba itama ta dauki nata dana yarta tabar falon cikin fushi tafice a fusace ta barsu nan.
Shiru falon yayi kamar babu kowa a cikin sa ya jawo abinci ya fara ci sai dai yaji yai yawa loma biyu yayi yace wanan yajin fa haka bayan kin san yaji bai bani bashi a cikina ?
Tace yayi yajine miyan ni ban maci naji ba ai balle naji yajin shi yace yayi kyau ya ture abincin gefe ya jawo laptop din shi yana dubawa.
Tai dan jim a wurin can ta mike zata fice batare data dauki kayan da aka basu ba yadan dago kai yana kallonta, yace su kayan da kika bari a nan fa ?
Tace dashi ban ga abinda zanyi dasu bane don ban rako ko wace mace ba zuwa duniya yace sai ki dauki na yarinyar ba matsala ai idan kinyi hakan don dama nasan zakiyi hakan tun can.
Ita dai ne da bata da zuciya har yanzu bata san matsayin ta a gare ki ba take sauran bin ki har tana wani jadda min wanan ne na anty na don zasuyi mata kyau sosai kuma sun fi laushi.
Yanzu bakiji kunya ba agaban wa tan nan kika nuna bakin cikin ki akan Rahama abinda su ya kamata ace sun nuna wai sai ke data
Showing 285001 words to 288000 words out of 456145 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96 Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153