ta bayan gida da yake ta kofan part dina ne a bude na jawo kofan na rufe tare da mashi key don ba haka muka saba ba a part din.
Na shiga nagama shirina nafito nace Fatima ta tashi su rufe kofa kada kuma ta bude don kowa ya rufe tace yau harda su anty sun shige ne ?
Nace eh na samu ta shige ko har sun rufe kodana shigo tace amma dai anty wanan matan kwanakin nan tana da wata manufa dake fa ?
Mumushi nayi kawai nace da ita yanayi ne kawai kin san akwai lokacin da mutum yakan ji ba dadi da kowa.
Tace kai haba dai anty a yadda aka san ku gaskiya dai yanzu akwai wata a kasa dai kawai ni shiyasa ma yanzu na daina zuwa don ko gaida ita naje yi baki yadda take karba min bane wallahi.
Koma dai may ye Fatima Allah ya sauwaka kawai don ba abinda yafi karfin ubangiji ai.
Nai mata sai da safe ta rufo kofan ni kuma na shige wurin maigidan na samu har ya shige ko na rufo nabi bayan shi.
Na samu har yayi wanka dama na hada mai ruwan wanka dana shigo yafito ya shirya ina zaune a bakin gado nayi tagumi da hannu daya.
Rama naji yace na amsa da na,am daddy yace may ke faruwa ne wai tsakanin ki da anty ki ne ?
Na dago kaina da idanuwa na da suka ciko da hawaye nace daddy wallahi babu komai nima ban san may ke faruwa ba haka dai kawai na wayi gari naga canjin yanayi tsakanina da ita na karasa ina fadin yanzu har yaran ma anty ta hana su mamay ni.
Yace kin tabbatar da cewa iyakar abinda kika sani ke nan tsakanin ku nace wallahi Allah daddy ban san naiwa anty wani abuba a iya sani na.
Matar da nake dauka a duniya banda wanda yafi min ita in ba iyayyena ba da suka duka suka haife ni akan may zan yarda na saba mata bayan irin halarcin da tai min a rayuwana.
Yace yayi kyau to ki kwantar da hankalin ki indai kin sa ba wani abu kikai mata ba wanda yakawo sabani haka a tsakanin ku.
Don ina mai jin kunya ace yau wani ya fahinci akwai baraka irin haka a tsakan ku sai ai maku dariya ai.
Iyakar gaskiyan ke nan na fada ma yace zanyi bincike nagano gaskiya amma idan kece baki da gaskiya kada kiji mamaki don zan saba maki don ni bani son karami yana raina babba gaskiya.
Nace dashi nagode daga haka ya jawoni zuwa jikin shi dama a shirye nake da in tare shi don nasha gyara tun daga jikina har kasa na.
Aiko na san ya yaba don gyaran ya tsuma shi fiye da tsanmani na don kamar ya zautu ya nuna min kamar ba gobe duk ya haukace min sai sambatu yake faman sakewa.
Ni dai tunda yace dani na bar zancen a hannun shi ban kara kulawa ba ina dai binta sauda kafa ita kuma tana faman share ni haka na muke tafiyan mu.
Hanani hurda da yaran nata da batason ina yi bai sa na fita batun yaran ba ina da hurda dasu sai dai a cikin taka tsantsan nake komai don mun riga da mun saba dasu ko Allah ne ya hadani dasu ta sanadin su.
Ranan daddy yana shigowa ya hangeta tsaye da kawar ta tayo mata rakiya tun daga nisa ya sheda ko wacece ita.
Mamaki yake may yakawo ta gida shi bayan tsawon wanan dadewan don yasa zaman su da anty ba alheri bane don ba mutumiyar arziki bace ita.
Har ya fito mota matar tana faman washe baki data gan shi yana fitowa baibi ta kan su ba sai anty ke cewa Falmata na gaishe ka fa besty.
Ya juyo fuska a murtuke yana cewa waye hakana sai matar take cewa baka shedeni bane Yusuf naga kamar baka gane ni ba kuma.
Yace fuska babu walwala na gane ki mana ba Falmata Bukar nane dana sani a baya tace nice mana naga kamar baka shedani ba dai ne ?
Yace na shedaki ai daga haka bai tsaya ba ya wuce zuwa part din shi bai tsaya ta kan su ba kuma.
Ashe mutumiyar har yanzu dai halin mijin naki yana nan dai a yadda na san shi wai ni yaushe zai canza ne halan.
Kin dai riga da kin san halin shi don haka may ye damuwar ki ga yan mazan yana nan yadda kika san shi dai sai ma abinda ya karu.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON HAKA CIN AMANA NE BA, A YAFE BA DON ONLINE NOVEL NE, , , ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA DAKE DA ALLAH DON ONLINE NOVEL NE KIN SANI.
60
A daidai wanan lokacin ne na shigo gidan daga school ina gajiye dogon riga ne har kasa nayi rolling da gyalen shi banda fuskana baka ganin komai a jikina.
Da fara,a na fito daga motar ina cewa anty sannu da zuwa ta kwashe ni tun daga sama na har kasa ta watsar kamar bada ita nake ba na gaida su.
Sai dai ba fuska a garesu gaba dayan su sai na koma wata banbarakwai dani haka naja kafana nashige ciki raina yai matukar baci da yadda sukai min din.
Ina shiga na samu yaran sukayo kaina da murnan su nafito wa kowa da tsaraban abinda yakeso suka shiga murna suna jin dadi.
Na dan zauna muka taba hira dasu na dan lokaci har lokacin uwar bata shigo ba tana waje da bakuwar ta.
Bayan shiga na bakuwar tace da anty Saade amma dai ina ganin ha banza wanan yarinyar ta barki ba da har zaki dauki tsaleliyar budurwa haka kibawa mijin ki.
Anty ta nisa tana cewa bari kedai Falmata haka kowa ke fada min niko gaskiya a lokacin hankali na duk ya gushe ne sai ina ganin aiko bayan zan samu mai tallafawa yarana dashi kan sy maigidan yanzu ne fa ta kara murjewa haka da ita ni kaina ai yanzu nasan nayi kasada babba wallahi.
Nan da suka dan taba yan maganganun su na mata a tsakanin su basu su jima ba sukai sallama da junan su bakuwar ta wuce ita kuma ta shigo daga ciki sai dai bata ji dadin irin yarda besty ta ya nunawa bakuwar nata halin ko in kula ba haka a fili bayan ya san tun farko tare suke
Ta sani sarai ba yaune karon farko da yake nunawa falmata halin rashin mutunci irin haka ba tun a shekarun baya haka yake nuna wa Falmata din halin tsiya bata taba damuwa da abinda yake nuna mata din ba sai ma dai ta nuna ai halin shi ne a hakan bata damuwa sam.
Tana shiga ta samu yaran nata faman murna da dan abin da na kawo masu tsaraba wanda hakane dama da wuya na fita ban kawo masu komai ba daga waje.
May ye wanan ta tambaya cikin daure fuska jinior ya karaso inda take yana cewa anty ta sawo min cracas da guguru.
Ta mika hannu tana fadin ban nan yaron yaki ta kwace da karfi daga hannun shi tana cewa shegu kawai ana zuba maku aguma kuna faman hadiya kullun.
Anty tana zaune falon tana faman fada da yaran daddy ya shigo yana tambayan Jinior abinda ya samay shi tace kukan banza yake ji sai Nasir yace daddy mummy ta kwace abinda anty ta sawo muna kullun yanzu idan anty ta sawo muna abu sai mummy ta hana muci.
Dago kai yayi ya kalleta inda take zaune sai faman dakilan wayan ta take hankalinta a kwance.
Yace Saade zakizo kiji kunyan wanan abin da kike wata rana duk tsawon lokacin da kika dauka da yarinyar nan bata cuta maku ba sai yanzu ne zata cuce ki abin ma har da yara kuma ?
A wullakance ta dago tana cewa dashi kishiyace fa Rama kishiya kuma ba abin yarda bace kasani.
Ya huce yace falmata falmata ko to ki sani wallahi nina fada maki idan baki rabu da wanan falmatan ba sai ta kashe ki da ranki kina kallo.
Falmatan ce zata kashe ni kuma besty akan matarka kake mata wanan mugun shedan wai may boyar Allah nan tai maka ne haka baka kaunar ta tun baya.
Yace nina san abinda baki sani ba amma watarana idan Allah ya nuna maki nufinta akan ki.
Allah ma ba zai yarda ba kaida yanzu haushinta kake ji don ta tayar dani daga barcin da nake na dauki amanan kaina dana yara na na dankashi ga kishiya tana cuta na.
Cuta fa kikace Saade ce Rahama ce zata cuta maki din kuma Rahama fa Saade dan Allah ka barni nayi harkan gaba na kowa tashi ta fishe shi kawai.
Ok yayi idan haka kiia zaba wa kan ki amma ni kada ki saka min yara ga shirmay ku ku ruda min su don Allah na rokeki ni dai nasan Rama bazata taba cuta maki ba insha Allahu.
Eh tunda son ta ya rufe maka zuciya ai ba zaka taba ganin laifin ta ba idan tayi maka ai zaka gane amma ni na dawo rakiyan ta ko.
Ya mike yana cewa yayi Allah ya kyauta kin daiji abinda na fada maki ban son a saka min yara cikin wanan shirmay naku idan ke zaki zubar da girman ki akan ta.
Daga haka yaja jiki yabar falon ran shi a bace yana fita ta bishi da kallon takaici don yabi ya wani zauce akan yar karamar yarinya.
Da dare na shirya sai part din anty na samu bata falon zaune sai na shiga daki a zaune take tana cin abinci a kasa ga waya a hannun ta tana kwasan dariya tana cewa shiyasa nake son ki mutumiyar.
Tana ganina ta canza annurin fuskan ta tace Falmata bari zan kira dan anjima kadan.
Wuri na samu na zauna tare da gaida ita ta amsa min da kyat sai dan shiru ya biyo falon kuma ba wanda yai magana a cikin mu.
Sai can na daure ina cewa da ita anty dama wurin ki nazo tace ai gani ko sai nai shiru don ban san may zance da ita ba ma.
Can dai na daure nace dama anty nazo na roke ki ne don Allah idan har nai maki ba daidai bane ki yafe min don Allah don ni ban san abinda nayi ba anty na daiga kin dauki zafi haka dani ne daga sama na karasa cikin kuka.
Tace kinga Rama ni baki min komai ba yanayine kawai ya kawo hakan ko kin manta ke kishiyata ce yanzu kina ganin zaman mu zai ci gaba da dorewa ne cikin amana yadda kike nufi ko may ?
Na dago kai da sauri na kalleta cikin mamaki nace subbahanallahi anty kishiya kuma kikace dani.
Anty nice kuma kishiyar ki a yau ?
Ba kishiya na kike ba Rama yanzu may kike tunda mun hada miji daya dake ai kishi tsakanina dake ya zama dole dama rashin sani ne yakai ni ga hakan da kike gani.
Shiru nayi ina sauraren ta don maganan ta ya daure min kai, bata kuma kara magana ba sai ma sharenin da tayi taci gaba da cin abincin ta hankali kwance.
Ganin ba zata tanka min ba namike ina cewa don Allah dai kiyi hakkuri koma may nai maki don ni ban san laifina ba gareki.
Ta dago kai ta kalleni tace o bakima sani ba ko dama haka duniya ya gada ai kaga mutum a rana ka dauko shi ka sa a innuwa yace kai zai cuta kuma.
Ikon Allah nace a fili anty cuta kuma kada Allah ya kawo ranan da zan cuta maki a rayuwana bake ba ma anty koda wani naki ne a duniya.
Yaushe kuma ai sai dai kada a kara dama tun farko saida aka jiye min haka amma ban san may ya hau kaina ba a lokacin na nace ni sai kin shigo gidan nan ina gani kamar mafita ne hakan gareni ashe guba na daukowa kaina ban sani ba.
Hawaye kasu dumi suka kara zubo min har nakai kofa tace daga yau ma gajiye ban yarda da ita ba don haka idan zata koma wajen ki da zama ne wala,ba,asa ni dai badani ba kuma.
Juyowa nayi nace don Allah anty kiyi hakkuri kada ki bari matsalar nan ya fita waje har wani yaji mu yai muna dariya akai.
Tace ji na nawa kuma tunda yanzun na fahinci komai an dade ana cutana ni ban fahinta ba sai da masu sona suka wayar min da kai nagane.
Anty suka dai cuce mu amma ai wanan ba wayar da kai bane ki dai kara tunane akai kafin ki zurma ciki.
Kada fa kiyi min rashin kunya Rama inma mijin ki ya turoki don kizo ki min maganan banza ki koma ki fada mai ko shi yayi kadan wallahi.
Ni ban ma san kunyi magana dashi ba akai ni zuwan kaina nayi don naji laifina tace to yanzu ai kinji ko ?
Na fice ina kuka daga dakin ita ko ko ajikin ta shedan ya riga yai mata huduba ko ra hau ban tsaya ba dakina na koma na samu su fatima na kallon su hankalin su kwance.
Wayana na dauko na kira innata don ita kadai zan iya fara fadawa wanan matsalan dake batun kunno min kai kuma.
Bayan inna ta gama saurare na tai salati tace kai amma dai mutum abin tsoro ne wallahi idan tana ganin kinci amanan ta ne ga haka ta manta ita ta hada ki da mijin ta ki bar mata gidan mana sai ki bar mata mijin ta.
Nace to inna idan dai naga abin yaci gaba zan bar masu gidan su tunda dama itace ta sakani yin haka dana bata mata gara na barta kowa ya huta.
Washe gari tun sa safe sai ga gajiye ta shigo min da kukan ta wai anty tace ta bar mata part din ta dawo gurina da zama ita an samo mata mai aiki sabuwa don yanzu bata yarda da ita ba kada mu hada mata kai mu cuta mata.
Hankalina ya tashi sosai naso zuwa wurin ta nai mata magana amma kuma sai na tuna yadda mukayi da ita jiya da dare.
Dole na hakkura wanan zance sai daddy dole nan muka zauna da Gajiye da Fatima muna magana akan matsalar.
Gajiye ce ke fadin nifa sai ina ganin wanan matar mai yawan zuwa suna shigewa daki ne ta juyawa hajiya kai a lokaci daya haka ?
Nace zato mukeyi gajiye tun da bamu san may ya kawo wanan matsalar ba haka sai dai biri yai kama da mutum irin yadda matar tun ganina na farko da ita take dauka na da zafi ko kishiyana ce ita ya tsaya hakanan wallahi.
Sai da na tabbatar daddy ya fito zuwa lokacin na saka zullubeben hijabina na nufi gurin shi na samay shi shida hindatu a falon suna karyawa don da alama ma sun gama ko.
Gaidasu mayi da kwana sai shan mur hindatu keyi nasan ba komai bane fushi take may kuma ya kawo ni gurin shi don tasan ni bani shiga idan bani ce da girki ba tunda muka taba samun matsala da ita a baya kan hakan.
Yau baki shiga school din ne yace dani yana goge bakin shi da tisue daya dauka saman table din.
Nace zan shiga dama kai nake jira ka tashi magana nake son muyi da kai yace ok ai gani ko sai na dan kalli inda hindatu take zaune gefen shi.
Yace ko maganan ta siri ne ko kai na kada mai alaman eh sai yai murmushi yace hindatu bamu guri don Allah muyi magana yan mintina.
Take ta canza fuskan ta har yafi na farko tafara kanan magana ciki ciki yace nace ki bamu guri muyi magana tunda har kikaga ta shigo wanan lokacin ai kin san magana ya kawo ta ko ?
Tace nifa ban shiga hakkin mace ba don may za,a shiga min hakkina haka a hana mutum sakewa da mijin shi don Allah dai.
Nace kiyi hakkuri anty ba dadewa zanyi ba nima dole ce takama na shigo maku yanzu din ai.
Ta wani bata rai tafice daga falon tare da rufo kofan ya dago ya kalleni ya sauke ajiyan zuciya yace ina jin ki may ke faruwa ne wai ?
Kuka na fara ina mashi bayani nake cewa ni zan bar gidan tunda na fahinci akaina har wasu zasu shiga matsala irin haka ba zan so na toshewa kowa hanyar samun shi ba ni.
Yake cewa dani amma baki da hankali ko bazaki barni na aiwatar da binciken da nakeyi bane zakizo min da wani zance kuma can na daban.
Nace daddy anty fa cewa tayi wai na cuce ta da yn uwana da sani na na shigo don na yaudare ta ni may nai mata haka har take wanan hasashen haka a kaina.
Koma may ye nace ki barni da ita zamu fahinci juna keda ki ta hakkuri dama haka zama ya gada ai zo mu zauna zo mu saba nace dashi na gode sai na mike tsaye da zumar na fita.
Wani irin jiri ne ya kwashe ni sai naga kamar
Showing 252001 words to 255000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85 Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153