ta ga banza.
Suna barin gurin ya bude mota motar shi suka shiga don ya fahinci magana ce mai muhinmanci ta siri kuma da alama bata son a ji koma may ye din..
Sunan shi ta kira a hankali take cewa da fatan abinda zan fada maka bazai zazzafa ma zuciya ba zaka tausasa zuciyar ka ka fahince ni da kunnen basira.
Yace insha Allahu mama nai maki alkawari koma may ne indai bai sabawa sharia ba zan yi nazari ko na rugumi ko may ye da zuciya daya da hannu bibiyu.
Tace masha Allahu nakuma gode Allah yai maka albarka da fatan samunbalheri ga abinda zamu tatauna din yace amin.
Tace Yusufa ina son na rokeka da farko da kayi hakkuri kuma ka kara hakkuri da iyalin ka kowa da irin rayuwan da Allah ya kaddaro mai dashi.
Yusufa ina son in roke ka ba don nakai ba ko na isa ba sai don hangen alherin da abin zaizo ya haifar daga baya.
Kayi hakkuri bukatar da matar ka ke binka dashi na auren yar uwarta ka yarda ka cika mata burin ta a kan hakan.
Don ni gaskiya Saadatu duk ta sare min gwiwa na da wanan zancen don haka zancen abune na a tsaya a duba bisa ga hujjojin da takawo din.
Kaga Saadatu dai mace baza, ace bata kishin ka bane tanayi kaima ka sani abinda manufan ta ya hango ne sai an daure za a hango shi din.
Sannan kuma aure ne take kokarin kullawa aure kuma kowa yasani sunnan ma, aikine sallalahu Alaihim wassalam.
Bai kamata ki daukan shawaran ta ba tunda itace da kanta ta bukaci da ai haka din baiwa kaine ka bijiro mata da zancen ba.
Balle tace anyi mata butulci ko wani abin cin fuska da zarafi, tazo ta mutu din da take ikirari kazo kana da ka sanin rashin cika mata burin ta tun tana raye.
Ka ga idan abin yai dadi ko bayan ta zata sha addua ga wanan hadin da tayi tsakanin ka da yarinyar nan.
Idan ma bata mutum ba dai itace ta bukaci yin hakan da kanta da bakin ta ba wai wani ya tilasta mata yin hakan ba ita ta nema da kan ta.
Tazo din ta mutu yaranta dakai da take ganin zasu iya fadawa wani hali kazo kana kukan rashin yin haka daga baya.
Jikin shi ne yai sanyi don bai taba tsanmanin wanan magana bane mama Laraba ke neman shi ba dayi.
Saadatu ta bashi mamaki matuka da ta nace akan wanan magana haka har yakai tun sunayi su biyu a tsakanin su gashi yanzu takawo maganan ga magabatan shi.
Yanzu shi yaya zai iyacewa mama hakan bazai yuyu ba bayan kwararan hujjujin da ta kawo mashi yanzu a gaban shi wanda ita da Sa,adatu ke gani hujjane a garesu.
Shi fa bai taba jin son Rahama da aure ba a rayuwan shi ba asali ma dai mamakin mazan da ke ta hauka akanta yakeyi don baiga abin burgewa gareta ba gaskiya sai dai idan farar fatan ta tane ke rudin su.
Shi bayan Saadatun shi fa baitaba tsayawa kallon wata mace bata bashi sha, awa haka na ba.
Ko su wa yan nan dake gidan shi aure daine mukkadari kawai a tsakanin shi da su har yake zaune dasu don biyayya kawai.
Amma bawai don yasan wani dadin zama da mace ba may mace zata iya maka wanda zai iya saka natsuwa ko shagalta a kan ta duk shi bai san wanan abin ba.
Can dai ya nisa bayan ya fahinci mama tagama fadar abinda zata fada mai shi take saurare yanzu.
Yace mama nagode da wanan shawaran naki tunda haka take bukata da kan ta insha Allahu zan yi kokari naga na cika mata gurin ta akan hakan.
Sai dai kuma bazan so jin daga baya tadawo tana wani korafi ba da bakin ta akan yin hakan kuma don mama kin san halin mata akan kishi kuma.
Ita Saade na rasa may nene ke damun rayuwa ta data yankewa kanta wanan danyen hukuncin haka ba ?
Mama tace yanzu ai koma maye dai itace ta bukaci ganin hakan a rayuwan ta ko naka yanzu shine kayi kokari kaga ka kwatanta adalci a tsakanin matayen naka.
Don tserewa hushin ubangijin ka a gobe kiyama Allah kuma yai maka albarka ya daukaka zurianka.
Yakare muna ku daga sherin makiya da mahassada nagida da na waje sai ka jajirce sosai gurin kwantata adalci akan iyalin ka don nauyi ne mai girma ya kara hawa kan ka yanzu kuma.
Na kuma ji dadi kwarai na rokeka alfarma irin haka kuma kai min shi a take babu bata lokaci don haka yanzu abinda nake son ka dashi shine.
Kabar wanan zancen a ranka itama Saade sai dai ka shirya yanda neman auren naka zai kasance idan har Allah yayi sai dai aji kawai anyi auren.
Don baiyyana shi zai iya kawo muhawara mai karfi har takai karshe azo a samu akasi a hakan.
Yace hakane mama insha Allah zan bi al, amarin a tsanake yadda abin zaizo a cikin sauki ba tare da rayuka sun baci ba akai.
Tace hakan na da kyau Allah yai maka albarka tagi ka huta abin baka dama aanan shine maganan kawai .
Yai mata godiya tare da sallama tana ta saka mai albarka tafita yaja motan shi yana tafe yanajin wani irin abu a zuciyar shi.
Shi yanzu ma ta ina zai fara ne wai takan Saade ko ta kan wanan yarinyar da akalaka mai akai ko kuma da maganan jama, a zaiji.
Mahaifin shi dana Saade ne suka fado mashi arai dole ta kan su ne zai fara bai tafi gida ba sai da yaje kasuwa ya samu Abba suka gana dashi akan maganan.
Abba yai murna kwarai da jin wanan labarin yake cewa yai matukar farin ciki da jin haka aiko ba komai Saadatu tayi jahadi babba anan, don aure ta hada don farin cikin ka.
Yasan Alhajin shi na gona a wanan lokacin don haka ya juya akalar motar shi zuwa gida inda ya nufo gidan cike da natsuwa da karin imani a zuciyar shi.
Don maganan da mahaifin Saade yai mashi a yanzu ya kara sa jikin shi yin sanyi ga ala, marin kowa na fada mashi cewa aure ne yayi kawai.
Yana shigowa gida ya nufi part din shi duk da sanyin Ac daya kunna a falon bai hana shi jin zafi ba a jikin shi.
Zama yayi tare da mike kafafuwan shi saman dan table din dake a tsakiyan falon.
Ya dafe kan shi da hannun shi daya yana jin kan nashi na matukar sara mashi a lokacin.
Shidai Allah ya gani wanan auren yafi ko wani zo mashi da rikici a rayuwan shi yanzu shi dawani ido zai kalli Saade ko dawani ido zai kalli Rahama wai a matsayin matar auren shi da zasu raya sunna a tare zaman aure fa ba zaman wasa bane anya kuwa Saaden shi tayi la, akari da wanan abin kuwa a yadda yasan mata da kishin tsiya.
Yanzu dai zaiga Saadatun don yaji ta ina zasu fara bullowa zancen don komai yanzu yana hannun ta ita da ta kawo maganan.
Zai danka mata komai ta gudanar yadda take bukata shi nashi idone kawai yaga iya gudun ta.
Yana zancen zuci Zulfa ta shigo falon da ganin yanayinta kasan bata da lafiya a lokacin .
Jin an shigo falon ne yasa shi bude idanuwan shi dake a lumshe ya sauke a kan ta.
Yace da ita lafiya yau kike kuwa ta samu guri ta zauna daga gefen shi tana cewa yau tunda safe a kwance nake na rasa gane kan jikin nan nawa duk kwanakin nan.
Yake cewa ki shirya muje asibiti yanzu adan kara dubaki muji may likitan zaice akai.
Ta mike da kyat tana fadi bari naje na dan kimtsa kafin ka gama sai na fito.
Tana barin gurin yake cewa a ranshi bari ya shiga gun Saade ya ganta tunda hakkanta ya cin ma ruwa ta kai ga yadda take son ganin su.
Fitina kawai take son kirkiro mashi yana fama da fitinan wasu takara saka shi ga wani sabo.
Yamike zuwa part din na anty muna zaune sai kwasan dariya muke Jinior ne ke bin mu yana cizo wai hakoran shi na kaikayi inji anty.
Ganin daddy ya shigo falon muka shiga gaidashi tare da kokarin mikewa mu bar falon don su gana inda nake zaune nake gaida sai baima tsaya falon ba ya nufi bedroom din ta yana fadin ke may ya hanaki zuwa school yau ko ba a karatu ne yau din.
Ta bi yan shi tana fadin ina zata fita mahaukacin soja ya saka security's dinshi akan ta ko ina tabi binta sukeyi yi
Yace binta kuma garin yaya haka ya faru ban sani ba kuma ke baki sanar dani abinda ake ciki ba tace yanzu haka kai nake jira ka shigo nai maka maganan ai.
Don ashe wai har can kauyen su ya tafi gurin iyayyenta ya nuna masu kudi nan dai tana zama take labarta mai abinda ke faruwa take cewa dashi yanzu haka ita duk a rude take ta rasa yaya za, a bullowa zancen don ta fahinci wanan sojan ba karamin tantiri bane gaskiya kamar aure dole ne ga mata a gari ko ina amma ya nace wa mace daya haka ?
Yace yanzu ma zancen ta ya kawo ni gurin ki ai bukatan ki ya biya tunda har kina son hadani da mamana fada.
Yace daga gurin mama furin Abba na nufa na fada mashi kina akan bukatan ki sai dai ki sani ba korafi ko wani magana akan hakan daga baya.
Don bani na bukaci yin hakan ba kece da hujjan ki mara tushe kin samu mama kin mata dadin baki ta hau ta zauna nai magana tace ban yi mata biyayya ba kuma don haka yanzu dabara ya saura gareku.
Sai ki san yadda zaki tsara tunda kece kika hada abinki da kan ki ba wani ya hada maki ba.
Tace Alhamdullahi Allah nagode ma dajin wanan labarin farin cikin hakika Rahama alheri ce a gare mu besty ba zaka gane manufana ba sai bayan anyi abin idan Allah ya tabbatar insha Allahu.
Idan har kana tunanen zan tsaya kishi da Rama a rayuwana kayi kuskure ni don ka nai wanan hadin amma ka kasa fahintana cikin saukin kai.
Kaima kasan abinda mata kewa bakin kishi ai abu daya ne ko toni ina iya hadawa danawa da nata duk ta kwashe na bar mata ita kadai in wanan ne?
In dai har zakai muna wanan alfarman ni da ita don ni may yarage gare ni banda bautan Allah kuma yanzu.
Wani kallo yai mata yace kada ki soma wanan maganan idan ba haka ba wallahi yanzu nace na fasa tace rufa min asiri idan ka kara botse min kuma wa na san zai taro min kai kuma ?
Ban ni dai yanzu nasan yadda zan bullowa wannan yar butsar din tawa don nasan akwai rikici babba tsakani na da Rama nan gaba.
Baki ya tabe yace wanan matsalar kune ni dama ban dauka aka ba balle ku tsanmani zan saka maku baki ga zancen ku.
Tace ai wallahi dole ka saka don kaine ma zakai jagora gurin lalashin abinka don yanzu ta tashi daga Rama ta koma Raman besty kuma.
Haushin zancen ta yake ji fita yayi daga dakin ba tare da ya iya bata amsa ba don haushin maganan yakeji.
********* ********* *********
Duk kwanakin nan biyu idan mun zauna da anty bata da wani zance sai muna huduban yadda zama da miji yake da abinda ya dace mace ta dinga yiwa mijin ta.
Sai nake ganin don Gajiye mai son yin aure ita da maigadi takeyin maganan don zancen su yayi nisa sosai kowa yasan shi zai auri gajiye yanzu.
Don har daddy yasa a gyara masu can baya inda aka gina wa masu aikin gida ba kowa ke zama ciki ba sai shi maigadin da yan komatsen shi keciki dama.
Don haka wani lokaci idan anty na magana har naka yiwa Gajiye dariya mu saka mata wakan shakiyan ci nida su Amira taita murmushi tana jin dadi.
Don haka nakan zauna nai ta sauraren yadda anty ke faman mata nasiha kan hakkin da ya rataya akan mata dakuma namiji daya rataya akan shi ga matar shi.
Nidai har nagaji dajin hudubar anty akan aure da sun fara zan kunna game muyu ta bugawa nida Nasir muna ihun mu ban tsayawa sauraren su .
Ranan Jumma,a da safe daddy yashigo muna falo muna karyawa yana saye cikin wani shadda yaci aiki mai ruwan dark blue sai maiko shaddan ke yi.
Anty tace dakyau nawa sai goga na Ram, , , sai kuma tai shiru tanacewa Allah ya bada saan tafiya aje lafiya a dawo lafiya mukuma ji alheri.
Ya dan dubeta cikin tsiga maikama da harara yake cewa shi zai tafi sai sun dawo kenan, Anty ke cewa tana gaida mutanen gida idan sun tafi.
Bayan ya fitan shi na dago kaina inacewa anty ina daddy zai tafi yau haka aha wanan kwalliya irin haka gashi ko kayan sun matukar karban jikin shi sosai wallahi.
Tace da gaske Rama kayan sun karbe shi nace aikema anty kin gani bana gkina ta murmushi ba sunyi maki kyau ke nan kema.
Gajiye kece hajiya garin su zai tafi ne ko may dariya tayi tace Gajiye shi ai haifafen dan garin nan ne kowa nasa na cikin garin nan gaba daya yan uwan shi ta uwa ta uba.
Unguwa dai zai tafi nan ba nisa bane kwarai nake gani zai tafi a tare muke fadin Allah ya tsare hanya tace amin na mike na kwashi kayan zuwa kitchen ina mai jin haushin rashin shiga na school da wanan fitinanen sojan ya haddasa min kwana biyu ga zarah har gida ta biyo ni kan rashin ganina da batayi kwana biyu.
Ban fito ba sai da na wanke kayan na tsane su na dawo falon na samu Gajiye na gyara gurin na samu kujera na haye tare da kwantawa na mike flat tare da lumshe idanuwana a hankali ina jin raina ba dadi ko kadan a lokacin.
Yar aikin Zulfa ce tashigo tana tambaye gajiye wai tana da goro ta san ma uwar dakin ta gajiye ta ballo goro cikin wani leda tabara tafice daga falon namu.
Gajiye ke cewa nikan hajiya kodai da zaki samune ko ya xon kwanan duk sai matar nan ta aiko neman goro gurina.
Anty tace hakanake gani gajiye kamar ciki Zulfa ta samu shine take wahal da ita haka wallahi.
Daga yadda nake kwance na mike da sauri ina fadin Ciki kega anty Zulfa Allah sarki har nayi mata murna wallahi tun mutuwan hanifa dama bata sake sake jiku ba a gidan nan kamar yadda take a baya.
Keko mutuwar da fa akwai zafi Rama balle irin Zulfa data sawa yar ta rai a gidan nan kamar ikon Allah.
Murmushi nayi don nasan ko ita anty ba baya ba ai gurin son yara sai dai na wani yafi na wani ne don ita tana kawaici akan yaran ta.
Waya anty ta dauka sai naga ta mike tashiga daki tajima a ciki sai tafito jikin ta duk yayi sanyi a lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
.IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE IDAN KIN YI GANGANCIN KARANTAWA NA BARKI GA ALLAH, , ,
IDAN KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA ALLAH YABI MIN HAKKINA A KANKI CIKIN GAGAWA YARWA ALLAH YA SAKA MIN AKAN WACCE TA FITAR MIN DA NOVEL DINA, , ,
34
Haukan kiran da Soja ke min yafi karfin na ibrahim da nake ganin ya damay ni a baya da kira hakan yasa ba shiri na kashe wayan nawa gaba daya.
Dama waya ba damuna yayi ba don ban faye amfani dashi ba nazo nagane cewa Farida ce tabashi layi na haka yasa mukai fada sosai da ita.
Ta kwashi nata ya nata tabar gidan da yamma wai tayi fushi tana gani zan bata hakkuri ne ta tsaya.
Batasan yadda nakeji zan iya yin komai a lokacin ba gashi tsoron wanan bakin sojan ya fara kamani don abu yake kamar mara hankali.
Don har zuwa yayi ya samu daddy da maganan cewa ko daddy ya yarda ya aura mashi ni da girma da arziki ko kuma yasan hanyan da yabi ya aure ko ta karfin tsiya ne.
Daddy yazo ya samu anty da maganan yadda sukayi da Soja mai sona yace yanzu dole ta samu mafita don wanan mutumin mahaukacin gaske ne.
Wani mafita kake son na samu mafita guda ne shine ka yarda da bukata ayita ta kare ko ba shike nan ba.
Yafita daga dakin cikin fushi ya barta da tunane ita kadai a dakin ta na fito cikin shirina zani makaran ta nazo na sallamay ta dakin ta.
Nan na samay hankali a tashe tace anya Rama fitan nan naki kuwa yau zai yuyu .
Da sauri na juyu nace anty lafiya dai ko ?
Tace ina fa lafiya Rama wanan
Showing 138001 words to 141000 words out of 456145 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47 Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153