suka fita sun dauka zasu dawo sai gida ya nufa dasu don sai daya biya wurin hajiyan shi suka gaisa itama din dai fadan tai mashi bata gane komai ba a gareshi.
Muna nan sai gashi ya shigo da yaran gidan part dina ya nufo dasu yana fadin ga karin baki kin samu kuma.
Na dago don naga bakin sai naga yaran Zulfa ne ya shigo dasu gabana yai mugun faduwa amma a fili na nuna farin cikina ga ganin su.
Nan muka zauna da yaran suna ta jin dadin ganin yan uwan su har dare naga bai ce yaran su fito ya mayar dasu ba gida.
Ban yi magana ba sai gashi ya shigo da dare yake cewa wanan ta bugo maki waya ne na tambaye shi wa ke nan fa ?
Yace Zulfa mana nace wayan ma baya hannu na ai yana ciki yana charge wata kila ta kira ban sani ba dai.
Yace yanzu hajiya ta kirani take tambayana yaran nasan sun tafi gunta ne da tsegumin su da suka iya.
Yara ne kuma ba zan maida mata su ba sun dawo gida ke nan don ba zan barsu a can ba su lalace da mugun hali.
Yana gama magana kiran wayan ta na shigowa gare shi again ya dauka ba ko sallama yake cewa da ita lafiya wai ?
Idan kirana kikayi akan yara ina son ki cire su a ran ki don ni na karbi yarana daga hannun ki daga yau.
Bai jira a binda zata fadi ba ya kashe wayan shi yace dani ki basu wiei su kwanta nan da yan uwan su ba dama nai magana amma duk da haka sai da nace to amma daddy, , ,
Katse ni yayi dacewa ko ba zaki iya rike min su bane na sani shiru nayi ban tanka shi ba yace idan baki iya rike min su zan kwashe su na kaiwa Fatima ko Aisha su zauna a wurin su.
Nace akan may daddy ba zan iya rike ma jinin ka ba koda kuwa sun fi nan yawa ne kawai dai gani nayi kamata yayi kayi hakkuri uwarsu ta dawo hakana ta zauna dakin ta.
Kada yin hakan ya jawo maku matsala irin na zumunci a tsakani ai yanzu ta gane kuren ta ko.
Rahama ina warning din ki a kan zancen nan tun farko don haka ki iya kan ki daga shiga zancen.
Allah ya baka hakkuri bai ce uffan ba ya juya ya fice daga dakin ran shi a bace nabi bayan shi da kallo har ya bace min na juya ina kallon yaran dake barci tare da sauke ajiyan zuciya.
Don nasan cewa wani sabon aiki da rikici ya samay ni kuma ke nan in ba son dora min laifi may zai hana shi shiryawa da uwarsu ta dawo ta rike yaran ta da kan ta .
Mikewa nayi na gyarawa yaran kwanciyan su tare da sauran yaran na samu wuri na kwanta nima don da safe nasan ban da wani sauran time din kai bakine zasu fara shigo muna ta ko ina.
Tun da safe Zulfa ce da mahaifiyar ta tare da su mama hanne autan su hajiyan daddy sukai muns sallama a gidan.
A lokacin yaran sunyi wanka suna zaune suna karyawa koma su nuna sun ga iyayyen su a gidan basu nuna hakan ba sam.
Mun gaisa da su sama sama don fuskan su babu annuri a cikin sa ko kadan a lokacin sai wani daurewa da suke min kawai.
Bayan mun gaisa ne mama hanne take cewa dani ko may gidan ya fito ai muna iso gun shi nace da Jinior ya fadawa baban su ga su mama sunzo .
Bayan fitan yaron ne mama zulai mahaifiyar zulfa ta dan nisa tare da fadin ikon Allah ke kuma naki sallon yaidaran ke nan ki kore iyayyen yara ki sa miji ya dauko maki su a wurin ki don wani manufa na sheri.
Murmushi nayi nace ni kaina ai ba daban nake ba a gidan balle na saka shi yin abinda zai cuta mai ko wata a gidan nan mama.
Nima mace ce mai haihuwa idan na saka shi yin haka watarana nima haka za ai min a kan diyana ai .
Ga Zulfa nan idan tayi fada dani ko wani abu da har yasa na jawo barin gidan mijin ta da yaran ta ta fadi yanzu a ji.
Idan ma laifine ni akaiwa laifi amma hakan da sukai min bai damay ni ba a rayuwa na don ba shine farko ba a tsakanin mu da ita.
Wanan dadin bakin ne kike cin mijin naku dashi ai ko yaushe bai iya fahintar komai akanki idan bake ba baya ganin kowa da gashi a idon shi.
Yara dai ne yau sai na tafi dasu in ma tarbiya ne ban dashi a gida na da har yaje ya dauko su yakawo maki ke uwar iya tarbiya ba zan dauki wanan rainin ba ni.
Mama kada kiga laifin Rahama a cikin zancen nan don ba ita ta dauko yara ba ni mai abu na dauko su na kawo mata su da kaina ba don ta so ba ita ma.
Mara kunya kai yanzu bakajin kunyan kare wanan mayaudariyar da ta gama da kai da matan ka yara dai ne yau da su zan tafi ba zan bar gidan nan ba sai da jikokina tunda kai ka zama sallamamay namiji sai abinda ta saka kakeyi a rayiwan ka.
Kana ganin don ka wullakanta yar uwar ka kamar kayi abin kwarai ke nan ko may kake ganin kayi zama da kai a gare ta ai bai zama dole ba ko ?
Haba mama don Allah ki bari abi zancen nan yadda ya dace shiyasa nace kada ma ki zo kika nace da sai kin zo din.
Yara dai ba ita ta haifa ba ta tsaya a iya wa yanda ta haifa ma tayi iko dasu ba wanda bata haifa ba ta bari idan ta kashe uwar su sai ka kwaso ka kawo mata din amma ba yanzu ba.
Mama nifa ban yi fada da Rahama ba don da abin ta na ta tun ranan da abin baikai hakan ba ma da kuma ina bin shawaran ta na kama kaina duk wanan abin da bai faru ba dani.
Ke dallah rufa wa mutane baki wawiya mara wayo kawai kishiya ce har zaki tsaya kina wani yabo haka don rashin sanin ciwon kai.
Mama don Allah ki bari abin zancen nan yadda ya dace a fahinci juna ba wai hakan da kike yi ba mana don Allah dai.
Mama gaskiya Zulfa ke fadi gyara ya kamata ayi ba wai hakan yadda kikeyi din ba don shi babba gyara aka san shi dashi ko ina.
Ban iya gyaran ba sarki iyayi da munafunci ki mun shiru ko yanzu naki ya samay ki a wurin nan don ke yar kauye dake kin yi kadan ki fada min abinda ya dace nayi kiyi da wa yanda basu san ciwon kan su ba ga sunanan a gaban ki.
Daddy yai murmushi tare da kaiwa zaune yana cewa to yanzu kin gani ai zaki kama kan ki na fada maki tun farko ki barni da yan uwa na kuma matatace ni na san mafita da sauki ga kaina.
Amma akan zancen nan na zulfa da zan biye maki da yanzu mun samu matsala dake akan damuwana da kike yi ta dawo dakin ta a hakan ne mutum yai laifi ba a tsawata mai ba ake son wai na mayar da ita gidana.
Nan gaba idan ta tashi min wani kullin kuma sai yafi wanda sukai min ke nan a baya ni da diyana dana haifa kafin su kashe ni su kwashi ganima ni zan fara ganin nasu bayan tukun.
Sai mahaifiyar nata tace Allah bai yarda kaga bayan diyata sai dai taga nata nan dai taita sake bakaken magana inda take shiga ba nan take fita ba shi kuma ya kafe akan ba zai ba da yaran ba ya dauko su ke nan gidan shi.
Text ne ya shigo min a waya ina dubawa naga Zulfa ce take cewa dani na bawa maigidan hakuri na tura mata cewa mu bada tare yanzu a gaban kowa a wuce wurin.
Itace ta fara mikewa zuwa gaban shi ta tsugun na sai nima na mike na yi kamar yadda tayi tare da fadin don Allah don annabi duk abinda zulfa tayi a yafe mata kaddara ne insha Allahu ba zata sake ba da yardan Allah.
Kuka sosai zulfa din keyi itama tana rokon shi da ya yafe mata don Allah mama hanne ne tai magana yadda mukayi hakan itama tayi takai kasa tana fadin don Allah Alhaji karami ka yi hakkuri ka mayar da zulfa dakin ta ta zauna da iyalin ta.
Shiru ya dan yi tare da sadda kan shi a kasa ya rasa abinda zai fadi a wurin ita ko mama Zulai sai jikin ta ya mutu ta kasa ci gaba da fadan da takeyi.
Mama Hanne ta ce Rahama ko ba komai ni dai yau kin fitar da duk wani zargi a zuciya dama zulfa ta fada muna komai yadda kikai masu shawara da su kama kan su da wanan shedaniyar yarinyar da ta shigo cikin ku amna tai biris taki daukan shawaran naki
Yanzu may gari ya waya wa aka bari a cikin maganan ba ita ba da take fama da dacin rai akwai abinda yafi zafi da kunya ace ka dawo gidan ku da zama ka kashe auren ka bada son ran ka ba.
Mama zulai ta bani mamaki da naji tace Alhaji karami kayi hakkuri bacin raine dama ya kaini ga hakan yadda ka rufe ido kaiwa yar uwar ka sai nake ganin ba don kowa kai hakan ba sai don Rahama don muna ganin burin ta ne na ta zauna ita kadai ya kai kai masu hakan da kayi.
Har lokacin baiyi magana ba da kowa yana duke da kan shi yayi shiru kamar mai nazari sai mama hanne ta sake cewa ni wanan abin ma da yaya tayi kunya ya bani don a tsakanin mu bai kamata haka ya kasance ba kan diyan mu.
Ga zahiri mun gani zulfa bata da gaskiya a cikin maganan nan amma kuma zafin rai ta hana mu ganewa kai babba ne kuka kai keda ragamar aure a hannun ka don haka don Allah kayi hakkuri da yar uwar ka ku zauna lafiya.
Ai yanzu in kunne yaji gagan jiki ma ya dauka don ta zauna gidan nasu taji abinda ke cikin sa in har wani abu ke rudin ta dama da take hakan.
Iska ya furzo tare da dago kan shi idanuwan shi sun kade sunyi ja jawur dasu yace da mama hanne din.
Mama a matsayin ku na uwayena da banda wasu bayan ku idan nace ban hakkura ba a yanzu ban kyauta maku ba.
Amma a gaskiya irin yadda mama zulai tazo min koda borin da zatai min yafi hakane na riga da na yankeyank yanke shawara zulfa ba zata dawo gida na ba da sunan aure.
Da sauri mama zulai din tace kada kai muna haka don Allah nima ai na fahinci itace bata da kan gado yanzu.
Yace yanzu ai tunda ta fada da bakin ta komai ya wuce zata iya dawowa dakin ta ta zauna sai dai ba zan tafi da ita Abuja ba kuma.
Dama ga ta nan ya nuna ni da hannun shi inda nake tsugun ne a gefan shi kamar mai neman gafara, yace itace ta matse ni akan sai na tafi da ita can ni kuma na riga da na san halinta kamar yunwar cikina kan sari ka noke.
Duk wanan dadewan da kukaga tayi can don ita Rahamar ba mai tafiya da magana bane inda ta fada nan zata bar shi.
Shiyasa zaman nasu har yai dadi amma data amu irin ta kinga ta zauna ta zubar da kanta gun karamar yarinya ga banza.
A daiyi hakkuri yanzun ai tasan ta duniya kishiya ko wacce ka san tane sosai ina kake daukan yarda gaba daya ka bata balle wacce ta san ta shigo maka a bakuwa.
Ya mike yana fadin shi zai fita adai ja mata kunne ta yi hankali don idan ta sakw zasu hadu fiye da hakan.
Nan ya fice ya barni tare dasu sai kuma aka koma bani magana ana wai idan naga tayi abinda ba daidai ba na dan rika saka ta a hanya.
Nace mama ai a bar zancen girma a wurin miji a girmay ta girmay ni sosai ma ba kusa ba ita bata lurar dani ba sai nice zan lurar da ita ta dai gyara halin ta kawai shi yafi.
Munyi sallama dasu akan da dare zasu dawo da ita dakin ta ayi buki da ita nai masu rakiya suka tafi zar kunya dasu.
Koda daddy ya dawo lokacin baki sun dan cika gidan na samay shi a dakin shi zaune saman gado na gaidashi da dawowa ya amsa min.
Yana cewa ashe har gida ya fara cika hakan ne da baki don naje shiga naga mutane sun cika wurin.
Nace hakane sai dai ai gidan baya cika idan matan gidan basu kammalu ba baki daya don Allah daddy tunda kayi hakkuri da Zulfa ta dawo itama Niima ai mata hakkuri ta dawo haka ai yanzu sun horu ko sosai.
Wani irin kallon yai min tare da fadin wai ke rahama wata irin yarinya ce mara zuciya haka duk abinda matan nan sukai maki baki gani ba sai wani rawan kai kike wai su dawo dakin su.
Halin su na nan ba wai sun canza bane don haka ita zulfa zan yi dubaiyya akan zumuncin da diyan dake tsakanina da ita ne kawai amma ita wanan da kike magana yanzi fada min riban da na samu a cikin auren ta dana yi.
Dama kaddaran aure ne kawai dake tsakanina da ita yanzu kuma Allah ya kawo min saukin bacin ran da nake zaman yi da zama da ita.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON ONLINE NOVEL NE, , , ,

106
Kafin wani lokaci gidan ya fara cika da jama, a masu zuwa buki don haka banda wani lokacin kaina don yawan jamaan da suka taru.
Daddy bai shigo ba tun fitan da yayi da safe muna tare da su zulfa sai ga hindatu ta shigo tana fadin waiko kin san Zulfa zata dawo gidan nan kuwa?
Don ga ya can naga an bude part din ta ana ta gyara tundazun kinga namiji ko munafuki dubi yadda yake tayar da jijiyoyin wuyan shi a baya amma ashe har sun shirya ba wanda ya sani.
A raina nace gaji kishiya ko nice ma haka zatai bakin ciki da dawowa na gidan sai dai a fili murmushi nayi nace da ita kin sai ai tsakanin miji da mata dama sai Allah.
Balle su da suke yan uwa kin san dama ai da wuya su rabu ko ba iyali a tsakanin su balle ga iyali a tsakiya.
Tace ke dai dama munafuncin maza ba karewa yake ba shiyasa na dawo daga rakiyan namiji yanzu indai bai shiga gona naba yaje can yai tayi balle na miji irin namu mai son tara iyali haka da yawa in bashi ba mu biyun nan ma bamu isheshi ba don Allah dai ?
Mamaki ta sake bani nace da ita kai maman ihisan ke nan da wani zance a tare fa muka samay su duk dake da ita ba wani tsaraiyya a tsakanin ku.
Amma nikan ko ajikina idan ma wasu zai karo basu zasu dawo ba duk daya a gare ni tai min kallon mamaki don jin abinda na fada mata.
Tace haka dama zaki ce ai na sani don ke kin iya boye abu a zuciyar ki ba irin mu bane masu fitarwa duniya ta sani.
Dariya ta bani nace to yanzu da ace na saka a raina wa aka bari a cikin zancen don haka kinga ai gara dai mutum ya tsaya a matsayin sa kamar yadda kika ce yanzu.
Nifa ban sa akai balle nauyin zancen ya damay ni a zuciya tace ai kin huta wa ran ki wallahi yanzu haka zata dawo babu ko kunya a idon ta.
Mamaki tabani nace a raina lallai manya sunyi gaskiya laifi tudune ka take naka ka hangi na wani ke nan ita ta manta da lokacin nata harda sakin ?
Ta mike har ta fara tafiya ta juyo tana fadin yanzu kuma nasan ita ma wanan fitsararar itama dawowa zatayi ke nan ko ?
Ai dai yanzu mai daki shiyasan inda ruwa ke mai yoyo don shi ke da kayan shi ba wani ba in dai mutum ya shiga gonar ka shine ba zaka kyale ba.
Tace ke ai zaki iya sai ankai inta,ha zaki tankawa mutum amma nikan gaskiya yanzu da sake sosai a wurina wallahi.
Allah dai ya sauwaka nace da ita ina murmushi bata fahinci komai daga wuri na ba ta fice tana bakar magana da akan mijinta da matan shi.
Daddy bai iya shigowa wurin na ba don jama, a da sukai yawa a gidan don haka na shirya mai dan abin tabawa na samay shi dashi a wurin shi.
Kamar kullun yana
Showing 435001 words to 438000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146 Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153