Tana kwance ta rasa dubara ga bakin ciki da yunwa na addaban ta a lokaci daya mikewa tayi ta suri hijjabinta ta saka sai gidan su.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA HAKKIN AMANA YANA KANKI ALLAH YA GANKI, , ,

22
Tun da safe mukaji ana dukan kofan shigowa part din mu ina kitchen ina hada abincin yan makaranta wanda kullun da nauin abincin da nake girka masu.
Da sauri na fito zuwa kofan ina budewa naga wata mata tana da matukar kama da hajiyan mijin su anty.
Nai ma matar ina kwana ta amsa tana kokarin wucewa ciki tana fadin lafiya kuka kwana ko ?
Na bata amsa da lafiya kalau mama sannu da zuwa ta wuce tana fadin ina dakin Saaden yake na nuna mata dakin na koma kicin abina naci gaba da aikina.
Daidai na kanmmala ne kuma stil naji ana sallama muryan namiji ne da sauri na fito ina karba sallaman na shi yana tsaye daga kofan mu na gaidashi yace ina maihaihuwan take nace tana ciki yace fada mata ga Bashir yazo.
Najuya na shiga dakin suna zaune har wanan bakuwar tana dauke da yaro na sanar da ita zuwan bashir din tace nace ya shigo daga ciki.
Na juya na fada mai na koma kitchen don na kawo mata abin karyawan ta.
Ina shiga naji mutumin na fadin tun dare ya damay ni da kira sai nazo naga halin da kike ciki ko za, a tafi asibiti ne ashe ke Allah ya kawo maki saukin haihuwa haka ?
Matar da ta fara shigowa tace ni ai wallahi Alhaji karami ya tayar min da hankali da kyat naga gari ya waye min wallahi.
Tace mata gidan sun san da haihuwan kuwa don ban ji duriyan su ba ko da na shigo sai shi namijin yace anya Yusuf bai fada masu ba.
Matar tace bari ai yanzu na shiga na fada masu naji idan basu ji bane amma ai haihuwa da ciwo ya kau da komai da suke ji a ransu cin tuwon kishiya ranko.
Mama Altine dake zaune gefe ne take cewa banda yaran nan sun dauki kishi da zafi wallahi ace ko gaisuwa na musulunci babu shi a tsakanin ka da dan uwa balle in yana cikin wani hali ka sani.
Ko kwana ki data kwanta asibiti bance matan sunyiwa yarinyar nan sannu ba har ta dawo gidan nan ban gan su ba gaskiya.
Matar tace daurin gidin hakan suka samu daga yaya amma ta yaya zan bar gidan dana yana ci da wuta har na mara ma abin naya don son kai.
Yanzu cikin su ukun nan waye bare a cikin su tunda duk abu guda suke ma zama sai a zauna a sulhunta komai kowa ya tsaya maysayin shi amma ba ayin hakan.
Yanzu ba don Allah ya kawo wa yarinyar nan dabara dauko yan uwanta kusa da ita ba yaya ke nan ga yadda haihuwan yazo mata haka a gida.
Bashir yace ai ina ga abinda ke tayarwa Yusuf da hankali ke nan don ma yana jajirce ma akidar tasu ai da abin yafi nan.
Mata sam basu da tausayi akan kishi wallahi in bashi ba may ye a cikin hakane wai kazo ka samu mutum da mijin shi suna zaman lafiya da rufawa juna asiri kace ina suka fito kai dole sai naka akidar zaka kawo a cikin gida.
Bayan sun san auren su dashi auren kaddarane haka Allah ya nufa dashi don yana mai bin umurnin iyayye akayi shi ai da basu isa ba wallahi.
Muryana ne nake cewa anty ki tashi kici abincin kada yai sanyi.
Ta dan dago daga inda take tana fadin Ramana abinci kikai min tunda safe haka ?
Matar tace to ai shine kyau shine jegin asali kaci a binci sai jikin ka yai kyau da sauri ba wanan shaye shayen zamanin da mata keyi ba.
Tashi ki karya kin san jikin ki ko banza ba lafiya ne da shi ba ki daure kina ci koba dadi yafi jikinnki yai kyau sosai.
Sallama su anty Aisha ne kannen maigidan su biyu suka shigo suma dau nasan daddy ne ya rudasu suzo suga matar nashi take dakin ya cika da jama, a.
Ina ganin haka na sa a raina yau ba fita school gareni ke nan don ga baki a shiyan mu tab.
Matar data shigo da farko naji sun kira da mama laraba ashe kina nan tace ba dole ba dana ya hanani barcin dare sai nazo na duba mai matarshi naga halin da take ciki.
Su anty Aisha sukace tun da asuba ya bugo muna waya wai tunda na karata nurse nazo na duba jikin ta na gani.
Mama laraba tace ai Alhamdullahi yadda yake zaton abin ba hakana bane da sauki gaskiya bari naje gurin wa yan can marasa hankalin naji may ya hana su shigowa har yanzu su duba yar uwar su da tai gwajin arziki .
Kai mama ai da kin kyale su inji anty hadiye da suka shigo tace ni banga abin damuwa da lamarin su ba wallahi tunda Allah ya sauke ta lafiya ita da baby a kyalesu kawai shi yafi.
Bari tace inji Aisha basu da kirki wallahi kwanaki sai da nai ma hindatu tas akan Saade ta dauki bakin ciki da hassada ta dora kan wanan cikin a ranta.
Wai kullun tace bata da lafiya amma ta iya shigewa daki tai ciki da namiji su masu lafiyan ma an ki basu cikin ji min maganan hauka anan .
Wallahi ban san lokacin da idona ya rufe ba nai mata tas a gurin sai da ta raina kanta.
Take cewa wai ai dama saade duk ta asirce mu hajiya ce kawai tafi karfin ta cikin mu.
Nace ni na san batai muna komai ba halinta dai a gare mu ne ya asirce mu ba asiri ba.
Basu da hankali kin san halin yaran yanzu ne su shigo gida su samay ka da matar ka suce sai sun rabaka da ita ko ta halin kaka don bakin kishin tsiya da hauka ai kishiya abokiyar zamane.
Hadiye tace inda sun zauna lafiya da anty saade ai ba karamin karuwa zasuyi ba da ita mutumin da bai dauki duniya da girma ba ai dadin zamane dashi.
Mama laraba ta fice daga dakin tana jaddadawa anty ta ci abinci sosai ta bar tsakura
Anty ta ce ni dai wallahi Rama yau kin ja min cin abincin safe haka yarinya da shegen akidan tsofaffi haka ina ni ina cin abinci mai nauyi haka da safe ?
Aisha tace ai wanan sister din naki wallahi tayi ranan ta tafi tabar ni da sha, awan ta sai data gyara min gida na tsab ta dawo gidan nan.
Duk taron matan nan an rasa wace zata daga tsintsiya ta gyara guri haka muke zaune cikin kazanta sai zuwan ta wallahi ta taimaka min ba karamin dadi naji ba.
Jifa part dinki kamar ba a haihuba kimai neat dashi gwanin ban sha,awa wallahi.
Antyna tace Rama akwai tsabta ai bata son kazanta ga ta da sanin ya kamata kinganta nan tun zuwan ta wallahi ban taba nuna mata yi min kaza ba itace tasan ya kamata bakiji na daina zancen neman mai aiki ba yanzu.
Sai dai yanzu data fara karatu dole na samu mai aiki amma ban son yar birni kauye nake son a samo min yar ma daidaiciya yadda zan iya controling din ta.
Aike dai anty da yar birnin da yar kauyen sai dace yanzu duk abin daya ne ai inji anty hadiye.
Nan dai sukai ta hiran su a tsakanin su suna raha Bashir yace shi zai koma don zai tafi aiki ne yai masu sallama ya fita tare da cewa matan shi zata zo in an jima.
Mama Laraba a dakin Zulfa ta fara shiga tana zaune da kayan barci a jikin ta shiyan nata sai wani tsami yakeyi wanda ma bataji ko rabin shi ba a dakin mai haihuwa daya dace ace can akaji wanan abin.
Tana ganin mama tace mama kece da safen nan injin dai lafiya nagan ki gidan yau kuma da safe haka ?
Au bani da ikon zuwa ke nan gidan lokacin da naga dama sai anzaba min ke nan ko ?
Shiru tayi tasan maganan da taiwa maman yaci mata rai ke nan tabata amsa da hakan don Zulfa bata son taga suna shigowa gidan ko yaushe shiyasa ma da suka fahinci gidan yanzu ba kamar da can da anty take ita kadai bane da suke zuwa gurin maigidan ko ita sukawo koken su garesu kuma ya taimaka masu koma bai nan anty zata iya taimakawa da dan abinda ke gareta.
Amma zuwan yaran nan biyu gidan yasa kowa ya jaye daga shiga gidan tun zuwa da wata daga cikin yan uwa tayi Zulfa tace ana yawan damun su da zuwa kullun sai wani yazo kuma rokone su ba, a bari yai masu hidima yadda ya dace sai dangi.
Take labatin ya bazu ga dangi kowa ya kama kan shi yanzu basu zuwa suma basu zuwa inda suke zumunci na batun lalacewa.
Nan dai take cewa to ni ba wani abu nazo yi ba baki da labarin yar uwar ku ta sauka ne tunda dare halan ?
Sai da ta ya mutse fuska take cewa ya bugo min amma ai naga gida daya muke ita bata fada muna ta haihu ba sai shi dake wata kasan zai bugo muna waya.
Mama Laraba tace lalai Zulfa kinyi nisa shi mijin naku bai isa ba ke nan ya fada maku kubi sai naki ra, ayin ko anya zulfa kin wa kanki shimfidan arziki kuwa ?
Kada ki manta yadda kukai tabin mu keda uwar ki akan akama kafa ai auren nan a tsakanin ku yanzu kina ganin kin samu shiga shine kike fito da kalar ki kina hura hanci ko?
To kiyiwa kanki kiyamallaini tun yaron nan baidawo ba naki ya samay ki gidan nan wai ke baki tunanen mutuwa ne arayuwan ki komay ?
Ran Zulfa ya baci don mama laraba na yar mahaifiyarta ne data fada mata magana sai dai duk da haka tace mama ai ko ba, a kama kafa ya aure ni ba Allah yayi aure a tsakani da shi dama yaya za, ayi tunda Allah yayi shiga kima daram ba fita.
Zulfa ni kike fadawa haka to ki sani ni ko uwarki bata kallon idona ta fada min magana haka kai tsaye don akwai mutum biyu a tsakani na da ita.
Ki sani ni tallaka ne cikin dakin mu amma ban dogara da abin wani ba nawa nake mikewa na bida don haka babu mai kallon idona ya fada min maganan akan abin shi.
Nasiha ne nai maki ba lalai bane sai kin dauka indan zaki gyara ki gyara Alhaji karami ne kin san halin shi tun baki shigo ba.
Idan zaki sauke girman kai ki rufawa kanki asiri kije ki gaida yar uwar ki ki mata barka da arziki daya fi maki.
Zulfa tace mama laraba da kece kika haifeni nake cikin wanan daulan bazaki ce najeyiwa matar da bata kaunan farin cikina barka ba.
Amma yanzu nagane zumuncin baki wasu keyi wa yan uwan su ba har zuciba saade dai kishiya tace matar mijina Yusuf sai naga daman zuwa gaida ita.
Muushi mama tayi don yasan halin rashin kunya irin na yayan yar uwata halima don haka tace ba laifi dunuya ce girma gareta ai .
Mama ai tunda naga don saade ta haihu kika yo sakkon zuwa da farar safiyan nan da wani manufa kika shigo.
Ba laifi ni na tafi dama nace bari nazo naji dalilin rashin shigan ki gurin tane kuma naji nagode.
Ni fa mama kada ki kuma kulla min wani sbon sherin ina zama lafiya a dakina zaki zo ki samay ni da sabon fitana in dake kika haife ni bazakiyi min haka ba ai.
Mama laraba da takai kofa ta juyo ta kalli Zulfa cikin takaici tace lalai kan ban haifeki ba zulfa kuma bama zan taba haihuwan irinki jaira ba a zuriata.
Tasa kai tafice zuciyar ta cike da kunan mugun halin diyar yar uwar nata dama tasan wanan auren ba wani abin arzikin da za, a kulla a cikin sa.
Bata daddara ba Part din hindatu ta nufa ta samu yar aikinta na kwashe kaya don itama gurin kamar ba sabon guri ba babu gyara yadda ya dace.
Yar aikin tace tana ciki bata tashi ba tace ta diba mata ita can tafito tace wai tana tafe taci gaba da abinda takeyi.
Sai tsawon wani dan lokaci har mama na batun barin gurin sai gata tafito tana cewa a,a mama kece tafe ?
Suka gaisa take cewa da ita dama na shigo nace baki samu labarin haihuwan yar uwar zaman ku bane tun daren jiya.
Ta bata rai tace bata fada min tahaifu ba mama sai shine ke bugo min waya idan na gama zan shiga na lekata ai.
Koba komai mama ta dan jin sanyi gun hindatu tunda itama da ake kira da fitsarara yau dai batai mata fitsaran ba.
Kamar yar yar uwan haihuan ta data nuna ta isa a kanta amma ta rufe ido ta yaba mata magana masu zafi haka.
Tace hindatu ku dinga ba kan ku shawaran arziki kin ji zaman duniyan nan na dan lokaci ne ba mai daurewa bane kada zafin kishi ya rude ku.
Na kuma gode da mutun tani da kikayi yanzu don baki tsaya ja dani ba yadda na zata shi gyara kayan ka baya zama barna ni zan koma nabar ku lafiya.
Tace nagode mama zan shiga idan nayi wanka yanzu sai anjima tai sallama ta fito.
Nan ta dawo ta samu su Aisha tana fada masu abinda ya faru tsakanin ta da su .
Ran Aisha ya baci tace ita Zulfa har ta isa ta fada maki magana mama watau harta manta da lokacin da ta tare a gurin ki don taga an yarda anyi auren su da yaya don tasan cewa yana ganin mutuncin ki da kiman ki cikin uwayen mu ai barta wallahi sai tagane tayi maki rashin mutunci.
Shiyasa tun farko ban so ace kin je ba mama don yanzu jinkan su suke wani abu basu ganin kowa da mutunci a idon su.
Nan dai nake jin wasu bayanai a cikin hiran su akan family su inda na fahinci yan uwan mahaifiyan mijin anty suna da dan yawa a dakin su.
Amma shi maigidan anty yafi shakuwa da mama laraba a cikin su don kamar ita ta haife shi yake jinta.
Ashe shine dalilin da yasa ma tazo yanzu din don ita yake ji a matsayin uwa a gare shi ita hadiye yar tace ashe amma a gurin mahaifiyar su Aisha ta tashi.
Yinin ranan haka yan barka ke shigowa gaida anty dayi mata barka da arziki.
Niko ranan aiki kaman zai kashe ni amma banji komai a raina ba don ma ban dauke shi komai bani a gurina.
Sosai na mayar da hankali na ga anty na gurin kula da lafiyan ta wani lokaci har da na dan jaririn ya duk da mama na iya kokarinta akai amma jiki yayi nauyi yamzu mama sai a hankali take.
Ba komai zata iya aiwatarwa a kan lokaci ba haka yasa nakoma busy sai dare nake samun hutawa yadda ya dace.
Naga mata masu shige da fice nasan yan uwan anty da ban sani ba akan wanan haihuwan duk wacce tazo taga yadda muke da anty sai ta tambayeta a ina ta samau ni sai tace dasu sister din ta ce ni kawai.
Sai suce wai amma dai akwai mace a gurin nan yarinya kamar ita ta zauna ta tsara kan ta hakomai nata acan acan dashi.
Anty kance to kwalelen ku ban ba kowa kaunata sai nazaba mata wanda ya dace zai kula min da abata ayi wasa da dariya su wuce.
Sai bayan kwana biyu da haihuwa ranan sai ga hindatu ta shigo part din mu yin barka sai faman yatsune yatsune takeyi a lalace tai barka ana mika mata baby tace abarshi ai ta gan shi.
Tai sallama ta tafi mama tace ikon Allah ana dai kishi a nan harda jajiri da baiko san duniya ba ake kishi kuma ?
Zulfa bata shigo ba a cewan ta ai anty ba tura da kanta a fada mata haihuwan ba sai dai a cikin ranta kishi takeyi wai don samun guri anty ta kara haiho namiji tafi hindatu zafin kishi sai dai takan yi kokarin dannewa don hindatu masuyi yanzu ne ya kare yanzu datayi ya wuce ke nan bata da riko kamar zulfa.

Shigowan safe daddy yayi garin lokacin ina kitchen ina aiki sai ihun yara naji suna taron shi da dawowa.
Haka yasa nasan dawowan shi ina kitchen ina ci gaba da aikina na tuna ruwan flask din anty ya kare da sauri na nufi dakin don in dauko ban tsanmani yana cikin dakin ba a lokacin sai dana shiga na ganshi zaune saman gado kusa da ita sai mama da kasa Anty Aisha da yazo tana saman kujera.
Gaishe da dawowa nayi shima yai min sannu da fama da kokari nai dan murmushi na wuce zan dauki flask din.
Naji yace wai wama ya karbi haihuwan nata ne haka a gida ?
Anty Aisha tace mama mana tunda itace a kusa daga inda
Showing 78001 words to 81000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27 Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153