fitinan haka ?
Na dire karshen magana na ina mikewa tare da kama hanyan fita part din raina a bace.
Ina fadin ai talaucin da take min gori ko yaushe a kan shi ba fin mu tayi ga Allah ba ya bata.
Daga haka na fice na barsu ina fita anty tace nasan za, a rina don mai hakkuri bai iya fada ba.
Yanzu kai daga kaji zancen ta shine zaka zo ka hau mutane da masifa in ace kullun abinda ake ana fada maka ne ai ba, a zaman lafiya gidan nan.
Tsuki yaja ya fice daga part din ina shiga part dina kuka yazo min yanzu shi ke nan don ya kasance anmin dole sai kuma aita musguna min ban ramawa ko may ?



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, DON HAKA CIN AMANA NE YAR UWA , , ,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA NA BARKI GA ALLAH YABI MIN HAKKINA AKAN KI NA CIN AMANAN , ,
46
Tun wanan ranan na kama kaina ban shiga tsabgan kowa agidan tun safe nake ficewa sai shidda zan dawo gida.
Na dan shiga gurin anty na gaida ita daga haka kuma sai gobe ko zaman hira banayi idan tai magana sai nace karatun exam na keyi shiyasa.
Ido ra samin wani lokaci gajiye kan shigo mu dan yi hira ta dan min magana mai kama da nasiha ta wuce.
Gaiwan da nakeyi wa matan gidan yanzu na daina sai dai su wuce in wuce idan mun hadu su bini da harara.
Yaran ne kan shigo duk dare mu dan bata lokaci dasu wataran inda sunyi barci tare zamu kwana dasu.
Yau Na dawo da yamma lis duk da agajiye nake kuma yamma yayi sosai ban wuce ba na shiga na gaida anty tace min ya karatu nace Alhamdullahi.
Daga haka na wuce ciki nai wanka nafito da alwala na tayar da sallah na dade zaune a gurin bayan na gama adduoina na shiga tunanen duniya.
Sallaman anty ne naji ta shigo har bedroom dina ina ganin ta namike zaune ina cewa anty ina wuni.
Bata amsa min ba ta samu guri ta zauna tare da kura min ido na tsawon wani lokaci gyara zama na nayi da kyau don nasan tunda naganta magana ne yakawota guna.
Tsawon dan lokaci mu haka da ita ccan tace dani Rama haka zamuyi dake yanzu ?
Na dago kai a hankali na dan kalleta sai kuma na dukar da kaina a kasa tace ban taba zaton tun yanzu zaki iya watsa min kasa a ido ba haka ?
Nace anty ni kuma tace ke mana Rama dan maganan da akayi ya wuce kin rike shi a ranki kina ta fushi da kowa a gidan.
Kina ganin matakin da kika dauke shine mafita a gare ki ko may ?
Nace anty gara na bar masu mijin su kowa ya huta tunda nice matsalar su agidan.
Dana zauna ina jawo maki matsala keda mijin ki akan gaskiyana fa ya rufe ido a gaban mu yai maki rashin mutunci.
Bazan tsaya don ina yar kauye diyar tallkawa ba adinga ci min mutunci da mahaifana da basuji basu gani ba.
Shine matsalan ki ke aiko in kishiya ne har fiya da haka zakiji a gareta tunda burin kishiya shine kullun taga bacin ran kishiyar ta a fili kinga sunyi nasara akan mu ke nan.
Amma kina haka basu ba koshi may gidan dariya zai min yace aigashi abindana shuka tun ba aje ko ina ba ga abinda aka girba akai.
Tausayi ta bani tunda ita har yanzu gani take a ranta itace ta sa daddy ya aure ni bawai yana so bane yayi.
Namiji fa mai mata fiye da daya dama haka yake idan halinsu ya motsa basu tsaya bincike sai dai su yanke hukuncin da suke gani shine daidai a garesu.
Haka halin maza yake kin sani ra, ayin kan su suke bi bawai abinda sharia ya kidanya ba.
Nace anty ni kan ba zan tsaya kullun ana zagiki da iyayyena ba kuma ace mutum wai kada ya rana dan ta fada min na fada mata shine kuma zai zama laifi anty ?
Ki daina wanan maganan Rama abinda ta fada mashine yai amfani dashi amma nasan ai zaizo ya gane gaskiya wata rana da kan shi.
Nace ai ba sai ankai wata rana ba mijin su daine na bar masu abinsu ba shi ke nan ba dama don kine na daure nake wanan rayuwa yanzu ko anty don Allah a hakkura dai hakana.
Ke yanzu matakin da ki ka ga yafi maki ke nan Rama watau ban isa ba dake ke nan yadda nake tunane a baya ?
Nace anty kin isa ke ma kin sani da ba don ke ba wa ya isa yai min haka a zauna lafiya sanin kankine duk abinda nake akan ki nake yin shi a duniya.
Tace to naji na kuma gode don nasan kina min bawai ban sani bane Rama ?
Yanzu fada min matakin da kika son a dauka nan gaba nace wani mataki zan dauka anty banda na bar maku mijin ku na koma gaban iyayyena ko kasa suke ci su kwaba su bani yafi min darajan akan wanan irin balain haka.
Fitinan safe daban na rana daban kullun cikin tunane da zulmi gari ke wayewa mutum don bai san da wacce za, a tare shi ba duk kuma baka tsira ba kaine mai laifi dai.
Tace ashe Rama da sauran ki ina cewa kin kai ashe baki kai ba dama hakan ai shine kishin .
Idan zaki jawo mijin ki ku zauna lafiya yafi maki inkuma kince ba zaki tausasa zuciyar ki ba akan kishiya kinaji kina gani ki koma yar kallo da reno a gida.
Don hakan da kikeyi ba zai kaki ga komai ba akarshe sai tarin nadama da dana sani nan gaba.
Nace idan na zauna ganin kwam ke nan a cikin ku anty exam nake jira na gama next week na kama gaba na don ban zama a na wullakantani har abin kema ya shafe ki.
Lalai ma Rama wai kina hauka ne ko may da kike fadin wai ke zaki tafi zaki tafi ina wai ?
Har kina ikirarin kin bar muna mijin mu kishiyace zakiyi fushin zuciya kice kin barwa miji Rama aiko in haka zakiyi wataran za, ayi bake wallahi.
Nace ni yafi min anty nagaji wallahi bazan iya ba ai tawa mutum cin mutunci har iyayyen shi in kuma kai magana ka rama ace ka taba matan gida a sauke ma balai.
Ni dama nasan Allah ne ya jefoni cikin ku ba wai son raina bane don bazan iya wanan bakin fitinan ba haka.
Gara na bar gidan kowa ma ya huta in dai don nice ban ko sauke ba balle ince a tayani azawa akai.
Wai ko Rama kin ko san aure kuwa auren ma kuma na mai mata da zaka zauna da kishiya ?
Nace ai in ban sani ba yanzu na sani tunda zahiri nan na gani akan gaskiya na akaci maki mutunci.
Badai ke akaciwa bani akaciwa ko kuma ni din dakike jiwa na sake kece bazaki sake ba ke nan.
Ashe hasashen da nake a kan ki na zaki iya ashe abin ba haka yake ba ke nan tun yanzu gashi kina son watsa wa mutane kasa a idanu.
Na dauka ko a bayana zaki rike min alkawari ashe ni ke haukana agurinki abin ba haka yake ba.
Kina ganin idan kinyi haka kin kyautawa iyayyen ki damu ke nan Rama.
Anyi magana kice ke zaki wuce zaki wuce zuwa ina don dan wanan magana kawai.
Nace anty da na zauna ana min sheri ace kuma ban magana don ana takama da an fini asali ko wani abu gara na bar gurin tun ana sheda juna da ido biyu.
Na dukar da kaina wasu irin hawaye suka fara zubo min a lokaci guda ina fadin ni ban iyawa anty gaskiya mijin su daine yasa suke min haka ko to na bar masu abinsu azauna lafiya.
Kuri tai min da ido tana kallon yadda nake kuka cikin tausaya min don tasan cewa itace tasani cikin wanan rayuwan haka da nake ciki.
Ga dukkan alamu magana na ya shigeta sosai don tasan nikeda gaskiya ga maganan babu dai yadda zatayi ne kawai akai.
Sai dai duk irin yadda nake ji bazata bari na tafi ko ina ba don tasan bacin raine yake damuwa na haka irin namaza da suke kunsawa mace.
Don ko ita da farko ta dau abinda zafi amma yadda taga na dauka sai take gani idan batayi saurin kawo iyakar abin ba zai iya jawo matsala fa kowa ma.
Naji tace yanzu dai kin nuna min ke nan ni bban isa dake ba Rama kin daina jin maganata ko ?
Cikin kuka nadago nace anty ba hakana bane don Allah kiyi hakkuri ki barni na tafi gidan mu ki raba wanan auren da babu komai a cikin shi sai bakin rigima da rashin kwanciyar hankali komai nayi a gidan nan ba fita zanyi ba .
Don ni nazo na samy su da mijin su kinga kuwa idan nace na nace sai na zauna nan gaba abinda za, ayi min sai yafi wanan ma .
Don Allah anty ki barni in tafi ki huta su huta ba sai ina nan ba za ai fitinan dani.
Kiroka min a sallamay ni na bar maku gidan ku ku zauna lafiya dakowa shine mafita.
Na karshe maganan ina mai fidda sautin kuka cikin ban tausayi ita dai ido ta kura min kawai tama rasa may zatace dani a lokacin.
Idan anki sakin fa ?
Muryan daddy ne da bamu san yana tsaye daga kofa ba yake magana tare da karasa shigowa dakin kai tsaye hanayen shi zube cikin aljihun shi.
Dagani har ita muka daga kai muna kallon shi don ba wanda ya tsanmanci zuwan shi a wanan lokacin.
Nace aiko ba saki zan tafi don shine sauki a gareni dana zauna inda matsayina baikai ba ana zagina da iyayyena idan nai magana ace naiwa matan gida rashin mutunci haka.
Ban saba sakin mace ba ni a rayuwana don haka in ma shine gurin ki a ranki kiyi gagawan kawar da wanan shawaran don baki da nasara anan.
Laifi kikayi kuma nai magana kewaye da baza, a maki magana ba kan abinda bai dace ba kice ke baza, a gyara maki ba ?
Nace ai wanan ba adalci bane daga jin maganan mutum daya sai azo a samu sauran da fada da cin mutunci ni gaskiya wallahi bazan iya ba.
Don ana takama anfini anfi iyayyena sai na zauna a na takani yadda akeso har da baren gida kuma ace kada na rama.
Wanan yanzu matsalarki ce wanan nidai ba zan yarda ana min rashin tarbiya ba agida na kyale ko ma waye ?
Nace ni duk wanda ya sanni bai cewa banda tarbiya a cuce ni kuma nai magana karo na farko ace banda tarbiya ai Allah na gani yasan mai gaskiya.
Yace hmmm haka kuke ashe duk mata ke kingani da idon ki ba labari aka baki ba ko yake cewa anty hakan ?
Ya juya zai fice daga dakin nace ai ita tasan halina bazatai min hukuncin da bashi ba akaina.
Anty tace ana magana kuma ka juya zaka wuce ba akai karshe ba.
Yace may kike son nace mata kuma bayan kinji magana tun farko zagine bani so ko ita ai nai mata magann haka.
Daga haka ya juya abin shi ya fice anty tace kin gani kinga galin maza ke nan shifa bawai ya rike maganan bane fa yayi a lokacin kuma ya wuce gareshi.
Nace ya wuce mana tunda ita an mata yadda take so taji dadi tai dariya tace anya Rama ba kishi kika fara yi ba kuwa ?
Nace anty aiko kishi nake ba zan so na jawa wani halaka ba a rayuwa su dai da suke kishina zan bar masu miin su a huta.
Don Annabi yace kasowa dan uwan ka abinda kakeso wa kan ka ba zan yarda don ni ki zauna ana bata maki ba haka.
Tace to ni dai na baki hakkuri kiwa Allah kibar zancen nan hakana don Allah dai ya wuce hakan ma da kikayi ya isa.
Don ko ba komai gobe idan wani abu ya faru a tsaya ayi bincike kafin a farwa mutum daya.
Don Allah kiyi hakkuri ki koma normal kamar yadda kik da farkko da kowa kinga ko yaran ki yanzu da sun fara damuwa da rashin ki.
Ta mike tace na barki lafiya komai ma ya wuce don Allah ban son a kara tayar da zancen kuma.

********* ********* *********
Ranan da zan karbi girki nayi komai sai dai kafin ya dawo masalaci har na jera komai na dawo dakina na zauna don nasan idan anty ta fahinci wani abu zatai min magana.
Ko da daddy ya dawo daga sallah ya samu abincin shi a falo sai dai bani a cikin falon kamar yadda na saba idan nakai na zauna sai yaci na kwashe kayan.
Haka ya zauna zuciyar shi a vunkushe ba dadi ko kadan ya dan taba kadan ya bari duk da abincin yayi dadi kuma yasan nina girka shi da kaina.
Shiru shiru baiga na shigo ba yanayi yana kallon agogon falon har gooma saura ya mike ranshi a bace zuwa cikin gida.
Part din anty ya biya bani ciki sai yara dake kallo ya shiga gurinta yai mata saida safe ya fito.
Direct part dina ya nufa kofan yana a rufe ya murda sai yaji shi abude yake ban riga da na rufe ba ko.
Ina zaune a kasa nayi rigingine da kaina a saman kujera idon a rufe ina karatun kur,ani da kai ina dan juya kafana daya dake a dage.
Yashigo har yai tsaye a kaina ban sani ba sai kamshi shi danaji yasani gane yana dakin.
Na dan bude idanuwa na a hakali na gan shi a tsaye akaina na maryan na rufe tare da kai aya na sadakallahul azeem.
Yana tsaye dai ya kura min ido baiyi magana ba sai yakai zaune saman kujera.
A hankali ya mika hannun shi ya dan rugumoni na jaye jikina sai ya dan sauko ya kama yatsun kafana a hankali yana dan ja cikin tsigar wasa.
Ina jin hakan har cikin raina sai na dake kawai ban yarda na sa a raina ba balle abin yai tasiri a jikina.
Ganin ban bada wani reaction ba yasa naji yace humm Rahama ashe haka kike da riko ban sani ba.
Yana batun rugumoni na ware idanuwa na nace please daddy stop nace daddy ina ganin kimar ka da darajan ka sosai dakai da matar ka shiyasa nake rage wani abu.
Ni ba yar kowa bace kuma ba yar birni bace face yar kauye fakiriya kamar ko wace yar tallaka.
Yana jin abinda na fadi naga ya mike ya koma saman kujera ya zauna yai shiru can naji yace.
Rahamaa zauna da kyau muyi magana dake bani son irin wanan rayuwan da matana sam.
Jin abinda ya fadi yasa na dan kara gyara zamana don girmamawa gare shi.
Yace nasan kin san dai aure mukayi wanda ake ganin a bisa kaddara mukayi shi ni dake.
Amma iyanzu dani dake mun san aure ne na so da kauna mu Allah ya tabbatar muna akan mu.
To dan may kike kokarin son tarwatsa muna farin cikin mu a hakan da kikeyi yanzu ?
Wanan abin da kikeyi zai sa dani dake dama antyn ki ai muna dariya don idan tayine daniyar fanshe haushi to haushin ta kara akaii.
Duk macen da kika gani a gidan nan nasan halin kowa a cikin ku dakuma haka nake zama da kowan ku.
Yadda na dauki kowa a gidan nan haka kema na dauke ki don a matsayi daya kuke gare ni.
Idan naa kyale ki har kika saba da zagin iyayye irin na Hindatu haka zaki saba dayi kema baki jin nauyi da kunyan yin haka ga kowa.
Amma ni magana ta nayi shine akan gaskiya sai dai ku kun kasa fahinta saboda akidar ku na mata.
Koda ban gurin kukai fadan nasan wa zai fara zagi a cikin ku amma sai na fifiita ki nai maki fada don ki gyara tunda ita nayi nayi ta daina ta kasa bari ya zama mata hali zagi a bakin ta ba komai bane ita a wurin ta.
Nace amma daddy shine zaka hada har da anty kai mata tas matar dake iya kokarin ta akaina akan may zan zauna ana bata mata rai sabodani ko yaushe bayan tana fama da kanta.
Yace nafa san abinda nakeyi Rahama ita saade da tasan halina aikin ga bata dauki abinda zafi yadda kika dauka ba ke.
Daddy ni banin son har wata rana magana ya kai ga hajiyan ka tazo tai min yadda naga tawa anty kaga kawai ka sauwake min kowa ya huta tun ba, aje ko ina ba.
Tun yaushee hajiya taji zancen ai sai dai kada akara kawai amma tun ranan mahaifiyar hindatu
Showing 198001 words to 201000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67 Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153