maigadi nakeji yace don Allah hajiya kada ki kula mata koda sun dawo gareki don sunce zasu dawo su samay ki.
Nace ai a shirye nake da zuwan su muka shige Fatima ta rufo kofa tana bani dariya.
Can gida da ra koma da kuka ta shiga gidan su tana fadin wai na asirce miji na hanata zaman lafiya dashi a gabana ya koreta gidan.
Tace mama ki duba fa duk irin kudin da muka kashe wai amma ace har ya dawo yana rawan kafa a gun wanan yarinyar haka.
Shine yan uwanta sukace zasu zo gidan su min dukan tsita suga abinda za, ayi akai.
Allah ya taimakeni bani gidan har yaran shine suka koma da cewa zasu dawo.
Da maigidan ma ta dawo maigadi ya fada mai komai ranshi yai matukar baci yace ai zai je yaiwa mahaifinta kashedi kan haka.
Yana fitowa sallah gidan ya nufa ya shiga har ciki ya samu mahaufanta yai masu magana yace wallahi duk wanda ya taba mai mata sai yasa an daure shi kuma ya saki hindu din.
Mahaifinta ya bashi hakkuri yace yaya zancen komawan ta gidan yace ba yanzu ba baba sai tagama yawon ta duk inda take son zuwa sai nabata izzinin dawowa gidan.
Tana kallo ya barta gida ya dawo shi kadai nan ta shiga hauka da zagi saida ta gaji.
Ya dawo gida yauma irin najiya ne ta kasance tsakanin mu nasha murza saida na yabawa aya zaki ranan .
Da safe aka sallamo anty muna shirin zuwa sai gasu sun dawo gida da ita nan muka cika ta muna murnan dawowan ta.
Nan dai muka sha hira don taji sauki sosai tabi part din ta da kallo komai tsab kamar tana nan ba wani canji a cikin sa.

********* ********* *********
Ranan monday da safe daddy ya shirya yace zai tafi abuja tunda muna hutu na shirya tare zamu tafi.
Ban so ba don ban son barin anty tunda bata gama warkewa ba sosai amma yai min jan ido dole na shirya muka tafi tare dashi.
Acan daddy ya gwada min ba wata mace a gaban shi bayan ni don ya gwada min so na sahihi a can bamu komai sai murzan junan mu kawai da mukeyi.
Satin mu biyu muka dawo inda na dawo masu da tsaraba mai yawa naba kowa a gidan mun samu hindu ra dawo dan Alhajin shi da kanshi ya dawo da ita gidan .
Yaso ya nuna bai yarda da dawowantw ba gidan amma yana jin mahaifin shi ne ya dawo da ita dole yai hakkuri ya kyale ta sai dai ya kudurta a ranshi zai dauki mataki akanta sosai.
Tun wannan lokacin takon zaman su ya sauya a baki daya tsakanin shi da ita ta rasa gane kan komai a gidan.
Sai ta dauki laifin gaba daya ta dora akaina cewa nine nayi mata asiri takoma haka da mijin ta.
Ni dai ban kula a haka mukai rusuming makaranta na koma inda wanan time din pratical yai muna yawa muna zuwa asibiti gurin gwaji ban da time ko kadan ga fitinan daddy daya sani gaba bai iya boye fleeling din shi a gaban kowa.
Zulfa ta haihu ta samu yarta mace yaso saka mata sunan mama Laraba watau Fatima, amma tace bata yarda ba har yaso ya kawo masu fitina tsakanin su anty ta raba gardama tace tunda bata so kayi hakkuri kada a saka ta dinga cusgunawa yarinya a banza kaikuma bazakaji dadi ba gaskiya.
Dole ya hakkura ya barta tasa sunan da take so din suna Nusaiba yarinyar taci dama dashi tazo duniya ke nan.
Kamar kada ta haihu sai ita kuma ta fara bulo da nata tsula tsiyan a cikin gidan don ita macijiyar soshiya ce mai sari kanoke ta iya munafunci sosai.
Idan ba mutum yayi da gaske ba bai taba gane sherin ta amma da yake anty ta taba fada min sai nake hankali da ita sosai bana shiga harkan ta duk yadda taso jana ajiki naki yarda da ita sam.
Harkan business din cf shi yana ci gaba ga aikin su da yake samun girma ya kkara zama bunkasashe sosai matashi mai tashen naira.
Tafiya ya kamashi zuwa waje inda kai tsaye ya nuna cewa dani zai tafi bai tsaya tambayan ra, ayin kowa ba bayan ya taramu yake fadi.
Ina jin hukuncin da ya yanke nace daddy da sauri daddy karatuna bazai bari nai tafiya mai nisa haka ba don Allah a taimaka min ajenye wanan tafiyan dani.
A hasale yace karatun ki yafi maki tafiya dani ko may Rahama ?
Na duk da kaina kasa sai hindatu ce tace ai dama hakane ga rashin adalci ita da kake son zuwa da ita bata damu ba muda ke son zuwa ka hana mu.
Tsawa ya daka mata yana cewa ki rufe min bakin ki ke yanzu in kina da hankali ba abin kuya bane a gurina ace ban taba fita da Rahama ko ina ba duk zaman ta gidan nan.
Ita kuma da anyi magana sai tace wai ita karatun ta karatu kike ko bauta aure da zaki dinga fakewa ga karatu kina kuntata min.
Kowa a gurin ido ya sa mai yadda ya rufe ido yana fada haka akan tafita da mace a gaban kowa ba kunya kuma kowa ya gane manufar shi.
Anty da dama ba halinta bane idan an zauna yin magana don kama mutunci sai tace baka riga ka yanke hukunci ba yace hakane tace to ai shike nan ke Rahama sai ki fara shirin tafiya bashi ke nan ba zance ya kare kai kuma kayi hakkuri tayi kuskuren yi maka mussun da tayi.
Tana fadin haka ta mike ta bar falon hindatu tai tsuki tace munafunci dai baiyi ba wallahi.
Wai mutum ya dinga karya da cutar kan shi wai shi don ace dashi nagari salihi ko may oho ?
Zulfa ta mike tana cewa wanan kuma matsalar mutum ni dai nasan idan zuwa na yazo babu mai tauye ni ga zuwa ai ya kwana gidan sauki.
Ta mike ta saba yarta a kafada ta bar falin sai nima namike nafice abina na barshi da hindatu tabi bayana da harara.
Taja tsuki tace ni banga abinda wanan figagan yarinyar tafi wani dashi ba amma kake wanan rawan kafan akanta.
Yace kema ai nayi a kan ki dai ko kuma har yanzun din ma inayi ko akwai abinda nai wa wata a gidan nan ban maki ba ?
Tace gashi kuwa kai min akwai ranan da ka taba jajircewa akan sai nabika a bainan jama, a haka yadda kayi yau akaina ?
Kyaleta yayi yaci gaba da abinda yakeyi tagaji da zama ta mike tafice falon rai a bace.
Sai da dare dana shigo gurin anty na zauna take cewa yanzun nake batun tura Gajiye ta kira min ke sai gaki.
Nace na tsaya gyara wardrove dina ne da akai min gogu jiya nake cewa da ita wai anty ni sai naga kayana har guda biyu an yanka min ta kasan zanin sai rigar ta wurin hammata shima an gutsira.
Tace yanka fa nace wallahi anty to kada kiyi amfani da su ki bayar dasu a sadaka don ba a san may akayi da shi ba.
Shiru mukayi kowa da abinda yake tunane a ranshi kan wanan bakon al, amarin sai can anty tace dani Rama may zai sa mijin ki yace ga abinda yake so ki ki tsaya kina gardama dashi a gaban kowa haka.
Nace anty ni ba wai nayi gardama bane kawai naga karatuna zai tsaya ne don yanzu kinga ko yaushe muna zuwa gwaji asibitoci.
Wai karatun may Rama kina ganin cewa ko kinyi wannan karatu besty zai barki kiyi aiki ne.
Cikin mamaki na dago kai ina kallon ta tace sa,arki daya shine kin fara karatun nan kafin kuyi aure kuma yasan yadda kike son karatun nan shiyasa ya daga maki kafa kawai.
Amma idan kina mai wanan gardaman haka kan bukatan shi zaki iya jawowa kanki matsala nan gaba.
Nai shiru na dan lokaci can nace anty nagode insha Allahu zan kiyayye hakan na fara shirin tafiya ba wasu kaya na dauka ba sai dogon riga guda biyu.
Tashin dare zamu yi don zamu biya saudiya muyi umura yace haka yasa nai shawaran idan naje can sai na saya kawai.
Ana jiran afito da kayana sai ga yar jakka na fito dashi duk matan nashi suna tsaye suna ban kwana dashi.
Duk suka bini da kallon mamaki na karasa gurin anty duk wanda ya ganni yasan ban son wanan tafiyan a raina na karasa gurin anty .
Na rugumay ta sai kuka tadan kashe murya tace dani may ye haka Rama kada kiba mijin ki kunya please.
Na daure na share hawayena nake cewa da sauran sai mun dawo a takaice daga haka na shiga mota muka bargidan da yaran suna daga min hannu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA GASKIYA, , , , ,

IDAN KIN BIYA KIKA TUWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH DON HAKAN CIN AMANAN ZAMANE, , , ,
50
Mun isa Aminu kano international airport kai tsaye muka nufi gurin screening don mun zo a makare.
Bamu dade ba aka fara shiga jirgi ina wanan ne karona na farko da zan fara shiga jirgi a rayuwana.
Sai da na dan dafe kaina bayan belt din dana daura saboda yadda na ji dagawan mu.
Tsawon lokaci muka dauka a zaune tun ina marmari har na fara gajiya da zaman.
Da asuba muka isa saudiya inda naga wani yusuf yazo taron mu a jidda nan ya dauke mu zuwa masaukin da aka tana dar muna mu dan huta.
Hotel ne tsarare mai hawan bene kusan goma sha tsayawa fadin tsaruwan wurin bata lokaci ne nidai yar kauye sai aukin baza ido nake ina kallon ikon Allah.
Na fahinci daddy yana fushi dani ne wanda bai rasa nasaba da kin biyo shi danayi da girma da arziki.
Sallah nayi tundaga magariba ishai da asuba ban ko tsaya neman abinda zanci ba don barci da gajiyan dake tare dani.
Barci nayi sosai sai sha biyu na falka koshi yunwa ne ya falkar dani lokacin dole na tashi abinci na gani an aje min na fada ban daki na sake wani wanka nafito na zauna naci na koshi sannan namike na kimtsa jikina.
Daddy bai dawo ba sai da yamna lis suka shigo shi da abokin shi ina jin bashi kadai bane nai sauri jawo hijjab dina na saka.
Nai masu sannu da zuwa tare mikewa na bar falon nan suka zauna tare da baje wasu takardu da ban san ko na may ye ba.
Ina ciki kwance sai gashi ya shigo dakin da saurin shi yana cewa na miko mai wani jakkan shi da muka zo dashi shi kuma ya dauki laptop din shi ya fita nabi bayan shi dauke da jakkar.
Na tsugunna don girmamawa na aje mai a gaban shi inda yake zaune saman kujera masha Allah yusuf yace cikin hausan su na yan saudiya yake fadin.
Wanan dabiar na matan hausawa yasa nakeji nima naje nageria nayo aure a dinga min haka.
Murmushi daddy yayi kawai ni dai nabar gurin tun ba, a jamin wani sabon fitina ba kuma ina fama da wani.
Sun dauki lokaci a tare sai dare so sai ina shirin kwanciya naji daddy yana kirana a falo.
Na mike da sauri na nufi falon suna tsaye tare da mutumin yake cewa Yusuf zai tafi yana son ku yi sallama ne.
Yusuf din ya juyo gareni tare da cewa hajjiya Rahama na gode ni zan tafi sai ki kula min da mutumina kin san shi da ka,ida don nasan halin shi sai kinyi hakkuri sosai duk da naga alaman kina da saukin kai sosai.
Daddy yai murmushi yace yusuf sheri kuma zakai min kasa ta dinga dauka na mugu kuma yace na san ka ne ai.
Kudin su na can ya miko min masu yawa yace amarya kiyi hakkuri da wanan mijin naki bai fada muna da ke zai shigo ba shi yasa ban shiryawa zuwan naki ba.
Na karba cikin girmamawa tare da godiya suka fita daga dakin sai baya fitan su na kallin koren kudin dake hannuna masu yawa an rubuta masu Riyal , , , ,
Na bude bakina don mamakin yawan su duk da ban san adadin yawan su ba a hannuna amma nasan ba karamin kudi bane hakan.
Na koma daki tare da dora kudin saman drower na koma na kara mulke jikina yadda ya dace na kwanta.
Ban dade da kwantawa ba barci ya dauke ni koda daddy ya dawo ya samu nayi barci ko bai tayar dani ba sai da ya gama abinda yakeyi ne ya zo kwantawa yaga kudin da aka bani, na aje a saman kujera yasan shi nake jira dasu barci ya dauke ni.
Bai tayar dani ba don yasan gajiya ne don haka shima dama a gajiye yake ya samu guri ya kwanta.
Sai da asuba na falka ranan ko sallah nafila ban samu yi ba na idar ne yana zaune saman sallaya yana karatun kur, ani.
Ban zauna ba na koma na kwanta tare da dauko wayana dake kashe tun a jirgi na kunna.
Gari na haskawa sosai ya mike ya fada yai wanka ya fito dogon riga kawai ya zura ya hawo gadon shima ya kwanta nasan dan hutu yake so a ran shi.
Mikewa nayi daga kwance don har barci ya fara dauka na nace dashi daddy ina kwana ya gajiyan hanya ?
Alhamdullahi yace dani a takaice ya gyara kwanciyar shi da kyau tun ina tunane a raina har nima barci ya dauke ni.
Ban falka ba sai lokavin sallah azahar nai wanka nayi sallah sai kuma na fito falo ashe yana falon zaune sai aiki yake cikin laptop din shi.
Banyi magana ba na wuce wurin fridge din falon wanda sai wanan lokacin na bude shi drinks ne a ciki shake na zaro wani danaga anyi da mangoro.
Na samu kujera na zauna ina dan tsotso ina duban takardan da nazo dashi na karatuna kamar nasan da wanan kadaicin na dauko takarduna wanda sune suka cika min jakkata dama.
Karatuna nake hankalina kwance inayi ina tsotson drinks dina mai sanyi sosai jikina ya bani kallona yake ban dago ba naci gaba da karatuna sai da na kwatanci lokacin sallah yayi na mike na shiga ciki nai sallah ban fito ba kuma ban nemi abinci ba.
Ina gamawa na shafa addua na nafito na dauki takarduna dana bari na koma ciki can na ci gaba da karatuna ina yi ina hutawa sai tunane kawai a raina.
Ranan yin zur daddy bai fita ba yana zaune yana ta fama ture ture a laptop din shi bai kula ni ba nima ban kula shi ba.
Ina gama magariba na kwanta abina sai barci sai da ya gama ya shigo dakin ya samu nayi barci hankalina a kwance.
Ya dan tsaya yana kallona yaga yadda gashin kaina ya barbaje a kaina har ya dan rufo min fuska, ga takarduna danake karatu sun zube a kasa ya karasa bakin gadon ya duka ya kwashe min ya aza saman drower.
Yai wanka ya fito sai da ya shirya ya koma gefen gado ya kwanta zuciyar shi fam da tunane yaso ya tayar dani amma sai ya daure ya ja ya rufe jikin shi.
Kwanan mu uku a jidda muka kwasa zuwa birnin madina bamu kwana ba saida muka mika gaisuwar mu zuwa ga mafificin halitta tare da sallah a masallaci mafi daraja muka dawo masaukin mu.
Shirin kwanciya nake ya shigo dakin ya danyi abubuwan da yake na al, ada ya tako zuwa inda nake kwance zama yayi dap dani yadda jikin shi ke gugan jikina yake cewa Rahama nasan idon ki biyu kina jina ki tashi muyi magana.
Don bazan yarda falala da daukakan dake cikin garin da mafi fiyayyen halitta yake kwance ba ya wuce muna cikin wanan halin na rashin fahintar juna ni dake ?
Jin abinda yace yasa na bude idona tare da cewa daga kwance fushi daddy ni bani fushi da kai ai.
Akan may zanyi fushi da daddy na riban may zanci idan nai fushi dakai a rayuwana daddy kana a matsayin mijina kuma gin shikin rayuwana ?
Murmushi naji yayi tare da cewa ban tabbatar da ina da wani kima ba a gunki tun da har kina iya share ni na tsawon lokaci.
Rahama kin bani mamaki don da wani yace zaki iya tauye min hakkina ki hanani abinda Allah ya halasta min akanki zanyi mussu ga hakan.
Amma sai gashi kin rufe idon ki kin juya min baya ba ruwan ki da damuwa na bayan kin min laifi amma girman kai ya hana ki ki bani hakkuri ga hakan.
Nace cikin wani murya daddy nice kuma nai laifi bakai da ka rabani da diya na ba kazo dani nan kasar mutane ka watsar dani, dani da babu duk daya a gare ka.
Yai murmushi tare da sa hannayen shi ya juyo ni gare shi yace ke shine naki fushin na rabaki da yaran ki
Showing 216001 words to 219000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73 Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153