ba abu bane mai wuya a gareta.
Sunan matar aka tambaya tace hajiya taoe kiran ta da shi amma taji Saade na kiranta da Falmata ne.
Falmata daddy ya nanata sunan yace dama nasan za, a rina ai don Falmata bata bin Saade haka ga banza.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,

65
Nidai a bangare na ba wani shirin suna nake ba sai zarah ne ma tazo min da zancen abinda zamu yiwa kawayen mu idan sunzo kudi na bata da buhun shinkafa da sauran abubuwa sauran da babu zata je ta saya ne can.
Don ni ba wasu kawaye ne dani ba can sosai ashe abin ba hakana bane ance wanda yariga ka kwana yana riga ka tashi ita Zarah ta san kwanan wasan.
Ranan daren suna sai ga sakon kaya wanan matar mai aikin anty ta shigo dashi wai anty ce tace a kawo min kayan baby ne masu kyau sai turamay zanuwa guda goma.
Nan gardama ya fara wasu suka ce wai a mayar mata a dauki kauan baby din kawai wasu kuma sukace wai duka za, a mayar mata dasu ai abinda ba don Allah akeyin shi ba azo ana maka gori daga baya.
Duk sai da na bari sin gama zancen su nace bazan mayar ba kada fa ku manta Allah ne ya kaini ga wanan matsayin ta sanadin alherin wanan boyar Allah.
Don may baza mu jinkirtawa hukuncin Allah ba kaddarane fa yana a kan kowa duk wanda Allah yaso da jarabta.
Nidai Rahama bazan taba manta halarci ba a rayuwana komai tai min da nai hakkuri ban rama ba bagashi Allah ya nuna mata gaskiyan abin ba.
Don haka cin fuska baida kyau ni ba chof and clean your mouth bane bazan taba mantawa da halarcin ta ba a kaina don tazo ta canza daga baya.
Attu tace kin yi gaskiya nima ba zan so ace amayar mata da kayan nan na tunda ba marasa godiya muke ba.
Mama da Attu ne suka tafi wurin ta sukai mata godiya inda suke fada mata cewa ai dare yayi ne shiyasa ni ban samu shigowa ba wurin ta.
Washegari tun da safe gidan ya fara cika inda bakin arziki masu zuwa taya mu murna kamar yadda idan an haihu akeyi a ko ina ranan suna.
Tun safen nan Zarah tafara zuwa da masa da ta dauko daga gidan Anty Amina da miyar shi sai abin sha da ta shigo dashi.
A lokacin ina daki muna magana da Attu da mama sai ga Zarah din yake fada min abinda ta kawo nake cewa da Gajiye ta aika a kowani shiya da masan ina lake da yaran anty na da suke tare dani tun safe.
An kai kowa ta karba ba wani fitina a hakan da sukayi haka yasa duk abinda aka kawo zance ta aika masu dashi zuwa goma na rana bakina suka iso garin.
Sam banyi tsanmanin zuwa su ba sai gasu da yawa su ashe bus daddy ya tura masu dashi ban sani ba.
Nan na shiga murna da ganin su na ma rasa waye zan tarba a cikin su don murna can bayan Larai na hango mama Laure tana kalle kallen shiyan nawa cikin damuwa da sauri na karasa gareta ina murna da zuwan ta sai dai ba wani fuska sosai dariyan yake take min kawai.
Har da amaryan babana ashe akazo nan guri ya kaure da murnan ganin su nasa Fatima ta bude masu dayan dakin da bamu amfani dashi duk da akwai komai a cikin sa nan suka shiga da kayan su.
Maman Altine ma tazo don duba jikin Anty data dawo daga waje sai da sukaci suka sha ne mama amaryan babana tasa Fatima ta kirani.
Nan take min bayanin abubuwan da sukazo min dashi nayi mamaki kokarin da iyayyena sukai min haka.
Zuwa karfe daya yan gari suka fara shigowa sai da hankalina ya daga don ganin yawan taron da akai min.
Ana tsaka da shagalin taron suna ne mukaji hayaniya ya kaure wai ashe hindatu ce ke fitina don may za, a yanka shanu da raguna biyu aikowa da ta haihu rago daya ya yanka mashi.
Daddy baiyi magana ba sai yan uwan shi ne suka tanka mata don Aisha ce tace da ita idan ci gaba yazo wa mutum ana son ya canza lokacin haihuwan ki daban wanan daban.
Shi ya bata haushi nan suka raba gari a tsakanin su har yakai yan uwanta sun so su saka baki fitinan yai nisa sai da daddy yafito da kan shi ya tsawata masu suka bari.
Lokacin da kawayena suka fara zuwa sai wiri ya rude da gulma a yan garin mu suna mamaki wa yan nan matan yan gayu wai ace kawayena ne su.
Gashi duk wacce zata shigo da ledan ta na gift zatazo min duk wanan jigilan da nake bai hanani yawan zuwa duba lafiyan anty ba ina kuma shiga na bata magani idan time yayi.
Walima sosai mai gyara harka ta hada min inda aka gaiyyato malami yazo yaiwa mata wa,azi akan zamantakewan aure a wurin da hakkin iyayye da yayan su kuma.
Nan ma anci ansha anyi photuna aka kuma watse lafiya ranan yan garin mu suka so komawa amma yamma yayi nace su bari su kwana da safe akaisu kasuwa sai su tafi.
Sunyi amanna da shawara na haka suka baje akaci gaba da sha, ani dasu sai dare kawaye na kowa ya kama gaban shi nan aka shiga gyaran wurin dan a samu wurin kwanciya.
Ni dai har akaci aka sude banga ko mutum daya ba daga ban garen matan gida banyi wani dogon mamaki ba don nasan za, arina dama da hakan.
Muna daki ne zaune ni da su Rukkaiya da Suwaiba daddy ya shigo part din bayan ya gaisa da mutane a ya nufi dakina din.
Sun gaisa da yan uwa na kuma gabatar mai dasu tunda sunayen su yake ji sai yake tambayan su mazajen su ?
Sun fice sun bamu guri mu gana dashi nan yake tambayana muna dai lafiya ko ban tare da wani matsalar komai ko ?
Nace lafiya muke sai yake tambayana may za, abawa yan gatin mu idan zasu koma, ne yace wancan karon da anty ki mukai shawara, sai nace ko yanzu ma da ita zaka kara shawara daddy aita inda aka hau tanan ake sauka .
Yafice zuwa dakin anty ban san yaya sukayi ba sai yake cewa dani ta na fada mai kawai abinda ya dace nan na fahinci akwai matsala ke nan nace dashi yabasu turamay da dubu biyar din su ashirin da biyu ne dama sukazo har kanne na maza da akazo min dasu su biyu.
Washegari sai ga Anty Aisha da kyautan tukwaicin ta kawo masu nan aka shiga murna naba mama Laure da amaryan baba suwaiba da Rukaiyya zanuwa a boye kada sauran ran su ya baci.
Rukaiyya na dankawa duk wanda yagani yai magana sai tace kayan sako ne zatakaiwa wata don nasan idan ba ita na bawa ba wani zai iya bude ledan yace ya gani a hannunta.
Wuce wan su yasa naji wani irin kewan su ya kamani sun so tafiya dani gida amma daddy bai yarda ba yace ba al, adan gidan shi ne hakan ba sai dai duk wanda zaizo ya zauna dani yana iya zuwa.
Don hakane aka barmin Attu da mama Abu matar maigari su zauna dani a dakina kamar yadda ya umurta din.
Yan suna duk wanda yazo yaga yadda anty ta soye sai a koma gefe a dinga tsegumin hakan .
Tun washegarin suna ban zauna ba ina kokarin kula da anty duk da ba wani karfi jikina ke dashi ba sosai amma haka nake daurewa ina bata kulawa mama Altine ma bata koma ba tana gidan tare da ita.

********* ********* *********
Dan hutun sati biyu kawai na samu nafara fita makaranta don saura wata shidda in kammala karatuna.
Ban zuwa da yaron sai dai yanzu dole nakan dawo karfe biyu in bashi nono in koma don abin ya taru yai min yawa akaina.
Ba girki nake ba shiyasa na samu saukin fitinan matan gidan don ba ruwa da zancen kowan su sai dai mu hade wani lokaci a compound din gidan kowa ya wuce.
Ranan sai ga maigidan ya kira mu a falo don har anty saida ta halarci wurin nice na shigo a karshe ina dauke da baba a kafada na.
Ina shigowa duk suka mayar da kallon su akaina sallama nai masu na samu wuri zan zauna naji daddy yace miki min shi nan mu gaisa.
Yana karban shi yake cewa babana yaya naga kana ramaywa kuma kaida kafito da girman ka yanzu naga ya fada kuma ?
Humm, umm ikon Allah dai bai karewa a duniya muna dai ganin mamaki kan agidan nan yaya za, ayi dama yaro yai kiba ido yai mai yawa haka.
An haifi dan gwal sai wani faman tarairaya shi ake kamar shine farau din zuwa gidan nan kafin wasu hindatu uwar rashin mutunci ke maganan.
Daddy yai murmushi ya kaiwa yaron kiss a fuskan shi yace bashi bane farau sai dai ki sani wanan babana ne sai dai kuyi hakkuri don ba mai wasa da alamarin mahaifin shi.
Tanan kuma aka bullo muna ai magana ace tsohon gida ne ba mai bakin takanwa akan tsohon gida.
Ina jin su nai shiru ina duban wayana dake a hannu na sai naji daddy yace bana son abin jawo magana please.
Yace na kira kune don ina son kowa takawo min sunayen mutum uku da zasu sauke farali a ban nan isha Allahu in an hada ya tashi mutum goma sha nawa mutum biyar sun kama sha bakwai haka nai casting din plan dina.
Gaba daya falon kowa yai shiru baka jin motsin kowan mu sai can daddy ya soma wasa da yaron dake hannun shi.
Zulfa ce takawar da shirun da cewa amma yayana mutum uku dadai ka kara muna ko daya ne ko ?
Ni ba mashi ba yadda duk kan mu muna da bukata muma ai banji an anbace mu ba daga tafiyan ko ana nifin har mu ke nan wai ?
Baidai yi magana ba sai anty ne tace shin kowan mu kujera uku daidai komai sai lokacin yace Saade so kike na wata yafi na wata yawa ne komay ?
Ke kuma dake fadin gar kukuna da bukatan zuwa ai idan zaki koma ne sai ki shirya ki dauki kujera daya daga ciki ko.
Zulfa idan har baki gode da ukun dana baku ba kina bukatan kari zaki iya karawa da kudin ki ai zaki iya ko ?
Nan kowan su ke magana mikewa nayi don agajiye nake nace mun gode daddy Allah ya saka da alherisa yasa badi afi hakan .
Yace Amin Rama nagode na nufeshi zan karbi yaron yace barshi zan kawo shi idan nagama ganin shi.
Ina ruwan dan baka saba ba na kauye ya samu burodi toshine may son kin nuna ke wai ta kirki baki korafi ba akai tunda ba a saba ganin kyautan kujera ba.
Hindatu ce ke wanan maganan nace da ita cikin sakin fuska shiyasa ai nake godiya wanda ya saba ma naga ai ya karba bai mayar ba.
Aikin banza ke nan ashe da so kike nace ban so ki kara da naki kikaiwa mutanen kauye ko ?
Nace shi aikin Allah da tallaka da mai kudi duk daya suke a wurin ubangiji ko ba a bani kujaran ki na karaba nagode da wanda aka bani tunda ban saba gani ba gashi yau Allah yakaini ga gani da raina.
Ina fadin haka na barsu a falon kowa ranta bai mata dadi ba don kowa da abinda ke damun shi ina tafe ina mamakin haleya irin na wasu.
Ta yaya za ai ma alheri mai tarin yawa haka amma ace mutum wai bai gode ba har ya tsaya korafi haka ?
Jama, a duniya mai na kashewa matan daddy ne dukkan su uku suke hattara na haka ne don nasan kowan su zargin ta ya shafe ni.
Ni may zan masu a rayuna nayi fari a gun su yanzu ma ayi muna abin arziki nayi godiya yazama kuma laifi don har anty na bataji dadin kalman godiyan danai amfani dashi ba a gurin.
Bayan na dawo daki na kwanta sai kuma tunanen yanzu wa zan bawa wanan kujeran kuma na san dai Inna ta da Babana suna daga ciki insha Allahu to dayan kujeran fa kuma ?
Maigari a, a ina Attu dai ko mijin ta kakana namiji don ban ko kawo zancen wani ba a fanin mahaifina don ba damuwa sukayi ba damu a baya.
Dan dama yanzu da sukaga baba nada dan rufin asiri suna dan sha, ani dashi don bukatan abin hannushi.
Can kuma na koma tunane watau daddy yana da wadata hakane ashe da har zaiyi kyautan kujerun makka har haka da yawa.
Sam bai nuna yana da zarafi hakan don shi ba mutum bane mai son yawan karyan duniya mutumin da hayaniya ma aikine a gareshi bai da ko yawan abokai haka agari.
Idan harkaji yace wani abokina ne to tabbatar wani harkan business ne ya hadashi damai shi din.
A hankali na lumshe idanuwa na ina kwance rairai ina kallon sama banji shigowan shi ba sai kafana danaji anja min.
Na bude idanuwa na daddy ne a tsaye saman kaina rugumay da yaron yace tunanen may kikeyi haka a kwance ?
Murmushi nayi na yunkura zaune ya miko min yaron nakarbe shi ina gyara mai kwanciya don yaton barci yake yi daya shigo dashi.
Nace daddy mun fa gode yace da akai may kuma again ?
Nace makkan daka ba yan uwan mu mana yace godiyan bai isa ba ke nan har yanzu ina son mutum wanda idan an mai alheri ya sani ba wanda zakaiwa alheri yai maka korafi ba naji dadin godiyan ki Rahama don haka mutum hudu zaki bani daga bangaren ki.
Da sauri na dago kaina nace mutum hudu daddy yace haka nace Allah nagode ma na fadi a fili nace mahaifana da kakanin na nake son suje daddy.
Yace wasu daga ciki ke nan nai saurin cewa Attu da mijin ta mana ai banda wasu kakan nin da suka fi min su a duniya don ni dasu na bude idona.
Anya Rahama baki son kai ba anan don banji ki sa kowa daga bangaren mahaifin ki ba sannan kuma in ga kara aiki hada da maigari su tafi ko ?
Nasan maigari ya cancanci hakan agare ni amma kuma aida girma na ya gani ga wayanda sukai wahala dani kuma ma suke a cikin yi har yanzu din.
Daddy dai bai min magana ba yabar dakin washegari da safe bayan nai wanka na shirya naje part din anty don na gaida ita tun daga kofan shiga dakin ta nake jin muryan ta daga daki tana magana sama sama.
Akan may zakace komai daidai da Rama zaka dinga min idan da nasan wanan auren cin amana zai koma min tsakani da kai da ban hada shi ba wallahi.
Duk irin rawan kafan da kake akan yarinyar nan duk ina kau da kaina naga abin yanzu yana son ya wuce wuri kuma hakana .
Saade wai may yasa kika canza gaba daya ne hakana please halin da ban sanki dashi ba a baya yanzu shine kike kirkirowa kan ki.
Tace dole ne na nuna maka abinda ka dauko yi min abaya akan sauran matan ka nai magana ka daina shine yanzu ka dawo da yin shi akan Rama.
Ke Saade ya ishe ki haka na gane ke baki san ana tausaya maki ba baki tausayawa rayuwan ki balle na wani.
Na fahinci baki kaunan a zauna lafiya har may naiwa Rama wanda ke ko ku ban maku shi ba a gidan nan.
Ko ku daban kuke gare ta da zan mata abu a kasa da ku nagane abin naki akwai son kai sosai a cikin shi.
Kamar yadda kike da iyagiya uku akan ki nawa haka itama take daure dashi a kanta don haka bazan wullakanta kowa ba don wani yaji dadin rayuwan shi.
Abinda na bayar ke nan wa kowa don haka in zaki bani list din ki ki bani idan kuma bazaki bayar ba duk daya a waje na.
Ke yanzu ba abin kunya bane agare ki ace kina wanan bakin kishin akan yarinya karama da kika tayar da hannun ki duk kin bi kin sakawa kan ki fitina haka kan abu daya.
Maimakon in shiga sai kawai naja kafana na juya na fice daga gidan ba tare dana bari sun san naji maganan su ba.
Sai dai na tafi da tunane da mamakin anty a raina wai shin haka kishi yake yasa mutum ko yana cikin wani hali bai tunane bai tunanen makomar shi, sai yayi wanan halin .
Ko dana dawo gida haka kawai sai na fara jin nima dan tsanar ta a raina kamar yadda yanzu nasan kishi yasa bata kauna na ko kadan sai dai dariyan hakori kawai.
Zama nayi da Attu da mama na fada masu komai sai da suka gama jina suka ce dani dama tana
Showing 267001 words to 270000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90 Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153