ada can nakanji na bar maki mijin ki don irin wanan halaiyar da kike nuna min a yanzu.
Sai dai a yanzu bazan iya barin daddy ba sai idan shi da kan shi ya bude baki yace na bar gidan nan digo baxan kara ba zan bar maki gidan ki har ma da dan dana haifa dashi.
Anty nabiki nabiki don mu sasanta a tsakanin mu amma abin yakiya a tsakanin mu aure dai nakeyi a gidan nan ba zaman banza ba kuma ke ce sanafin shi don Allah na roke ki da kada rashin mutunci mai tsanani ya biyo baya a tsakanin mu.
Ina fadin haka ban tsaya ba na fice daga part din don raina ya riga da ya baci yanzu na fahinci anty dama amfani tayi dani don wani bukatan ta kawai.
Ashe ba don Allah ta sani yin wanan auren ba dama don wani bukatan zuciyar rane ta sakani ban iya wuce ba school gidan mahaifinta naje.
Bayan mun gaisa dashi yake tambayana anty din nace Abba dama nazo da magana ne akan anty din nan dai na fada mai duk yadda mukayi da safen nan da ita.
Kai ya girgiza cikin takaici yace dani Rahama al, amarin yar uwarki sai addua yanzu kawai don ni sai nake ganin ko akwai wani abinda Saade taiwa Allah ne a baya wanda ya sa ya baiyyanawa duniya halinta a yanzu.
Nai mai godiya bayan yagama min nasiha kamar yadda ya dace duk uba na kwarai, yaiwa yar shi nai mashi godiya na bar gidan.
Tun ranan gaba daya ba dadi a tsakanin mu daddy ya gaji ya kawo ido yasa muna yadda na share alamarinta yai mashi dadi sosai don shine kwanciyan hankalin mu gaba daya.
Bana jin dadin hakan amma ya zama dole muyi zaman yar tsama din don kwanciyan hankalin mu tunda yanzu ba boyo kowa ya gama fahinta halin da muke ciki da ita din.
Allah ya taimake ni nagama karatuna lafiya na kuma samu sakamako mai kyau na alfahari dashi ga duk wanda yai karatu koda ba irin namu ba mai tsawon shekaru haka mai yawa.
Ranan da na karbo takardan ban shiga part dina ba sai da nakaiwa anty ta gani ba laifi na samu yan arzikin na kusa tai min murna.
Ta miko min takardan na karba nace a hankali da ita anty na gode da ba don ke ba yau ba zan kai ga wanan nasaran ba don Allah duk abinda nai maki kiyi hakkuri dani ki yafe min haka Allah ya kaddara da rayuwan mu.
Amma ni bazan taba mantawa da irin alherin da kikai min ba a rayuwana don kece silar zamana a wanan matsayin da nake ciki ayau.
Ko bayan raina anty bazan taba mantawa da irin halarcin ki ba a gareni don Allah anty ki yafe min ki bari nai maki biyayya irin wanda na saba maki a baya.
Shiru naji tayi batai magana ba nima ahirun nayi ganin bazatai magana ba yasa na mike na dauki hand bag dina zan bar wurin tace dani.
Rama nasan kina hakkuri dani sai dai gaskiya har yanzu zuciya na ya kasa yarda da alamarinki na ba bu soyayya a tsakanin ki da Besty ba abaya sai nake ganin kamar rufa ido ne kukai min dake dashi a yadda kuke yanzu.
Nace ban taba cin amanan kowa ba a rayuwana kuma koda nayi ke kin sani anty zan rokeki ki yafe min akan abinda nai maki din.
A zamana dake ban taba jin digon son mijin ki ba ko daidai da rana daya kai asalima ni koda kika aura min daddy ba wai ina son shi bane anty kema kin sani.
Nayi ne a bisa ga kwarin gwiwan da kike bani a lokacin wanda ban san cewa da wata manufa ahskan ba a likavin a ran ki.
Tace banda wani manufa a lokacin a kanki Rama don a lokacin sai nake ganin kamar kece zaki share min matsala ta ban san ba aiwa Allah shishigi ga alamarin shi ba yanzu gashi nayi abin ya koma min a ciki kuma .
Nace idan kin dauke shi a haka anty ni har gobe a shirye nake da nai maki biyayya akan bukatun ki indai bai sabawa Allah ba.
Tai murmushi mai kama da ansa ta a dole tace kaiyya dai Rama ai an bata goma daya bai gyaru ba ne yanzu fa a matsayin kishiya na kike wace mijina kuma ke ji da bukatanta gareshi.
Don may Rama ba zanji zafin ki ba akan haka ko yaushe ganinki nake kamar kina sace min farin cikina ne a kullun kina mayarwa a kan ki.
Yanzu idan nace zan bar maki mijin ki anty zaki soni kamar yadda kike kauna ta a baya can yadda muke dake.
Tace Allah dai ya gyara kawai Rama ki roka muna Allah abinda yafi zama alheri a rayuwan mu yafi zancen barin gida a gare ki nace to shike nan zan ci gaba da rokon ubangiji don dama ina yi sai dai na kara kawai.
Na koma wurina cike da tunanen wanan halin da muke ciki ance karshen kiyayya soyayyane to shin haka karshe so yakke ne ko kuwa namu ne yazo da akasi haka wai ?
Wata zuciya ne tace dani ba haka bane naku ya hade da kishine shiya jawo maku matsala a tsakanin ku.
Kishi ita anty tafi kowa kishi ke nan ake nufi ko kuwa dai a kaina ne kishin ta yafi yawan zafafa ne wai.
Daddy ya dawo bayan kwanaki nakai mai takardabn nawa ya gani ya samin albarka yace yanzu saura services ke nan kuma ko nace haka ne daddy.
Yace a ina zakiyi services din naki ke nan ?
Sai nai shiru yace bakiji bane nace dashi anan kano ke nan tunda ina da goyo zan nema anan din.
Yace a, a, a Abuja zakiyi tunda ina da gida can babu kowa a cikin sa kinga sai ki je ki can kiyi idan lokaci yayi.
Nasan akwai wani sabon rikici ga iyalin shi sai dai naja bakina nai shiru kawai har ALLAH ya kaimu lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE HAKAN BA ONLINE NOVEL NE, , ,
67
Abin ya dan yi dama a tsakanin mu sai dai yaranta sun shiga rudu a hakan yau ace su yi min magana gobe ace dasu su fita harka na bata kwarai bace ni.
Amira da yake mace ce kuma ta fara girma sai ta fara bin akidar uwar ta a kaina duk kuwa da shakuwan dake a tsakanin mu da farko.
Nasan za, a rina saboda ko diya mace akwaita da saurin daukan akidar uwar ta fiye da na da namiji sosai.
Mazan daine ba ruwan su zasu zo koda kuwa baba yana barci su ce sunzo ganin shi ne bani hana su idan idon shi biyu zasu dauke shima su tafi part din su dashi ne ban saka komai a raina.
Sai ranan Jinior ke cewa dani little mum wallahi Amira dukan baba take idan na dauke shi kiyi mata magana ta bari.
Banji dadi ba a raina sai dai a fili cewa nayi da ita haba Amira keda dan kanin ki kuma zaki doke shi may wanan yaton ya sani da za, a doke shi.
Ashe ta kwasa ta fadawa uwarta wai na kamata ina zaginta akan baba nan uwar ta hau ta zauna sai abinda ta rage a bakin ta.
Har tana cewa ita bataga wani da a gidan nan ba da za,a haifa wanda yafi diyanta ni har wani haihuwa nayi kodon naga shi ne na haifa da cikina zan tsiro mata da wani tsirko akan dana.
Ni a baya may ye ban wa diyan ta ba wa yai min magana ai babu muguntan da ba nai masu ta sani kuma take kawar da idon ta.
Nasir dake zaune a gefe yana ta cin abincin shi tun fara maganan sai ji nayi yace haba mummy maimakon ki mata fada ta daina zakice kuma wai ta doke shi.
Nasir idan baka rufe min baki ba anan yanzu ranka zai matukar baci a gurin nan wawa mara tunane kawai.
Mikewa yaron yayi yabar abincin ya fice daga falon nata ran shi a bace a raina nace namiji ke nan dama yaya halin yan mazan yake ko a banza.
Yaton nafita na mike ina cewa anty kiyi hakkuri ni dai nasan ban ci mata mutunci ba akan dan uwan ta don bazan raba su ba dukan dai da akace tana mashi ne nace ta daina banyi wayo ba tukun.
Lalai yanzu Rama bakya jin nauyi da kunya ace kina fada wai akan danki kan yan uwan shi rabawa tunda ba tare aka haife su ba ai dole a raba su.
In ba shi wanan shashan da bai san ciwon kan shi ba har yanzu ita Amira ai da take da wayo kinga ta gane komai ko.
Allah ya kyauta nace na bar falon cike da mamakin son kai irin na anty ita daya dace ace tayi magana akan abinda yarinyar keyi dabai dace ba wai kuma ita ke goyon bayan karya akan hakan.
Ni a tunane na kishin anty a kaina zai tsaya kawai ba zai kai ga dan dana haifa a gidan idan har zatayi dubi ga irin yadda naita dawainiya da nata yaran a baya can.
Amma sai gashi ita da kanta ke bada daman ai wa karamin yaro na goye wanan abin haka.
Wasu kishin su na hana su tunanen ranan haduwan su da Allah, yana da kyau duk abinda mutum zaiyi ya dinga tuna makomar shi ga ubangijin shi.
Kamata yayi zancen ya tsaya a iya ni da ita kawai amma yanzu na lura har Amira yarta ta shigo acikin al, amarin namu wanda hakan bai dace ba a yadda maigidan burin shi ko yaushe yaga hadin kai ga zurian shi.
Ni kan tun wanan ranan bana yarda a shiga min da yaro wurin su indai ba tare dani zan shiga dashi ba kuma ko nashiga din dashi yana manne a jikina koda kuwa yannen maza sun dauke shi ne idan zan fita zan karbe shi mu fice tare.
Ance riga kafi yafi magani ina hakane kada wani abu yazo ya samu yaton wirin sakaci na abin yazo bai muna kyau ba nida su baki daya.
Na kan dai ta tunane a raina dacewa watau ita kishiya sunan ta kishiya dai da kowa kishi ya hada ka sai idon ka ya rufe ka aikata komai a kan ta.
Yau wai ni Rahama ce ke gudun barwa matar da tafi kowa sona a duniya dana dana haifa da cikina don gujewa cutarwa daga gareta.
Gashi kullun idan muna waya dan muna waya da Innata maganan ta gare ni shine yarinya kiyi hakkuri.
Kin auri namiji mai mata da iyali da yawa sai kin kara hakkuri da kowa dashi da iyalin nashi, kada ya kasance kullun ki zama mai matsala a cikin su ki bari ai maki yafi ace kece mai yi din.
Idan kin zama jaruma akan duk wani abinda zai bullo daga garesu ba sai kin ce zaki dauki fansa akan komai ba Allah na gani kuma shi mijin naku ai yasan komai don duk namijin da ya tara iyali yasan halin kowace daga cikin su da halin kowa suke zama dashi.
Ke dai ki masu biyayya don nasan ki dashi shi biyayyan ki akan su shine zai kara maki daraja da martaba a garesu wata rana.
Kin zama kamar walkiya acikin su yanzu don idon kowan su yana akan ki motsinki da takon ki a idanuwan su yake don haka ki daure ki cinye jerabawan dake a gaban ki.
Kada kiyi wasa da ibadan ki dan ganin samun duniyan da kikayi addua yazo gaba da komai a tare da ke.
Da fatan zaki zamo wa mijinki cikin matan aljanna sai an daure ake samun wanan matsayin a wurin ubangiji Allah ya tsare ya kare ku ke da zurian ki baki daya.
Nace amin inna a sanyayye haka na wuni sukuku ranan da mukai waya da innata sai faman sakawa da warwarewa nake a raina ina neman mafita akaina.
Ga dai daulan duniya da hutu a gidan daddy amma kishin matan shi ya hanani mike kafa inci shi da dadin rai kullun garin Allah zai waye da sabon fitinan da zai bullo kai.
Da wuya a wayi gatin Alah ba ace ga abinda Rahama taiwa wani ba agidan yanzu ma dan dama dama zulfa don ita bata faye shiga harka na ba agidan.
********* ********* *********
Maigidan ya dawo daga tafiyan shi anty ta fara girki sai zulfa tayi hindatu ce yau zatayi kwanan ta na karshe a girkin.
Don haka a washegari ni zan karbi girki ke nan ban wuni a gida ba na tafi wirin kitso da kumshi na gyara jikina tsab da yamma Aisha ta tayani na gyara part dina don gobe muna da aikin yi in Allah ya kaimu.
Tunda na dawo daga gyaran jiki babu wacce ta ganni a cikin gidan don ban fito ba karfe uku muka dora girki don tuwo nake son yi don nasan shi yafi son ci sai dai bai samun hakan ne sosai.
Mun gama na kwashe a kula bayan na daure a ledoji na rufe miya sai da yamma zan hada amma komai yana a tanade.
Karfe hudu da rabi na dauki kayan gyara na nufi part din maigidan na fara gyarawa komai sai dana gyara shi tsab a part din na fito na koma wurina.
Na hada miya ban bar kitchen din ba sai da na kammala hada komai na kwashe miyan agushi a kula na rufe.
Wanka naiwa baba itama Aisha nace taje tai wanka har Atika mun fito muka saka kamshi a part din zakace ko anan maigidan zai zauna.
Wanka nayi na gyara jikina tsab da yarona English wear na saka a jikina don dare yayi na tsaya a gaban mirro na kalli kaina naga nafito yadda nake so ga kasa na yasha gyara dana durawa cikina tun yamman jiya nake faman tsuma kaina.
A ka idana bana shiga wurin daddy sai na tabbatar da matan shi sun gama shiga wurin shi gaida shi sannan zan shirya in tafi.
Yanzu ma natabatar da sun gama shiga na dauki kayan abinci zan fice yaron ya sa min kuka don ya iya kiuya yanzu sosai dan kwanan biyun da baba fita muna tare a gida dashi na dauke shi na goya yana kuka muka fice zuwa kaima daddy abinci.
Sai dai nayi rashin saa na samu hindatu a falin suna magana da shi na jera abincin tare da yi mai sannu da dawowa a lokacin.
Na hada komai yadda ya dace ina duke a gurin anty ta shigo falon suka gaisa dashi yaron na kuka a bayana yace dani miko shi mana nan ga uwarshi ko zaiyi shiru idan ya ganta.
Tace a, a barshi nima ba zama zanyi ba nazo ne kawai na gaida kai ai yace kama mata shi mana ta gama abinda takeyi ko.
Ban da lokacin wanan gaskiya zan je na huta ne tace ta juya tafice daga falin hindatu ma ta mike tana mashi sai da safe nagama hada komai na sauke yaron na fara bashi nono.
Ya sauko ya zauna yana cin abincin shi hankali kwance can dai kaina yana sade akan yaron dake shan nono yana ajiyan zuciya don kukan da yayi.
Daddy sai abincin shi yake ci hankali a kwance don ba karamin abinci yake ci ba, can ya dago kai yace dani kin ko ci abincin nan ke ?
Nace sai wanan yayi barci nake son na zauna naci yace wai may yasa kin san kina shayarwa kike wasa da cin abinci haka har yanzu Rahama ?
Yana magana yana bude bowl din dana saka mai gassasan nama acikin sa ya jawo zuwa gaban shi yace duk kin wani bushe min a idona da gani bakya son cin abinci may ke damun kine wai haka Rahama ?
Ba komai daddy kila shayarwa ne kawai yace ban yarda ba still dai kuna da matsala da antyn ki a gidan nan don yanzu ma na fahinta akwai matsala don ta kama maki yaro amma a gabana Saade takiya.
Nace wanan ba komai bane ai daddy yanzu ba gashi na kama shi yayi shiru ba ya daina kukan da yake dama kiuyane dashi kawai.
Yace kada ki boye min Rahama don ni nan nasan komai ke gudana a tsakanin ku wanan dalilin yasa nake son dauke ki a kusa da ita ko zaku samu sasauci a tsakanin ku.
Nace daddy wanan maganan na tafiyana Abuja shi zai kara haifar da wani sabon kiyayya a tsakani na dasu.
Ya dago kai daga duken da yake yana yagan naman gasshen dake gaban shi yace dani Rahama shin waya aje ku a gidan nan dake dasu ina duk a karkashi na kuke dai ko ?
Don haka ina da ikon zantar da hukuncin da duk naga dama akan ku hukuncin dana yanke kenan shi kuma za,a zartar yadda nake so din.
Shiru nayi ina cin gaba da bawa yarona nono yana ta faman sauke ajiyan zuciya, daddy ya lura da cewa ban ji dadin
da hukuncin daya yanke ba amma shine kawai yake gani mafita a gare shi a
Showing 273001 words to 276000 words out of 456145 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92 Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153