gidan nan mun ga abu a lokacin ai ko yaushe uwarta na gidan.
Nace ashe ko yanzu mu gan su ke nan tunda abin nema ya samu tace zakiko ce kin ce indai sune a nan zasu tare muna.
Bayan sun dawo ne muka tafi gaida ita da jiki sai wani basar da mu takeyi daga kwance ni dai na juya nafito na bar dakin.
A falon su muka hade sa Raliya nace da ita an dawo tace eh kada ta zargi may ya kawo mu nace munzo duba maman ihisan ce ba lafiya yanzu suka dawo asibiti.
Tace ta samu wurin an kama mata ne ai sai taitayi kullun mutum a kwance yaya zaka gane lafiyan jikin ka.
Ban dai tsaya ba na wuce abina ina mamakin irin wanan zaman nasu kullun cikin rashin jittuwa suke a tsakanin su.
Wani abinda ke damuna ban fadawa kowa ba sai dare yayi fever ya rufe ni da naga abin yai min yawa nace bari dai ne test nagani ina aunawa ya nuna min possitive.
Ga lissafina ma nawa yana gaban na hindatu da kusan wata biyu naha bakina nai shiru a tsaye naita rama da renon cikina dama na iya.
A gajiye na dawo da ciwon kai da zazzabi a falon mu ma na kwanta na kasa karasawa dakina
rage kayan jikina ina son kai din ya dan lafa min.
Hayaniyar da ake da fada da tsawa yasa ni mikewa zaune daga part din su Hindatu ne ake wanan fadan sai ga Zulfa ta fito tana fadin yau kuma an tayar ke nan.
Ita ce ta tafi sai ma na karajin hayaniyar yai yawa na mike na tafi daidai lokacin da hindatu ke fadin ba yau ba na sani sarai cikin nan ya tsonewa kowa a gidan nan ido ana bakin ciki da samun shi.
Ciki ne dai na sama ba ruwa za, a zuba min na fadi ya zube ba komay zakuyi Allah ya riga ya dasa min shi sai na haife shi da yardan Allah ya taka yarda kowa ke takawa a gidan nan.
Da an debe tsanmanin sake samu a gare ni yanzu anga na samu sai bakin ciki nake gani iri iri ana nuna min.
Zulfa tace akan ciki ake nuna maki bakin cikin gaba daya gidan nan ko may ina kowa na dashi banga abin bakin ciki ba ai.
Don Allah malama rufe min baki kinji may ye ban sani ba har dan kaini asibitin da akeyi sai da akai bakin cikin shi gidan nan ko an dauka ban sani bane wai.
Ban yi bakin ciki da dan kowa ba nawa tun yana ciki har an fara nuna bakin ciki dashi to ta Allah bata mutum ba dai.
Cikine Allah ya kawo shi inda yake so in mutum ya isa ya kwace mu gani ko yayi in yi banza ne.
Tsuki na ja na juya kawai don sai naga kamar ta samu tabin hankali ne ma ciki da yake ciwo don hauka wai take kadagi dashi.
Na koma na kwanta inda na tashi tare da lumshe idanuwa sai ga Zulfa tace Rahama kin gani ko waiko hindatu na da hankali kuwa.
Na bude ido nai murmushi nace da hankalin ta mana tsaba iskanci ne kawai da rashin imani ke damunta.
Shi dai cikin kamar akwai wanda bai taba yi shi ba acikin mu zata tsaya wanan haukan haka ?
Zulfa tace ni dama ba yauba na kula da ita ko abu ka bata bata ci ko zuwa nan yanzu baki ga ta daina ba.
Kin san ance wanzan baya so a jikin shi kin manta da abinda ta taba yi min ne akan cikin baby ?
Nace kai wanan ai rashin imani ne tace to shi take ganin kowa ma zai iya a halaka mata cikin nata.
Nace Allah sarki tai ta kanta kowa ma nashi ya ishe shi balle yaje daukowa kan shi wani nauyi da hakki.
Tun ina ciwo a tsaye har na kai kwance lokaci guda na ramay nafada ban iya cin komai ba wanda ya kawo cikine dani in dai anyi magana sai nace dasu ulcer ke damuna kawai.
Ga seminar yazo min zan tafi india haka na daure nai tafiyan na dai jene amma ban iya tabuka wani abin kirki ba a can.
Na dawo duk na fada na ramay sai da doctor fati tazo har gida ta daura min ruwa don ido rufe na dawo gida.
Lokacin ne daddy ya gane cikine dani da yaji muna magana da ita ciki har yakai wata hudu a jikina lokacin.
Bayan tafiyan ta ya dawo dakin fuskan shi babu annuri ya samu wuri ya zauna idanuwa na suna a lumshe yake cewa dani.
Rahama cikin kika sake boye min bayan kin an yadda mukayi dake a baya kan cikin Haidar nace akan may zan boye ma daddy.
Ba yau daine mukai test ba muka gane cikine dani amma ni may zai sa na boye maka idan na sani.
Sai naji ya furzo da iska daga bakin shi yace may kike so a saya maki ko zaki iya ci yanzu ?
Nace bana son komai faten wake dai nace helen ta dafa min shi kawai nake son na sha ko za dan ji dadin bakina.
Ba zaki ci kaza mai zafi ba a sayo maki ko zai gyara maki bakin naki nace bana son komai faten dai ne ya biyo min a rai kawai.
Ya juya ya fita yana fadin Allah ya sauwaka yana fita zulfa ta shigo tana min sannu daidai kawo min faten wake da helen tayi.
Na mike da kyat na shiga bayi na wanke bakina nace da ita don Allah mu hada hannu ko zan samu na dan sha da yawa.
Waiko Rahama anya kuwa ba kani jinior ya samu ba dama yace wa hindatu shima ai maman su zata haihu.
Murmushi kawai nai mata na dan fara diban faten ina sha a hankali sai da na samj nasha sosai sai ko ga amai ya taso min.
Da sauri na mike na shiga bayi tana min ba a tana fadin aiyya abin yazo muna nan ashe akwai magana kuwa.
Mai kurin ciki yau ta samu kishiya sai yaya ke nan yanzu za, a yi cikin da akace damu kwalelen mu gashi an samu.
Ban yi aman da yawa ba na fito na fada saman gado ina nishi da kyat nace kai ni wanan abin ma kamar sabo ya koma min wallahi ko.
Tace har yaushe Rahama aike abin naki na da kyau tunda baki jimawa kike samun ciki wanan ne kika jima shiyasa.
Tace ni kinga cikin Hanif wani likita ya ban magani sai ko gashi Allah ya kawo min cikin da wuri ban ko dade da fara sha ba ma.
Nace ko yanzu idan kina sha sai na gwada rubuta maki ki saya ki sha tace da sauri wallahi ina so gaskiya da zan samu.
Nace bari na rubuta maki ida na tashi yanzu kan sai a hankali gaskiya tace kai dana gode wallahi gorin da shegiyar nan tai min yana ci min rai sosai tun ranan.
Nace cikin lumshe idona ni wallahi bani ma son ta sani sai dai ta ganni dashi kawai daga sama yafi tace haka za ayi ai kuwa.
Da safe daba danji sauki sai gata rana min tunin maganin na rubuta mata ranan ta tafi ta sayo takawo ta nuna min nace mata sune nan na fada mata yadda zata sha.
Nace ni kan wallahi da nasan lokacin da cikin nan zai shiga ai da ban bari ba don ni yaran na ma dana samu na godewa Allah haka na.
Tace na raba ki ba irin guda nan ake wanan magana ba kin dai ji abinda aka fada muna ai gara taga kowa dashi tasan ba ita kadai bace mace a gidan data iya daukan ciki.
Ni dai murmushi nai mata kawai na koma na kwanta don banda aiki sai kwanciya yanzu shine nakeyi na da ji dadi a rai na wani lokaci.



Don Allah ina mai kara baku hakkuri dani da fatan zaku fahinci yanayin da nake ciki don wasu na ganin kamar da gangan nake kin rubutawa a kullun, .
Bayan sun sa ba haka nakeyi ba ko na dade ban daukan lokaci mai tsawo haka ban rubuta ba.
Matsalar waya ce wayan taki min rubutu yanzu yadda nake so shiyasa bakujina ko da yaushe.
Sai ida na da samu aro nake rubutawa na turo maku don Allah kuyi hakkuri dani yan uwa.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,

96
Sannu Sannu komai yake tafiya a gidan mahaifiyar Hindatu tazo itace take kula da ita wai bata jin dadi a lokacin.
Na dawo daga aiki na samu ta iso na shiga gaida ita da zuwa a wullakance take amsawa cikin wani basarwa.
Ban tsaya ba na fito bayan mun gaisa da ita irin yadda naga ta sha min toka a fuskan ta.
Ban sake komawa gaida ita ba nima nawa ya isheni lokacin karfin hali kawai nake nima don ban jin lakka a jikina.
Washe gari na fita gin aikina ban ko bi ta kan bakuwar gidan ba nace naje gaida ita da kwana don naga alaman akwai magana gare ta.
Na isa wurin aiki ban zauna ba na shiga duba marasa lafiyan da naiwa aiki suna kwance.
Bayan na gama round ne na dawo office na fara duba masu zuwa ganin likita nakai wani lokaci ina dubasu na gaji na huta.
Doctor Fati ce ta shigo wurina muka zauna muna hira da ita take tambayana hindatu na dan maide baki nace jiya koda na koma na samu mahaifiyar ta tashigo garin dubata ai.
Mamaki ne ya kamata sosai tace kamar dai shine haihuwan fari gareta da sai mahaifiyarta tazo dubata.
Idan ba don alamarin kishi ba minti nawa zaki duba abinda ke damun ta ki sani shine zata tsaya wahal da mutane haka ko yaushe ?
Nace cikin murmushi ni fa kishiyace kin sani kuma ko han dubata ba nasani matsala ce ta ciki nima shike damuna yanzu haka amma na daure ina normal activities dina lafiya.
Yadda nake ji din nan kuwa nasan da itace da wata kila sai an bata gado ta kwanta ma.
Kin san ance kowa ya samu rana yai shayen sa wuri ta samu da tace kai yace sannu da tace kafa yana wayyo Allah na.
Sai ta bushe da dariya tace anya doctor ba kishi a ciki zamcen ki kuwa nace ba dole nai kishi ba tunda abinda take fama dashi shine nima nake fama dashi yanzu haka.
Ta sake bushewa da dariya tace to ai bashi ba doctor kece kika tsaya kina wani muku muku da naki cikin kamata yayi ace tasan kina dashi zakiga ta shiga hankalin ta ta daina duk wani sallo da yangan da take maku a gidan wai ita mai ciki.
Naja tsuki tare da cewa ai baki san halin ta bane ita fa kanta kawai ta sani a duniya bayan haka bata san komai ba haka rayuwan ta yake ko yaushe.
Mun dan dauki lokaci muna hira daga karshe muka juya kan maganan zuwa wani buki da zamuyi washe gari na auren diyar wata shugabar mu data gaiyyace mu.
Na biya na dauko yara daga school muka dawo gida a gajiye na iso ban tsaya ba na shiga wanka na fito daidai Aisha ta shigo ita ma a gidan.
Nan ta zauna ina shiryawa muna hira da ita tana bani labarin wai taga Raliya a hanya amma bata tsaya ta dauke taba.
Nace ina mikewa tsaye Aisha to may ye abin damu ba gaki kin dawo gidan ba zafin ki yake ji na sani ba yau ba duk wani wanda ke tare dani matar nan bata kaunar shi na ciki na ciki ne da ita.
Mun fito falo mun zauna sai fa Zulfa tafito tace ashe kun dawo ina barci daga barci kallo ya dauke ni a wurin .
Nai murmushi nace da ita ai dole ki dinga barci maganin da kike shane haka zai ta saki jin kasala kafin ya bi jikin ki da kyau.
Tace haba ni kan ai na manta cewa zai iya bani wani yanayi irin haka har nake ta mamakin may ke sa ina jin irin haka ne wai ko da yaushe yanzu ?
Abinci zamuci ta zauna take bani labarin wai dazun tunda safe an kwasa da maigidan da mahaifiyar hindatu a gidan.
Nace subbahanallahi may kuma ya faru haka ne wai take cewa dani nuna mai tayi kamar bai kula da yarta yadda ya dace shine shi kuma yau yai fushi ya fada mata magana son ran shi.
Ni tunda ma tashige ban sake gani giccinta ba tun safe nasan amsa daya bata ne bai mata dadi ba don ita kamar yar nata take kin sani.
Murmushi nayi kawai ban ce uffan ba a fili sai dai a cikin raina ina mamakin wanan irin rayuwa haka ace yarka ta dade gidan miji amma kullun kana mayar da ita karamar yarinya wai kaine may taya ta kishi.
A can kuma dakin hindatu uwar ce tsaye tana magana da cewa yanzu na kara tabbatar da cewa wanan yar kauyen yarinya ta dauki kanta wata tsiya.
Don tun zuwa na datazo tai min sannu da zuwa bata dawo ba gaida ni bance ke ma ki mutunta wani nata don itace ta fara.
Mammy haka Rahama take fa ke tama yaba da ke da har tazo tai maki sannu da zuwa har nan isan dai ba wani dalili mai kwari ba zaku iya shekara ma a gidan nan baku hadu da ita ba.
Don ko yaushe ita busy take har nan gida yanzu da aka gane ta biyota zakiga mata nayi da mazajen su tana duba su.
Tace kuko wawaye kuna zaune baku baki baku fari har yar kauye tazo ta fiku sanin kan ta duk cikin matan gidan nan ita zaka kalla ka san tana zaune a cikin daula da jin dadi ta bar ku jan gadin gida da haukan son miji a baki.
Kai haba mammy keda kan ki ke dadin wanan magana kuma har may Rahama tafini dashi da zaki fadi haka.
Tace tafi ku wayo da sani kai mana nayi nayi dake ki nemi aiki amma son jiki da kai ya hanaki nema kun kwanmace ku zauna a gida kuna kallon kishiyoyi suna fita nemawa kan su abin dogaro har yaushe ta shigo gidan da tai nisa haka ta haku tazara.
Kin san dai yau idan mijin ku ya fadi ya mutum wanan yar da kuke gani sai tafi kowan kason abin da ya bari.
Tace mama duk mun san da hakan ai bashiyasa kikaga ina son nima in tara ba Allah dai yasa namijin zan haifa nima.
Tace bakije an gwada ki ba ne ko may har yanzu?
Tace ranan nayi mashi magana yace min shi baya son wanan maganan ko may Allah ya bashi ai karuwa ne ba a rainawa.
Uwar tace ai dole ya fadi haka an cika mai gida da diya maza yana kallo yanzu bai damu da wai sai wani ya haifa mai su ba tunda ya riga da ya samu ko.
Kin san ance wai su yan kauyen nan akwai abinda suke sha wai don su haifi diya maza saboda su gaje gida ko suyi ta samun masu taimaka masu da noma.
Mammy wai da gaske ?
Uwar tace ke haki taba sanin haka bane ko may ?
Ai kibar bakauye inda kika gan su kin ga kishi da bakauye da bafillatana akwai wahala sosai a rayuwa.
Sai hindatu tace kin ko ga ita Rahama dama zubi biyu ne ita don wurin uwa bafillatana ce ai duk su ta kwaso don uwar ta sai mutuwar Saade ta taba zuwa gidan mu har muka gan ta.
Kice naku ya samay ku ashe ni ban ma taba sanin wanan maganan ba sai yau haba shiyasa muke aiki kullun kamar bamayi .
Nan dai sukaita suratan su har uwar nacewa ai sun hadu damu kin san su fa yaro bai zuwa aure haka kara zube sai sun shirya yaran su tsab.
Tace shiyasa dama nace a daurewa shegiya mahaifa kada ta kara haihuwa a gidan haka ya isa kowa ma ya samu tunda ba ita kadai bace mai cikin haihuwa.
Sun kai wani lokaci suna zancen su na shirka a tsakanin su inda suka sha alwashi cewa ba zan sake haihuwa ba agidan na tara yara maza bulbul dasu kamar kiyon agric a gida duk wanda ya gan su sai yaji sha awar su.

********* ********* *********
Washegari Jumma,ane daddy ya fita da yaran maza zuwa sallah kamar yadda a ko wani jumma, a yake fita dasu
Sun dawo akan idon mahaifiyar hindatu don sai ya zaga ko wani part dasu sun gaida kowa a gidan kafin su dawo inda muke.
Bayan fitan su ne mahaifiyar nata take cewa kin ga abinda nake fada maki kullyn ko ganin irin wanan ai takaici ne a gidan nan ba kunya yake fifita diyan shi maza akan kowa.
Jifa yadda ya tasa su a gaba ya fita dasu
Showing 393001 words to 396000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132 Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153