san darajan ki da kimarki ne zaki nuna hakan.
Kamar zatai magana bayan ya gama maganan shi sai kuma taja bakin ta tai shiru kawai tafice batare da ta dauka ba.
Ya bita da kallo har ta bace mai ga gani yaja tsuki yaci gaba da yin abinda yakeyi a laptop din nashi.
Koda ta koma part din ta babu irin tunanen da batayi ba akarshe sai ma ta tura Amira wai ta dauko kayan a falon baban su don ko tsaya ta duba dama batayi ba don haushi da takaicin da taji.
Amira tazo daukan kayan daddy yace gasu nan ta kwasa a saman kujera yace idan kinje ki turo min Soja yazo ina neman shi.
Nan dai yarinyar tafita tana murna tana shiga tace mummy amma kayan nan suna da kyau wallahi kuma kalan nan ya matukar burge ni.
Tace aje su nan don Allah sai yaran suka shiga daukan nasu suna farin ciki da samun kayan.
Nan Amira ke fadawa Nasir sakon daddy bai tsaya ba ya tashi yafice yaje gun amsa kiran da akai mai din.
Sun dan taba hira yaron ke tambayan mu yace muna gaidasu Nasir yace daddy idan anyi hutu ina son zuwa wurin small mum amma mummy mu tace wai bazan tafi ba yace ka bari idan anyi hutun sai na turo a dauke ka ko ?
Yaron yaji dadin ya fara murna can kuma yace ina son inga baba nasan yanzu ya kara girma sosai kilama yana tafiya ?
Sosai daddy yaji dadi a ran shi yadda dan shi ke son dan uwan shi do ko yaushe a cikin tambayan shi yake idan sunyi waya dashi.
Nan dai suka juya hiran kan karatun su inda ya fadawa uban abinda suke bukata yace gobe zai bada kudi sai a sayo masu in Allah ya kaimu.
Sun dan taba hira yace yaje ya kwanta gobe akwai school har yaron yakai kofa yace daddy kada ka fadawa mummy batun tafiya na don zata hanane idan taji.
Yai murmushi yace bazan fada mata ba ai sai dai taga kawai mun tafi ba shike nan ba yace hakane daddy.
Bayan yaron ya koma take tambayan shi kiran da uban ke mashi yace ya tambayeni ne abinda muke so a saya muna sai tai shiru kawai batare data kara magana ba.

********* ********* *********
Ni dai na fahinci tun zuwan daddy idan na kira anty da kyat take amsa min tana min magana a cikin basarwa sai dai ban fahinci komai ba ga hakan.
Komai yana gudana kamar yadda ko wani gidan maaurata yake gudana, duk da ba a wuri daya muke zaune ba a rasa dan abinda kaje ya dawo a tsakani.
Wani lokaci zanga abin bacin rai don kirkiri a gabana wata zatai mai waya da tana da bukatan kudi haka zai tura masu ina kallo niko dake nan zaune tare dashi ba wai kudin yake bamu ba.
Sai dai babu abinda na rasa a gidan don ko kayan kwalliya haka zai sayo muna su pad da sauran abubuwan bukatu na mace dana gida.
Ina gani sai dai hakkuri da haka din don na fahinci shi idan bakai ka tambaye shi kudi ba bai iya fitarwa yaba mace su haka kawai.
Gashi su suna can suna zaton ni ina nan ina jin dadin rayuwana ne tare da maigida su suna can anbarsu abinda basu sani ba suma dake can sun fini samun daga gare shi.
Kwance nake na mike a saman dogon kujeran dake falon tunda na dawo jikina nake jin ba dadi sosai.
Atika da tadawo daga school ta debo abinci a plate tazo inda nake tana ci take naji wani irin tashin zuciya ya kamani.
Da sauri na mike na bar falon don ma kafin na shiga ban dakin har na fara amai ko dan yadda naji yazo min a lokaci guda.
Sai da na watsa ruwa na fito na saka wani dogon riga a jikina falon na dawo na kwanta duk jikina ya mutu min da nauyi.
Hiran su suke amma na kasa saka masu baki yadda na sabayi ko yaushe sai ma idanuwa na dana lumshe kawai ina jin jikina ya sake min.
Yamma lis yashigo gidan kamar yadda ya saba wani lokaci don yawan goslow da ake dashi.
Sai sannu da zuwa suke mai ina kwance da kyat na iya bude baki nai mashi sannu da zuwa ya samu kujeran dake daga gefe na ya zauna.
Hira yake da Atika don abokiyar hiran shi ne a wanan lokacin idan ya dawo gida, sai dai duk maganan da suke idona yana a rufe don ban jin dadi.
Jin shirun da nai masu ne bayan gaisuwan da mukayi ban ce dashi uffan yasa shi dagowa yana kallona yace yaya akayine nagan ki a kwance a wanan lokacin haka ?
Na dan gyara kwanciyana ina fuskantar shi inacewa dashi yau ban jin dadin jikin ne ina ga zazzabine ke son sata na dai.
Wani aman ne ya kara zo min a lokacin na mike da sauri na nufi dakina tunda nai wanan amai din jikin nawa ya kara sakewa.
Da kyat nai sallah daga haka na haye gado na kwanta tare da dunkulewa wuri daya, take kowa yasan bani da lafiya yaso muje asibiti amma nace ya bari harda safe idan na fita zan sa a dubani can.
Sai cikin dare zazzabi yaso ya hanani barci dole nasha paracetamol na dan samu saida a jikina da safe da kyat na lalaba na shiga asibitin.
Na dan yi treatment din kaina cikin ikin Allah kuma sai na samu sauki sosai daga haka na fita batun ciwon koda ya dawo ya samu na samu sauki bayan wayan da nasha daga gareshi yana tambayan lafiya na.
Naci gaba da abubuwana normal sai bayan kamar sati kuma sai na fahinci duk dare sai zazzabi ya rufe ni da kyat zanga safiya ya waye min sai kuma na mike tangaram dani.
Abindai yai yawa gashi ban son daddy ya fahinci hakan sai mukurkusa nake ni kadai ban fadawa kowa ban da lafiya ba.
Amma kana ganina zaka san na fada sosai na ramay harda dan wuya nayi don wahala.
Kwance nake don yau da wuri na dawo gidan don jikin yakiya min sai da na dawo nasha magani daga inda nake kwance bayan na dan ji sauki kiran layin zarah nayi don mun kwana biyu bamu gaisa ba da ita.
Mun gaisa muka dan tambayi lafiyan juna kwana biyu nake cewa wallahi Zarah ban da lafiya duk kwanakin na sai dare yayi zazzabi yake rufe ni sosai.
Abinda ya fito bakinta shine kinyi test kuwa Rahama nace wallahi Zarah tsoro nake ji ina son yi amma ban san result din da zai bani ba.
Tace baki da hankaline Rahama maye a ciki da zakice wai kina wani jin tsoro to wallahi ni raina ya bani ciki kika samu.
Gabana naji ya fadi don abinda nake gudu ke nan dama nace kiwa Allah ki rufa min asiri duka duka baba watan shi fa goma sha uku yanzu Zarah.
Tace to may ye na wani tsoro cikin banza ne da da uban shi, wallahi kiyi test ki san abinda kike ciki kada kizo ki halaka kan ki da wasu drugs can na daban.
A sanyaye nace da ita naji zanyi Zarah amma don Allah maganan ya tsaya dagani sai ke don Allah ban son ko daddy ya sani tace an gama amma don Allah kiyi test din nace naji zanyi.
Sai bayan na gama komaine na shiga daki na auna kaina abinda dai nake gudu din ne ya faru don ya nuna min positive akwai ciki ke nan tare dani.
Wani irin faduwan gaba ne yazo min a take hankalina yai matukar tashi sosai sai ga wasu hawaye na sulalo min a idona.
Tsoro farfgaba da tausayin yarona ya kamani nace na shiga uku ni Rahama yaro da baiko kai lokacin yaye ba ace kuma ciki gare ni.
Ni yaya zanyi da maganan mutane kuma akaina yanzu tundai kishiyoyina musan man ma anty ya zama dole naja bakina nai shiru nasan mafita da cikin nan tun kagin ya baiyana a hanani wani yunkuri akan shi.
Haka na lalaba na kwanta tunda safe sai ga kiran Zarah tana tambayana yaya kinyi kuwa Rahama don jiya ban iya barci ba ina tunanen ki.
A sanyaye nace da ita wallahi Zarah nayi yabani positive tace bagashi nan ba zaki tsaya Allah yai maki sani kuma ki cuci kanki a banza.
Nace zarah nina shiga uku yaya zanyi da ciki ga goyo kada yaro na yazo ya cutu ni gaskiya zan san yadda zanyi wallahi ko.
Tace kai ke kan Rahama sai ina gani akanki yar fari ta kare wallahi cikin da ake nema da kudi ke Allah ya baki shine zaki sakaci dashi.
To wallahi ahir din ki don idan kikace zaki wani yun kurin barar da cikin nan kin san ba karamin fitina zakuyi da mijin ki ba ke ma kin sani dai.
Nace Zarah ni yaya zanyi ga ciki ga goyo ga kuma wanan aikin da ba hutu a gare shi nakin dai na shiga uku wallahi zarah.
Tace waiko Rahama kan ki daya kuwa kike fadin wanan maganan haka ko harkin manta da irin gorin da ake maki a baya har ana kiran ki da wai ke juya ce baki haihuwa.
Tace ni dai abinda zan fada maki shine kiyi hakkuri don ba aiwa Allah shishigi ga alamarin shi don baki san ko wani irin da ubangiji ya aiko maki ba da har kike wani ikirarin zubar dashi.
Idan kinyi hakkuri har kwana nawane kin haife abinki kamar yadda kikace kikama bakin ki sai dai a ganki dashi kawai kowa yasha mamaki ba shi ke nan ba.
Nace naji Zarah na kuma gode da kulawan ki akaina Allah ya raba mu lafiya tace amin koke fa zakibi ki tayar wa kanki da hankali bayan kin san cewa akwai illa ga mai karamin ciki idan tana saka damuwa a ranta.
Koda muka gama waya da Zarah ni hankalina bai kwanta ba sai sakawa nake ina warwalewa ni kadai a raina ban fita ba ranan don weekend ne ba zuwa ko ina ranan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , , ,

71
A cikin rashin walwala nake duk kwanakin nan don damuwa akan cikin dake a jikina ga tausayin yaron da nake goyo dake kamani.
Nayi sakaci da ban yi saurin gane hakan ba da wuri sai da abu ya zauna sosai a jikina don yanzu ni kaina ba zan iya cewa ga adadin watannin cikin ba sai na duba don ba al, ada nake ba da nake goyon.
Sai ma da daddy yai tafiya ne kafin ya dawo na danga jini na kwana uku kuma ya dauke take na tuna tun wanan lokacin ban sake ganin komai ba kuma har wanan lokacin.
Bakina naja na tsuki na tsurawa sauratan Allah ido sai dai idan na kalli baba sai yaton ya bani tausayi dole na hado mai magani wanda nasan zai gina mashi jikin shi na kuma dinga sa Aisha tana bashi abinci inganttace mai kara bashi lafiya.
Alhamdullahi don sai ma naga ya kara min kuzari sosai fiye da da can baya da yake rashin walwala sosai haka zan faki udon mutane na rugumashi in ta kuka don sai ina ganin zan iya rashi ne.
Ina kwance da yaron dayai filo da jikina muna barci a falo don ban fita ba yau ina up, mafalki nake ko mai don muryan Nasir danaji a kunnuwa yana fadin little mum.
Na bude idanuwa na da kyat na sauke su akan yaran dake tsaye a kaina har su hudu cikin mamaki da murnan ganin su ne ya kamani a lokaci guda na mike ina fadin Nasir kune ko mafalki nakeyi ne wai na jawo jinior zuwa jikina.
Muryan daddy ne naji yana fadin ke yanzu baki da wani aiki sai barci mun shigo muna sallama amma barci ya dauke ki haka ji yadda kika kwanta da yaron nan idan ya fado fa.
Shi da kan shi ya gyarawa yaron kwanciya na juya wurin yaran da har sun zauna ina masu sannu da zuwa yaran mata sai bin gidan da kallo sukeyi tako ina.
Sai ga Atika ta fito tana ganin su taji dadi tace Lah Amira kune kuka zo ashe Amira din tabi Atika da wani irin kallon mamaki.
Nasan ba komai bane sai mamakin yadda ta canza a dan lokaci kankani haka zaman birni dama kai baka sanin ka sake sai dai wani ya gane maka hakan.
Jin hayaniya yasa Aisha da helen fitowa su ma sannu da zuwa suke masu ba bata lokaci sai ta juya kitchen ta dauki masu ruwa da abin sha takawo masu.
Nan dai na zauna dasu ina tambayan su mutanen gida Nasir ya kasa hakkuri ya mike zuwa inda muke ya dauki yaron a kafadan shi.
Take yaron ya bude idanuwan shi yana kallon dan uwan shi kamar ya sheda shi sai ya danyi murmushi ya lafe a jikin dan uwan nashi yana sauke nunfashi.
Ya shedani nace haka yake dama idan yaga maza ya kama bin su ke nan yana son su dauke shi abinci Aisha ta kara kawo masu Amira ce ta fara bude kulan naga ta kurawa abincin ido kawai.
Munan dai zaune tare da su daddy ya shige dakin shi ban ko samu bin shi ba nai mai sannu da zuwa da kyat na mike na bi bayan shi dakin nabar yaran nan zaune suna cin abinci.
Ina shiga na samu zai shiga wanka nace sannu da zuwa yace ai na zaci murnan ganin yaran ki bazai bari yau na samu taro ba.
Nace abin ne ya bani mamaki don banyi tsanmanin zuwan su ba din yace dama ina sun supraise dinki ne yasa ban fada maki cewa anan zasuyi hutu ba ai.
Nace daddy nagode yace da akai mai kuma nace daka kawo min yaran nan don sada zumunci a tsakanin mu ina kewan su wallahi sosai.
Yace to ai gaki gasu yau sai kewa ya kare yana fadin haka ya shige bathroom ya rufo kofan duk da ba wanda zai shigo dakin don bani yarda kowa ya shiga dama dakin saboda sirin mu ne.
Na juyawa nayi na fita zuwa falin na samu yarsn sun gama cin abinci nace yanzu abinda za, ayi shine na nunawa kowa dakin shi ko inda zaku zauna musha hutun mu.
Nace kai Nasir dakai da Jinior daki daya zaku zauna Aisha kaisu dakin can na kusa da hanyan fita tunda ku maza ne.
Nasir yace dakyau little mum shiyasa nake son ki wallahi ko yaushe ina son mummy ta raba min daki da wanan amma taki sai tace waini yaro ne.
Nace to aini yau gashi na raba maku dakin ko sai ka zauna can abinka daga kai sai Jinior kawai Amira kuma zaku zauna dakin dake kusa dana su Aisha ina fatan tsarin yayi maku daidai sukace yayi mum.
Bayan kowa ya shiga nashi dakin ne sun yaba da kyau da tsari din dakunan don ko ina akwai gado da mirro da kuma drower aciki duk da ba kowa amma a gyara suke don helen na gyara su akai akai.
Daddy bai fito ba sai da zai tafi sallah inda yasa Nasir da Jinior a gaba suka tafi wurin sallah tare dashi.
Da dare gaba daya muna falin sai faman hira ake kwasa wasu na kallo daddy ya fito daga dakin shi nasan abinci yake so na mike na shirya mai table yadda ya dace ayi.
Nan ya zauna ya soma cin abincin bai dade da zama ba yaji kukan baba yace a miko mashi shi inda yake nan suka zauna suna ci tare.
Daga inda Amira take zaune naga ta kura masu ido tana kallon su, nasan ba komai take kallo ba sai yadda daddy keyi da yaron take kallo kawai.
Bai jima ba ya mike ya bar mu don yanzu gida ya cika ba halin zama yadda ya saba yi muna da muke mu kadai a gidan.
Ban dauki lokaci ba nai masu sallama na wuce na samu daddy can har ya kwanta don yana da gajiya a jikin shi na tafiyan da sukayi din.
Ranan dai shi kan shi bai fahinci komai ba a gareni don bani da lakka ko kuzari a tare dani don haka maneji kawai mukayi muka kwanta asuba ta gari.
Da safe mun tashi na hada break fast a gurguje nayi komai tun kan yaran su fito muka bar gidan kowa ya kama gaban shi.
Bayan fitan mu da dan wani lokaci yaran suka fara fitowa daya bayan daya suna karyawa Amira ce kusan fitowan karshe ida take fada da Ihisan wai ta kwashe madara ta bar mata kadan.
Sai Aisha tace bari na karo maki ai akwaishi ba iyakan shi ke nan ba ta karfi roban taje ta zubo mata madara mai yawa a store takawo mata.
Amira ta kalli madaran tace yana da yawa ke nan ashe shine aka zuba muna dan kadan a roba muda kayan uban mu ?
Kafin Aisha tai magana jinior tace sai fada anty ta cika muna roban nan har baki sannan madaran da aka bari ai a gida ba haka
Showing 288001 words to 291000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97 Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153