duk abinda yayi sai ya koma mai.
Attu tace amma malam ya dace abata tsari wanda zaibi jikin ta don ni ina tsoron matan birni wallahi ba imani ne dasu ba akan kishiya.
Malam yai murmushi yace Attu ai shi wanan matsala bawai matan birni ne kawai ba har na kauyen idan Allah ya hada ka da maiyi hakane ke faruwa.
Ita hankalinta ba a kwance ba kaima naka da kake tare da ita ba akwance yake ba.
Bawani abu zan ma jikan ki ba sai tsari da zan bata tasha shi yanzu anan Allah ya tsare mu baki daya mu dasu.
Ya fara binciken wani abu a cikin kayan shi muna kallo yajawo ruwa cikin wani gora ya karkada ya mikowa Attu yace tabani na sha tamika min take na sha da bissimillah a gurin namiko mata dan roban da nasha yace Allah ya tsare ya kare.
Muka ansa da amin yace kiyi biyayya ga magabatan ki sai a zauna lafiya dakowa banga wani matsala mai yawa ba ga al, amarin ki sai yawan tarin alherin hakan idan Allah ya yarda.
Can ya dauko wani abu yace dani karbi wanan na sa hannu na karba yace murzashi da hannun ki biyu sai ki shafe fuskan ki da shi har zuwa kirjinki.
Nadaga hijjabina nayi yadda yace nayi yace Allah yabada zaman lafiya ya bada zuria masu albarka mukace amin.
Har zamu mike yace da Attu idan an kai ta kada ta shiga gidan sai ta karanta fatiha da kulhuwallahu falaki da nas kin gasu nan ba karamin abu bane faidar su yafi jin su da mukeyi amma muna sakaci gurin amfani dasu.
Mukai mai sallama na dawo gida gurin dana shafa wanan maganin ga kamshi gashi kuma inajin yana shiga jikina kamar wani abu na min yado a jikina lokacin.
Haka dai na daure har yazo na daina jin hakan da nake ji.
Nai mamaki ganin zarah tazo tare da wasu yan mata course mate din mu da muke dan shiri dasu nasan aikin anty ne hakan.
Taro sosai akai masu da yamma sai ga mama Altine tazo tana ra yan kamay kamay bata daiga canjin fuska ga kowa ba don an tare da mutunci yadda aka saba.
Can daki inda muke Zarah ce ke faman bamu dariya wai tana min lacture din yadda zan dinga yi na sace zuciyan miji ga sauran kishiyoyi na.
Dariya ma take bani take cewa oh dariya ma kike min wallahi ko kishiya daya zaki sama dole ne fa sai kin zage damtsem ki gurin zama karuwan gida karuwan dakin ki.
Don Allah ki daure ki fitae da kunya ga idon ki Rahama ki rage wanan halin rashin magana a gavan mijin ki don zai iya cutar dake yin hakan.
Samu kayan da kika san na jan ra, ayime ki dinga saka mai idan kuna ku biyu kai bama ku biyu ba nuna masu fa ke kece kawai a wuce gurin.
Nafisa tace aiko akwai wasu kaya english wear da suka fito masu kyau na mata su ya dace ki saya da mun isa sai ki basa na sayo maki su wallahi zaki shana sosai a cikin su ga jikin ki zai dauki kaya wallahi.
Ba wani buki bane akayi andai yi walima wanda yan uwana su Rukaiyya sunzo kuma sun nuna su nawa ne a gurin kuma an shirya dasu za, a tafi birni gurin kaini idan za, a tafi kaini din .
Babu abin da mama lauratu ta harta amna duk abinda akaci akasha sai da muka aika mata dashi.
Ba laifi iyayyena sun min gata duk da maigidan yace kada akawo ni da komai mata ya bukata mata kawai za, a kai mai.
Amma sai da maigari yaba da kudi akai dubula nakiya da alkaki da sauran abubuwan da ya dace aiwa amare.
Su mama laraba da ya uwata biyu sai Aisha da Fatima da wasu mata uku daga dangin su suka zo tare da kayan lefen su.
Nan guri ya cika da yan kallo ina daki na shirya cikin jan lafaya da anty taba Zarah tazo dashi cewan ta wai shi zan saka ajikina.
Kalar shi kamar ja ko purple gashi nan dai mai kyau da shi da tai makon Zarah na shirya jikina tsab.
Basu dade ba sukace a fito masu da amarya zasu tafi don kada yamma ya soma lokacin sai da akaini gidan mu nai masu sallama babana yai min nasiha sosai ma ratsa jiki tare da samin albarka ga aurena.
Muka fito muka nufi gurin maigari shida mutanen shi da matan shi suma saka saka min albarka ina kuka aka kama hanya dani zuwa sabon rayuwa agidan da na tsawon rayuwa a cikin shi.
Sai fanan tunane nakeyi yadda zamana zai kasance cikin wa yan nan mutanen masu wuyan fahinta.
Kaina naduke muna a motar dani da Attu da mama laraba dake zaune a gaba tare da driver da suka zo dashi.
Attu ta duko a hankali take ce min na fara adduan da malam ya fada min a raina hakan na soma jero adduoi a cikin zuciya na harda ma wanda malam baice ba duk na dinga yi a raina.
Nai mamakin jin cewa wai mun iso garin nan na ci gaba da jero addua gaba na sai faduwa yake faf faf faf duk na rude na rikice.
Muna shiga gidan naji daya daga cikin matan ta rangada guda irin mai sunan ruda kishiya.
Aiko haka din ne ban yi tsanmani zanga mutane ba cike a gidan sai dana gama addua na fito ne naga ko ina makil da mutane yan uwa da abokan arzikin su sun zo.
A hankali ina rike a hannun Attu da mama Altine muka fara tafiya zuwa cikin gidan.
Anty tasha kwalliya sosai tafito tare da mutanen ta sai ji nayi ta rungumay ni cikin murna da jin dadi muka kara har ciki da yake idona yana a rufe na dauka a part din anty muke.
Dakatawa mukayi daga kofan anty na fadin adakata tayi addua ta shiga da kafar dama.
Nagama ta duko a hankali ta rada min Allah ba da hassan da hussaini Nasir ya samu yan uwa.
Kuka na saka a hankali tana rike dani har zuwa uwar dakin da yake mallakina ta zaunar dani a bakin gado na zauna da bisimillah a bakina.
Gaba sai faman faduwa yakeyi abinda ban sani ba shine ashe tunda aka gyara part din sai wanan lokacin ta shigo gyaran da akaiwa part din yafi duk sauran part din dake gidan kyau tsab an kashe kudi sosai a gurin.
Take taji wani kishin hakan ya tokare ta yaya akayi besty ta farawa da iyawa yai masu haka akaina wanan ai kamar rashin adalci ne take gani.
Nan dai aka gabatar da abinci ga baki da sukai min rakiya daga kauyen inda yan uwana ne sai yan uwan mahaifina dana Innata su goma sha biyu akazo dasu.
Mamaki suke wai yau ni Rahama dake cikin su Allah ya kawo cikin wanan daulan duniya hakan.
Aka tsiyaye aka barni da yan uwana da kawaye na duk da haka fuskana yana rufe ban bude ba har lokacin.
Naji an fado min a jikina tare da rugumay ni naji yace little mum kika tafi ki kika barni why ?
Nasir ne jin muryan shi yasa na bude fuskana a hankali tare da rugumo shi a jikina.
Sai ga Amira da gudunta tafada min ajiki tana murna da farin cikin ganina rake cewa mummy tace bazaki kara wuce wa ki barmu ba wai kema yanzu kin zama matar daddy mu.
Murmushi nayi na jawota a jikina ina tambayan su kunci abinci Amira tace dani Nasir baya cin komai sai dai yasha drinks har da dukan shi mummy tayi.
Nacewa Nafisa ta debo min abinci na basu mama Altine na gefe tana kallon mu nan nafara ba yaron abinci ya ko soma ci a hankali.
Ina cikin bashi anty ta shigo dakin da kawayen ta sunzo su gannin suka samu yaran na a jikina ina basu abinci da hannuna a hankali.
Wata kecewa ji yaran nan da akayi dasu suci abinci amma sukaki yanzu gasu suna ci a nan.
Suka dan yi min nasiha suka fice daga dakin aka barni dasu Attu da mama suma nasiha dai suke min anan zasu kwana sai washe gari zasu tafi.
Bayan na bude idone nabi dakin da kallo sai lokacin na fahinci ba part din anty muke ba ke nan nima an bani nawa part din ke nan a gidan ikon Allah yau ni Rahama keda part a wanan mamakeken gidan na Daddy ke nan.
Bayan Sallah magariba sai ga mama Laraba ta shigo take cewa na shirya zamu falon maigidan dukkan mu.
Bata dade da fita ba sai ga Anty na tashigo take cewa oyya mike maza ki shirya zamu hadu a part din maigidan za, a muna magana a can.
Ita da kanta ta shiryani tsab cikin wani lafaya mai launin purple colour ta dauko turare kala kala duk ta feshe min jikina da.
Duk wanda ya ji yasan cewa ni amarya ce ga zanen lallen da akaimin ya kara haskani ga kitso da aka yarba min kanana akaina.
Bakishiya ba ko natare da kishiya ta ganni sai taji wani abu ya soke ta a ran ta balle kishiya.
Gaba daya matan gidan har maigidan duk suna falon shi a zaune tare da su mama Laraba da yan uwan ta da sukaje dauko ni kauyen mu tare zuwan mu kawai ake jira sai gamu mu mun shigo anty tana rike da hannuna fuskana yana a rufe lif kamshin turarena sai daya razana duk wani wanda ke falin lokaci sa kishiya fargaba ke nan.
Anty na kokarin zaunar dani saman kujera amma saina zamo kasa saman kafet na zauna.
Kowan su kishi ya turniketa sai kada kafa sukeyi cikin takaici da jin haushi nikan duk nasha jinin jikina a lokacin.
Ina jin mama ce ta bude taron da addua tare da soma kiran sunan maigidan sai na Saade zulfa sai hindu a karshe.
Tace to yau ga Rahama Allah ya kawo ta cikin ku a irin matsayin da kuke kuma a gidan nan watau na matar gidan itama.
Don haka kai Alhaji dakai zan soma don Allah don Allah kayi kokari ka kwatan ta adalci a tsakanin iyalin ka haka shine zai kawo maka kwanciyar hankali ga iyalin ka.
Kowan su anan zaman ka yau sukeyi babu banbanci a tsakanin su sai har idan kaine ka soma hakan .
Don haka kowa ya tsaya a matsayin shi babba ya rike girman shi karami yarike girman shi na karanta kada wata ta shiga hakkin wata a cikin ku.
Idan kunyi hakan gidan ku zai zama abin sha, awa gakowa kuma gurin zuwa ga ya uwa.
Amma idan har ba zaman lafiya kamar kullun babu wanda zaku gani yana zuwa gurin ku.
Don haka kuda yau tazo ta sama a gidan ina mai kara baku hakkuri da ku kara yin hannkuri ga yadda auren yazo a bazata gareku haka Allah ya kaddara akwai aure a tsakanin su dama haka abin yake ga Allah.
Da fatan za, a zauna lafiya cikin kwanciyan hankali batare da wani fitina ba duk amana kuke a gurin shi.
Hindatu tace Allah yasa haka mama amma ina da magana sai lokacin daddy dake zaune a falon kamar baya ciki yai magana yake cewa ki bari tagama maganan ta mana may ye na gagawa.
Tace ai ba zancen gagawa bane sai gaskiya don wallahi bazan lamunci yarinya taimin rashin kunya ba don tana takaman ita wai matar gida ne don ba kunyane fa Rahama sai in wa yarinya dukan tsiya wallahi.
Yace tunda ga yarki an kawo maki ko?
Zulfa tace kinji ko mama tun baki tashi ba dama nasan indai yaya ne ba wani adalcin da zai shuka anan tunda tun farko yana son Rahama dama.
Sai lokacin anty tai magana tace wanan kuma zargine irin naku amma babu soyayya tsakanin su a baya gaskiya kuma kun sani.
Don Allah malama ki rufe muna bakin ki munafuka kawai ai duk bakin ku daya badake aka hada baki akai muna hakan ba hallan don a tozarta mu.
May ye na tozarci a cikin kara aure ba, a kara aure ku aka auro ku kuka shigo inji anty kowa dai tashi tafisheshi kawai.
Nan fitina ya fara kowa na fadawa dan uwa bakaken magana a tsakanin su.
Hawaye ne ke zubomin daga cikin mayagin da nake rufe har kaina tun ina yi a boye har yafito fili na kasa boye kukana a gaban su ba kowa yajamin wanan zargin ba sai anty na.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, DON BA A YAFE MAKI BA , ,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YAR UWA DON ALLAH YANA GANIN, ,
40

Duk yadda anty tayi dani wai na koma part dina na kwana ki nayi nan muka kwana nida su Nasir a dakin da muka saba kwana don sai da na bari anty ta shige na fito na dawo dakin na kwanta.
Sai washegari ta gan ni kwance a dakin ko shi cikin kargin hali ta taso gabanin asuba don ta duba lafiyan yaran ta sai kawai ta samay mu kwace tare da yaran duk sun haye min jiki muna barcin mu hankali a kwance dasu.
Muryan ta naji da asuba tana tayar dani dan sallah nai mamaki yadda yau nai barci haka har sai da aka tasheni wai kamar nai wani aiki.
Na mike zubur ina salati nace anty mun makara yau ko gashi ban hadawa babeis dina abincin makaranta ba.
Tace yanzu Rama saida kika kwanta da yaran nan don Allah ban tsaya saurarenta ba na fada ban daki kada na kara makara da sallah.
Nafito na fara gabatar da Nafila nakawo asuba nayi na dan dauki lokaci ina addua na mike na nufi kitchen.
Ranan faten doya nai masu yaji kayan lanbu sosai da drinks na zuba masu a gorunan su.
Na hadawa kowa basket din shi nai masu wanka na shirya su da sauri har na dauko hijjab zan kai su wurin mota sai nayi wani tunane naja na tsaya a sanyaye nace Gajiye don Allah zoki kai su bakin mota.
Sai bayan ta tafi ne na soma gyaran dakin naiwa dakin tsab na koma falo na gyara shi tare da saka kamshi dakin anty na shiga na fara gyara har nayi nisa ga gyara motsina ya tayar da ita.
Tace Rama may kuma kikeyi nace anty ina gyaran daki ne tace haba mana Rama kinga haka zai yuyu kuma ace kin saura gyara min daki yanzu.
Don Allah daga yau ki bari ki je ki shirya Hamza idan ya dawo kai yara zai saukeki makaranta maigidan yace bai yarda ki fita ke kadai ba don wanan mahaukancin sojan bai fita zancen ba har yanzu.
Ni kaina saida tsoro ya kamani don na tuna yadda mutanen shi suka dinga farautana a baya.
Karasa aikin nayi na wuce dakina na part din anty nai wanka na saka wasu zannuwa da riga na kawo katon hijjab dina na dora sama ban yi wani kwalliya ba irin yadda na saba yi idan zan fita.
Na dauki takarduna na nufi dakin anty nan jinior ya lake min wai zai bini da kyat anty tai mai wayo na samu na fice ina mata sai na dawo.
Ina fitowa na samu hamza ya na jira na a waje sai muka hade da hindatu ta fito a cikin shirin ta zata fita daga gidan tana ganina ta bini da harara.
Na kawar da kaina kamar ban ganta ba har ta doshi motar ta ko may ya faru kuma naji ta kwalawa Hamza driver kira ya je da saurin shi gareta cikin girmamawa.
Tace wai so take ya kaita uguwa yanzu yace cikin dan girmawa hajiya don Allah kiyi hakkuri tun jiya da dare Alhaji ya bugo min waya na kai amarya school.
Kam kazan uban nan hamza ni zance ka kaini guri kace wai Alhaji yace ka kai mai wata can wani guri ?
Ka ko san abinda kake fada min kuwa da bakin ka zakace min wai zaka kai wanan mara mutuncin wani guri ?
May kake nufi ko shi Alhajin may yake nufi ko kana nufin ta kaini matsayi ne a gidan ko ta fini ?
Ba hakana bane hajiya Alhaji ne ya bani umurnin yin hakan yanzu zan aje ta na dawo don yanzu ya kirani yana min fada wai ban kaita ba tun dazun kada ta makara.
To bazaka kai taba sai na gama lalura na ai ya saya mata mota tun tana kwartuwan shi ko ?
Hamza dai ya dukar da kai don maganan ya soma fin karfin shi don shi namiji ne ba ruwan shi da zancen kishin matan gida.
Yace hajiya sai dai kiyi hakkuri don bazan iya ketare umurnin Alhaji ba na gyara maki naki.
Ya juyo ya barta tsaye ta rusawa kowan mu zagi na fitan arziki ni dai na shiga mota yajani muka fice daga gidan.
Muna kaiwa naiwa hamza godiya na fada mai six zai dawo ya daukeni daga school din yaja mota bayan yaga shiga
Showing 168001 words to 171000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57 Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153