zan kife a wuri da sauri na dafa kujeran shima ashe yagani ya yo kaina ya rike ni yana fadin subbahanallahi kin gani ko zaki jawa kan ki wani matsala kuma can.
Hindatu ce ta shigo ta samay mu a hakan da sauri ya sake ni yana fadin ki lalaba kije ki kwanta ki dan huta.
Wani kallon banza ta watso muna batai magana ba na samu na mike da kyat na bar falon daki na koma na kwanta sai barci kai nauyi ya dauke ni.
Ranan ban shiga school ba koda na tashi na samu miscalled din Zarah yakai shidda a wayana nan dai na kirata muka gaisa take tambaya na ko may ya hanani shigowa yau.
Nace dan matsala ne ya ke faruwa sai kuma banjin dadin jikin nawa shine na dan kwanta ashe barci ya dauke ni ban sani ba.
Mun kai wani lokaci muna waya tana fada min abinda akayi a ranan muka kuma shiga wani hiran da ita sai da muka gaji na kashe wayan .
Wanka na mike na shiga nafito na gyara jikina na nufi inda su Gajiye suke muka zauna muna hiran mu dasu.

********* ********* *********
Yashigo part din daidai lokacin da bakuwar yar aikin anty take dauko mata abincin ta a falon.
Gaidashi tayi kallo daya yai mata ya kawar da kai gareta matar ta fice daga falin ya juya gare ta yana kallon ta yace wanan kuma fa daga ina take haka ?
Tace sabuwar yar aikina ce yar aiki kuma ya tambaya tace dashi eh yace ina ita gajiye din kuma tace na sallamata na dauko wace na yarda da ita.
Rai bace yace kamar yaya kin sallamata ita wanan din kin san ta ne ko kin san halinta ne ?
Tace ko ban san ta ba tafi min zama da mai cuta na yace gajiye din ce take cutan ki kuma Saade ?
Don Allah mu bar zancen tunda na fada ma komai ba shike nan ba yace bashi ke nan ba kan don ba zan zauna da wanan matar a gida na ba na fada maki.
Tunda abuyazo kaina yadda baka so ba yanzu ai dole ka fadi hakana babu inda zata ita nake son zama da ita ba wata bacan.
Yace bako a gidan nan ba na fada maki wai may kike nufi danine haka Saade na dai biki da lalama amma naga abin naki sai gaba yakeyi.
Sai kayi abinda zakayi dama ai kaji dani zaman dole kake dani tunda ba komai nake tsinanama ba ko ka samu yarinya karama yanzu kana murza.
Koma may ye naji don haka sai ki san dabara tun ban shiga rigan arzikin ki ba rayuka sun baci mara tunane kawai.
Yafice rai a bace ya barta tabishi da harara tana cewa ni za aiwa burgan maza ko may ?
Bai tsaya ba ya fice yaje ya samu mahaifin anty ya labarta mai komai dake faruwa a gidan shi tsakanin mu da anty din.
Mahaifin nata ya murmusa yace kaji halin mata ko kamar ba ita bace nan da kukan ta akan a bari ka auri yarinyar nan.
Yace ai Abba cewa tayi yanzu kuma wai asiri ne su kai mata abba yace kai mata sai a barsu kawai in bashi ba keda kikai aikin lada dan kankanin lokaci kuma kizo ki zoje ladan naki haka ta hanyar shimay irin nasu na mata.
Wana Falmantan takai shuuma babba wallahi ai dole muyi kokarin rabata da ita yace da daddy ya tafi zai zo har gidan da kan shi ya samay ta ai.
A ranan kuwa Abba yazo gidan inda yai masauki a falon maigidan a can aka kira yar tashi ta samay shi sun buga wuta sosai saida Abban ya nuna mata bacin ran shi akai ta dan sauko.
Sai dai taki yarda sam da zancen canza yar aikin da tayi dole aka hakkura aka barta da wacce take son zama din acewan ta.
Nan daddy yasa akirani nazo yake cewa dani don Allah nayi hakkuri da abinda ya faru ina kuka nake kara ba anty hakkuri idan na saba mata ne tace ita ban mata komai ba sai daddy yace babu inda Gajiye zata tafi ta zauna dani don auren ta ya kusa dama shi ke nan sai a wuce wurin.
Nan dai muka watse muka barshi da yar shi yana kara dan mata nasiha yake cewa kefa da bakin ki kikace yarinyar nan ta sama maki magani akan matsalan ki kuma yanzu alhamdullahi alama ya nuna kin samu lafiya shine zaki saka mata da wanan halin da kika tsiro da rana tsaka.
Ki sani fa da kanki kikai tabin yaron nan akan ya auri yarinyar nan yanzu kuma anyi auren kina samun lada zaki bata zancen ki a dan kan kanin lokaci haka har may akayi ko ga zaman ku in akwai rayuwa bazaki kwadayin kema kiga kin saka wa yarinyar nan ba kada fa ki matan da irin halarcin da kukaiwa junan ku abin gwanin ban sha, awa daku.
Jikin ta yai sanyi da kalamin mahaifinta sai dai gaskiya hudubar Falmata ya riga yayi tasiri a zuciyar ta sai dai zata rage wani abu don bin umurni kawai.
Da Abba ya fito sunyi mai rakiya hindatu nagani tasan da akwai magana don Abba baya zuwa gidan haka a banza kai tsaye.
Can ta samu Zulfa da zancen duk da ba dadine a tsakanin su ba take cewa da ita mutanen ki fa ina ganin zumunta ya watse a tsakanin su don akwai magana koma may ye ai ji zamuyi muna zaune don sai na gano komai ke faruwa din inji Zulfa take fafin hakan.
Ranan dana karbi girki har lokaxin bana jin dadin jikina daurewa kawai nakeyi gashi da dare jikina yai wani irin mugun gashewa da zafi amma daddy bai sani ba.
Hakana nake daurewa har na gama girki na gashi ba wani daddy tsakanina da anty sai dai dan saukin anin ina gaishe ta ta karba min harda tambayana ya school tanayi.
Sai dai ba wani dogon hura a tsakanin mu kamar da can baya bani dau gajiya da zuwa gurin ta gaida ita duk da na fahinci bata son hakan.
Matsala kuma yar aikin ta kazama ne ko girki bata iyaba gashi part din duk ya lalacemata kullun sai sunyi fada da daddy ya kasa cin abincin abin ya fara damunta sosai sai rikice ya fara samuwa a tsakanin su take cewa wai ya dai gaji da ita ne kawai yake kirkiro mata matsala a tsakanin su.
Ranan suyi rikici sosai har ya daga hannu ya mareta fada sukayi ba dadi a tsakanin su sosai harta jefo zancena a cikin maganan fada sukayi take fadin wallahi sai taga bayana a gidan nan.
Ranan kan makiya sun dara don tabar abin fada a garesu hankalina yai matukar dagawa sosai nake cewa da ita nikan anty zanbar gidan don dama kece sillar shiga na a ciki.
Nan na barsu nafice falon da aka taru masu ban tsaya ba su gajiye da fatima na bani hakkuri na dauki handbag dina na fice daga gidan ban masan inda zan nufa ba sai can dabara ya fado min na wuce zuwa gidan Amina course mate dina na kuma roketa kada tafadawa ko Zarah ina gurin ta zaune.



ZAINAB iDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON ONLINE NOVEL NE WANAN BA A YAFE BA, , ,

61
Gajiye ce tsaye a waje cikin tashin hankali tana jiran dawowan maigidan daga masalaci wurin sallah magriba daya fita.
Tana ganin shigowan shi ta tare da sauri tafara gaida shi a cikin tashin hankali take fadin Alhaji dama uwar dakin mu ce tun safe kuna wanan rikicin da hajiya ta fita bata dawo ba har yanzu.
Ya juyo da sauri yana cewa da ita wa kenan Rahama ko wa tace dashe ita Alhaji yace ina ta tafi har wanan lokacin tace wallahi ban sani ba don bata kai war haka a waje.
Yace da ita yaji ya shige ciki kawai ya barta tsaye a gurin dama duk yinin wanan ranan rayuwan shi a bace yake sanadiyar fadan da sukayi da anty din.
Yana shiga ya furzu iska daga bakin shi yana fadin a fili ina wsnan yarinyar zata shiga kuma har wanan lokacin haka?
Wayan shi ya ciro daga aljihun gaban rigar shi ya shiga kiran layina duk iya kokarin shi bai samu layin ba gaba daya.
A Lokacin ne hankalin shi yai mugun tashi azaton shi ko ina gidan Abba ko na mahaifan shi ne sai yai dabaran kiran su da sunan gaisawa dasu amma har ya gama gaisawa da kowan su baiji an sako mai zancen Rahama ba.
Haka yasa ya dan shiga cikin damuwa sosai don shi baiga dalilin da zai sa na saka kafa nabar gidan ba don badani akai fitina ba ai suna na ne kawai ta shigo cikin zancen su.
Har dare sosai bani ba labarina a gidan dole ya hakkura ya kwanta cike da damuwa gashi anty ce da girki bata shigo gidan ba.
Ita ko uwar gaiyyan bata ma san cewa bani gidan ba har lokacin tana can ta dauki fushi da kowa a gidan don tana ganin an mata tozarci a bainan jamaa.
Tun da safe ya buga kofan part dina Gajiye ta bude kofan tambayan ta yayi da ta dawo kuwa ?
Cikin damuwa tace dashi wallahi bata dawo ba Alhaji ko gida ta tafine dai yace an ya ban tsan manin zata tafi gida don da sun bugo waya ai.
Cikin ikon Allah yana komawa part din shi sai ga maigari yakirashi suka gaisa yaji yana tambayan shi muna dai lafiya ko ?
Wanan yasa ya kara tabbatarwa da ina cikin garin dai na samu inda na boye je kawai amma ai duk inda nake zai gane.
Anty suna gaisawa da Falmata take fada mata abinda ya faru Falmata tace bana fada maki ba wanan yarinyar annobace a gare ki .
Don ta riga da ta asirce ki ta ko ina ba ki da sauran motsawa dole ne asama maki makarun abinda tai maki tun kan ki cutu da yawa.
Sunyi da ita zata shigo gidan su kara tataunawa zuwa rana don su san abinyi akai a cewar ita falmata din.
Sai dai suna gama wayan a bangaren Falma sai ta sauke wani shu,umin murmushi kawai tana magana a zuciyar ta ita kadai.
Daddy ya kira Bashir yazo nab yake labarta mai abinda ke faruwa a gidan shi har da barina gidan danayi bai san inda na nufa ba.
Nisawa Bashir yayi bayan ya gama sauraren abokin nashi yace watau su dai mata haka halin su yake basu da tabas akan halaiyan su ?
Yanzu ita Saade harta manta da irin halarcin alherin data shuka da Allah ya baku rabo tsakanin ka da Rahama aida ankai ga diya biyu a gidan nan da ita.
Nan dai suka yanke shawara akan su shiga school tunda sun san a wanan lokacin da nake ga ganiyar gama karatuna babu inda zan tafi na bar karatun nawa ai.
Sun shiga school din da tambaya suka isa department din mu inda suka rasa wa zasu tambaya sai ga wata daga cikin dalibai tafito da ganin ta yarece ita don tai kama da kabila suka gaida ita.
Nan Bashir yake tambayan ta ko tasan wata Rahama anan department din tace da hausa gaskiya da wuya da nan san abinda take karantawa ne sai lokacin daddy yai magana yace matar aure ne tana yawan shiga CRV assh color tana shekara na shidda ne yanzu.
Tace ok nagane ta wata fara kyakyawa mai kamun kai bata da yawan hayaniya sosai kawar Zarah Ko ?
Yace ita,
Tace nadai ga shigowan Zarah din dazun amma ban san ko ita tana ciki ba don ko tana nan baka ganin ta sai idan sun fito zuwa sallah.
Tace dasu tana zuwa ta juya zuwa ciki daddy yai tsuki yace wasu akwaisu da surutun tsiya wallahi wanan dogon bayanin waya tambaye ta ne wai ?
Bashir yai dariya yace ai ta taimaka muna koba komai munji wani abu gamay da Rahama din anan suna cikin magana suka hango fitowan ta da Zarah tana saye da hijjab daidai gwiwan ta.
Tana ganin daddy tai mamakin may ya kawo shi kuma gashi yau bata ga na fito ba ko ba lafiya ne dai yazo complain.
Suka gaisa sai yaji tana cewa ince ko lafiya daddy yau banga mutumiyar nawa ta fito ba nayi kiran layin ta har ba iya ka ban samay ta ba tun jiya.
Ganin wanan yarinyar ta farko taki tafiya takuma tsare su da idanuwa yasa shi cewa lafiya kalau wallahi dama mun zo ne mu ganki jin haka yasa lydia barin wajen tai masu sallama zata tafi bashir yace ta dakata ya bata dubu biyu ta wuce tana masu godiya.
Bayan tafiyan ta Bashir yace doctor Zarah dama kawar ki muka zo nema a nan don tun jiya tabar gida bamu san inda ta shiga ba kuma.
Munyi zaton kuna tare ne sai gashi kuma munji kina fadin ke ma kina nemanta ne yanzu ?
Cikin faduwan gaba Zarah tace bata gida ina ta tafi kuma ?
Daddy ne yai magana wanan karon yace ko akwai wata kawar ta da kika sani ko zata tafi can gurin ta anan garin ?
Tace wai da wuya wallahi don Rahama bata faye shiga mutane ba in dai ba wacce ban sani ba ne amma kuma an tambaya can gida kauye ko tana can.
Yace da wuya don munyi waya dasu suma suna tambayan lafiyan ta dazun da safe kin ga bata can ke nan.
Nan dai tai masu alkawarin cewa zata taimaka ta bincika duk inda ta san na sani tagani ko Allah zai sa a dace.
Sukai mata sallama suka tafi kasa zama tayi anty Amina tana ganin ta take tambayan ta ko lafiya ?
Tace anty kawatace ke cikin dan matsala yanzu mijin ta yazo nan ya wuce Allah ya sauwaka tace tabar ta bata kara magana ba.
Koda ta dawo gida ta samu na gyara mata ko ina na gidan har girki nayi mata don daga ita sai kaunar ta ne zaune kuma duk suna fita zuwa makaranta yaran ta da mijin ta basu garin suna can Enugu zaune inda mijin ta ke aiki karatu ya tsayar da ita a kano sai ta samu hutu take zuwa.
Ina zaune a falo ta shigo gida da yamma kamar yadda muke dawowa a wahale tace kai kai kai lalai yau gidan nan yasan yayi bakuwa kan.
Nagaida ita muka zauna ina tambayan ta abinda akayi tai min bayani can tace Rahama maigidan ki fa yazo neman ki a school yau shida abokin shi.
Kawar ki ma naga ta shiga damuwa don bata ma zauna ba nace Allah sarki nasan Zarah tafi da haka wallahi.
Nan mukai magana sosai da ita kan matsalan abinda ke faruwa dani take cewa ni yanzu Rahama banga abin tashi ba anan ?
Tunda dai mijinki bai maki komai ba matsala dai da kishiya ce don may zaki biyewa rudin shedan ki baro dakin ki ?
Nace anty Amina gaskiya barina gidan shine alheri gara dai na bar mata mijin ta a zauna lafiya tunda kinga matan nan tai min halarcin da ba kowa ce mace ne zata iya yiwa bawa shi ba.
In dai nice zan kawo mata matsalan farin cikin ta gara dai na barsu kowa ma ya hutu tace a naki tunanen ba ina zaki kai son mijin ki a zuciyar ki ko shi yaya kike son yayi da ran shi a rashin ki ?
Gashi kwana daya har ya fara yawon neman ki a gari haka ni idan zakibi ta nawa kiyi hakkuri ki koma dakin ki ki share kowa taita haukan ta ita kadai.
Don ko batace ba dama Allah yayi akwai aure a tsakanin ki da shi tun farko ki daina wani tunanen wai don ita tasa ya aure ki ta dawo kuma tana cuta maki haka ?
Dole fa sai kin nuna mata kema din mace ce tunda kikaga ta fara wanan halin idan ba kunyi fito na fito ba ba zaku taba zaman lafiya ba yadda kike so da ita.
Don ko yaushe magana ya tashi cewa zatayi ai a dalilin ta ki ka aure mata miji gashi mata fara zargin kun dade tare dashi tunda tana bakin ciki ya nuna yana son ki haka.
Watau ita so tayi ki ta zaman takura tana juyaki yadda ranta yaso ki zauna baki da incin kan ki ko kadan sai yadda tayi dake ke nan ?
Nace ba hakana bane Anty da farko fa zaman mu gwanin ban sha, awa ne don ko makara nayi ban tafi gurin maigidan ba zokiga yadda take bata ranta akan hakan yaran ta kuma tana matukar son yadda muke muamula dasu .
Shigowan wanan kawar nata ne a rayuwan ta ya kawo muna duk wanan matsalan da muke ciki da ita a yanzu din.
Tace kai haba Rahama in har son Allah da Annabine ai babu wacce ta isa ta shiga tsakanin ku irin yadda kuke da ita din nan.
An dai tarar da hali dama akwai wata a kasa kece dai da kike zaune da ita Allah ma,aiki kike ganin ba wani abu a zuciyar ta amma
Showing 255001 words to 258000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86 Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153