na mika mata kullan dana soya kaji nagyara mata kamar miya nace gashi mama mu zamu tafi.
Baba har ya bude nashi koyana fadin a, a, a duk ni keda wanan abin haka yaushe rabo danaga haka gareni.
Itako ta karba tana wani tabe baki Aisha ne ta fito ta bude taga abinda ke ciki tace , a, a, a muma bari mu tsaya mu kwashi rabon mu nan.
Baba sai albarka yake saka muna da fatan alheri da gamawa da duniya lafiya.
Muka fice dan tafiya kadan don unguwa gudane sai gidan mama laraba muka shiga mun samayta a falon ta tana ganin mu taji dadi tana lale marhabi da sarakuwa na yau kune a gidan an tuna damu ke nan.
Jin haka yasa Farida dake dakinta lekowa taga ko suwaye tana ganina ta sake labule zata koma ciki.
Nace ai idan ni bazaki gaidani ba kya tsaya ku gaisa da dan uwanki ko may yai zafi hakane wai.
Ta karasa fitowa tana cewa saidai haka amma bake ba tunda kin munafunce ni muna tare.
Zaki fara haukanki da wauta ko itadai Farida ta gaida da daddy ya amsa mata a dake ta shige sai bayan na gaisa da mama ta tambayeni sauran mutanen gidan nace duk lafiya muke.
Tashi nayi na shiga gurin Farida na samay ta kwance ta ba da baya na zauna ina dafa ta nace haba mutumiyar maiyai zafi hakane tsakanina dake ?
Tace bar ni don Allah ni ai kin bani mamaki wallahi ace muna tare wai zaki auri daddy ban sani ba Rahama ?
Nace Allah sarki yadda kika ji zancen wallahi Farida nima haka naji shi ban san komai ba akai har yanzu na kasa fahintar inda zancen ya fito har yau din nan.
Tace ina ko zaki sani tunda bukatan ki ya biya dama haka kikeso ai shiyasa kikaki soja dake son ki kamar may.
Nan dai mukai ta fafatawa da ita wanda hiran namu duk kusan gatse ne take min kan auren daddy danayi.
Can naji mama na kirana nazo mu tafi nai mata sallama nafito taki rakani nan mama ke cewa dani naita hakkuri da kowa kada nasa zancen hajiya a raina nace lah mama ai babu komai hajiya ai uwatace duk abinda zatace dani ya nake gareta.
Muka fito muka nufi gidan Abba shima sai albarka yake sa muna daga haka muka juyo zuwa gida.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
ODAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU, IDAN KUMA KIN KARANTA DAKE DA ALLAH YAR UWA DAN NA FADA MAKI, , ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YABI MUNA HAKKIN MU A KANKI DON RASHIN TSORON ALLAH YA KAIKI CIN AMANAN ZAMA, , , , , ,

44
Mun dayi nisa naji yace dani ba tare da ya juyo inda nake zaune ba cikin damun akan hajiyan shi da al, amarin farida.
May ke faruwa tsakanin ki da Farida ne haka naga kamar tana fushi dake ko ?
Sai da nai ajiyan zuciya nake cewa dashi nima ban sani tundai da zancen auren nan yazo naga ta dauki zafi haka dani.
Yace kyale mahaukaciyar banza bata da hankali nake gani wanan yarinyar Zulfa na gidana take son ita ma wai na aure ta ?
Cikin mamaki nake kallon shi yace kwanaki ta turo min da sako mara dadi, nayi bincike na gane ashe itace take hasala wanan mahaukacin sojan dake son ki ashe ?
Shiru nayi cike da mamaki wani shago ya tsaya da mota ya shiga shi kadai sai gashi ya kwaso muna kayan snacks da su sweet da sauran abin yara sai drinks masu tsada da ya sawo.
Yake cewa tsaraban yaran ki ne don zamu samu sun dawo gidan yanzu nace Allah ya saka da Alherin sa.
Daga haka yaci gaba da tukin mota tare da mayar da hankalin shi ga titi sai sautin kira,an ke tashi a motan.
Muna gaf da shiga gida ya dan rage sautin kira,an yace cikin wata murya mau kama da na tausyi tare da dan shafo fuskan shi tun daga kai har zuwa haban shi yace.
I hope abinda ya faru tsakanin ki da hajiya baki dauke shi da zafi ba a ranki ?
Murmushi nayi tare da harde yatsuna cikin yan uwa ina dan wasa dasu na dan kalle shi nace daddy ai hajiya uwace kuma gaskiya ta fada don babu karya ga maganan ta.
Ban kai wanan matsayin na Allah dai ne ya nufe ni da hakan a kaina amma nima nasan gaskiya ta fada sai dai maganan zargine kawai matsala.
Wallahi tunda na dawo a matsayin mata a gidan ka ban taba taka part din wata mace ba sai na anty sai ko da wanan abin ya samu anty Zulfa anty tace na rakata.
Stop thinking that babu sunan ki ko na Saade ga wanan matalan matsalarsu ce can da ta shafe su.
Na sauke ajiyan zuciya muna shiga gidan har Zulfa na a haraba zaune saman farar kujera tana shan iska tare da wasu mata biyu.
Bin mu da kallon mamaki takeyi bayan motar ta tsaya bai bari mun fita ba ya juya yana dauko kayan dake seat din baya daga nisa inda suke hangen mu sai mutum ya dauka ko nice yake runguma a mota a haka.
Zuwa can muka fito ina kokarin karban kayan a hannin shi ne yace no barshi jida hand bag din ki kawai.
Ina gaba yana bina baya naji sunyi tsit basu magana da alama mu suka bi da kallon.
Ina shiga da sallama yara sukayo kaina da gudu kamar nai tafiya ne mai nisa suna min oyoyo.
Na rugumay bayan sun sake ni na je inda anty take zaune na dan rugumay ta tana fadin lun dawo nace da ita eh lokacin daddy da ya tsaya waya ya karaso da ledoji a hanayen shi.
Na mike da sauri na karbi ledan anty tana mashi sannu da zuwa tare da tambayan shi yaya su Alhaji da Abba ?
Yace suna lafiya bai zauna ba yake cewa zai tafi yai shirin zuwa sallah lokaci ya gabato.
Wanan ledan kuma fa na may ye nace nasu Nasir ne tsaraba aka sayo masu.
Nasa hannu ga jakkana na fidda kudi nace anty gashi wanan yan dubu Abba ne ya bani sai wanan kuma Alhaji mama laraba taban wanan turaren wutan na fito da kwalban na aje a gaban ta.
Tace masha Allahu ai an gode kuwa motsi yafi labewa ke nan na mika mata tace cikin kallona kamar da mamaki may zanyi dasu kuma Rama ?
Nace ki karba ki aje a gurin ki mana tace haba dai wai ke ko yaushe yarinya ce ke ko may ?
Don Allah ni rabani da abin dariyan ki kin ji na kirga dubu uku naba gajiye sai anty tace abude ledan muga tsaraban ko ?
Ina kiciniyar bude ledan naji tace dani kun samu hajiya a gida ko take annurin fuskana ya sauya nace eh a hankali daga haka ban kara magana ba.
Haka yasa ta fahinci akwai matsala duk yadda akayi kawai dai ban fadi bane na barshi a raina.
Bayan na bude ledan yaran suka kewaye ni suna na basu na shiga dunbuzowa ina mika masu uwar tace Rama duk ina zasu da wanan haka?
Nace Anty nasu ne fa su aka siyawa shi abarsu su sha abin su ai nace da gajiye tazo ta diba.
Kiran sallah da aka fara shine ya tayar damu gurin mu ka watse zuwa sallah zuwa yanzu na dan fara sabawa da part dina can muka nufa ni da yaran gaba dayan su.

********* ********* *********

Bayan na idar da sallah yaran nata nasu suna kallo suna gardaman su na jingina kaina a bayan kujera kaina ya na sama.
Maganganun hajiyan shi ne ke fado min a rai da take cewa wai yar matsiyata mai farir kafa .
Ni dai na san gaskiya ne ni diyar tallakawa ne ba diyar kowa ba a duniya don ubana bamai kudi bane ba basarake bane kuma ba wani babban malami ba a kasa.
To amma shi farar kafar da tace min na maynene don a sanina anawa macen data shiga gida aka tsiyace ne wanan lakanin na farar kafa.
To ni may ya sa zatai min wanan mugun taken haka mai mumunan saurare da ji.
Ita kuma farida bilhakki fushi take dani na aure mata daddy bayan ta kwallafa ranta ga auren shi don tun tana karama ake cewa da ita matar yusuf shine ta rike hakan a ranta har ta girma dashi.
Bara ga laifin Zulfa ba da tai masu shamaki a tsakanin ta dashi sai laifina ni da banci ba ban sha ba ga zancen ta leke min.
Na dan zakuda na gyara kaina da wuya na yai min tsami nace akwai Allah don shi ya riga yai wanan hadin.
Kiran sallah akeyi shine yasa na mike na tayar da sallah isha,i tare da jero adduoi na shafa jinior ya tako zuwa inda nake ya haye min jiki yana cewa abinci zai ci wai.
Nace to bari nazo muje sai na baka ko amma ku tsaya ai wanka kafin mu fita na kwashe nai masu wanka sai ga gajiye ta shigo take cewa hajiya tace wai kizo kikaiwa Alhaji abinci dare ya soma yi.
Nace to gamu nan zuwa yanzu zan shafawa Amira maine tai murmushi ta juya taje tana fadawa anty.
Tace yaran nan maimakon su tsaya nan ai masu wanka shine sai sun tafi can sun sata aiki da wani zataji.
Gajiye tace hajiya ai Rahama bata gajiya da yaran nan barsu kawai suyi ta sha, anin su tace aina barsu.
Mun fito daga part dina na rufo don anty ko yaushe tana nanata min idan zan fito na dinga rufe kofa don a kwai hanya daga nan cikin dogon coridor din part din mu wanda ya bulla waje ta bayan gida inda wurin zai sadaka da hanyan part din su Zulfa sai falon sai part din maigidan dake tsakiya shine ya raba part din su da namu din.
A falo suke muna shigowa yaran na dan wasan nin su anty tace to bissimillahi sun dawo ke nan yanzu zasu saka kan mutum ciwo kenan.
Na durkusa na gaida ita ta amsa min take cewa kina can kina biyewa wa yan nan har mijin ki ya dawo yai ta jiran abinci.
Nace kai anty wai kuma mijina daddy ne mijina mijin ki dai anty tace ji min yarinya ni dai dauki abinci kikai kada yai ta zaman jiran ki.
Saye nake cikin wani dogon riga baki anyi hanayen shi da wuyan shi da material blue yaji duwatsu sosai yana walkiya na daura dan kwalin shi a kaina daurin na dan kwali ba rolling ba.
Ina zuwa sallama na keyi amma ba, a amsa min ba na sa kai na shiga falon zaune yake shida Zulfa suna fuskantar junan su sai dai suna gani na sukai shiru.
Sai da na jera kayan abincin a kasa na juya inda yake zaune nace daddy ina wuni yace Alhamdullahi.
Anty ina wuni nai mata ba laifi don ta amsa min a takaice tace amaryan daddy ke nan ?
Kai wallahi kuna bani dariya wai daddy shu wannan suna ai sai a canza shi don abin da nauyi wallahi.
Daddy yace sai ki canza mata keda ke jin nauyin hakan ni banga abin nauyi ba anan ?
Haka kawai ta wani dinga kiranka da daddy kamar wata yar ka can ko karamar yarinya ne ita yarinya na shigewa da kai daki har safe ta wa mutane kilibibin kiran ka da wai daddy ?
Yace ku kuma na gane shine zafin ku ko wai Zulfa may yasa baku son a zauna lafiya ?
Ke in kina da hankali wanan yarinyar ai ta gama maki komai idan kinyi dubaiyya irin halarcin da tai maki a baya ?
To abin zai kuma zama na gori ne yanzu wanan ai halin zama tare ne amma wanan ai ba zai sa na yarda da kishiya ba ko wacce ke tare da kishiyana a da can baya.
Allah ya kyauta yace Rahama shiga ki dauko min charger na bedside yana nan makale.
Tankar banji abinda suke fafatawa ba da Zulfa a kaina na mike tabini da kallo yadda jikina yake shocking duk takawan da nayi sai mutum ya dauka yanga nakeyi a hakan.
Bayan na shige ne taja wani uban tsaki tare da dawo da kanta gareshi tana cewa wai yaushe wanan kucakar yarinyar har ta koma hakane ban sani ba ?
Murmushi yayi tare da gyara zaman shi yace kuna dai zubar da mutuncin ku ga wanan yarinyar ranan da zata fara baku amsa zaku raina kan ku don na tabbatar na bakunta take maku kawai idan kunci gaba ba zata juri hakan ba gare ku.
Ko yanzu ma idan zata iya ai bissimillah Hindatu ce ta shigo sai maganan nasu ya tsaya anan.
Tana ganin Zulfa zaune suna magana ta dauka maganan girma da arzikine sai ta hade ranta tana cewa dashi.
Na dauka kai kadai ne dama magana nazo dashi zan tafi na dawo idan ba zan samu lokaci yanzu ba.
Zulfa tace kina nufin in tashi zakiyi magana dashi ke nan ko may kike nufi da wanan maganan taki ?
Nan kuma suka kaule da fada a tsakanin su shi dai yana zaune yana jin su sai dakilan wayan shi yake yi kawai.
Ina fitowa na samay su a hakan suna ta fitina a tsakanin su ganin na fito ina bin su da kallon mamakin abinda ya kawo masu fina yanzu yanzu don ban ma san shigowa Hindatu ba.
Na kara inda yake tare da rusunnawa nace daddy gashi ya dago daga abinda yakeyi yace min tnxs.
Maimakon na zauna sai na juya zan bar masu falon lokacin ya dago kai yana cewa dani ina kuma zaki ki bani abinci naci na kwanta.
Duk sai sukai tsit suka juyo kamar suna min kallon gareni komawa nayi na zauna daidai inda abinci yake na fara bude kulolin abincin .
Tuwon Alkama ne da miyan karkashi danye sai bussashen kifi da yaji da kayan yaji.
Ok idan kun gama sai ku bani guri zanci abinci yanzu .
Haba dai ai magana kowar mu tazo dashi sai dai mu yi mu fita kawai yace ba yau ba don banda time din hakan kuma .
Yana fadin haka ya mike ya sauko daga saman kujeran ya zauna akasa kusa da inda nake zaune yana gyara zaman shi tare da jawo roban ruwan wanke hannun dana aje a gaban shi.
Basu baya yayi yana fuskan ta na ina gamawa nima zama nayi a kusa dashi tare da gyara zaman gaf dashi muna fuskantar junan mu.
Bussimillah yayi ya soma cin abincin shi haka tasa Zulfa fara mikewa ta fice a hasale itama hindatu tabi bayan ta dama ba zaune take ba tana tsaye bayan kujera ta dafa ne don ganin Zulfa da ta sama a falon tare da shi.
Abinci yake ci hankalin shi a kwance ya miko min wayan shi yana fadin saka min cajin wayan nan.
Karba nayi da hannu biyu na mike zuwa jona cajin ya dan bini da kallon tausayi.
Bai san may yasa mata akan kishi basu da tausayi ba yasan ina dakon bacin ran abinda mahaifiyar shi tai min a raina da yamma.
Yanzu su kuma a kan hauka sunzo suna kara dada min wani sabon tention don baki kishi mai kama da hauka don ko kan su basu bari ba kuma wai suna kishin wata.
Na dawo na zauna a inda na tashi yake cewa dani ba zan so ace wata rana zaki kasance cikin irin wanan rayuwan ba.
Rayuwa irin wanan baida amfani da ace kamar yadda suke caza min kai irin haka Saade take da yanzu zaman garin nan ya gagareni.
Bana son rayuwa da fitina irin haka amma sai gashi yau Allah ya nufi rayuwa na da irin haka.
A da can baya idan naga mata suna caza kan gidajen su haka nakan ga sakacin kamar daga maigidan yake.
Ashe abin ba haka yake ba hakkuri ne da kawaici tare da dubaiyya irin na maza ke sa suna sakawa matayen su masu yawan fitina ido haka.
Yau sai gashi na wayi gari a cikin irin wannan rayuwan da ban taba tsan mani zan yi hakkuri irin haka ba.
Ya jawo roban ruwan wanke hannu ya fara wankewa yana fadin nasan komai daren dadewa idan ba su daina ba hakkurina zai iya koma min ciwon zuciya.
Da sauri na dago kai ina kallon shi don jin abinda ya fada yace kina mamakin hakane ko.
Haka din ne zakiji yanzu an kwanta da mutum sai dai a wayi gari ace babu shi bakomai bane zuciya ta gaji da magana nauyi yai mai yawa ya buga.
Yanzu dai yan kinji abinda hajiya tace a gaban ki duk da tasan irin rayuwan hakkurin da nake da yaran nan a gidan nan amma ita bayan su take goyo ni nata nine mai laifi .
A sanyaye nace daddy kayi hakkuri Allah zai kawo ma mafita dayar dan shi insha Allahu.
Showing 189001 words to 192000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64 Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153