may zan dauki zafi dake ni ko ba su suka fadi haka ba ai bani fushi balle su suka fadi .
May ye kishiya bata iya fadi a kan ka don ta bata maka rai kan shi ni wallahi in ma sunyi ne don naji haushi ni kan dadi ma naji da besty zai taimake ni ya aure ki ai nafi kowa farin cikin hakan.
Wani kallon mamaki nayi mata kamar zanyi magana sai na juya naci gaba da kwasan kaya na kawai.
Take cewa wai ba zaki ji abinda nake fada maki bane Rama ki daina wanan kwasan kayan da kike yi babu fa inda zaki.
Zanyi magana sai ga gajiye ta shigo dakin tana cewa hajiya kiji wa yan nan matan da basu da tsoron Allah.
Yanzu naje kai wanki naji suna fadin wai dama ke suka so duka amma Rahama ta kwabsa masu shiya su kuma sukai mata wanan kazafin dan kiji haushi ki koreta su samu su gasa ki yadda suke so.
Anty tace to ke kinji ni dama ai nasan sherin su ne hakana barsu nan inda kika gan su an sherin mutana ne.
Tace ai naji wallahi suna can har yan aikin su suna dariya wai ai dole yanzu Rahama ta bar gidan don koke ko mai gidan dole ku koreta.
Allah yafisu yafi sherin su babu inda zata sai ma suji haushi wallahi don yanzu ma zan sa aima Rama abinda basu taba zato ba a gidan nan tunda haka suke so.
Gata nan mara wayo wai ita barin gidan zatayi tunda sunce maigida na son ta ko yace yana son ki ba mace kike ba halan kuma sun san kifi su da komai wallahi.
Sai kibar gidan suji dadi su zuba ruwa a kasa su sha niko ki barni da bakin ciki ba shi ke nan ba tana fadin haka ta juya ta fita daga dakin ta barni nan tsaye na rasa abinda zanyi a lokacin.
Sai Gajiye tace Rahama kiyi hakkuri idan kin tafi ai dadi zasuji ki mayar da kanyanki ki maida komai ba komai sai bakin ciki ya kashe su kin dai ji abinda hajiya tace ai.
Indan kinyi haka baki kyauta mata ba kije ki samay ta ki bata hakkuri a wuce gurin don Allah nan na durkusa ina kuka wiwiwi raina kamar zai fita.
Nasir ne ya taso daga inda yake ya rugumay ni yana fadin anty yi shiru kinji kyale maman Husna sai na halbe ta da bindagana.
Najawo yaron a jiki Amira ma tazo tasa hannayen ta tana share min hawaye tana fadin nai shiru sai taba hanifa da husna kashi tunda maman su sun sani kuka.
Kuka nake sosai sai ga anty ta dawo dakin takawo min jinior daya damay ta da fitina tasan gurina yake son zuwa lokacin yadda yake mata.
Yadda ta gan mu sai muka bata tausayi yaron ta miko min tafice itama kukan takeyi a lokacin.
Haka na wuni cikin bacin rai yaran ko suna manne a jikina duk inda nake suna saman jikina.
Muna falo zaune nake saman one seater amma haka suma suka manne min ga jinior saman jikina mu hudu mun makure a guri daya anty na dakin ta cikin bacin rai.
Daddy ne ya shigo part din wanan katon ya sauya kayan jikin shi zuwa kananan kaya wando baki da yar rigar tieshirt ja an rubuta mai THE KING da ruwan zaiba a gaban rigan.
Idanuwan shi a kan mu ina saye cikin digon riga light blue mai dogon hannu sai hulla da na dora a saman kaina.
Yaran na ganin shi suka mike zuwa gare shi suna daddy Nasir ya rike shi yace daddy please dont live anty to go.
Ya shafa kan yaron yace to go where ?
Yaron yace she said she is living us soon.
Inda nake ya kalla yace kada ki ruda yaran ki Rahama inkin yi haka baki kyauta masu ba kin ga sun shiga damuwa sun ganki a cikin damuwa.
Daddy wai zaka auri anty inji mummy husna harda mummy mu inji Amira take tambayan uban nata.
Shafa kan ta yayi yace mummy husna bata da hankali karya takeyi jinior ke mika hannu uban ya dauke shi wai.
Ya karaso inda muke ya dauki yaron yana cewa big boy may ke damun ka haka kake wanan raman ina mummy tana ciki ko ya juya da yaron zuwa cikin daki inda anty take ya samay ta.
Ta na kwance ta dunkule a guri daya jin shigowan shi dakin yasata dago kan ta idanuwan ta da taci kuka ya rine yayi ja dashi.
Yace kema kukan kike yi kamar yaran ko may kina son jawa kanki matsala kuma ko bayan kin san ba lafiya ya ishi jikin ki ba.
Yanzu abinda Matanka sukai wa yarinyar nan don su fashe haushinna akan ta sun kyauta ke nan besty ?
Yace ai ba ita sukai wa kazafi ba ni sukai wa sheri ni maigidan da sukaiwa zatlrgin sheri amma zasu gane kuren su ai sun san halina.
Shiru sukayi sai can anty tace Besty may zai hana ka auri Rahama ne shi kadai zakayi min ka fashe min haushina idan sunyi ne don naji haushi sai ya koma masu .
Babu daya daga cikin su da zata taba zaton jaka zai iya faruwa tunda sunyi ne don sheri dama.
Kina da hankali kuwa Saade nine zakice na auri Rahama may zanyi da wata mace kuma kosu ba dai da rabon aure bane a tsakanina dasu da kuma takuran magabata.
Mata uku ma yaya na iya daku balle na kara dauko wa kaina magana shin kin ko san naiyin maganan da kikayi yanzu kuwa besty da wani ido kike son yarinyar na ta kalleni da kuma duniya.
Tace an so what ba aure bane kuma Allah ya halasta maku auren mata har hudu a rayuwan ku, kana kuma da karfin yin hakan ta ko ina idan ka so yin hakan.
Ban son jin wanan maganan please gashi har yara sun san abinda ake fadi yanzun nan su Amira suka tare ni da zancen a falo ina dadin haka please.
Ai sai ki kori yarinyar a gurin ki bayan kin san irin taimakon da take maki a rayuwan ki a gidan nan.
Tace ai don tai makon da take min ni da yaran nake son taci gaba da zama damu a cikin gidan nan ko ba komai ko bani nasan zata rike min diya na yadda ya dace ai.
Dan Allah ki rabani da wanan tunanen yaran naki ko kema kin haukace ne irin na sauran ban sani ba ban son na kara jin wanan magana daga bakin ki kuma please.
Yaron ya aje mata ya fita daga dakin a hasale komai jin shi yaka yai mai baki kunci ya mamaye mai zuciyar shi yana tunanen may zai yi ya bata wasu hindatu rai akan haka.
Hajiyan shi ke neman shi can ya nufa amsa kiran mahaifiyar tashi tafe yake a motan shi yanayi yana shafa sajen fuskan shi a hankali.
Tunanen maganan da sukayi da Anty yakeyi ran shi na kara mai kuna a lokacin harya kawo gidan mahaifan nashi.
A falo ya samu mahaifan nashi su duk suna tare sai Aisha da ya samu tazo gidan a lokacin ganin su nan suka gaisa ya samu guri ya zauna.
Ya fuskanci mahaufiyar tashi yana cewa hajiya gani kince kina nema dazun da rana bani gari yanzu na dawo shine na shirya nazo.
Hajiya batason magana a gaban mijinta ba amma kuma babu yadda zatayi dole tai maganan a ga ban su hakana.
Alhaji yaya akayi haka kuma yar aiki ta daki matan ka kuma baka dauki mataki ba a gidan wanan ai raini ne da wullakanci kajawa matan ka hakan ?
Yace yar aiki hajiya ?
Ba yar aiki take ba may take a gidan ina matarka ce ta dauko ta kalar dangi ta zauna da ita samun wuri kuma yasa har takai hannun ta ta daki matan ka kamar wata yar chaina da ita tai masu kaca kaca da jikin su.
Suma ai taron banza ne suka kasa taruwa suyi wa yar banza duka tsiya sai ta kasa motsi a gurin gobe ta kara gigin kai hannun ta duka wani kuma.
Hajiya Rahama ba yar aiki bace na fada maki haka ba yau ba kaunar saade ne ta dauko ta taimaka mata.
Duka kuma ita Zulfa ita ta fara dukan yarinyar ita kuma ta rama hindatu taji haushi ta yaga mata riga ta mareta itama ta rama hakan.
May zance in ba fadan karya zanyi ba tunda daurin hannu ke garesu daga magana sukai wa yar mutane duka don suna takama sun fita.
Dariya Aisha dake gefe tasa tace Rahama ta zama shago ke nan duk ta watsa su amna anyi kattan bamza wallahi.
Amma dai basu kysuta ba inji Abba dake sauraren su koni ne tunda su suka fara bazan ce komai ba ai.
Haba Alhaji ka bari ai mashi magana haka bai dace ba wallahi yaya zata doki matan gida su da gidan mijin su ina ruwan ta da fadan kishin su da zata saka bakin ta ciki.
Yace hajiya har ni Hindatu zata kalli idona tace wai ina tare da Rahama ta sani ba yau ba.
Ni zatai wa zargin sheri da kazafi irin haka don ta raina ni ko may saboda suna ganin suna iskanci son ran su ina kyalesu idan mace nake so kasa nawa nake zuwa ina ganin mata iri iri ban nema ba sai kaunan saade zan nema kuma.
Ni hajiya yaran nan sun kai min ko ina wallahi saboda ku fa nake zaune dasu haka na amma ba wani jin dadin zuciya da nake samu garesu.
Kai mata ho idan ma kana son ta aiba abin boyo bane ko tunda Allah bau haramta maka yin hakan ba sai ka auri abinka shike nan.
Mahaifin daddy ne ke fada mai hakan yace in har akwai alheri ga auren yarinyar kaje ka aure ta ni nace gobe su kara kazafi da kyau kuma.
Haba Alhaji wanan wani irin shawara zaka bashi haka kuma ana neman mafita ga yarinya tazi ta addabi mutane da gidan su.
Ko ni nan ta taba min rashin kunya saida na hada ta da yaruwar nata nai masu tas tashiga hankalinta.
Don haka bani son zaman yarinyar nan a gidan man kaje ka sallamay ta tabar masu gidan su takoma inda tafito kaji na fada maka.
Ni kuma nace babu inda zata kinji hukunci na wai may yasa ku mata baku da hankali ne komai girman ku ai idan ta tafi sai a dauka da gaske ne haka maganan yake son ta yakeyi din.
Ba, a aure mukasa su ya aure su baiso hakan ba a lokacin ban son maganan shirmay dama don wanan shiriritan ne kika kira shi yabar abinda ke gaban shi yazo nan.
Ni mahaufin ka na baka baki jeka auri yarinyar in har haka shine mafita a gareka suje su mutu yaran banza kawai da basu san arziki ba tashi kafita na sallamay ka.
Aiko da ka auri yarinyar nan yayana daka more rayuwan ka tun da matan ka kaf babu mai zatin ta a gidan ka kishin haka ne yasa suke zargin ka kawai.
Gata da tsabta ga kirki ga girmama na gaba wallahi yarinyar tayi hundred percent ni dai a gurina matsala dai Saade da zataga an mata cin fuska kawai.
Babu cin fuska gareta don itama haka take so a ranta ban dai amince bane kawai.
Idan kana so kawai kayi abinka yayana samay ke dallah rufewa mutane baki mara hankali ba za, ayi ba nace nikuma nace yaje yayi idan yana son hakan sai may.
Yai masu sallama yabarsu nan suna zabga muhawara akan maganan hajiya duk ranta a bace yake kan maganan mijinta yaki bari taiwa danta fada yadda take so.
Yana tafe tuki yake amma yana tuna maganan shi da iyayyen shi yadda ta kaya masu lalai namiji namijine.
Yanzu har Abba ya yanke hukunci a kan shi kai tsaye shi bai dauki yin haka ba wani matsala a gurin shi.
Batare da laakari da laakarin abinda matsalan zai jawo ba ga iyalin shi da kuma kusancin dake tsakanin saade da yarinyar ba don ya zama matsayin cin amana ga saaden ke nan yayi.
Duk da hakan ba komai bane idan yai niyyan yi amma ba zai iyawa Saade haka ba koda yana son yarinyar ne kuwa amma a wajen wasu mazan hakan ba komai bane ai.
Amma hakan da kowa ke bani shawara shine zanyi na rama bakin cikin da yaran nan sukai min kai tsaye da zina suke nufin ina neman ta nikuma sai na aurota na jefa cikin su badon saade ba ko da kuwa yar aikine yarinyar amma Saade tai min katanga ga hakan da sun sha mamakina wallahi ko.
Haka yake tafe a cikin damuwa yakasa samun natsuwa zuciyar shi zafi take mashi da radadin wanan masifa daya wayi gari dashi yau din.
Haka ya nufi gurin bashir da bacin rai yana ganin shi ya fahinci bai cikin dadin rai ga yanayin shi yake cewa may kuma akayi ne wai nagan ka wani iri dakai.
Fitowa yayi daga motar batare da ya bashi amsa ba ya jingina bayan shi ga motan tare da harde hanayen shi guri daya.
Bashir yace mai mata biyu ance baida natsuwa kaiko mai mata uku yaya dai sunyi halin nasu ke nan ko ?
Yace bari kawai bashir suna son su haukatani nida gida sun azamin tention kaina ya dau zafi wallahi sosai.
Ka duba fa wai ni Hindatu zatace ina tare da sister din Saade don wullakanci da rainin wayo ?
Kai haba garin yaya kuma wanan maganan yazo mata haka ita kuma hindatun ?
Yace garin iskanci da rainin wayo mana saboda samun wuri nan yake fada mai yadda abin yafaru da yadda sukayi da saade a kaina.
Aikin banza to kai may zaka tsaya jira tunda har Saade da Abba sun baka go ahead kan maganan ba sai ka amfaka ba ka gwada masu ka isa kai keda gidan ka.
Yace haba Bashir kada ka zama dan akuya mana yarinya tana kirana daddy kasa daddy sama nace kuma zan aureta ai da na zama dan kuya dai.
Nasan dai bakin cikin da zan masu ai nayi niyar canza masu mota dukkan su na fasa ita zan sayawa a satin nan kuma nace a koya mata suje su mutu da bakin ciki bashi ke nan ba.
To may kayi idan kai wanan kawai kada ka tsaya kallon ruwa kwado yariga fadawa ruwan idan zaka nuna mazan taka kanuna masu kawai shine mafita.
Tsaki yaja ya fada motan shi yana cewa sai kajini ni zan koma gida komai ma bakin shi nake gani wallahi.
Ya wuce Bashir na mashi sheri mai mata uku ba abinka sallah kada kaja muna ayan mata.
Bai zo gida direct ba sai da ya tsaya shagon sai da waya ya sowo dalleliyar waya mai kyau da tsada ya nufi gida dashi.
Muna falo har anty bayan sallah ishai yashigo falon nan yazauna tare da mika mata wayan yace ki bawa yar ki shi sai na kunsa masu bakin cikin da suka jefani.
Takarbi wayan tana yaba kyawon shi tace Rama kin fa faso gari gori da sheri yaja maki alheri gashi inji daddy ku yasaya maki.
Na dago kai da mamaki ina cewa ni anty tace ke ma dawa baa gaban ki ya bayar ba na karba tare da zuwa inda yake zaune na tsugunna ina cewa daddy nagode Allah ya kara rufa asiri yace amin tare da mikewa tsaye.
Sai da ya soma tafiya ya juyo yana cewa ki koya mata mota nan da sati motar ta zai zo sai na dasa masu abinda suka dasa min su ma.
Yafice daga dakin dariya anty tayi bayan tabi bayan shi da kallon tausayi tasan yau mutumin nata yadau zafi sosai dama haka yake inda wani yai mai bakin ciki sai ya rama ta ruwan sanyi.
Tace Rama aiki kazafi yaja maki alheri insha Allahu akan su zai kare bude wayan mugani kin ji.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA HAKKIN AMANA YANA KANKI DON ALLAH NAGANIN KI YAR UWA, , ,

27
Hamza driver anty tasa yake koya min mota gani da kan dauka kafin wani lokaci har na iya tuki yakan bani na jawo mu dawo wa gida idan mun gama.
Wani lokaci kuma yasa na zagaya cikin gari yana gefe yana kallon yadda nake driving din har ya tabbatar da na iya tukin motan a lokacin.
Don anty ta tabbatar kayan store din mu da muka kwashe ta bani na kaiwa mama laraba da su yan uguwan su abin azumi naje na dawo tare da Farida data biyo mu tace a gurin mu zatai azumin ta.
Ganin naje lafiya na dawo anty taji dadin hakan sosai takira mijin ta ta sheda mashi iya motana yace yayi kyau sai taji shi.
Su ko suna zauneba haraban gidan su fitar da fararen kujerun roba wai suna hira sukaga dawo na cikin motar anty.
Hindatu tace yaushe wanan somayen ta fita gidan nan ne ?
Zulfa tace ban ma lura motarta baya gurin ba sai yanzu ko ina taje yau kullun kule a gida
Showing 102001 words to 105000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35 Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153