su da sinan diyan su take kiran su dashi sabanin su dake kiranta da sa,ade kai tsaye haka.
Guri anty ta samu ta zauna a kusa da ita tashiga bata magana tana bata hakkuri tace da anty nagode maman Nasir.
Yaune rana na farko da ta kirata da hakan anty tace ki dinga kai kukan gi Ubangiji don shi daya baki kuma ya karbeta a inda akeson ta yafi sanin hikiman yin haka dayayi.
Idan kin dage da addua dakai kukan ki garshi sai ya baki abinda ma baki zata ba daga garshi ki dage da yawaita karanta Innalillahi waina alaihin rajiu, Allahuma ajirni fi masibati wa, akalif, lil hairan min ha, , ,
Sai kiga Allah yai maki sakayya da mafi alherin sa amma wanan kukan dakike bashi ne mafita ba a gareki don zaki iya jawa kanki wani ciwo kuma again.
Bafa ke kadai ba mutuwan yarinyar nan ya shafa ba kowan mu yataba wallahi Rahma sai da na tashi tsaye sosai akanta take cin abu yanzu don ta saka abin a ranta sosai wallahi.
Zulfa tai murmushi tace dole ne maman Nasir don ba karamin shakuwa ne a tsakanin su ba ban kara gaskantawa ba saida naga yarinyar nan tai kundunbala kan Hanifa ta fada ruwan nan don ceto ranta amma kuma Allah bai bar muna ita ba wallahi.
Har taji sauki cikin dare saiga ciwo yataso kamar conbultion tana fisge fisge shine bai sake taba har ta tafi da shi.
Anty ta sauke ajiyan zuciya tace Allah yai mata rahama yasa ta huta tamike tanace kiyi hakkuri ki fitar da damuwa a ranki kibita da addua shine tafi bukata yanzu a garemu.
Tana fita Zulfa ta sauke ajiyan zuciya tare da lumshe idanuwan ta a hankali tace rayuwa ke nan koba komai dai yau Saade tai min rana don duk abinda ta fada min yanzu gaskiya ne.
Ita Hondatu ma na fahinci kamar dadi abin yai mata babu wani damuwa akan mutuwan yarinyar nan a kanta ji yadda take magana a falo don kawai ni da ban da kowa yanzu a gidan maji haushi.
Yanzu ai nasan zamana da ita a gidan nan dama can dai ai ba wai wani son tsakani da Allah muke wa juna mu ba don kawai mu hade kaine muci karfin Saade kwai yanzu ko tunda babu mutunci ta iya min haka ai kowa ya kama kan shi kuma.
Tun wanan ranan gaiyyan hadin kai a tsakanin su ya watse ba ruwan wata da wata agidan kowa tashi ta fitar dashi kawai sai zaman ma yafi dadi a haka don an rage yawan tsegumi da gulman anyi an ce.

********* *********
*********

Mun shirya kamar yadda anty ta bukaci na shirya na rakata unguwa ni da Farida sai yaran da muka fita dasu ranan Gajiye kawai muka bari a gida.
Wani katon shago takaimu kayane na redmaid na kasan waje nan muka zabawa yaran kaya masu kyau kala biyar biyar sai ni da Farida dake da kala hudu hudu nan itama ta zaba masu kyau da tsada nata takalma handbag da sauran kayayyaki haka muka dawo gida a gajiye .
Ban zauna ba tare muka karasa aikin girki da Gajiye sai baya mun idar da sallah mun sha ruwa aka baje kayan da aka sayo muna kallo.
Na kwashe na anty na kai mata dakin ta na samayta a kwance tace tagaji bata jin dadi don azumi ma ba kullun takeyi ba don yanayin jikin nata.
Nace bayan na gaida ita, ga kayan ki nan na shigo dasu tace Rama don ki fa na sayo su saboda ba zan iya saya maki su ba a gaban Farida .
Don bai yuyuwa na saya maku komai iri daya da ita tunda ba wai wani abu take muna ba banda hira da kwanciya.
Nace a sanyayye ma gode Anty Allah ya kara rufa asiri tace amin zaki iya ki barsu a nan sai idan ta tafi ki fitar da abinki.
Sallah saura kwana biyu mun samu hutu ta kwashe mu zuwa gyaran kai da jiki a saloon din da take zuwa gyara wanda ko ni daya yanzu tana turawa can.
Ba karamin gyara akai muna ba mun dawo muka samu an kawo muna dinkunan da ta bayar ai muna nan kan ta fitar da banbanci a fili don nawa sunfi na Farida sosai.
Take naga Faridan ta hade rai naji anty na fadin kai tella dai ho dinkin nan kusa wata uku fa a hannun shi sai yanzu ya hado da wanda na bashi na sallah yai maku.
Sai dataji haka ta dan sake ranta nace kai dan adam ho gashi ita ba, a more mata sai aukin hira da barci idan kuma za, a sha ruwa itace ta farko gurin fitowa aci abinci bata jin nauyi da kunyan hakan.
Ranan Sallah tun safe muke aikin girki a lokacin har Farida tai wanka ta shirya cikin daya daga cikin atamfan da aka dinka muna.
Ban samu kaina ba nida GaJiye sai zuwa shadaya saura na rana don anty ce mai girkin sallah din.
Wanka mukayi bayan mun kara tsabtace falo da dakunan gidan muna atamfa muka saka dogon riga ne wanda akaiwa dinkin manyan hannuwa mai dagwari biyu daga hip din rigan ya kamani sosai kasn shi ya wani bajewa sosai ina tafiya yana bajewa a kasa.
Kicibis mukayi da daddy dake shigowa part din wanda ina ganin dawowan su ke nan a gidan tun fitan su zuwa sallah.
Yana saye da manyan kaya a jikin shi farare kal dasu da hullan shi da ya dace da aikin da akaiwa kayan dake jikin shi.
Kayan sun matukar karban jikin shi sosai yadine mai matukar tsada sajen fuskanshi ya kwanta qa fuskan shi lun lub ya kara mai kyau da kwarjini sosai.
Gefe na dan rakube ina cewa sannu da dawowa daddy barka da sallah ?
Yace an sha ruwa lafiya Allah ya maimaita muna nan naji gajiye tana gaida shi kamar yadda na gaida shi.
Ya saka hannu a aljihun shi ya ciro bandir din yan dubu daya daya ya kirga ya fara mikawa Gajiye ya tana godiya ya kirgo ya miko min na rusunna nakarba ina godiya.
Saiga Farida itama tana gaida shi itama ya bata nata ta karba tana kallon hannuwana.
Ya shige dakin anty yajima sai gashi yafito yanayin shi ya sauya ga yadda ya shiga dakin don gajiye na mashi a huta lafiya bai amsa mata ba yafita da zafin rai.
Kusan hakan ne ke faruwa dasu yanzu ba kamar yadda suke ba a baya a tsakanin su da zai fito da fara,a.
Lokacin ina cirewa nasir fararen kayan dake jikin shi zaici abinci don nayi mai mutumin shi watau masa da miya yaji kayan hadi yayi laudi sosai.
Saida yaron ya fara cin abinci ina gyara mai zama naji anty na kwala min kira da sauri na mike zuwa amsa kiran nata.
Zaune take ta caba kwaliya nagani na fada takecewa dani don Allah ku fara fita da abinci falon daddy yanzu.
Nace gaba daya zamu kai tace kukai duk abinda kuka shirya mai ba tsaya ma munyi magana ba ya fice yana fushi daga maganan gaskiya kawai.
Nake cewa anty don Allah kibar batawa daddy rai tunda shima baya son a bata maki tace barni dashi kawai Rama baison maganan gaskiya ne shi.
Naiwa jinior daya falka daga barci wasa yana washe baki yana min dariya nace bari na je na dawo na dauke ka kaji.
Tace zai je gaida daddy ne shima nace cikin washe baki anty yanzun daddy ya bamu barka da sallah a falo ni dasu Gajiye da Farida.
Tace ya riga ni baku ke nan don yanzu nake da niyar ba kowan ku dama nace to anty bari mu dawo sai kibamu naki ke nan.
Mun kwashi kayan sai falon maigidan a can muka samu hindatu tare dashi itama ta caba kwalliya ba laifi tayi kyau sosai.
Wasu abokan harkan shi ne yan chaina su biyu tare da wasu masu zubin iyamurai suka shigo falon cikin raha da dariya.
Anty na bayan mu nan suka fara gaisawa da bakin da alaman ta san su dama ga yadda take gaisawa dasu din cikin sanayya.
Mun kara shigowa da wasu kayan abincin a lokacin duk sina zaune har Zulfa ma ta shigo gaida bakin nasu da sukazo masu yawon sallah.
Wanda naji sun kira da mr Benjamen daga cikin bakaken fatan ke cewa woow kubani wanan beautiful sister din mana naku hajiya.
Sai aka kwashe da dariya ban da su Hindatu a gurin yace I realy mean it gaskiya idan zaku bani ita ina so don na huta da gorin ku hakana naki aure har yanzu.
Raina na hade a lokacin don jin haushin kafiri wai ni yake so haka sai anty ce ke cewa ai ba addinin ka daya da ita ba.
Kaga babu aure tsakanin ka da ita yace ba matsala ai in har tana sona zan barta tayi addinin ta nima nayi nawa ba shi ke nan ba.
Bamu hakan mu ga addinin mu indai kai mace ne ita namiji zaka iya aurenta .
Yace kai addinin ku fa akwai hikima a cikin sa sosai watau shi na miji a wani addini baida dama ya auri wata mace na daban daga cikin addinin ku ko ?
Anty tace hakane Mr Benjemen yace gaskiya I love the girl wallahi kuyi hakkuri ku bani ita mana please.
Daddy ne ya katse su ta hanya cewa su fara cin abincin da aka jera masu ko don su samu su tattauna abinda ya kawo su yi.
Nikan zamu fita don mun gama abinda mu keyi mutumin ke cewa damu muzo mu karbi goron sallah mu.
Farida ce ta karasa nikan kallon mai kama dana tsana da daddy ya jefoni dashi sau daya yasa duk na rikice a gurin .
Nafara hanyan fita naji mutumin nacewa beauty zomana ki karba please kada kiyi min rowan wanan beautyfubeautiful face din naki please.
Juyawa kawai nayi na bar falo do ba zan iya jure irin kallon tsanan da ake min ba haka na ga shi ya hade rai kamar bai taba murmushi ba balle dariya a duniya.
Farida ce tazi min da kudi masu yawa wai mutumin yace a bani goron sallah na kuma yace wai abashi nomban waya na amma daddy ya koro ta gurin.
Anty dake kusa dashi zaune ta shake murya tana cewa dashi yadda shi kadai zai iyajin abinda take fadi.
Malam idan kai baka so ka bari masu so su taya mana wanan hade rai na may ye haka kuma ?
Wani kallo ya watso mata tare da tsuki yana cewa baki da hankali nake gani yanzu sai nakaiki an auna ki gaskiya.
Suko sauran matan sun zaci wani zancen soyayya suke a lokacin take kowan su ta hade ran ta tasha toka fuska ba fara, a zulfa ta fara cewa ita zata tafi ke nan su huta lafiya.
Hindatu ma tamike tana masu sallama anty ce tare da mutanen dama ita sukafi sani don shi benjemen abokin karatun su ne tun a makaranta suke tare da daddy din da ita.
Bata jima ba tai masu sallama tafito inda sauran suka bata alheri mai yawa wai su raba gaba dayan su har mu.
Ta dawo da kudin a hannun ta nan ta zauna falo tana magana taga ban cikin dadin rai take tambayan may kuma ya faru dani haka ne ?
Cikin bata rai nake cewa haba anty kafiri zaice yana sona don ya raina min hankali dariya farida ke min tace kinga sai muje church musha rawa ke nan.
Maka nakai mata a baya daga inda nake take cewa daga fadin gaskiya yaga abinda keyi mai ne mana ke wani namiji zaiganki haka bai rola maki ba.
Muna zaune anty ke cewa dani raba kudin nan daidai har ku da wa yan can akai masu nasu kisaka Gajiye datasha aiki a cikin rabon ita ma .
Sai gashi kowa ya tashi da kusan ashirin ashirin su anty da abokan zama ta na cirewa ashirin ashirin sauran har nacire muna na kuma cirewa sauran yan aikin su hindatu dubu biyar biyar a ciki.
Nai mata bayanin yadda na kasa tace kin kyauta haka ake so suma ai su lasa ko ?
Tace Farida takai masu nasu har yan aikin nasu abasu nasu don ni bata son ta turani gurin su inba dole ba.
Farida nakai kudin tamikawa kowa har yan aikin sai Hindatu tace da ita may nene wanan ana nufin iya kudin da suka bamu ke nan ko may wai ?
Farida tacd shi nagani nima don a gabana aka raba tace na kawo wa kowa nashi nakine wanan.
Tace ke may kika sani koma kinbsani ne aiba zaki fadi ba don kan ku daya kwadai ya rufe maku ido kamar wata tsiya ake kulla maku banda aikin wahala da kuke mata.
Fita tayi ta barta tana bakaken magana a falon ta ta dawo ta fadawa anty abinda tace da ita da takai masu.
Anty wanan irin abin nake gudu wallahi duk yadda kayi baka fita a gurin su na boye na gane may wai ?
Run gumay nake da Nasir da yai barci a jikina idona akan tv dake aiki ana wasan barka da sallah yara nata mika gaisuwan su ga yan uwa da abokan arziki sai ga daddy ya shigo falon nan muka shiga gaidashi yana amsa muna cikin basarwa.
Guri ya samu ya zauna a falon tare da cewa shi wanan baya barci sai a saman jikine ?
Anty tace haka ta saba masu dashi wallahi ai akwai aki randa Rama ta bar gidan nan ga yaran nan .
Yace yanzu wanan ta samay ni wai kudin da su John suka baku ba a raba daidai ba yaya akayine wai ?
Salati anty ta saka tacd kai wanan abin wai damay yai kamane tace Allah yasa gasu a zaune kai maganan nan fada mai Rama yadda kika raba kudin.
Nafara koro mai yadda nai kasafi tace to kaji don ni ita namikawa nace tafitar da na kowa har masu aikin su sai da Rama ta fitarwa da nasu amma kuma suce wai hakan baiyi ba.
Yace nasan ai bazakiyi abinda bai dace ba akai zargine kawai irin nasu takeyi ina laifi anba kowa yasamu.
Anty tace ni idan bai mata ba sai na hada da nawa duk ta rike bashi ke nan ba.
Yamike yana cewa akan may zaki bata nata wata fi idan bata so ba sai ta dawo maki dashi ba dama ai ba donta aka bayar ba don wa yanda sukai aiki ne suka ba da.
Ya fara tafiya yake cewa ke je shimfede yaron nan hakana ya kwanta ku daina bata shi dayawa ace yaro bai barci sai a jiki zaiyi barci kamar wanan.
Na daga yaron tare da jan kafana da duk yai sanyi na fice rugumay da yaron a kafada na zuwa dakin mu.
Ya juya gurin anty yana cewa kema ki dinga mata fada ta daina shagwabasu haka mana abin yai yawa wallahi.
Rama da yaran nan ne sai Allah nagaji na sa mata ido dasu kagan su na yanzu basu iya zama sai a saman jikin ta sun riga ta saba masu da hakan ko .
Nima dana shiga shirin kwanciya na fara yi bayan na shimfide yaron sai dai nasan ko na kwanta a lokacin dole na fito don rufe guri saboda anty a gurin maigida zata kwana ranan.
Ban jima da kwanciya ba naji muryan anty tana cewa dani har kin kwanta ne haka da wuri Rama ?
Ko fadan da daddy ku yayi na yaran kike wa fushi kuma ai gaskiya ya fada girma fa yaran keyi ke ko kina dada shagwabasu haka.
Zama tayi a bakin gadon da nake kwance tana fuskantana sai duk nabi na tsargu da kallon da take min a lokacin .
Tace yafara takurawa rayuwan ki ko a gidan nan da sauri nace wa anty ina mikewa zaune daga kwancen da nake tace dani daddy ku mana .
Kallon mamaki nai mata nai wani tsuru tsuru dani nace a hankali cikin karfin hali anty daddy ne zai matsa min kuma ?
Dake dashi anty ai a karkashin ku nake don may bazan gode maku ba balle ni anty wani matsi daddy ke min a gidan nan mutumin da zan share kwanaki ban gani ba idan ba ya shigo nan wani sain na gan shi ba.
Ni idan bakuyi min fada anty ai abin bakyau kuma duk yadda kuka zartan dani ai a karkashin ku nake kuma ni wallahi ma banji yai fada ba a kan yaran nan.
Tace na dauka shine kika shigewa daki ai kina fushi don maganan da yayi din ?
Nai murmushi nace kai anty wai fushi kuma kin san yau tun hudu idon mu biyu nagajine kawai shiyasa na dawo na kwanta ni da mutumina kada ya falka yaji bana kusa dashi.
Ta mike tsaye tana fadi ai na sani tace nidai tasi kafin jaririn naki ya falka din Allah ki shirya min yarona mu tafi ki rufe kofa.
Tare muka fito daga dakin da ita zuwa dakin ta ina gana sakawa yaron over roll take cewa dani ta fito daga bandaki ke nan.
Showing 111001 words to 114000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38 Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153