ku kama kanku don Allah lokaci yayi da zaku dage wurin mai da kan ku abin kwarai don mahaifin mu yai alfahari da haihuwan mu.
Sai naga Suwaiba na kuka tace Rahama laila ke mutum ce dake da mahaifiyar ki duk irin abinda mukai maku a baya baku taba rike mu dashi ba.
Haka ma wanda mahaifiyar mu ke maki baku taba kallon mu dashi ba balle ku rike mu da hakan a ranku.
Don Allah Rahama ki yafe muna duk abinda mukai maki da wanda kika sani dama wanda baki sani ba.
Nace Anty don Allah kibar wanan magana don ni ban taba rike dayan ku da wani abu a raina ba ni dai fatana naga mun rike zumuncin mu da Allah ya kulla a tsakanin mu.
Nan dai mukai ta magana nai masu bayani kan gyaran gidan da maigidana yace aiwa baba idan nazo sukai murna sosai suna cewa.
Ai wanan abin Rahama ba baba akaiwa ba mu akaiwa don mu zamuyi alfahari da hakan a gari.
Ban bar gidan ba sai da na dan masu nasiha na zaman lafiya a fakaice sukai min godiya muka barta.
Gidan Rukkaiya muka tafi naga dakin ta tabani matukar tausayi nasan auren take son zama shiyasa harta daure cikin irin wanan rayuwan haka.
Bayan na dawo gida na samu mutane da dama sunzo gaida ni, wanka nayi don nagaji sosai bayan maigari ya dawo cikin gida taro ya watse a fadan shi ya zauna dani muna hira.
Har cikin raina naji dafin hakan sai nake ji dama ace shine mahaifina, ban boye mashi komai ba na halin rayuwan da muke ciki da kowa a gidan don ina jin shi tankar shi ya haife ni.
A rin yadda ya daukeni a matsayin diyarshi tankar wacce ya haifa yace dani na kara kwantar da hankalina su dai basuyi wa mutum sheri amma duk abinda mutum ya debo akan dan su zai koma a kan shi in hairan in sheran.
Nai mashi bayani kan gyaran gidan da nake so aiwa mahaifina yayi murna kwarai kamar shi akaiwa alheri haka.
Nace ina son asama min wanda zaiyi aikin muyi magana dashi inji yadda aikin zai kaya.
Ba bata lokaci ya aika akira mai Ado magini yazo yana neman shi maza maza.
Ba, a jima ba muna wurin zaune da shi sai ga Ado maginin yazo yai sallama bayan ya dan fita sun gana ya aiko a kirani nai bayanin yadda nake son ginan ya kasance.
Yace nan zuwa safe insha Allahu zaizo min da list din komai aji yadda za, ayi ginan.
Sai bayan sallah isha,i ne muka shirya Fatima ta rakani gidan mu don inga mahaifina.
Mun shiga gidan da gani ba zaman lafiya ko kadan na wuce gaida mama da kyat ta amsa min gaisuwan da nai mata.
Na wuce inda babana yake zaune saman shimfida, muka gaisa dashi yana murna da farin cikin ganina yace ai harda nace idan baki shigo ba da daren nan sai na shiga da safe na ganki can wurin uwar taki.
Nace baba ai na fadawa mama amarya cewa zan dawo da dare yaji dadin har cikin ran shi jin nakira matarshi abin son shi da mama.
Yace ai na dawo Lanto taks gwada min irin alherin da kika zo kikai masu bayan wanda kika aiko dashi jiya kuma ?
Nace ba komai baba ai uwaye na naiwa ba wasu ba, nan na fada mai yadda daddy yace ayi da gidan .
Yace anya Rahama bamu takurawa mutumin nan ba da bani bani ga irin taimakon da yai min kuma yanzu a ce yayi haka akan mu.
Nace baba ni wallahi ban taba rokon shi akan yai man wani abuba ko wani nawa ganin daman shi ne da ganin dacewan hakan dai yasa yakeyi.
Baba shifa daddy haka rayuwan shi yake don akwai shi da tausayin na kasa gareshi sosai.
Yace to Allah ya saka mai da alheri abinda yake nema na Alheri Allah ya bashi duniya da lahira mukace amin .
Sai ga amaryan baba tafito da abinci daga daki tana fafin har ina batun na aika maki dashi can su Jabir ne basu shigo ba ai.
Tuwon masara ne da miyar busassan kubewa sai kamahin kayan yaji yakeyi munaci muna hiran rayuwa da mahaifina yana fada min irin alherin da ya samu ga taimakon da daddy yai mashi.
Daga can naji mama na fadin an dai ji kunya wallahi babu kunya a fake ga maula a gurin suruki don kwadayi kawai.
Lauratu ki kama min bakin ki in ba haka ba kin san halina yanzu ranki zai baci a gidan nan.
Yo bakin ciki kikeyi don Allah ya mayar da yar da bakiso ganin da digon farin ciki ba a rayuwan ta haka ?
Kin sana rabu da iyalina masu so na da zuciya daya don mugun halinki don baki da kunya shine yanzu har zaki wagale baki kina fadin magana son ran ki idan fitsari banza ne kaza tayi mugani.
Banda marasa tarbiya da rashin mutunci da kika tara min a gida suna jawo min magana da abin kunya a gida dagari may kika tsinana min.
Sai naji amarya ta cabe da cewa ai dama duk wanda yace ruwan wani bai tafasa shiko nashi ai ko dumi baiyi haka abin yake.
Nace don Allah dai kuyi hakkuri kubar wanan zancen don Allah yanzu girma yazo ya kamata ku daina hakan.
Haka dazun kuka tara mutane a kofan gidan nan abin ba dadin gani don Allah don Allah na roke ku ku daina yin haka a rayuwan ku.
Daga kofan ta da take zaune tace ke kama kanki ke har yaushe kike da zaki wani tsaya wai kina muna nasiha inda bamu san asalin kolo bane da sai yace muna daga masar yake.
Baba yace Rahama kyale wanan mara mutunci don shedan ya auri zuciyar ta ba yau ba na kusa yadda kwallon magwaro na huta da biyan kuda.
Baba kayi hakkuri ka daina biyewa irin wanan maganganun na mata don ba girman ku bane hakan.
Ke kama min bakin ki ke har yaushe kika gama da naki matsalan don kin iya cin amana daga taimako kuka san asirin da kukaiwa mata kika aure mata mijin ta wallahu tir da halin yan cin amana irin ku a duniya.
Shiru nayi sai babane yace kaiyya ace halin mutim jarin sa ke kina ganin abinda kikeyi ko shi kowa keyi ne a duniya wai.
Don ba yarki bace ai da yarki ce ko ni mahaifinta baki bari taiwa alheri balle har makwabta su ma su samu.
Ganin nayi shiru ne yasa baba ya fahinci raina ya baci don haka shima sai yaja bakin shi yai shiru.
Mun dan zauna jugun sai nake cewa baba dare ya soma zamu tafi gida don akwai duhu yau a garin yace hakane Rahama Allah yai maki albarka ya tsare muna ku daga duk wani abin ki a duniya.
Nace amin baba mun gode namike mun tsayar da magana dashi da safe za, azo a samay shi ya nuna yadda yake son tsarin.
Nai masu saida safe sai ga yaran amarya sun shigo gidan tace yauwa hajiya ga yaran nan kin gasu tace kuyiwa anty ku godiya ko .
Nace au sune nan sannu ku ko kuna lafiya na dan shafa kanun su suka rusunna suna gaidani.
Uwar tace ai gobe in Allah ya kaimu zasu shigo su gaida ke can gidan.
Mukai masu sallama na fito inajin mama na fadin munafuncin banza da wofi kawai mutum bai iya da gidan shi ba yace zaizo gyaran gidan wasu ai duk zaman da mutum keyi a can muna da labarin shi a nan.
Ban da boyi boyi may aka gane a can din anzo za, a cimu da burgan aiki wai anga yan kauye ko ?
Naje gida ina fadawa innata yadda mukayi tace Allah ya kyauta ai ta riga tai nisa batajin kira tana fadin hakane don ta hanaki aikin ki na alheri ga mutane kin san shu,uma ce ta gaske ai.
Washe gari ma bayan mun tashi ina da gurin zuwa wuni gidan kakan nina daga can na biya gidan mama altine don ban sha, awan shiga gidan namu ko kadan.
Ado magini yazo muka fito ni da maigari ya fada muna nawa za, a kashe nai mamaki kwarai nace garin dadi na kauye gaskiya komai nasu da albarka yake. By
Na shiga na kawo mai kudi yace a ranan zasu fara saka foundation din gina nagani idan yayi kyau.
Sun tafi sun samu baba ya shiga dasu ciki don a auna yadda ginan zai kasance sai mama ke cewa ita kada a taba mata dakin ta abarta da abinta hakana.
Baba yace baki isa ba tunda ba gidan ki bane kuma bada kudin ki na gina abina ba dashi kika ganni kika shigo yadda nake so haka za, ai min.
Sai da takai har baba ya shiga ya linkida mata duka da farar safiya sannan ta natsu.
Aiki ya fara gadan gadan tanaji tana gani ga kuma jiki yai mata tsami ga banza.
Gidan kakanin na na nufa bayan yaran amarya sunzo mun gaisa suka tafi muka kama hanya.
Muna shiga Attu ke cewa dani tayi fushi sai da nagama ganin iyayyena da yan uwana nazo ganin su .
Nai dariya nace haba Attu ke fa ta daban ce bari nayi nazo mu sha hira a tsanake daku.
Nace ina tsohon mijin ki tace mijin ki yafishi yarinta ne balle ki kira min miji da tsoho.
Nan muka zauna aka shiga hiran yaushe rabo a tsakanin mu daga ni sai Atika mukazo don Fatima tana can ta shiga gurin yan uwan mahaifiyar ta.
Hira sosai mukayi da Attu take tambayana yaya baiwar Allah nan mai mutunci da karamci yaya jikin nata kuma ?
Nan dai na fada mata komai don wanda baici ka boyewa magana ba najikin ka dole ka fada mai wani abin.
Tace ki dai daure aita hakkuri ai tayi kokari wallahi ko a zamanin da can baya da wuya a samu macen da zata sadaukar da rayuwanta da komai nata ta zabawa mijin ta macen da zai zauna da ita don samun farin cikin shi tana kallo.
Da ace mata zamu kawar da kishi a rayuwan mu muna sadaukar da ran mu ga abinda zai amfane ne mu duniya da lahira da babu sauran macen da zata shiga wuta a lahira.
Gsshi kuma mutunci da kimarta zai karu sosai a gurin miji don dole nauyi da kunyanta ya hanashi wani abin koda yayi niyar yin hakan idan ya tuna da kawaicin da akai mashi shima.
Nace Attu Allah dai ya gyara amma ai maza yanzu ba sanin hakan sukeyi ba don suma yanzu mazan ne sai a hankali dole sai mace ta kai ranta nisa akan su.
Nace waiko Attu mai zogala na nan kuwa tace tana nan wallahi nace bari dai yau na shiga na leko ta.
Na hada tsaraba sai gidan makwabciyar Attu duk da suna da dan jayawa kadan tsakanin su da su Attu din.
Da sallaman mu tana ganin mu tace ikon Allah wa nake gani haka yau a gidan nan ko dai ido na ke min gizau ne wai.
Sai naga kamar Rahaman Attu nake gani a gidan nan nace cikin dariya nice din dai Nana mai zogala tace wallahi kama kawai na kurciyan ki ne nagani nai amfani dashi.
Tabarma ta shimfida muna muka zauna nan muka shiga gaisawa tana ta murna da jin dadin ganin mu.
Tace yaya kuke na dawo wani lokaci nake tambaya najiki shiru ake cewa wai ai kina birni kin yi aure a can.
Tace ke kadai ne ko kina da abokan zama ne nai dariya nace Nana abokan zama har uku nice ta hudu Nana.
Tace wai, tau Allah ya kyauta sai a hada aita hakkuri nace in sha Allahu Nana na mika mata ledan da muka shigo dashi ta karba tana cewa zan baki wani shawara.
Na gyara ina sauraren ta sai ta dakata ta na bude ledan da na bata take cewa ikon Allah harda tsaraba na samu haka Rahama wanan ya da alheri kike tun kina karamar ki.
Taita godiya can ta gyara zama tace kada ki yarda ki sabawa ubangijin ki akan dan wanan rayuwan da bai kai ko cikon cokali ba .
Kedai ki saka Allah a gaban komai sai kiga da farko za, a fara gwajin Imanin ki da abubuwa da dama.
Sai kin saka imani a ranki sai kiga da sannu ubangiji na walwale maki al,amuranki sannu a hankali.
Kin san Assma,ullahil, husna idan da zaki tsaya ki fake a garesu sai kiga da sannu ubangiji na maki falala a rayuwan auren ki.
Zaki iya karanta Ya Allahu yahu, 1000 zaki kuma iya nafila raka, a biyu, sai salatin Annabi da hailala saiki karabta Allahu yahu, kafa 66 shima wannan anayin sa don neman bukata a gurin Allah.
Ya Azeez minazeen 41 bayan duk sallah farillah na asubahi har tsawon kwana 40 akwai fa,ida sosai a cikin wanan kalman.
Idan kuma kina da matsala da mijin ki ko kishiya ta sakaki gaba zaki iya yin wanan zikirin Al Khaaliq kafa 5000 insha Allahu zaki sha mamaki sosai ga matsalarki.
Don samun tsari ga duk wani sheri ko kaidin da za, ai maki zaki iya karanta Al Mutakabbir sau goma safe da yamma.
Zaki kuma iya karanta subbahanallahi walhamdullahi Allahu Akbar ko yaushe ba adadi don samun farin cikin zama da mijin ki.
Naji wani irin dadi sosai ta kuma fara jero min irin hikimomin zama tsakanin kishiyoyi irin dubarun su na baya naji dadi sosai shiga na wurin Nana mai zogala don na karu sosai da ita.
Nai mata sallama na dawo gidan Attu ban bar gidan ba sai da yamma yayi na dawo gida a gajiye dan tafiyan da nake a kasa kwana biyu gabobina kamar nai wani aikin wahala dasu.
Gashi tun da nazo ban samu kiran maigidan ba shima banji ya kirani ba sai dana idar da sallah ishai ina gurin zaune na jawo wayana sai naga ashe ma a kashe wayan yake ban kuna ba.
Na kunna wayan sai naga ina da dan sauran caji aciki maganan da mukayi da Nana mai zagale ya fado min a rai data girman kai da son jan aji ga matan zamani shine ke kawo yawan fitina a tsakanin ma aurata a wanan zamanin.
Bayan mace tasan cewa a karkashin iko da mulkin mijin ta take amma sai wayewa da boko yasa mace ganin ai daidai take danamiji bazata iya kwantar da kanta ba ta samu aljannan ta dan boko da take takama ya ratsata ko wayewa.
Dil na danna kira a layin daddy kira daya biyu gana uku naji ya daga wayan tare da fadin Assalamu Alaikum.
Na karba mai sallaman nashi cikin girmamawa yace yau an ga daman jin motsin mu ke nan ?
Nace ba hakana bane ba mu da sevices ne daddy inda nake yace ok su baba maigari suna dashi a gidan su da nake samun shi mu gaisa ke nan.
Shiru nayi yace kin dai ga daman kiran layin mu ke nan yanzu kowa na lafiya ko nace lafiya muke daddy.
Nace naga sako gun Hamza an gode Allah ya kara arziki yace ai ba sakkon ki bane da fatan anyi yadda nace dai nace a sanyaye anyi daddy kuma sun gode.
Sai shiru nace sai anjima yace Allah bamu alheri na kashe wayan sai na kira layin anty tana dauka tace dani.
Kai haba haba dai Rama yanzu fissabilillahi kin kyauta ke nan Rama ki kashe waya gani da yara muna son jin lafiyan ki shike nan tunda kika samu gida da yan uwanki kin manta da kowa nan.
Nai dariya nace afuwan anty services ne babu shiyasa tace shine ko wurin kira na kudi baki zuwa ki kira kiji lafiyar mu Rama ?
Ga yara sun hanani shakat da tambayan yaushe mummy zata dawo sun damu na kiraki suji muryan ki amma ke kin tafi kin share mutane can.
Nace ai min afuwan anty abani su mu gaisa tace ai gasu tsaye sun min cirko cirko sunji ina kiran sunan ki a waya.
Nan ta basu muka shiga gaisawa Nasir yace na karbo mai ragon shi a wurin maigari ita kuma Amira tace na karbo mata lalle a wurin inna ta da kuli wurin mama Altine.
Mun gama wayan na lumshe idanuwa na daga inda nake kwance rigingine sai tunanen su da kewar su yazo min a raina .
A gaskiya ban kyauta ba ko ga Anty na da yaran ban masu adalci ba don nasan zasuji kewa na dama.
Gaskiya zama da manya ko zitartan su mutum zai dan samu wasu hikima a gun su gashi yanzu dan hikimar da Nana ta bani yai mun amfani yanzu yanzu.
Da ace sai na koma ne zan gan su da banji dadi ba sai nauyi da kunya zai biyo min baya.
Amma dan kiran da nai dabara yanzu nayi zai dan rage min wani nauyi a kaina ke nan.
Bayan na kwanta naji dadi a raina ko ba komai dai nazo gida naga yan uwa da abokan arziki na kuma godewa Allah da baiwar da yai min na zama abin kwatance a idon yan uwa da abokan arziki.
Zama mukayi mai ma, ana ni
Showing 231001 words to 234000 words out of 456145 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78 Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153