nima ban tabbatar ba sai yau don ban taba zuwa scaning ba don in ga may zan haifa sai dai ga yana yin zaman su nakan yi hasashen hakan dama amma kuma naga ba wacce ta taba haifa ma su sai nake ganin baku da kwansu a gidan nan ai.
Mama laraba tace waya fada maki shi Alhajin mahaifin shi ai haka suka fito mace da na miji ne macen ta rasu gun haihuwa ne shiyasa.
Sai mama laraba tace kunga ita ma din ai ai ubanta tagwaye yake biwa maza kuma duk suna nan da ran su a akauyen su.
A hankali daddy ya karasa bakin gadon ya dauki daya daga cikin su yana fadin wanan macen ne ko na mijin sai mama tace dashi namijin ne ka dauka ga macen can ai yanzu nake wa uwar sheri duk tabi ta makale mata kasan mu mata da son diya mace.
Mama Laraba tace ai nima sai da na fadi nace yau yar nan ta fado a inda ake son ta Rahama da son diya mace.
Addua yake baiyi magana ba sai da ya gama ya mikawa mama yaron ya dauko yarinyar yana binta da kallo.
Mama Laraba tace yaran nan ai sun yankewa mahaifin su kauna ana cewa Abdul yafi kwaso uban ga wanda suka kwaso shi da tushe har da dan bakin tabon dake hannu shi sai da yaran nan suka dauko.
Yana addua yana murmushi ya karasa ya rugumay yarinyar yana fadin Allah ya raya muna su a tafarkin musullunci ya sa masu albarka a rayuwan su duniya da lahira.
Yace ina yaran suka shiga ne mama tace ai suna school basu dawo ba har yanzu sai sun dawo muga hauka yau kan.
Hajiyan daddy ce ta kirani a waya na dauka ina saka kaya a jikina muna waya da ita take cewa sannu yar nan ashe an sauka lafiya ga Alhaji na gaida ke yace kin zama maman shi kuma yau.
Murmushi nayi na kara gyara kwanciya na ina fadin hajiya a gaida min dasu Aisha munyi sallama da ita mama ke cewa dani naga kin kwanta ai da ki tashi ki dan ci wani abu hakana Rahama tun dazu fa ban da tea ban ga kin sha komai ba fa.
Mama Laraba tace haka take haihuwan Haidar ai mun sha fama da Attu da ita nace kai Attu ta faye fada komai tace mutum sai ya ci shiyasa wanan karon na dauko mama bakina alaikum balle tana fama da tsufanta yanzu wani moriya zatai min kuma.
Daddy da zai fita yace dani Hamza zai zo da ita ai don ban tsaya daukan ta ba amma na bar sako yazo da su.
Abinda yabawa daddy mamaki shine har ya kwana ba matar da tai mai barka a cikin matan shi har ya fita yaje muna shopping ya dawo.
Yana zaune da yaran shi a falon shine Zulfa ta shigo wurin su tana tambayan shi wai kayan da aka shigo dasu rabawa za, a yi ne ?
Kamar yaya rabawa zakuyi har yaushe na sayowa kowa kayan amfani wanan baki ga na mai lalura bane ga tada jama, a a tare da ita.
Tace dashi gani nayi har abinda babu a namu ka sayo ai yasa na tambaya yace Zulfa na sayo nafa fahince ki a harkan nan.
Ke batulu ce ta karshe idan har kika bari Rahama ta fahinci ba da zuciya daya kuke zaune ba zakiji kunya ke kan ki kin sani.
Tace ban gane ba yace zaki gane ai idan har kishi ya jaki kika gane cewa duk abinda kikeyi Rahama na sane dake.
Amma kana bani mamaki wallahi Rahama rayuwana ne ko may ko uwata ce ko ubana yace da ita kada ki kawo min diban albarka a nan yanzu ran ki ya baci maki.
Don iskancin ku ya soma isata haka na kaya dai ne nace na mai haihuwa ne ku gunta nace Sani ya kai su.
Tace to shine may idan an hana muna kayan ai ba yau aka saba yi muna haka ba a gidan nan.
Take ran shi ya baci yace sai ta fada mai lokacin da ya taba ba wata wani abu ita bai bata ba a gidan.
Zata wuce yace dawo ai ba tafiya zakiyi ba tace gara na natafi don naga dama a jirace kake dani ai.
Yace kina tafiya wallahi yau baki kwana a gidan nan ido ta fitar tana mamakin shi nan yai mata tas sai da ya gaji ya kyale ta.
Barci nake a cikin barci nake jin muryan shi yana fadawa su mama zai mayar da ita kano ne dama idan yaje yana bukata wata acan don haka ra shirya ta koma kano da zaran an gama suna.
Mama Laraba fada take sosai tace shine matsalan Zulfa bata da wayo wallahi na lura ko dakin nan sau daya naga ta shigo shi ashe ita da manufa take hakan.
Ina jin su ban motsa ba don ni ba bakon abu bane a guna bayan fitan shi ne na tashi na kira Aisha da Amira da suke gida nace ta taimaka a gyara kayan su kai komai inda ya dace su aje.
Yan barka na shigowa harda ma wanda ban zata ba sun shigo gidan ganin yaran don fari jini irin na tagwaye.
Banyi mamakin rashin shigowan yaran Raliya ba don ko ita uwar sau daya ta shigo inda muke har gashi ana zancen suna yan kano sun fara cika muna gida ko.
Yaran sunci sunayen Saade da daddy kowa yai mamaki kara saka sunan shi da yayi yace a haka suka zo dama naja bakina nai shiru nan sabon gulma ya tashi kuma again.
Sunan yayi kyau sosai don har walima su Fati suka hada anyi rabon abubuwan daya dace sosai a wurin.
Naga kishi a gun matan daddy kamar cikin nan ba kowa keda shi ba a gidan ni Zulfa tafi ban mamaki wai a haka shiri akeyi sai tazo taga abinda akayi zata koma gefe tana magana kuma.
Yan uwa na sunzo min sosai don haka na kebe dasu nace mama zata zauna dani wanan karon don Attu bata zo ba.
Da zasu tafi kamar yadda ya saba yi masu alheri ko yaushe wanan karon ma haka yai masu ya ba kuma Suwaiba da Rukaiyya alheri su samu sanaar yi idan sun koma gidajen su.
Gida ya rage daga mu sai su mama dake zama damu din tun mama Laure na shan jinin ta har tazo ta sake jiki don komai sai ince uwata nima fa uwata a tare dani.
Munyi arbain ya shirya su mama suka koma gida suma da tarin alherin su mama Altine ce dai ya hana komawa tace a nan zata zauna da mu.
Sati na biyu da arban sai gashi da visaza zamu tafi umurah har yaran nawa gaba daya wanan abin ya dan kawo rikici a gidan sosai.
Ba fashi muka shirya din an shiga dogon zango na hutun makaranta muka wuce ba saudiya muka fara zuwa ba sai da muka tafi Egypt don jinior ya matsa yana son zuwa yaga gawan firauna da ta gani a waya.
Satin mu daya muka juyo saudiya nan muka samu wani gida mukai masauki zaka ce don mu akai gidan dama sai bayan zuwan mune na fahinci akwai aikin da shi kan shi maigidan yazo yi acan dama don baya zama a garin yana shiga wurare da dama a can don business din shi.
Wasa wasa sai da muka kai wata biyu a can waya kan da fitina daddy ya sha su a gun matan shi amma ko a jikin shi bai damu ba da komai da zasu fada muna can Raliya ta haihu na dauka zamu dawo ne sai da muka share sati hudu bayan haihuwan ta muka fara shitin dawowa gida a lokacin.
Dagani har yaran duk mun canza munyi kyau don itin daulan da muke a cikin sa mun dawo gida mun samu anyi wa gidan gyara na sosai don ashe bayan mu suma sai da suka koma kano a kai gyaran wuri yanzu part dina daban na Zulfa daban haka ma sauran suke.
Kwanan mu biyu a kasan bamu damu da muje mu yi wa Raliya barka ba don har yaran ban tsanmani sun tafi ba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,
101
Tun daga wannan rikicin da mukayi na kara fahintar alamarin kishiya dai abin tsoro ne duk dadin ki da kishiya ki tabbatar da kin boye sirin ki na yan uwan ki dana kawayen ta a gare ki.
Don da ace ni irin rayuwan Zulfa da ta shige min jiki kamar aminiyar gaskiya ke gare ni na yawa sake maganan duk wanda yazo mata a rai ba yan uwan ta ba ba iyayyen ta ba kawaye ba da miji.
Da na sha matukar wahalan zama da ita don nasan dan abu kada ne zai hada mu tafito tsakar gida tai min gori a gaban wanda nai maganan shi da ita ko ta samay shi gefe tace ai Rahama tace da kai abu kaza.
Amma sai Allah ya taimake ni duk zaman mu na kama bakina a gare ta bana zama ina sakin maganar kowa kamar yadda ita take zaman yi mun.
Ban yi ba ma tana koma gefe tace nayi din inaga nayi mata da yawa bani ba nasan muna samun irin wanan matsalan ga irin su da son shigewa mutum a jiki kamar da gaske son ka suke tsakani da Allah.
Don Allah mata mu kula kafin mu yi sauri yarda da mutum mu auna halin shi mu gane irin kalar mutumin da muke zama dashi don wata zata dade tana cuta maka amma bazaka san cewa ita bace ke cuta maka don irin su Allah ne ga baki fir,auna ga zuciya suke.
Ba wata kishiya a zamanin nan da zata ce tana kaunar ka da zuciya daya dole na ciki na ciki a zuciyar ta da kai.
Nima bawai bana kishin kishiyoyina bane ina yi sai dai ba can ba irin yadda su suke min din don har yarana sai na fahinci akwai hassada da bakin ciki a tsakanin su da su.
Tun dai yar Sa,adene da take karama na dauki son duniya ni da uban ta mun kwallafa ma yarinyar kamar yadda fita goma zanyi sai na sayo mata wani abin don shi abin yara mata avalable ne ko yau she zaka ga lates din abin kwalliya na diya mace haka uban ma yake da yarinyar yana kiran ta da sweeting shi mu kuma muna kiran yarinyar da sweet anty.
Haka yasa sai ya sayo mata abu idan anyi magana zaice saaden shi ce fa baida kamarta a duniya tare a gansu Allah ne ya hada su kuma ya raba su ba wai sun so hakan ba.
Zai dauki yarinyar ya fita da ita suje yawo tare idan zasu dawo da tsarabanta yake shigo muna sai dai yaran su rufeta suna karba a gurin ta.
Wata rana sun dawo shi da ita da Yusuf da wani lokaci ake labawa aje dashi idan zasi fita din tare.
Yarinyar tayi barci a hanyan su na dawowa don haka suna isowa gida ya dauko ta ga kafadan shi sai dayan hannun da ya kwaso ledojin da yai masu sayayya a a cikin sa hussaini mai sunan shi yana bin su a bawa da nashi kayan wasan da aka sayo masu.
A kofa sukai kicibis da zulfa da hindatu dake tsaye suna magana caaa suka bisu da idanuwa sai ita zulf ce take cewa dasu a, a anyi barci ne a hanyar yar baba ?
Yar so ne ai dole ne suyi abinda suka ga dama tunda sune diyan gaban goshi kowa ba da bane a gidan nan idan ba su ba.
Wani kallo ya bisu dashi sai hindatun ta sake cewa, dashi ana dai fakewa ga son matattaciya ana nuna banbanci kawai idan anyi magana ace wai wata Saade can da ta mutu babu dadin rai a tsakani.
Sai yanzu ne don cin amana za a fake ga yara ana wai kiran Saade da Yusuf can don kawai a nunawa mutane banbanci a kan su.
Su wa yanda ba a so din sai a kaisu a watsar inda ake watsar da yaran da ba a so mu gani shi zaifi sauki bai masu magana sai dan goga su da yayi ya wuce har ledan da ya dauko yana tokaran jikin hindatu din.
Zulfa tace ai ba zai kulaki ba an riga da an shanye shi tun farko baya ganin kowa a gidan nan sai su da uwar su kawai a idon shi da zuciyar shi.
Saman kujera ya shimfede yarinyar ya zauna a kusa da ita nan sauran suka rufe su ya dinga mikawa kowa ledan shi ya bada na yar wurin hindatu da bata shiga mutane yarinyar yace a mika mata nata.
Sai ga Jinior ya dawo da ledan yana fadin maman ihisan tace waina dawo dashi.
Daddy yace ka mayar kace nace ba nata bane na hussuna ne yaron ya juya da sauri ya koma sai da ya dan dade ya dawo yana zuwa yake cewa daddy har tace nace hussuna bata so sai kuma tace na kawo.
Bai yi magana ba ya mike ya bar yaran yafita ashe gun ta ya tafi tana zaune daidai tana cin cake din da ya sayowa yarinyar yace ke may ye hujjan ki na cewa a dawo min da abinda nabawa yarinyana.
Tace a cikin tsiwa ai ba ita ka sayowa ba nagani shiyasa nace a maida a bawa wanda ka sayowa din su kara.
Yace you are stupid by saying that mara godiyan Allah yau din kawai da ban fita da itaba har kika tsayar dani hanya kija fada min magana haka ?
Na kyale ki ne kawai don bana son yawan hayaniya a gaban yara amma duk ranan da kika kara min magana makamancin hakan zaki gane kuren ki a gidan nan ko na aikowa yaro da abu ki tsaya min iyayin tsiya zamu hadu dake a gidan nan.
Ya juya a hasale ya fice daga part din ta bishi da harara kawai batare da ta kara furta wani abuba.
********** ********* **********
Tun da na dawo gidan don aikin safe nayi nake kwance ina barci ina tashi wanka na fada na fito sai ga Aisha tashigo tana cewa dani daddy ne ya aiko da kankana na gyara mashi.
Nace ta bari na shirya na zo na gyara da kaina na fito na gyara na samu plate na saka tare da rufewa nakai mashi.
Zaune yake falon shi yayi dadaya yana aiki na shigo da sallamana falon dauke da fruit din a plate.
Ya dan dago kai yana kallona tare da amsa min sallaman nawa na samu wuri na zaune ina mashi barka da wuni.
Yace likita har angama ganin hanjin an dawo gida ashe murmushi nayi tare da gyara zama na daga gefen shi inda nake nace haba daddy bamu da aiki kullun sai fanin hanji kuma ?
To maye aikin naku ta fada tare da ture takardun dake gefen shi yana kokarin bude plate din dana aje mai a gaban shi na fruits din.
Yace masha Allahu mai kyaune ashe mai yashi kuke kiran shi komay naji ina son irin wannan kankanan sosai wallahi.
Ya dauki fork tare da yin bissimillah ya fara shan kankanan tare dace min bissimillah mana kisha mana na mika hannu tare da daukan daya nakai a bakina.
Yace dama ko ina son muyi yar magana dake sai gaki nace tau tare da dan tsagaitawa ina sauraren shi inji abinda zai fada min din.
Yace zancen daya da biyu ne ai na farko akan auren Aisha ne don har yau banji kince dani komai ba akan maganan kuma.
Na dan rausaya kaina nake cewa dashi to daddy ni may zance dakai kuma ?
To amma dai kin san nike da alhakin yiwa yarinyar nan kayan daki kamar yar dana haifa ko don yanzu haka kayan da na oda akawo masu ita da Amira inaga sati mai zuwa insha Allahu zasu shigo sai zancen bukin ban san ko maigari zai yarde min da na aurar da ita nan guri na ba kamar yata dana haifa.
Nace to daddy idan haka kake bukata ai ba matsala sai na fada mai don nasan ba zai hana hakan ba ai.
Yace to shike nan yanzu ina son sauran list din komai nasu don ko ita Amira din ina son komai nata ya kammala don bazata kai wani azumi ba a gidan nan gaba dayan su.
Nace ubangiji ya cika muna guri na alheri yace amin tare da kara kai kankana a bakin shi yace to sai kuma magana ta biyu dana ke son nayi dake.
Shine ina son wancan part din na Raliya wata zata maye gurbin dakin nan bada dadewa ba insha Allahu.
Da kyat na iya karasa tauna kankanan da nakai a bakina na hade amma a fili sai na daure nace masha Allahu Allah yasa da alheri a cikin yin hakan da za ayi.
Yace cikin farin ciki na gode da jin hakan daga bakin ki don har an gama komai budurwa ce yar sokoto ce kuma bana nai karo da ita.
Tana jami,a
Showing 414001 words to 417000 words out of 456145 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139 Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153