sai ferfesun kayan ciki da fruit's salada dana hada ko baiyi ba.
Sai lokacin naga murmushi a fuskan ta tace kai Rama baki da dama wallahi kamar kin shiga raina kinga nufina don ni ban koyi tunane hada mai salad din da yake son sha da dare ba ai sannu da kokari nagode kinji Ramana.
Kai haba anty sai kace wani abu har da gode min tace ai ba don ki ba ni wallahi na ma haune sosai nace kiyi hakkuri anty may ke cikin girki kuma ?
Tace hmm Rama ke baki ganewa ne wallahi amma fita ke ga daddyn nan naku wallahi.
Bayan na shirya nazo na karbi dan ta da muke kira da jinior na goya shi ina cewa magariba yayi anty kawo shi in saka shi a baya.
Har akai sallah yaron na gurina can sai gata ta caba kwalliyan ta ta shigo dakin mu ina tsaye ina jijiga yaron daya dan motsa Farida na saman gado kwance muna hira.
Tace Rama zo muje kitchen ki fitar min da abincin nasa mugani tare muka fita da ita zuwa kitchen din ta samu komai na hada yadda take bukatan a hada mata shi tace sannu da kokari yar albarka ranan da kika barni kan ai zan sha fama wallahi.
Nace cikin turo baki ni ina zan tafi in barki haka anty muna nan wallahi dake tace bazakiyi aure bane haka zakiyi ta zama a gida ke nace auren may kuma ni da zan zama likita inyi ta aikina ina maku allura.
Dariya tayi tace yar sheri akaina ke nan likitancin zai fara nace to anty gani gida wani likita kuma za, a kara kira maki idan na gwanan ce.
Baki da dama wallahi tana tsaye tana kallo na na hada fruits salad din na zuba a cikin wani bowl din ta mai fadi dama don salad akayi shi kawai.
Nan dai na ta fara fita da kayan nabi bayan ta da saura muka kai part din shi a babban falon shi na gidan muka jera a kan dining table.
Zan fito tace na tsaya mu dan kara gyara part din tare muka gyara komai na fito na barta a cikin part din nakama gabana nikan.
Har dare yaron na abayana babu duriyan ta a furin mu mama tace dakariya tana so tana kai kasuwa Allah ya rufa maki asiri kin hadu da mai kaunan ki tsakani da Allah.
Can gurin daddy kuma yana cin girki yana yaba dadin shi tave wallahi bani nayi ba aikin Ramane
Nan take fada mai tashi tayi ta samu kawai na gama hadawa indon itane ma aida har lokacin ba, a gama ba,
Yai murmushi yace nadai gane yarinyar nan ta bata ki yanzu da son jiki idan ta tafi ban san yaya zakiyi ba ai.
Take fada mai yadda mukayi da ita shima dariya yayi yace a kanki ke nan za, a fara gwada aikin nata tace kyale dakariyar yarinya kawai.
Yace amma ni ina mamaki wai kamar wanan yarinyar ace ta taba aure haka mutane basu da tausayi wallahi.
Tace aida kaga wanda ta aura din ne ma wallahi yafa fi Alhajinka tsufa Allah ki.
Yace kuma ta zauna dashi tace yaya zatayi kasan halin kauye da yaran kauye gurin biyayya.
Yace an dai hadu da mai tarbiya aiki kauyen yanzu sun waye sun rage wanan abin don ilimi yakai ko ina babu maiganin ta yace wai tayi wani aure can a baya.
Tace a dakin tama fa ta fadi yace kai tace wallahi ai in tana ma mutum hira sai ka sha dariya har yanzu fa Rama bata san kan aure ba barta dai rashin kunyan su na yan kauye yanzu kuma na samu duk ta barshi dan training din data samu yace aikin kyauta mata wallahi.
Shi ya bijiro mata da maganan tafiya na tace ya kamata ne a dan yi min sayayya da zan tafi dashi.
Yace zai duba gobe ya gani naga ta matsu da zancen ai jibi sai hamza ya kaita ko tai mashi godiya suna ci gaba da hiran su.
Zulfa ce ta shigo ta samay su wai zancen yar ta yace wai Zulfa may ke damuwan kine haka please?
Anty tace No wallahi tayi kokari bari naje idan batai barci ba na kawo maki ita yanzu ba shike nan ba.
Yace No ki barta har gobe idan Allah ya kai mi yanzu sunyi barci ko tace shike nan Zulfa tafice fuuu da ita daga falon tana kunkumi a bakin ta.
Ko da ta dawo ta samu na sauke jinior ina cire mai permpers zan saka mai wani take cewa ya tashi ko nace eh ya falka amma na bashi ruwa yasha ya koma barci
Tace ko na bar maki shi ku kwana nan ke nan tare nace Anty rufa min asiri kin san halin jinior idan yaso nono ya bare bakin nan baijin lalashi yanzu ma saan shi naci bai min kukan ba ai.
Sai da ta hada komai da zata bukata a can na yaro danata a cikin wata yar jakka tai min sallama ta tafi na rufe part din namu.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,


IDAN KIN BIYA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYA BA PLEASE IDAN KIN YI HAKKA KIN CI AMANAN ALKAWARI YAR UWA ALLAH NA GANIN KI, , , ,

25

Da safe bata fito ba sai wajajen karfe goma saura ta sauko daga dakin shi mukan har mun karya muna kallo a lokacin.
Sai dai abincin su yana shirye na hada komai daya dace ai masu tayi wankan ta tun a can ta shirya yaronta tana shigowa ta miko min shi ta shige dakinta ta saka tufafi a jikin ta.
Bayan tafito ne take tambayana abin karyawan sun na fada mata abinda nai masu na karyawa tace har da pepper chicking kikai muna nace Allah yasa dai yai dadi anty zaku iyacin jagwalgwale na ma kuwa ga yacan dai na shirya.
Ta kwasa ra nufi gurin shi da kayan abinci taba shiryawa ya fito a cikin shirin shi dama yana sauri ne .
Bashir na jiran shi zasu fita zuwa wani state daga bayan ta yake cewa har ina batun fita nasan bazan samu karyawa ba don yanzu kika fita.
Tace ka manta da Ramana tana gidan yace yanzu dai na tuna ya dan dafa mata baya ya ja kujera ya zauna tana fara budewa kamshi ya daki hancin su baki daya kwai yaji albasa a cikin sa sai bread da nai torseting nashi yaji hadi ga ruwan tea a flaska da wanan kazan dana gyara masu.
Nan suka zauna ci sai ga bashir ya shigo falon tare dashi suka zauna ya fara ci shima yana zuba santi yana cewa wai ko Saade akwai macen da ta kaiki iya girki jiya na tafi ina sanyun tuwon ki har amina na min sheri yau kuma ga wanan haka .
Tace aikin kaunata ce yace wanan yarinyar dake gurin ki kike nufi ko may yanzu itace keda wanan hadin haka ?
Don Allah saade ki ban ita mana na aura dama ina son karin mata kinga abin yazo min da sauki ke nan a gida nai gamo.
Don wallahi ko banza dai yarinyar dama ra hadu sosai tun randa na fara ganin ta nasan za, a rina anan.
Don Allah bashir ka rufa min asiri kada kasa Amina ta fara min kallon up side down muna zaune kalau.
Kaji matsalan ku mata wallahi da ankawo zance kuce ga kabali ku bata maganan.
Daddy ya dauki ruwan shayi yana kurba a hankali kamshin kayan yaji ya daki hancin shi bashir yace saka min baki mana mutumina.
Yace kun fi kusa ba ruwana wallahi matarka ta koreni idan naje yace kaima ka mara mata baya ke nan ko ?
Nan dai sukai ta hiran su daddy yana jin su bai tankasu sai da yaga bashir na kokarin su makara yake cewa don Allah idan ka gama shirmay ka kazo mu tafi don Allah.
Nan bashir ya mike har yakai kofa ya dan dakata ya juyo tare da durkusawa a kasa yana cewa tau anty mun gode sai mun dawo ke nan ko ?
Tace ban son sheri ko da gaske na girmay ku din ne da ake fadi na girmay maku na aure ku ina maku wayo.
Ya mike tare da daga kafadan shi yana cewa badani ba cikin wanan zancen ni gwaunatina na fara kafawa don neman kamun kafa.
Tace ba gurina ba ni dai tafi lokacin daddy ya karaso inda yake yana cewa don Allah muje da shirmay ku ?
Yace kai shirmay fa kace malam ina zancen shirmay ana maganan aure anan nagafa kuna son hade min kai kai da besty ka Yusuf ?
Nan suka fice suka barta tana hada kayan abincin takirani ga waya mukazo muka kwashe zu part din ta.
Lokacin ne take fada min gobe ne in Allah ya kaimu tafiya na ai mama naji tace gyara zancen ki don nima na tashi ke nan.
Dariya muka sa mata anty tace dama na sani mama tashin Rama tashin ki ita da zata tafi ta dawo kwana biyu fa zatayi kawai.
Nai saurin juyowa na kalli anty jin tace kwana biyu kawai zanyi tace to da kwana nawa zakiyi kuda kuka koma school.
Mama kan harta mike ta shiga shiri ba kakautawa ita a dole gida zata take cewa indai ba so ake sai yaro ya girma ba su kore ni da kafan shi.
Duk laladhin da anty zataiwa mama amma mama taki yarda dole itama aka fara shirin nata tafiyan.
Kayan da anty ta zube muna wai tsaraba abin ba a cewa komai don ni dai an wa inna sayayya masu yawa da kanne na samu sun samu harda baba bandir din shadda guda biyu ga kudin dinki.
Mama Laure ma turamay wax guda biyu su sabulu dasu omo da man shafa an saya mata su har kakanina da maigari da matan shi sun samu tsaraba gurin anty don mijin ta yaba da kudin enouhgh akai muna tsaraba dasu.
Ga buhuhunan shinkafa na baba na da maigari da jarkan mai guda biyu da sauran abubuwa abin ba, a cewa komai wallahi.
Sutura kan da su kula har da kayan mata anty ta hadawa inna ta su wai duk nata ne ita kadai bayan buhun kayan sawana dana tara masu a lokacin.
Tunda yaran sukaji zan tafi suka saka kuka suma dasu za, a tafi har yar gurin su hindatu da zulfa wai sai sun tafi.
Ita dai anty ta cewa na shirya yaran ta na tafi dasu kawai taiwa daddy bayanin yaran sun nace zasu bini bai so naje dasu ba amma sai anty take cewa tariga ta yarda naje dasu bata san yadda zata ce kuma kada naje dasu ba.
Dole ya hakkura amma yasa akai sai abinda zasuci idan mun tafi can kauye sai da aka shage but din bakin Jeep din Daddy da kaya muka kama hanya su hanifa nata faman birgima wai sai sun bimu.
Amma iyayyen su sun rike su ba inda zasu kauye a halaka masu diyan su cewan zulfa yar ta tillo daya akai mata kauye a sirce mata ita nan ma yaya aka kaya da ita tana kin ta balle taje can gindin maganin ai sai tace bata san ta ba ma nan gaba.
Daddy ya ce will you stop dat rubish zulfa waike baki da hankali ne ko may su yaran da za, a dasu sunfi hanifan ne ko may ?
Tace oho dai koma may ye ba a zuwa min da yarinyar a halakata a banza ya tsawata mata taja yarta suka shige part din ta tana faman turje turje a kasa sai tabi mu.
Mun kama hanya sosai Nasir tana lafe a jikina a gaban mota sai daji da yan kauyu ka muke wuce wa.
Karfe sha biyu mun isa kauyen mu ina kallon mutane suna al, amarin su irin na kauyuka kamar yadda aka saba a baya da muke can.
A hankali na sauke ajiyan zuciya daga inda nake zaune tare da lumshe idanuwa na yau gani a cikin mahaifana zan ga tan uwana da mahaifana da abokan arziki duk da ba abokai ke gareni ba ni.
Kofan gidan mama Altine motan mu yaja ya tsaya jiyiiin take hankalin mutane ya dawo kan mu ana son ganin ko su waye a cikin wanan irin dan kareriyar mota haka.
Muna na fitowa su Rukaiyya dake tsaye kofan gida da saurin ya illo suka sako muna idanuwa.
Ina fitowa gurin ta na nufa da dariya ina cewa Anty Rukaiya ta bude baki tana cewa lah Rahama kece kizama wata yar birni haka kamar baturiya dake ?
Tana dafani tana bi da kallona har bayana zuwa takalman dake kafana sai tace eyye Rahama ke kan ai kinji dadin ki wallahi sai faman tabani takeyi.
Nan aka turu ana kallon mu cikin sha, awa ga su Amira duk sun make muna ajikina kamar za, a kama su a lokacin.
Murtqn mama Altine ne ke fadin ke Rahama zo ki nuna mai kayan da zai sauke muna anan.
Da sauri nabar mutane nayo gurin ta sai cewa suke auyyo har da tafiyan ta ya sake wallahi Rahama ke kan kin ji dadin ki wallahi.
Na nuna ma hamza kayan mama ya sauke mata na nuna mai wanda za, a shiga dashi gidan mu nan su Rukaiya akabi buhun shimkafa suna ihu da murna an samu na sulalawa.
Dama tun can anty ta fadawa mama mu sauka gurin Inna na mu debe mata kewan rashin mu kwana biyu da tayi.
Muka shiga mota ina daga masu hannu nace zanje na dawo anjima muka wuce nan muka barsu a tsaye sun bimu da kallon mamaki.
Ana shiga da kayan cikin gidan mu mama Laure tana tsaye tana shurin fitowa don taji ana ihun ga Rahama ga Rahama tafito tana ashar tana fadin ina yar jakar uban shegiya ta dawo yawon ta zubar din ta ta debo cuta zata lakaka mun, , ,
Sai tai shiru ganin yara na mulmulo buhun shinkafan gwaunati a cikin gida ga jarkan mai da doya tagani.
Rukaiyya da murnan ta take larabarta mata yadda na koma tace ke rufe min baki wace bata san ciwon kan ta ba .
Gashi yanzu taje birni ta bude ido tafiku ke nan fa ake nufi yanzu fa ?
Rukaiyya tace don ma baki ganta bane mama ina zaki hada mu da Rahama yar birni da ita ko tafiyan tafa na yan gayu ne yanzu tana gwada wai yadda nake tafiya a gaban mama din.
Haushi ya kumay mama takai mata rankwashi a kai tace ja can ki bani guri mara tunane kawai.
Kamin mu boye kayan nan daga ciki tun su Larai yan gulma basu shigo sa ido ba yanzu ki gan ta gidan nan tashigo.
Suna gamawa kuwa sai ga Laira na sallama tace may na fada maku lairai na fadin ance yan birni sunzo harda abin arziki tana raraban ido bataga komai ba.
Tace ance har da abin arziki mana tazo maku ina yake mu rage kyayan idon mu kada a bamu labari.
Mama tace sai uban ta ya dawo idan yace a fitar zan fitar kowa ya gani tace ai kin fi danan Lauraru yanzu da ci yazo nine abin gudun ki kuma ko ?
Ina nan muka hau mota har birni dake dakyat muka sha gurin neman ta a can yanzu tazo da abin arziki zaki boye min ?
Mama tai mindinkis taki nuna mata komai har tagaji ta fice a gidan tana cewa aikoma maye muji ai idan yai wari.
Mama tace sai ku jira har tai warin kuji ba dai yanzu ba kan ban son sa ido da gulma wallahi.

****** ********* ******

Kofan gidan maigari nake mashi kwatance har ya kaimu suna zaune ana fadan ci fada tacika da manyan gari sukaga mota ya tsaya kofan shi.
Yan fada suna fadin ku gyara ga baki nan daga birni anyi aka shiga kakabe tabarmi don naki su zauna akai.
Sai ganin sukayi na bude mota na fito babu wanda ya shedani daga cikin su har na fitar da yaran daga mota dagani har hamza muka nufi inda suke zaune sun kura muna ido kawai.
Tun daga dan nisa kadan na cire takalman kafana haka yasa su Amira ma cewa zasu tsaya su cire nasu najasu nace suzo mu karasa hakanan amma sukaki don Anty tace duk abinda sukaga nayiwa babba suma suyi hakan.
Mun karasa na dan tsaya daga nesa ina gaidasu suka karba da maraba yarinya sannu ku dai da zuwa suna gaida mu da hanya.
Wani daga cikin su yake cewa yarinya daga ina haka bamu sheda ki ba fa ?
Nace baba Rahama ce yar gurin Audi mai awaki salati suka saka a lokaci daya suna Allahu akabar an koyi haka wallahi yarinya kece kika koma wata jamian birni bamu gane ki ba ?
Mai gari da kan shi ya daga saman kujeran shi yana mika hannu Nasir yazo gurin shi.
Tun nan na fara fahintar akwai zaman lafiya a tsakanin shi da mahaifiyata yadda muka samu taron arziki a gurin shi haka.
Na mike na nufi cikin gida tsufi suka bini da idon gulma suna ikon Allah birni take da Altine mai kuli kuli
Showing 93001 words to 96000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32 Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153