tai mata waya.
Nace daddy kagani don Allah kayi hakkuri hakana don gudun abinda kaje ya dawo kuma don kaga laifin zai dawo ne ya taru akan anty daga baya.
May kike nufi da hakane wai Rama kekina tunanen zan iya rabuwa dake ne ko may a yanzu ni sakin mace baya a cikin tsarina ko yana ciki bake ba kuma.
Wai ma may kika dauki aure ne ke kina daukan aure abin wasa nagani ko ?
Daga yau ki cire irin wanan zancen na zaki bar gida a ranki don ba a gida na ake wanan maganan ba.
Nai haukane da zan samu zukekiyar mace kamar ki na saka akan dan maganan da bai taka kara ya karya ba.
Don haka ki cire komai a ranki ki tashi muje ki bani hakkina dake kanki kada ki cuta min da yawa.
Kin hana ni ganin fuskan ki kwana biyu kin boye min wanan surar da nake gani naji sanyi a raina yanzu kuma zakice abinda Allah ya halsata min ma zaki min rowan shi to ba zan iya jure wanan ba gaskiya.
Don ya fita ya barni sai kawai na saka mai kuka wiwi maimakon ya tashi sai ma daukana yayi cak zuwa cikin bedroom dina Allah ya taimake ni tsab nake don bai kyale ni ba duk da kukan da nake sai da ya samu gamsuwa a gareni.
Ranan anan dakina ya kwana sai safe warwas yafito duk matan gidan sun fahinci komai ni abangarena koba komai na gwadawa hindu nima din mace ce kamar kowa duk da ni diyar tallkawane da take gani.
Washe gari ban fito da wuri ba kuma ba zuwa school don haka na baje nai hutun gajiya nai ta barci abina sai sha daya na tashi don banda damuwa nasan anty zata bashi abin karyawa idan ya nema.
Na tashi nai wanka na shirya na nufi gurin anty mu gaisa yaran na gida su suka fara tarona.
Nashiga daki tana zaune tana waya na samu guri a gefe na zauna har tagama wayan ta juyo gareni tana fadin kin tashi Rama ?
Nace ina kwana anty tace kin dai huce naga alama yau sai dai ashe haka kike baki ita turewa Rama ?
Murmushi nayi na dukar da kaina kasa nace anty ba hakana bane tace to komai mutum zaiyi idan an bashi hakkuri ana son ya sake yabar anin don gaba.
Nace nagode anty tace may ye na godiya Rama yanzun dai ki tashi ki batun ba mijin ki abinci na bashi na safe saura ki na rana don bazan daukar maki ba.
Na juya ina dariya nace kai anty ki dai cika ladan ki mana tace dayake baki da tausayi ba.
Zama nayi falo muka dan yi shirmay mu da yara hiran game ne muka taba karshe nace kowa ya kawo min haddan da akai masu atare dasu muke biyawa.
Haka uwar tafito ta samay mu muna karatu tace Rama rana fa yayi kin san yau weekend ne da wuri may gidan zan shigo gida.
Nace yanzu zan tashi ta koma tana kallon mu yadda nake ma yaran gyara karatun boko ne bamu samu yi ba nace sai da yamma zamuyi shi.
Namike ina fadin oya Amira taso muje kitchen muyi girki shima Nasir ya mike yace little mum nima dani za, a nace mu tafi shima jinior ya biyo mu.
Abinci lafiyye na hada kamar ranan za, ai wani bako ne sai biyu muka kammala komai a gurguje naje nai sallah nai wanka na shirya cikin dogon rigar material mai ruwan dark blue da kore.
Dinkin shi mai dogon hannu ta hannuwa an mai stly ya baje haka kasan rigar ma free stly akai min.
Kamshi kawai ke tashi ban dade da fitowa ba sai ga daddy ya shigo nan aka shiga gaidashi kunya da nauyin shi nake ji na kasa dago ido na kalle shi.
Yace akai masu abincin shi saida ya fita da yan mintoci na mike nace oya azo muje mukaiwa daddy anbici yau weekend ne muyi hira da daddy suka mike cikin jin dadi mukarbar anty da Gajiye kawai.
Yana zaune da waya magana yake a hasale koda muka shigo ya dago idanuwan shi da suka nuna akwai bacin rai a cikin su ya sauke a kaina.
Simi simi na fara aje kayan tare da gyara wurin sai naga duk falin ya hargitse min kwana biyun da nayi.
Ban zauna ba na juya na dauko abin gyara na gyara komai tsab na har ya gama waya na dawo gurin su.
Hira yake da dariya sosai da shirmay da suke zuba mai kowa na fada mai abinda zaiyi idan ya girma.
Da Amira ya fara tace ita idan ta girma police zatayi ta tare hanya da bindiga nace kai Amir police kuma tace eh mum bakiga police din hanyan school ba na tsaya a hanya duk wanda yazo na harbe shi Nasir yace karya kike yi ko mummy nine sojan little mum na harbe kowa har da maman ihisan dake sa little mun kuka.
Cikin harshen turamci daddy yace you see what you people are course to my children they start hetting people with dis eges.
Sai yace kai Nasir soja ai ba halbi yake yadda yaga dama ba yace daddy ni dai soja zanyi bakaji little mum na kirana da sojan ta ba.
Nan ya shiga jero muna haukan wa yanda zai halba in ya zama soja sai dariya uban keyi yana tambayan shi may zai sa ya halbe su ?
Yana fada mai laifin da sukai mai yace Amira tace har da gajiye zamu halbe idan bamu tashi barci ba sai taita dukan mu ko in zata muna wankan safe tai ta zagin mu a bathroom.
Nasir cikin halin nan na shi yace eh da ita zan harba first ranan kin manta ta doke ni wai na balla buttle din uniform dina.
Banji dadi ba yadda suke maganan abinda gajiye ke masu haka shima uban sai naga ya lumshe idon shi.
Hindatu ce ta shigo falon ta samay mu cikin raha haka da yaran ta ce ashe ka shigo yace eh, tace tana son zuwa unguwa ne dama.
Wai ke hindatu shi fitan nan kullun sai anyi shi ne jiya kin fita fa yau kuma kice fita zakiyi kowa na gida da yaron shi yana weekend.
Bin yaran tayi da kallo tace eh ai na gani tunda ga yaran so an tara ma a gaba sai dariyan ka akeji tun a waje suko wa yanda ba, a so su mutu.
Ni bance ba in ma sun mutu kwanan su ne ya kare tace ana dai makirci a gidan nan wallahi.
Idona na dan rintse kamar na bata amsa sai na daure muryan daddy ne kecewa makircin may kuma akayi ?
Tace ai dai akwai Allah don ko wani dama haihuwan shi akayi baga dalilin ware wasu ba anan kana hira dasu.
Yace kin bari yar ki tana hurda da yan uwanta ne ko tazo ne aka kore ta nan din tace tazo nan yin may cikin ku ta gane may anzauna ana maka wani kilibibi haka.
Yace dakata ya isa haka na idan shi ya kawo ki kaman hanya ki fice min uguwa dai ne ba kuma yau ba ba mai fita gidan nan yau.
Eh da yake mune ba amma wa yanda ake so ai su ko yaushe fitan su sukeyi ko ba tambaya.
Yace bako a gidan nan ba yanzu duk macen da zata fita dole sai da izinina idan kuma mutum ya isa ya fita ga kofa a bude ai.
Ko bani gari kuma mace ta fita bada sanina ba nace ban yafe ba fakat abinda ba, a yafe ba ai yawa garesu gidan nan tunda wasu don milki da isa har dakin su ake binsy akwana can.
Yace na kwana ina dakin matana na kwana ba dakin farka ba dai ko gida nane ina da right din da zanyi abinda nake so.
Wata fi a gidan ita da kake kokarin fifitata haka yace ya ishe ki haka kifice min da fitinar ki da baki da aiki sai tsegumin tsiya kullum.
Tsegumi kan ai kowa nayin shi bani kadai ba in ma kayi ne don ka gyara ma ta rai saboda ita yar gwal ce tayi fushi to ka sani yadda ka kwana da ita dakin ta kowa ma sai ka kwana a dakin shi.
Yace to ki jirani nazo kwana dakin naki get out from here mara tunane kawai ke kullun da sabon fitinan da zaki bullowa mutane dashi.
Ba sai ka koreni ba ai fita zanyi dama ba zama nazo yi ba ra, ayina ne na fada ta juya tafice tana fada har ta bace yai tsuki ni kuma na sauke ajiyan zuciya inda nake.
Amira ne tace kai maman ihisan fada fada da duka ranan ma akan ihisan ta daki jinior wai ya ciji ihsan kuma fa daddy ihsan ce ta shanye mai swwet din da little mum ta ba mu.
Amira bana hanaki yawan surutu ba hakana tace tana kama bakin ta na bari little mum.
Yace ai ki barta ta fadi anyi ne tunda kikaji sun fada tayi ne don bata da kai, ko kadan.
Ina kwashw kayan da sukaci abinci sai ga Zulfa ta shigo tana ya mutsan fuska ta samu guri ta zauna saman kujera.
Tace zan tare da bin kowa da kallon sai ta sauke ajiyan zuciya tace dan fita ne nazo fada ma.
Yace ba fita yau ko ina yanzu hindatu tazo na fada mata hakan ita don haka ku barni in huta please.
Inda yaran suke suna wasannin su takai ido ta bi su da kallo cikin takaici ni dai ina daga bayan kujera na tsaya tare da dafa makarai yan kujeran ta baya daidai saitin daddy din.
Batai min magana ba nima ban mata magana ba ta dan yi jim kamar zatai magana sai kuma ta mike ta fice rai bace.
Na sauke ajiyan zuciya a hankali na ce a rai na gidan danger ke na wanan gida kowa da tashi kalar fitinan.
Mun dade tare da daddy da yaran da alama yaji dadin samun lokacin da ya danyi dasu.
Ina ganin uku da rabi nace dasu oya muje mubar daddy zaiyi sallah muma zamuyi sallah.
Suka fita da murnan su muka kwashe kaya zuwa cikin part din anty nakai kitchen idan na idar da sallah nazo na wanke su.
Bayan na idar da sallah ne na dan zauna da casbi a hannuna ina ja a hankali cikin lumshe idanuwa na daga inda nake zaune.
Tunanen rayuwan gidan ne ya tsaya min a rai na sosai nace wanan indan mutum bai yi da gaske ba sai ciwon tunane ma ya kama mutum.
Da dare sai ga kiran wayan daddy akan duk muzo mu falon shi yana neman mu.
Nice ta kusan karshen shiga don ina bayan anty tana gabana mun samu su saraki matan gida a zaune a kusa dashi.
Na kula haka sukeyi idan ya kiramu gaba dayan mu sai suyi saurin fitowa don kawai su zauna a kusa dashi.
Ni dai ina zuwa na zauna kasa a gefen kujeran da anty na take zaune a kan shi daidai saitin kafan ta.
Yana ta aiki a cikin system din shi bai kula kowa ba a cikin mu har tsawon wani dan lokaci.
Sai can ya dan sauke numfashi tare da dago kai yana kokarin rufe laptop din nashi a hankali tare da fadin yaiwa kun zo ko.
Ya fara da bissimillah yana cewa dama nace a kira ku ne don ni tafiya ya kamani zuwa Australia.
Don haka nake son naji wace keda tafiya a cikin ku dan ina ganin zanyi wata uku ko hudu ban dawo ba.
A take gurin yai tsit bakajin motsin komai sai na na,uran da suke aiki a lokacin.
Kowa tana sakan zuci sai anty ne tai magana farko tace badani ba cikin wanan tafiyan gaskiya.
Nidai ina zaune karatu ma nake a cikin wayana ba sauraren su sosai na keyi ba.
Daddy yace nasani amma dole ne abaki hakkin ki akai ai.
Sai shiru ya biyo baya can dayaji shirun yai yawa yace ku nake saurare fa.
A lokaci daya suka hada baki gurin cewa dani zaka, sai yace to ban fahince ku ba dai ?
Wanan tace da ita wanan tace da ita yana jin su ya lumshe idanuwan shi sai da suka ishe shi yace a tsawace stop .
Kada kuyi min hauka anan ba shi na kira ku ba don Allah duk baku da tunane da adalcin gava dayan ku dakuke wanan haukan haka ?
Inda ku masu adalcine da sanin ya kamata bazakuce naje daku ba sai dai kuce na dauki Rahama mu tafi da ita.
Nima ba don uzuri ba babu wani tambaya da zan tsaya yi don nasan ita ya dace naje da ita din yanzu.
Hindatu tace tunda tafi mu ko may ko kuma mu bamu da hakkin zuwa ne daba za, a damu ba?
Zulfa tace nasan hakane ya kamata amma sai tun farko banji ka fadi hakan ba shiyasa nai shiru.
Yace naso zuwa da Rahama sai dai karatun da take yi bai son wasa acikin sa wanan uzirin ne yasa ba batun zuwa wani guri da ita a yanzu.
Amma ku sani nan gaba inda halin hakan za, a maimaita tafiyan idan hakan ya taso.
Don haka daga cikin ku ina son naji wacce za, a tafi da ita din ?
Sai kuma gardama ya kaure masu basu ko tsaya batun jinda sukayi yace nan gaba za, a maimaita tafiyan dani ba.
Nice na dago kai ina cewa amma sai naga kamar tafiya da anty Zulfa zaifi don taje ta samu kara ganin likita a can don lalurar ta.
Ke muna fuka waya saka bakin ki yar bakin ciki ni zakiwa bakin ciki ko bukulu ?
Ta na gargade ki da kiyi gagawan fitar da bakin ki cikin maganan nan don babu sa,ar ki anan kaji min yarinya karama da iskanci.
Nace wallahi yarinya na bayar uwarta daga fadin gaskiya sai ki dinga fadar magana wa mutum kamar kin haifi mutum ?
Magana ce ta gaskiya ake so shina fada amma idan nayi laifi kiyi hakkuri don Allah ?
Kaji kilibabba ki gama nuna min kiyayya yanzu a filin Allah kuma ki dawo kina wani yin hakkuri.
Ni dama can nasan babu mai kaunata a cikin ku da kike cewa aje da Zulfa may Zulfa ta fini da za,a da ita ko kuma may zata je ta tsinana mai a can.
Muryan shi ce yace Zulfa dama nima tunane akanki yake sai ki shirya mu tafi aje a duba lafiyan ki dana baby a can.
Shi ke nan kuna iya tafiya har anty na batun mikewa yace na tuna dakata sai ta koma ta zauna kawai bata dai yi magana ba ita.
Yace Rahama shiga ki dauko min briefcase dina a ciki wana ashh colour din, zaki dauki min nace to tare da mikewa zuwa daukowa.
Bayan na dauko ne na mika mai cikin girmawa ya bude tare da kirga kudi ya ce zo karbi ki mikawa antyn ki wanan tare da ci gaba da kirga wani.
Ina mika mata na samu wuri na zauna ya kirgo ya mikowa Zulfa nata dake kusa da ita sai hindatu.
Nice ya kirgo yaba a karshe ina karba hindatu na fadin kamar daidai ka bamu da ita nake gani ?
Yace ita wa wai tace wanan yarinyar da bata da kowa a tare da ita muko ga yara ga yan aiki da sauranvsu.
Yace eh daidai na baku ma ita ba mamata bace ko may ?
Tamike tsaye a fusace tana fadi kai kai ana dai rashin adalci kan agidan nan yanzu wacce bata da kowa za, a bawa komai daidai damu ?
Yace ashe da nake baki daidai da sauran abaya hainci nakeyi ke nan tun wanan lokacin ko yanzu ne rashin adalcin ya soma akan ita Rahaman.
To shi naga zan bayar kudin ki ko nawa ko wani abin kikafita dashi ke naga baki son azauna lafiya wallahi duk kika kara cewa tak a gurin nan sai ranki ya baci yace ku tashi ku tafi nagama daku ke nan.
Gaba daya muka mike zamu bar falon yace ke Rahama zo ki mayar min da wanan jakkar daki.
Na juyo na koma na dauka na mayar daki inda na dauko da farko na fito na zo zan wuce yace dani idan kin shiga turo min anty ki.
Kwana uku suka shirya suka tafi bayan mun sha nasiha mai kama da gargadi a gare shi kan fitina da kuma fita ba bisa kaida ba.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE HAKAN BA, , , ,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YAR UWA DON ALLAH ZAI TAMBAYE KI

47
Muna barin wurin daki na nufa na shirya tsab sannan naje naiwa anty saida safe.
Na samay ta tana saka kayan
Showing 201001 words to 204000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68 Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153