haka sukai maki da kika shigo ?
Jin rigiman nasu ba mai karewa bane yasa na mike naja hannun yaron da zuman mu fice mu basu guri.
Naji yace ina kuma zaki Rama, tsaya mana ki zuba min naci zaki wuce kuma ?
Kadan ke nan ai ga haukan yan kauye idan kace kwashe kwashe ka iya a gidan ka.
Wani irin malolon bakin ciki na hade jin abinda tace yasa na koma na zauna tare da fara bude kulolin abincin na dauko plate na fara zubawa kamshi ya bure falon gaba daya.
A hnkali nake komai nawa yana zaune ya zuba min ido yama manta da wata hindatu a tsaye a gurin.
Yace ga ruwa da abin sha can a fridge ki dauko min na mike zuwa inda fridge din yake na dauko mai.
Tabini da ido kishine karara a idon ta taja wani dogon tsaki daidai lokacin da najuyo zuwa inda suke.
Tace karyan banza sai dai kama wallahi amma ba dai hali ba kan muje zuwa mu gani in karya na zama gaskiya ?
Yace yaushe kuma ya mike ya sauko daga kan kujera ya zauna a kasa tare da lankwashe kafafuwan shi yana cewa Nasir dake zaune yana wasa da remote cikin rashin damuwa da abinda akeyi.
Yace my friend zauna mu karya ko ka karya ne don kai dan gidsn anty ne na sani ?
Yaron ya sauko ya zauna gap da uban yace dani Amarya amma kin san wanan abincin ba zai isheni ba nida ku don angon naki ci gareshi tundai abin cin amarya irin haka ?
Tsuki taja ta mike tafice daga falon tana fadin ai mu zuba a gidan nan wallahi sai yarinya ta raina kan ta tayi data sanin shigan katsalan dan din da tayi muna.
Murmushi yayi tare da dagowa ya mayar da fuskan shi gare ni yana fadin bisimillah mana zauna muci ko ?
Nace cikin kunya daddy zanci indan nakoma dakina ai .
No no no tare nake karyawa da matana ko baki san da haka bane don haka zauna muci ko sai na baki abaki zaki ci.
Kunya ya kamani yadda daddy yake abinshi hankali a kwance cikin rashin jin kunyana da nauyi kamar yadda ni nake jin nashi.
Zama nayi tare da daukan spoon din ina dan juyawa a hankali cikin plate din abincin sai dai na kasa kawai a bakina don kunya.
Debo abincin yayi ya nufi bakina dashi yana cewa ina ganin sai nabaki zaki ci don wanan kunyan naki ba zai bari kici ba nasan kuma bakici din ba .
Oya bude baki ki karba maza karbi kici kada ki zauna da yunwa nasani sarai baki cin komai yanzu.
Zanci nace cikin jin kunya yace karbi wanan din kici haka na bude bakina yabani na hadiye da kyat kamar an bani magani naji.
Da kyat na taune shi sai Nasir shima ya debo ya mika min murmushi ya sani daddy yace.
Kinga danki ma yasan bakyaci gashi nan yana baki ai na karba na kara hadewa daga haka kuma na kasa sakin jiki naci.
Sun kan sai cin abincin su sukeyi hankalin su a kwance dankali da kwaine bai ma damu da ruwan shayin ba.
A haka har suka gama ci ya goge bakin shi yana cewa zan tafi asibiti na duba Zulfa da yamma idan nadawo zamu shiga ki gaidasu hajiya da Alhaji.
Don haka ki zauna da shiri bayan karfe hudu idan na dawo na amsa a sanyayye da Allah ya kaimu.
Ya mike ya na shirin fita nace Allah ya tsare ya kare Allah yasa a fita a sa, a adawo cikin nasaran rayuwan duniya da lahira.
Da alama yaji dadin wanan adduan yace Allahuma amin nagode kwarai da wanan adduan naki mai daraja.
Yafice ya barmu na fara kwashe kayan nacewa nasir yazo mu tafi nakai kayan na dawo na kara gyara gurin ranan har cikin bedroom din saida na gyara shi tsab komai nai mai muhalin shi don dakin gaba daya bakacewa akwai matan dake kwana acikin sa ma.
Na dawo na samu anty ta fito falo take cewa dani ai na dauka kin kwanta ki huta ne daban jiki ba ?
Nace cikin kunya anty naga part din daddy yayi daudane na tsaya na gyara shi.
Tace tana gyara zaman ta aiko kin kyauta don idan baki gyara ba ma haka gurin zai tabbata da kazantan shi.
Don dai babu mai gyarawa acikin mu nice ma danake da dan lafiya ai nakan dan gyara mai sai ko shi idan yaga abin yai yawa ya gyara da kan shi.
Mamaki naji a raina wai har namiji mai mata uku ya tsaya gyaran part din shi da kan shi haka mutum kamar daddy ga komai na rayuwa a dakin amma babu gyara.
To su may sukewa kishi haka bayan ko kara basu kawarwa a gidan saidai mace tai wanka ta fita sau goma a yini shine kawai aikin su.
Can naji tace Nasir ke fada min wai mama husna tana maki fada kun samayta a falon ke nan ko ?
Na gyada mata kai tare da cewa eh anan muka samy ta da muka shiga dazun tace kada ki biyewa haukan su su haka suke kulun cikin jan fita don basu taba zama lafiya ko a tsakanin su haka suke badubar junan su ba shirin karya sukeyi tsakanin su.
Ni dai banyi magana ba sai naji tace amma don Allah daga yau ki daina zuwa da yaran nan gurin shi idan zaki tafi don kinga abakin shi nake jin komai fa.
Nace cikin murmushi anty abinci yake son na bashi shiyasa muka tafi tare dashi ai.
Tace to daga yau dai ki bari yaran yanzu wayon tsiya ne dasu wallahi sun san komai don ba yara bane yadda kike zato.
Remoto na dauka ina kunna tv tace dani bazakici komai ba ke nan haka zaki ta zama da yunwa ko ?
Ina ma son nai mashi magana akai maki kayan abinci a part din ki don ki dinga dafa abinda ranki ke so idan kin tashi.
Don ba zai yuyu ace sai kinzo nan ba ko yaushe cin abinci shi kan shi ai wani lokaci zaiso ace kin mai wani abu idan yana bukata.
Nace anty ba sai nazo nan nayi ba ni hakan ma yayi min wallahi tace haka nake so ban son gardama fa.
Sallaman su mama Zulaine ya katse mata magana suka shigo nan aka fara gaisawa dasu.
Mama zulai ce ke fadin munzo ne muga yar aikin hindatu don Zulfa tace muna ita ta kawo mata zobo don tasan tana so tasha da rana.
Kin ga kuma ance kwayar zubar da ciki aka bata tasha don ta rantse muna ita bata sha komai ba daga bangaren ta banda wanan zobon data sha.
Ikon Allah inji anty ita hanne din ta kawo mata zobon tasha ke nan ko ?
Mama zulai tace ai har ita wanan din ta nunani tace, tace wani abu tasha shi ya jawo mata matsalan kuma haka shima likitan ya fada muna ai.
Yanzu muna son jin ta bakin ita hanne din ne kafin mu tabbatar da hakan garesu ko ?
Anty tace amma sai nake ganin kamar wanan matsalan ta cikin gida ne don haka abari mana maigidan ya dawo sai a sanar dashi kinga ai shi zai san yadda ya bullowa al, amarin ko ?
Hakane amma ai kin san wanan kishiyar taku da shegen wayon tsiya anya zai fahinci gaskiyan maganan kuwa don tun shekaran jiya muka fada mai komai amma banga ya dauki wani mataki ba akai.
Zai dauka anty tace don munyi shigen maganan haka dashi ina ganin dai bincike yake a hankali don ya gane gaskiyan maganan.
Mama tace to Allah yasa idan har yana bincike ai mu bamu da tacewa kuma sai mu kyakeshi muga gudun shi ko ?



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU IDAN KUMA KIN KARANTA DAKE DA ALLAH.

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YABI MUNA HAKKN MU AKAN KI RASHIN KARANTAWA SHINE ALHERI AGAREKI IDAN BAKI BIYA BA DON GUJEWA DAUKAN ALHAKIN WANI A KAN KI, , ,
43

Na gama kwanaki na hudu da zan yi wanda daga wanan ranan zuwa turakar maigida ya hau kaina.
Anty ce ta karbi girki bayan ni inda duk wani aikin da za, ayi na maigida nice nake aiwatar mata dashi iyakan ta ta shiga dakin da dare.
Ni kuma zaun kwana tare da yara a part dina har jinior dashi muke kwana a tare da mu.
Idan nayi sallah zan zauna na roki ubangijina Allah nakan fara gode mai da irin rayuwan dana tsinci kaina a cikin dan shi ke da masanayan yin hakan a gurin shi .
Sai kuma na roke shi da yai min kariya da tsari akan duk wani abin ki ko shedan da zaitaba lafiyan jikina da rayuwana.
Na kan zauna sosai na tsayar da duk wani abinda ke a gabana gurin rokon ubangijina akan wanan rayuwan da na riski kaina a ciki na kasancewa da mijin matar da tafi ko wace mace daraja da kima a gare ni bayan mahaifiya na.
Yau gashi na kasance da mijin ta a matsayin nima matar aure a gareshi ya Allah kada ka nufe ni da cin amanan wanan boyar taka daidai da rana daya a rayuwana.
Satin Zulfa biyu aka sallamo ta daga asibiti nan ta dawo gida ta karasa jinyan ta tana zama da mama Luba kaunan mahaifiyar su maigidan ke nan.
Da kwana biyu ya kira mu gaba dayan mu a falon inda ya zaunar damu ya fara magana kamar haka.
Ba komai yasa na kiraku ba sai maganan abinda ya faru a cikin gidan nan kan abinda ya shafi zulfa gata nan.
Wanda ba don Allah ya gyara ba da anyi sanadin fitar cikin dake jikin ta yanzu.
Kuma wanan abin ya faru ne a cikin gidan nan inda aka bata magani tasha don cikin ya zube ba tare da sanin ta ba.
A iya bincken da nayi na gano inda matsalan ya dauko asali shine daga gurin mai aikin hindatu ce hanne.
Da sauri hindatu tace hanne fa yace kwarai sai dai nayi iya binciken da zan yi nagane cewa itama a cikin rashi sani ta aiwatar da hakan don ta rantse da abinda zai kashe ta bata san ta hada wanan abin da kayan hada zobon ta ba.
Shine dalilin da yasa zan dan ragwanta mata naso na kore ta ma gaba daya a gidan amma ance na kyale ta idan halin ta ne ai zata sake wani karo.
Magana yake amma gaba daya falon ba wai mun yarda bane dole dai akwai wani abu a kasa ai sai dai halin maza baka gane gabas din su kawai.
Nan hindatu ta haufadan karya wai kazafi akai ma hanne ita dai tasan inda ta sha maganin ta kawai.
Suka fara cacan baki a tsakanin su kowa na fadawa dan uwa bakar magana ni dai ina zaune na sada kaina a kasa ina sauraren su kawai.
Muryan anty ne ke fadin tashi mu tafi Rama muna da abinyi a part din mu tana gaba ina binta a baya muka barsu nan ba musan yaya suka karasa ba.
Sai da daddy ya shigo ne naji anty na mashi magana akan hukuncin da ya yanke yake cewa da ita,
Ki sa masu ido nasan abinda nakeyi kuma akwai abinda nake son na gano ayin hakan da nayi.
Ni dai kaina a duke yake don sam idan daddy yana tare da anty ina furin balain kunyan shi nake ji.
Shima sam baya sake min fuska sai ya nuna tankar bai ma san ina gurin ba lokacin.
Har na kanyi mamakin hakan amma daga baya sai naga ai hakan ma yafi sauki da ya sake min fuska kima ya ja muna matsala ai gara hakan kawai yafi sauki.
Har girki ya dawo kaina nayi shi a dadafe ba don naso hakan ba don sam ban son zancen girki a raina.
Yai tafiya haka yasa na sake jikina naci gaba da harkokina ina zuwa school sai dai cikin katon hijjab da daddy ya sawo min har guda biyar manya har kasa.
Na dan mai da jikina ko yaushe ina manne da anty na don babu canjin fuska akaina da tai min.
Bayan sati biyu ya dawo kowa na rawan kai suna futina mu dai part din mu ba wanda ya kula da haukan su don ni haushi da mamaki ma suke bani.
Akan namiji suke wanan haukan yanzu zaka ji su anjima kuma kaga sun shirya a tsakanin su.
Ni dai na fahinci cewa ina da rauni a gurin kasan cewa dana miji don hakan da nake ba wai rashin sabo bane ko wani kawai dai hallitane min hakan.
Tun da la, asar anty tace dani naje na gyara part din daddy don nasan nice da girki ranan.
Saida gabana ya fadi haka na dauki kayan gyara na shiga part din, yadda naga an hargitsa shi ba kamar yadda na gyara ba ranan da anty zatai girkin ta.
Komai a yamutse yake ban dakin ma bai shakuwa don da gani ba a wanke shi ba.
Ai gara zulfa ace tana bedrest ne sai dai ai a nan take kwana da mijin ta, amma ita hindatu mai yaci katfin ta da bazata gyara ba.
Nan na takarkare na gyara komai na darje makewanyin don nafi jin kyamkyamin shi sosai.
Gurin ya koma neat sai kamshi ke tashi yana kyali da dadin shaka komai nayi mai muhalinshi.
Ban dade da fita ba ya shigo part din tun a falo ya fara ganin sauyi don ya shaki kamshi maidadi.
Ya sauke ajiyan zuciya a fili yana fadin Allah yai wa wanda duk yai aikin nan albarka dama da safe da kyat ya iya yin wanka a bayi don kazantan shi.
Duk, lokacin da akace girki ya dawo kaina har kuka sai danayi a daki ni kadai ganin banda niyan zuwa gun daddy da dare anty ta matsa min da na shirya dole na tafi tun takwas na dare ta gargadani zuwa gurin shi.
Da kuka na na karasa falon ba laifi nayi kwalliya na cikin material mai ruwan milk da flower ja a jikin shi.
Na dora hijjab a sama nai mata sai da safe na wuce zanin da zan kwanta da rigar barcina duk da nasan ba tasiri rigan zaiyi ba acan amma dai na dauka na tafi dashi.
Nai sallama yana zaune idon shi akan tv sai wayan da yake yi jin sallama ya sashi ya dan dago kan shi yana kallona har na karaso kusa da inda yake zaune.
Durkusawa nayi ina mashi ina wuni daddy hannu ya mika min alaman inzo inda yake.
Ban musa ba na nufi inda yake ya kamo hannu na ya zaunar dani gaf dashi hakan naji wani nauyi da kunyan shi ya kamani.
Sai da ya gama wayan shi wanda na fahinci wani harka ne na business yake magana akai.
Ya sauke ajiyan zuciya tare da fadin amarya duk ni keda wanan kwalliyan haka ?
Kaina na dukar kasa don nauyi da kunyan shi da nake ji ya rufe ni amma shi ko a jikin shi hakan.
Yace sai dai kinyi mantuwa don wanan hijjab din bai dace ace kinzo min nan dashi ba don baida amfani a falon nan.
Jiki a sanyayye na kwabe hijjabin a hankali, naji ya sauke ajiyan zuciya yana fadin may zai sa ki boye min wanan kyakkyawan suran naki Rahama ki daina min rowan jikin ki please.
Tashi ki sauko min da abinci na nan don ni nafi son naci a kasa na saba da hakan tun ina karami a gida haka mama laraba ta koya min kin san ni zance rabin rayuwana a gunta nayi shi.
Shiyasa kike ganin ina matukar mutunta mama don duk wani tarbiyan rayuwa itace tabani shi gashi kuma ina amfana da abina a yanzu.
Na aje abincin tare da zaunawa na fara zuba mai baiyi magana ba haka yasa na dago ina tambayan ko ya isa.
Yace duk yadda kika zuba min ai cinyewa zanyi tunda shi kike bukatan naci.
Mamaki nake a raina wai ashe daddy haka yake amma idan ka gan shi a waje zaka dauka ko da matan shi bai maganan uffan dasu.
Amma ashe ba haka abin yake ba a badini sakewa yake da matan shi sosai fiye da tsanmanin mutum.
Ya fara ci inq zaune a gefe ina wasa da yan yatsun hannuwa na naji yace dama ina son magana dake.
Haka yasa na dago kaina da sauri na dan kalleshi naga abincin shi yake ci hankalin shi a kwance.
Sai da yai kamar loma biyu ne yace dama ina son tambayan ki wani sana,a baba yake yi a kauyen nan ne ?
Sai da naji gabana ya fadi to ni may zance ne yanzu sai dai na fadi abinda na sani kawai akai.
Nace ni dai na taso naga yana zuwa cin kasuwan kauye ya na samun abinda zai ciyar da iyalin shi kullun.
Yace nasan da hakan wani sana,
Showing 183001 words to 186000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62 Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153