yana mamakin wanan wani irin kiyayyane haka har da lafiyan mutum zai hada ?
May ya hada Rahama da hajiyane haka wai wanan abin yai yawa Raliya yace a ranshi don ba Raliyan ba kowa yanzu bata gani in ba Rahama din ba.
Sai dai kuma ko ita Raliyan ai bata tsira ba tunda tace tana barin ta da yunwa ta fita ko kuma a bata abinci ba dadi.
Yace kai hajiya ho Allah dai ta bar min ke naita ganin ki ko yaushe muna kwasan wanan draman naki.
Ya dawo da yamma rana daya suka dawo da zulfa sai dai ta riga shi isowa garin ita don har ta manta tayi tafiya ko.
Muna zaune da ita ya shigo falon mu muka shiga gaida shi yace da zulfa din ke kinga daman dawowa ai na dauka can zaki zauna kuma.
Tace kai kaji yaya in zauna gadin gida ko may ka kwaso mata ka gaba daya da yara ni zaman may zanyi can yace wa sanan maki nace ai dole daddy yai fushi anty daga zuwa kin samu wuri kin zauna in ya bude ido ba uwar gida ran gida a gidan.
Tace kaji Rahama dai da wani zance can muna dai uwargida ko ga amaren gida wake ta wata uwargida can kuma.
Mu dai raka ko a hakan mu samu dai a laba mu muci arzikin ku kawai tace su mama na gaida ku yace kin barsu lafiya dai ko tace eh.
Ashe hajiya suna nan har yanzu jikin ya kiya kuma sai jiya dana shiga ne Alhaji ke cewa dani ta samu wuri tai zaman ta nan nasan ba su dawo ba ashe.
Yace kai Alhaji koni ai ya kirani yana fada wai nazo na rike mai mata naki turota ta dawo an barshi daga shi sai yara a gida.
Nace ba a ga likitan bane har yanzu wai Alhaji ai yana da gaskiyan shi tunda ya tsufa dole yana son mai taimaka mashi kusa dashi ai.
Ya dan ja tsuki yace wani likita ba sun tafi dazun ba ance su ganki wanan algunguman Raliya nasan ita ce ke zugata ai.
Zulfa tace ashe suna ta ke nan kaima ka fara sani halin makirci na ta ke nan dai.
Ta maka mata harara yace dani ke taso ki hada min ruwa na watsa ko zanji dadi don nice da girki a ranan da ya dawo.
Sai da ya dan jima da fita na mike nabi bayan shi don hada mai ruwan wankan ca ya rike ni ban fito ba sai da nazo cewa yara su rufe kofa na koma.
Da safe na tafi wurin aiki ina office zaune ina tsaka ga aiki file din hajiya yazo table dina sam ban kawo cewa ita bace don ban san zananen sunan ta ba ma ni.
Nace su shigo sai gasu da Farida don tare suka zo dashi amma shi ya tsaya waya lokacin yace su shigo gashi tafe don dare jiya abin ya matsa mata sosai.
Kaina a duke yake lokacin ina rubutu sai da naji tace to babban likita gamu mun shigo sai a duba mu na dago da sauri na kalle su tare da mikewa tsaye.
Nace hajiya kune ashe dama ba a ga likitan bane ko may da aka turo file din ki nan wurina ban san kece mai sunan ba dana ce ki bari na dubaki ma a gida ai.
Sai ga daddy ya shigo office din yace ok sun shigo may aka ciki sai nai shiru can na dago kai nace hajiya yaya kike jin jikin naki ne ?
Yace ki fada mata komai don kinga na shi na karshe cikin mutum ukun da aka tura mu mu gani.
Na jawo takarda ta na fara rubutu akai sai farida ne ke min bayani cikin rashin fahinta amma ni na fahinci komai.
Na shiga jefo mata tambaya tana bani amsan abinda nake son ji na rubuta komai na dago na cire glass din dake idona nace gaskiya daddu sai mun cire mata mahaifa don idan ba haka sai na dan sasauta murya na kasa nace zai haifar mata da zuban jini da zai iya sanadin ta.
Tace a hasale tare da min dakuwa Rahama karbi nan tun baki isa saka dan kanfaiba rabona da jinin al,ada kinji.
Abin ya bani dariya amma sai na daure nace hajiya shi wanan din ba jinin al, ada bane jini ne na ciwo zai haifar maki ya koma cancer na mahaifa don haka don Allah hajiya ki daure ai maki aikin na tun kan matsala ta shigo.
Sai jikin ta yai sanyi tace na shiga uku ni hauwa,u yanzu ba wani maganin da zan sha ba sai an taba ni ba yar nan.
Nace hajiya haka shine sauki ba wai sai yaran mata kanana ke samun wanan matsakan ba harda tsofin da wanan matsalan ya sama ta faruwa dasu haka.
Nace hajiya kada ki ji komai wa yanda za suyi maki aikin kwararun likitoci ne don sun san aikin su cikin yan kwanakin da baikai sati ba zaki mike insha Allahu.
Jikin ta yai sanyi sosai ta juya gun shi tace yanzu yaya za, ayi yace hajiya aikinji abinda ta fada kiyi hakkuri a rabaki da wanan abin don Allah.
Nace hajiya taso ki hau gadon can mu gani ta mike da kyat jiki ba karfi ta hau gadon na sake labule na dauko abin awo ina dan duba maran ta daga kasa kadsn har nakai inda ciwon yake mata nace na ne yake tokare maki ko tace na ne kedai.
Nace idan ya gama zaiyi ruwa shine zai jawo maki wanan zuba jinin nan gaba kadan tun da har ya fara yi maki hakan.
Na kamata ta sauko muka dawo inda suke nace dashi daddy aiki zamuyu mata insha Allahu abin zaizo da sauki don haka zan bari har a aje magana sai a saka ranan da za ai mata aikin ko ?



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , , ,
98
Ba don hajiya taso ba aka tsayar da ranan da za ai mata aiki don gaskiya ya fara son sako mata jini ya koma servicer cancer mata.
Take hankali ya tashi don har ta koma Kano sai gata an kwaso ta ragai ragai an dawo da ita ba dadi ba bata lokaci nai setting din yi mata aiki a take.
Da safe zamu shiga da ita don haka da daren nan muka bata gado a asibitin mu inda za ai aikin.
Fatima da Aisha sun zo tare da ita don Farida dama tana nan wurin Raliya ta tsaya bata koma ba tana taya ta kishi.
A taya kishi mana don ko ga maciji batayi da mu ko wani nawa sai kule kule da makircin da suke yi ko yaushe a gidan.
Don ni har ya kai nai mata kashedi a kan dukan min diya da takeyi da zaran yaro ya fita yanzu zai dawo da kuka yace gwago Farida ce kamar yadda muka koya masu kiran ta.
Ranan ta daki Abdul har bakin shi ya fashe ga shedan mari da taiwa yaron yai kukan wahala har yai barci don wahala.
Koda na dawo na samay shi a falo yana barci jikin shi yayi zafi nake tambayan may ya samay shi ne ?
Sai Amira tai shiru na sake tambayan su ina a tsaye nace ba tambayan ku nake yi bane kun kyale ni haka ?
Sai Aisha ce tace dani wallahi gwagon shi ce ta dake shi har da mari sai da ya fadi bakin shi kuma ya fashe takuma hana yin shi kuka.
Take naji raina ya baci na juya zuwa part din nasu tana zaune ta tsefewa yar wurin Raliya kai na shiga da sallama na.
Suka amsa min ciki ciki na ce cikin rashin damuwa yau kuma Farida may ya hada ki da dan ki haka kikai mai wanan irin dokan haka ?
Tace a tsiwace ko kinzo ki rama mashi ne don naga kamar kinzo a fusace ko banda hurumin duka dan kine kike nufi don suna diyan gwal ko ?
Nace wani irin magana kike min haka dukan ne dai irin haka bai min dadi ba kawai tace to na dake shi ba kuma zan fada maki dalili ba sai naji shaka da makura.
Nace to ki sani kiyi na farko kiyi na karshe tunda abin naki da niyya ne kika yi mai wanan irin dukan haka har may Abdul ya sani da zaki dakan min shi haka ?
Tace dama bamu san asalin kolo bane da sai yace muna ai shi daga masar yafito har kewa da zakiyi min iyakan dukan dan dan uwa na.
Nace da ita dan uwa dan uwa fa kikace sai dai ni bana jin lissafin ki daga cikin yan uwan nashi kinga kuwa ban sani ba ke nan ashe ?
Kaji banza waike kina ganin kin zama wata tsiya yanzu ko kada ki manta ni Farida na san yadda kika shigo gidan nan da yan tsumakaran ki kina rabe rabe kafin kiyi wayau ki cin amana ki kwacewa mata miji.
Nace wanan kuma karya ne ki tambaya kiji ni Rahama ban da ragga balle tsunma a tare dani ko da nazo gidan nan don ni ba mai kashin tsiya bace kin kuma gani kin sani.
In ma har cin amana nayi aure na da daddy ai kafin nayi kece kika so yi keda har yau son auren shi kikeyi keda ke zuwa wurin mata tai maki goma na arziki.
Don ki aure shi kika kashe auren ki gaki nan har yau kin ki aure kina zaman jiran tsanmani don hauka duk da kuwa yar uwarki na cikin gidan amma kin rufe ido don kwadayin abin duniya sai shi.
Tace ke akwai wanda yakai ki kwadai ne daga ganin sarkin fawa sai miya yai zaki ina sai faman haihuwa kike ke a dole ki cika gida da shegun yayan ki masu kama da diyan kwara.
Wama yasani ko wanan farin ba surki kikaiwa mutane ba kina labawa da wasu diyan kwara can a gefe.
Nace ban da wani shakka a nan don dani dake ansan wacce ta rike darajan ta har gidan mijin ta diya kuma yanzu na fara haifosu a gidan nan sai nai dozen.
Mara mutunci kawai wacce bata san ciwon kan ta ba sai kwadayi da makirci don son abin duniya da kika sakawa kan ki ke da daddy kuma sai a lahira idan ana aure in kina da rabo ya aure ki can din ban sani ba.
Ina fadin haka na juya na barta tana jefo min zagi ina jin ta ina shiga hayaniyar mu ya tayar da zulfa dake barci take cewa dani wai yaya akayi ne raina ya baci ban iya magana ba a lokacin.
Nace ba komai kawai na juya sai Aisha ce naji tana fada mata abinda ya faru ta nufi yaron tana taba jikin shi tare da cewa nifa naji kukan shi a cikin barci na dauka ko dashi da yan uwan shi ne ai.
A daki ta samay ni na fito wanka lokacin na dan ji sanyi a raina nake mayar mata da irin bakaken maganan da muka fadawa junan mu.
Tace a, a abin na farida hauka ne ko rashin wayo yaya zaka doki yaro har da mari irin haka yaro ma kamar Abdul don Allah dai ?
Nace ai in halin tane gobe ta kara dukan min yaro ta gani bayau ba tun zuwan ta gidan nan abinda takewa yaran ke nan wallahi ina dai hakuri ina shanyewa ne kawai don na fahinci da manufa take duka su tunda basu kadai bane ai yara a gidan.
In don ta nice da daddy ba zaiji maganan ba gaskiya tunda ta fada min na fada mata an wuce wurin ke nan.
Amma yana dawowa da dare Zulfa ta samay shi da maganan duk yadda mukayi ta kwashe ta fada mai ya taso zuwa part din dina ya samay ni zaune na rugumay yaron a jikina na shafa mashi metholater a wurin ina bashi magani.
Su Aisha na ganin shi suka fita daga dakin yace may yaiwa Farida tai mai duka haka ba tausayawa nace ban sani ba ni dai na dawo na samay shi a haka nai magana kuma tace ban isa ba.
Yace shine har da bakin ta zata zargan min diya wallahi duk yadda nake da mutum bana daukan irin raini haka a gabana ya daga waya ya kira mama laraba yana fada mata duk yadda mukayi.
Mama tace dama na sani sai da na fadawa yaya may yasa ta barta can don nasan ba a kwashewa lafiya da ita in dai Farida ce .
Tursasata sai ta fada ma dawa diya ka sukai kama don in ma wani taji ya fada a sani yarinyar banza kawai mara hankali da tunane.
Bai yi magana ba ya juya ya na fadin ku samay ni falo yanzu ina jiran ku ashe bamu kadai bane a falon duk kowa ya kira a cikin mu.
Na shigo falon fuska ba annuri ina saye cikin dogon riga dinkin yan ethopian duk suna zaune a falon sunyi shiru gaba dayan su na shigo.
Wuri na samu na zauna nima ina sauraren abinda zai wakana a wurin can yai gyaran murya tare da cewa na dawo gida yanzu Zulfa ta samay ni da maganan abinda ke faruwa a gidan kan Abdul tsakanin uwar shi dake Farida.
Sai kowa yai shiru can naji muryan Farida tana cewa wai fa yaya don kawai na daki dan ta kowa yake da suna ma oho ?
Sai kawai tana dawowa ta samay ni da cin mutunci tana cewa wai na bar dakar mata yara akan may Rahama zata ce wai kada mm a tsawata wa yaran ta ita waye ?
Sai yace ita matata ce kuma dan tane kema kin fada yanzu da bakin ki cewa don kawai kin dakar mata da.
Yace ke Raliya ina son ki fada min may ya faru tun daga farko abinda ya faru.
Sai tace wa ni nikan ina ruwana da zancen su tunda ba dani akayi ba balle na saka kaina a cikin maganan su.
Yace tambayan ki nayi ba wai jawabi nake son ji daga gare ki ba, sai tai shiru ta na murmushi kawai yace uhumm ke fa nake saurare kada ki bata muna lokaci a nan.
Ganin ba wasa a fuskan shi yasa ta cewa a, a muna zaune ne sai yaran ke wasan ball a baya sai suka daki window side din mu.
Shine ita farida tai masu fada tace kada wanda ya sake wasan ball din to ban san yaya akayi ba shi Abdul din ya buga ball din.
Sai naga ta fita zuwa wurin su can naji kukan yaron ita kuma ta dawo take cewa wai yaron nan na Rahama karami ne ya sake buga ball din shine ta dake shi.
Hindatu tayi mata magana akan don may zata dake shi a nan suke wasa kullun kuma window din ba mai saurin fashewa bane.
Sun dai danyi maganan su suka bari sai ga ita Rahama da tadawo daga gun aiki ta shigo tana mata magana sai sukai ta cacan baki anan.
Daga karshe dai bayan sun fadawa juna magana sai Rahama din ta wuce zuwa shiyan ta ta bar mu a nan, don har ita Rahaman nacewa kada ta sake dokar mata diyan ta.
Jin haka na dago kai da sauri na kalli Raliya din don na fahinci ta fadi hakane don daddy ya fusata yace don may zan hana yar uwarshi yiwa diyan shi fada.
Yace ai gaskiya ne don ban taba jin Rahama tayi fada ba akan yaran ta a gidan nan sai yau don ko abin yayi muni mari Farida kewa ya mareki ga kuma bakin yaro yaro ya fashe har ya kumbura haka ?
Gaskiya Farida ina ganin gara ita Rahama ta iya kawaici a kan yaran ta ni gaskiya ban iya ba ko kadan don yaran nan amana suke a wurin mu.
Ana raba yaro da wasa ne ko may shin idan ma basuyi wasa a gidan uban su ba sun sakata sun wala a gidan wa ake son su fita suyi wasa.
Ko mata na gasu nan
dukkan su hudu nan
ko uwar yaro ne kuwa bata isa ta hana min da yara wasa a gidan nan ba don kuwa don su na gina gidana Idan basuyi wasa a nan ba sai a makwabtane zasu tafi suyi ko may ?
Uwar yaro ma bata isa ta dokar min yaro ba balle wani can daban sai ta dago kai ta kalli dan uwan nata sai kuma ta dukar da kan nata a kasa.
Yaci gaba da cewa ni bama wanan ba a cikin musayan harshen da kukayi naji ance kin ce yaran Rahams suna da surki wai diyan wani kwara ne ko may ?.
Ko zaki fada min dalikin ki na fadin haka ?
Kuma ki sani wallahi wallahi idan baki da hujja ga fadin haka sai na dauki mataki mumuna a kan ki kuma ki sani kowa ma ya sani.
Rahama da kike gani amatsayin bazawara na aure ta sai dai abinda na sani a kanta duniya ba su san shi don haka
Showing 402001 words to 405000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135 Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153