nema mata daban ?
Ya dago kai da sauri yana cewa wa haba mama ta dai zauna nan ida kowa yake ciki itama don kaita wani gida zai kawo min zargi ai ga sauran matan .
Yace hakan dai da kikace dama shine shawara na don ba kowa a shiyan zanyiwa masu gyaran guri magana suzo su duba asa mata duk abinda ya dace aciki.
Tace da zakaji sai ince gaba dayan su ka canza masu tsarin dakunan don kada su zarge ka akan hakan da za, ayi in yaso ita da take amarya sai a gyara natan yafi kyau zaifi.
Yace yadda kika gani mama zanyi magana dasu suzo su duba su ga abinda zasuyi akai.
Mama tace shi batun lefe fa yace yana hannun Saade wanan mun riga munyi magana da ita kafin ta tare sai a saya mata komai.
Mama ta kara cewa suma wa yan nan zakai masu nasu na fadar kishiya idan kuma kudin suke so su saya sai abadu a hannun su a dai wanye lafiya dakowa yafi.
Yace ba matsala mama zan yi magana dasu naji ra, ayin su akan hakan abinda yafi masu sauki.
Sun dauki lokaci da ita tana kara bashi magana don ta tausaya ma yadda zan zauna cikin matan shi haka dani.
Yace ba matsala mama Insha Allahu zan a kula kada kiji komai zanyi adalci yadda ya dace a tsakanin su tunda duk zamana sukeyi.
Bata koma gurin mama Altine yaba da mota aka kaita gida tana cike da mamakin halin na wasu mutane da basu da ganewa.

********* ********* *********
Inna na batun komawa gida har ta mike tana kara jamin kunne sai ga yar gidan maigari tayi sallama Anty na biye a bayan ta suka shigo gidan.
Ikon Allah hajiya Saade ashe kina hanya sannun ku da zuwa gabana naji ya wani mugun faduwa jin sunan da Inna takira a lokacin.
Inna ke cewa kinga ta ashe tana nan gurin kakan nin ta nufo shiyasa bamu san da zuwan ta ba garin.
Wani ajiyan zuciya anty ta sauke a baiyane tana fadin Allah mungode ma yanzu can gida da muka je cewa sukayi ba a gan ta basu san ma tana garin nan ba ke nan.
Tace wa zaiyi zaton zata zo nan din yanzu tunda ba wai ta saba zuwa gurin su hakana bane.
Attu ta ce da ita ta shiga daga cikin daki nan aka shimfida mata tabarma ta zauna suka ahiga gaisawa dasu.
Da kyat na iya tasowa daga inda nake cikin kunya nazo na dan tsugunna a gefen ta ina cewa ina wuni Anty.
Wani kallo ta watso min fuskan ta babu sukuni ko kadan a cikin sa, take cewa dani .
Rama baki son farin cikina ashe na girgiza mata kai cikin tashin hankali alaman ba hakana bane anty .
Nasan don ni kike wanan borin da kikeyi bawai don baki son Yusuf babe babu macen da zata samay shi a matsayin miji tace bata kaunan hakan.
To Rama yau dai ayita ta kare ni Saade nice nazabi yin haka gare mu kuma nice na kawo shawaran ayi haka din gare ki.
Na dago kai a hankali ina kallon ta cikin mamakin ta da baya kare min ko yaushe naga magana take da zuciya daya dani.
Rama na fada maki ina da dalilin yin hakan danayi zan fayece maki gaskiya yanzu idan kinyi niyar taimakona ko bayan raina ne idan kinji zaki iya hakan gare ni.
Idanun ta suka ciko da ruwa nima haka nawa ko su Inna da ke tsaye da Attu suna cikin wani yanayi .
Rama nayi haka dan yau ko bani a duniyan nasan yarana da mijina suna hannun na gari a duniya.
Suna inda babu cutarwa a garesu suna inda za, a rike min su riko na fisabillillahi.
Rama na yaba da tarbiyan ki na kuma yaba imanin ki kina zama da mutum da zuciya daya kin san yakamata kin iya zama da kowa da zuciya daya.
Wanan halin naki yasa nai nazari akan haka tun bayan kazafin da sherin da Hindatu tai maki ke da maigidan naga ai kamar shawara ne tabani ga hakan .
Shiyasa na shiga nafita ga duk wurin wanda nasan maigida zan saurari maganan shi har akaci galaban shi akan hakan.
Nasan ke mace Rahama da sannu zaki samu karbu a zuciyar maigidan kada ki dauka a yanzi bawai aure so ne kukayi ba a, a aure ne da ake fatan dorewan shi cikin nasara da kwanciyan hankalin ku nan gaba.
Don haka bana son cewan da kike ke yaya zaki hada miji daya dani nasan da haka ai amma na amince da ayi din zaki koya kuma zaki iya zama dashi din.
A ban garen yara ko yanzu banda matsala dake don baki gidan jiya da yaran sun baki tausayin dan rasakin da sukayi na kwana daya.
Yau din nan da kyat na samu aka shirya su suka tafi school don shi Nasir ya ce bamai mai wanka sai ke da kanki haka abinci ma jiya kin ci sukayi wallahi.
Don haka a wanan bangaren yanzu hankalina a kwance yake a hakan don kon riga kin maye gurbina ko anan saura ta fannin maigadan mu yanzu.
Wanan sai idan kin kwantar da hankalin ki a sannu zaki fahinci komai akan shi.
Daga haka ta koma lalashi na a ban baki kowa a gurin sai data bashi mamaki da tausayi yadda take magana gwanin ban tausayi wai duk akan mijin ta na sunna take wanan maganan haka.
Yadda kuka yazo mata takeyi shiya kara karyar min da zuciya na bani ba har inna da Attu dake gurin sai da suka karya da zancen ta.
Tausayin anty ya kamani sosai na fada saman jikin ta ina cewa anty zan yi komai a kan ki indai har yin hakan shine zai zama farin cikin rayuwan ki.
Rugumay ni tayi cikin kuka take cewa insha Allahu Rahama ba zakiyi nadaman wanan auren ba don Yusuf mijine abin alfari ga ko wace mace data samay shi a duniyan nan.
Sai bayan an natsune take cewa da Attu to yaya za, a bani ita ne mukoma ko yaya za, ayi yanzu ?
Attu tace a, a hajiya dadai kiyi hakkuri ki barta har ta dan kara samun natsuwa idan kun aje ranan da zata tare kinga sai azo a dauketa akaita dakin ta kin ga haka ma gata ne gare ta don asan tana da asali kodon gori wata rana kin san mu mata ba tabbas ke gare mu ba.
Anty tace ba laifi hakan ma yayi ai ba matsala sai dai tarewan nata ba zai dauki wani tsawon lokaci ba a yadda nake so don karatun ta duk abinda za, ayi nan da sati mai zuwa insha Allahu za, ayi shi.
Anyi sallama da ita ni dai ban fito ba duk da ina jin muryan bashir ta kyauren su Attu yana min sheri ina daki naki fitowa waje naji tashin motar su suka tafi.
Nan suka bar mu inna da Attu na kara bani hakkuri na daure ko don wanan matar na kwantar da hankalina akan ta.
Inna ta tafi gida take fadawa maigidan ta ai ina gidan iyayyenta nan ta samay ni shiya ta dade hakana.

********* ********* *********
A gaji ta dawo gida don ta dade batai tafiya haka ba sai bayan tayi sallah magariba ne Gajiye ta kawo mata abinci taci tasha magani.
Daga inda take zaune ta daga kai ta kalli yaran ta suka bata tausayi yadda rashi na, na dan lokaci yasa duk suka shiga damuwa haka inga yau ace nabar gidan gaba daya nayi aure a wani gurin yaya zasu kasance masu hakan.
Tafito daga wanka ne maigidan ya shigo ya samay ta bai mata sannu da zuwa ba sai take cewa dashi haba besty yaya zanbi ma amarya na dawo kuma babu ko sannu.
Yace na aike kine wanan matsalar ki ce don ke kika zabi yin haka nikin tuna min ma dazu mama Laraba tazo gida nan bakya nan.
Da sauri ta dago tana cewa dashi Allah sarki mun sha banban ke nan da ita yace hakane.
Tazo ne wai akan tarewan wanan yarinyar tana son taji ina za,a ajeta dakuma wai maganan kayan lefe.
Nan dai ya fata mata a furguje yadda sukayi da mama Laraba din taji yace part din dake kusa da ita za, a ajeni da sauri tace dashi na dauka ai ko zaka gyara mata wancan gidan da muka fito zaifi ta sake jikin ta ai.
Yace ba; da ra, ayin yin haka ga iyalina idan zata zauna nan inda kowa yake ta zauna don ba fin wani tayi ba nakuma yi magana da masu gyaran guri zasu zo su duba part din kowa suyi abinda ya dace suyi.
Sai zancen kayan lefen da tayi zan baki kudi ki hado abindaya dace ayi idan basu isa ba sai ki fada min na kara maku.
Sam Anty bataso wanan shawaran nashi ba nace wai na zauna a part din dake kusa da nata ba taso ya kaini wani gurin da bata ganin abinda zai gudana a tsakanin mu.
Don ita kadai tasan irin taushe zuciyar ta datake yi kan wanan matsalar shine mafita ga rayuwan ta kawai harta amince da yin hakan gare ta.
Amma babu yadda ta iya shike da gidan shi yadda ya tsara dole hakan zata daure ayi shi.
Sai bayan fitan shine mama tashigo dakin dama magana nacin ta tun fitan mama Laraba gidan ta barta da tunanen matsalan may ke damun anty ne wai harta yanke wanan danyen hukuncin a kan ta haka ?
Tace da ita magana nake sin muyi Saade ni uwarki ne baki da wanda zaki iya fadawa damuwanki bayan ni yanzu ina son ki fada min gaskiya wani matsala ne ke damun ki a rayuwa har kika yankewa kanki wanan shawara ki aura wa mijin ki yarinyar da kika tayar kamar diyarki a duniya.
Maimakon ta bata amsa sai kawai ta saka mata kuka itama mama kuka takama sukayi mai isar su subiyu a cikin daki babu mai basu hakkuri.
Can cikin muryan kuka take cewa mama ina da matsala a rayuwa na wanda ba kowane yasani ba sai mijina da mahaifina.
Da sauri mama ta tsagaita da kukan ta tana sauraren yar nata tace mama wanan matsala yasa naga kafin mai rabawa ya rabani da yaran nan nai masu gata na nema masu uwar goyo na gari da ko a bayana zata iya rike min yarana.
Nasan halin mahaifin su bazai taba yarda wani nawa ya dauki yaran nan ba ya rike a gurin shi dole dai a gidan nan zasu zauna.
Zaman su da wa yan nan matan mama hatsarine babba ina rayema basu sosu ba balle ace yau na fadi na mutu.
Ganin dacewan Rama ga wanan matsayin ne yasa na yanke shawaran hada ta aure da shi ko bani raye dai yarana nada wacce zata rike min su tsakani da Allah.
Ban san kuma bayana wazai kwaso masu ba yace ta zauna min da yarana ba ban san irin tarbiyan ta ba da zata basu.
Shiyasa kikaga na zabin yin haka amatsayin madogara babba a gareni ko a bayana bazasu wullakanta ba.
Shin wai may ke damun ki ne haka kike kirawa kanki mutuwa Saade ciwo aiba mutuwa bane ko sai mai lafiya ma ya tafi yabar maiciwo a duniya.
Ki fada min may ke damun rayuwan ki Saade ta dago kai ta kalli mama da ta tsura mata ido tana son jin karin bayani dafa gareta.
Tace mama in dauke da cutan sickle da farko shi likitoci sukace yake damuna har ya zama min coronic sai daga bayan nan bayan mun koma suke ce min kuma ya koma min Cancer.
A razane mama tace bari kira min wanan balain shine fa akace ya kashe uwar ki a baya can.
Tace cikin hadiye miyaun bakin ciki mama shine ke damun rayuwana don ma maigidan yana tsaye sosai a kaina ne da kuma ita Rama dana samu ta tsaya min gurin kulawa dani sosai aida ban kaiba killa ma.
Kuka mama ta saka wiwi tana salati tana fadin ta shiga uku yanzu Saade kina da wanan matsala kike boye min shi a rayuwan ki kuka suka saka a tare ba maiba wani hakkuri a cikin su.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU DON BA A YAFE MAKI BA DABARA YA SAURA GA MAI TSORON HADUWAN SHI DA ALLAH KAN HAKKIN WANI, , , ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA ALLAH ZAI SAKA MUNA AKANKI DON BAKI DA TSORON HADUWA DA SHI KAN HAKKIN WANI ALLAH NAGANIN KI IN BAMU GANIN KI, , ,

39
Jin fitinan nasu yaki karewa sai gaba yakeyi a tsakanin su ga su mama na ta tsawata masu amma basu daina ba.
Tsam namike tsaye na gyara lafaya na da kyau tare da dan fara takawa na nufi hanyan fita daga falon daddy da su mama suka bini da ido.
Ina kai kofa naji zulfau nacewa anty idan ma kin ba da goyon baya ne ai muna haka to dake za, a fara don kowa ai yana da kishi bamu kadai wanan yakin zai ci ba a gidan nan.
Anty tace sai dai kun makara a, i don gashi an fara daku kun kasa hade fushin ku a gaban ta kuna tonawa kanku asirin zuciyar ku.
Aure ne dai anyi shi inma mutum yace iya gatse ya iya ya sara agaban yan amin aiku kuka fara furta hakan yan amin kuma suka amsa maku.
Kalaman nasu ba dadin fadi amsan da suka bata ina ficewa mama tace kun gani karamar yarinya tafiku hankali da sanin ya kamata gashi ta fice bata iya tsayawa sauraren ku.
Ina zuwa na samu yan uwana zaune a falo suna kallon tv suka ban tausayi mutanen mu na kauye akwai son kallo gare su.
Nashiga daki nan nasamu Attu da matar maigari uwargidan su inna ta zaune a dakin Nasir da Amira kwance saman gado da alama jirana suke sukai barci.
Na gaida su na gyarawa yaran kwanciyan su na zauna gefe daya suke cewa dani ga ferfesu nan da shayi Gajiye takawo kowa kuma yasha cikin su.
Attu ke tambayana injin ba matsala dai ko na kwashe abinda ke faruwa na fada masu take cewa ni nasan akwai aiki ai.
Matar mai gari Abu tace ba wani matsala ai mama idan ta iya zama dasu sai a zauna lafiya ki fita batun su kada ki biyewa haukan su don dama dole ne sai sunji zafin abin tunda anan kike zaune dasu.
Kusa da Nasir na koma na kwanta na kura mai ido kaman shi da daddy sak nake gani yau har kamar ma ya baci.
Tsakiyan yaran na kwanta kewan su na kwana biyu yana shigana a hankali.
Idanuwana suna a lumshe muryan Anty ne ya ratso kunnuwa na tana fadin a, a ashe akwai aiki kuwa yaran nan yanzu nan suka zo suka kwanta.
Mama Abu tace da ita kin san yaro ida yaga fuska can yake tun fitan ku muna nan dasu har barci ya kwashe su gurin shigowan tane ta gyara masu kwanciya ai.
Na bude idona tare da dan mikewa kadan nace sannu anty tace sai na juya ban ganki ba falon murmushi nayi na dukar da kaina kasa kawai.
Tace basu son a zauna lafiya idan ba anyi fitina ba su basu jin dadin rayuwan su ko yaushe daga magana ta fahinta sai kice zaki ba yarinya kashi shine ai ya hasala ni ai tasan halin Rama sarai.
Take tambayan babu wani abinda ake bukata ko mama tace a, a Alhamdullahi hajiya mun gode wallahi.
Dukowa tayi inda nake zaune cikin rada tace dani shirya na kai ki gurin angon ki ko ?
Da sauri na turo mata baki gaba nace kai haba anty cikin yar shagaba tace dake may kike nufi haka za, a zura maki ido komay ?
Yarinya kinzo hannu ke nan ai may za, a fasa sallah ko salati ai kinzo hannu sai ki shirya don daddy ba wasa.
Take idanuwa na ya ciko da kwalla tace daga magana sai kuka ashe akwai aiki kuwa Rama.
Kwanta gaki ga mutanen ki ai ba yau ba sai baki sun tafi ai mu fara two two days dai ne aka tsayar da magana idan kin gama Amarcin ki yanzu su mama suka yanke hukunci don da wa yancan sunce sai dai ayi one one day yadda muka saba abaya.
Jin ta kawai nakeyi harta gama tai muna sallama takai kofa nace anty ta juyo nace maganin kifa ?
Tai murmushi tace ai dole insha Rama yau yadda nagaji din nan tun safe ban zauna ba fa sai dai gobe muyi maganan komai idan baki sun tafi.
Washegari da safe sai ga anty a dakin ta shigo Gajiye na biye a bayan ta da jakkar bako.
Ta samu guri ta zauna ina shafawa Amira mai ajiki nan na shiga gaida ita take cewa da mu.
Attu ga maigidan nan zai shigo gaida ku don zaiyi tafiya ne yau tafiya ya kama
Showing 159001 words to 162000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54 Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153