kawa ruwan ta ta tofa ciki kawai akwai hali dama can.
Mun dai tattauna sosai da ita tana kara koya min dabaran da kuma yadda zan zauna a cikin kishiyoyi na zamani .
********* ********* *********
Horn ake a kofan get maigadi ya taso ya duba yana ganin motan matar da maigidan yai mashi kashedi ne akan kada ya kara bude mata get idan tazo gidan .
Tana ganin shi gashi sai faman horn take ya bude mata amma yaki dole tafito daga motan ta cikin hasala ta nufi kofan tana fadin kai wani irin dan rainin wayo ne kana ganin kana kuma jin ana hirn bazaka bude wa mutum kofa ba ?
Yace na jiki na kuma ganki sai dai umurni ne aka bani akan bazaki kara shigowa gidan nan ba tace wani dan kazan uba ne ya haka wanan umurnin a kaina haka.
Yake cewa da ita maigidan ne yabani wanan umurnin a kan ki don haka kibar wurin nan kagin na kira maki yan sanda.
Tace har ni akewa barazanar kiran yan sanda wayan ta ta ciro takira Saade take fada mata abinda maigadin yai mata take ran Saade yai matukar baci sai gata tafito a fusace daga cikin gidan.
Ta nufi get din tana fadin malam musa rainin wayo ne yau kuma akaina ko may ko kana nufin kabi bayan Gajiye ne kaima ?
Yace hajiya ba hakana bane maigidan ne ya umurce ni da yin hakan kuma yace idan ta shigo gidan nan a bakin aikina wallahi.
Can ta fita suka ga juna da ita sun jima har maigidan ya dawo ya samay su a wurin ya shige ya barsu yasan malam musa ya fake aikin shi ke nan.
Da yamma anty ta shirya takai karan daddy da kukanta gurin mahaifinta ya daga waya ya kira daddy din yazo ya samay su anan.
Bai dauki lokaci ba ya iso aka kirata tafito nan takawo maganan da tazo dashi ra kara maimaitawa a gaban Abba da daddy din.
Daddy yace tabas shiyaba malam musa maigadin shi wanan umurni don Falmata ba matar arziki bace.
Yace tun baya sun taba samun wanan rikicin akan ta tun kafin suyi aure da kyat ya samu ya rabasu.
Sai gashi kuma yanzu ta sake dawowa cikin rayuwan su da manufanta akan su inda ta dawo da tsigar tarwatsa mai farin cikin gidan shi ga bakii daya.
Yace Abba na rasa ko Saade wata irin yarinya ce ita da bata da fahinta ko kadan wanan falmatan sam bata kaunar ta da alheri amma ta kasa fahintar hakan ita.
Gashi ta cusa mata mugun halin banza a rayuwan ta har takai ga zubar da mutuncin ta ga abikiyar zaman ta da suke zaman lafiya a tsakanin su.
Yanzu hakka Abba Rahama bata gidana yau kusan kwana biyar ke nan na tafi duk inda nake zaton zata tafi ban samay ta ba can.
Nasan kuma tayi hakane don ta nisanta kanta da mu don irin maganganun da taji Saade ta furta a kanta ranan.
Abba yace subbahanallahi yanzu ina yarinyar mutane ta shiga ba a sani ba shine kai kuma bakazo ka fada min ba a bincika ko zaa ganta.
Ya juya gurin Anty yana cewa kin gani kinga iri abinda kika jawo wa yarinyar mutane da kika dauko amana yanzu may gari ya waya akan wanan hadin ?
Kina ganin wanan yarinyar zata kara ganin ki da daraja a idanunta ko may tun da kin zubar da kimar ki a gareta ko ?
Ta dago kai cikin nadama tana cewa ni wallahii Abba ban ma san bata gidan ba tsawon wanan lokacin haka ?
Yace ina zaki sani kin dauki mugun abu kin sa a ranki wai ke kishi baki ji kunyar fadar cewa baki san yarinyar nan bata gidan nan ba tsawon lokaci haka ?
Har kina nufin kin manta da irin dawainiyar da yarinyar nan tayi na jinyar ki ko may ke yanzu kina ganin ita wanan da kika dauki amanan kan ki kika mikawa zata iya maki abinda wanan yarinyar tai maki a rayuwa ni nasan akwai abinda mijin ki ya sani yake boyewa akan wanan kawar taki amma ke hauka ya hanaki ganewa tai maki hudubar shedan kin hau kai kin zauna.
To ki sani mudfin kikace bazaki bi umurnin mijin ki ki zauna lafiya da kowa ba zamu raba gari dake baki fatan mu rabu lafiya dake ke nan .
Hawaye ne ya zubo mata take cewa don Allah Abba kayi hakkuri insha Allahu zan gyara ba zan kara wanan rayuwan ba Abba .
Yace yanzu ai zabi a gareki duk inda kika san yarinyar mutane ta shiga maza ki nemota a garin nan don ba zaki maidani mutumin banza ba.
Abamu yarinya don darajana amma yanzu kizo ki tsiro wa mutane shegan taka irin haka ?
Nan dai suka dawo gida har lokacin ba wani shiri a tsakanin su kowa najin dan uwa a ran shi.
Tana fita bata tsaya ba ta shige part din ta kawai ya bita da kallon takaici shima ya shige nashi wurin.
Yana shiga wayan Zarah na shigo mai ya dauka da sauri bayan sun gaisa take tambayan shi babu wani labari dai har yanzu ko ?
Yace wallahi Zarah ba labarin komai don har garin su na tafi amma bataje can ba ina dai sa rai da tana nan cikin garin akwai inda ta boye kawai.
Sukai sallama ta kashe wayan tana kashewa kirana na shigo mata da saurin ta ta dauka tana cewa Rahama kina inane haka ?
Rahama ina kika shiga duk kin dagawa mutane hankali don Allah ina kike yanzu wai ?
Nai murmushi nace haba Zarah baki ko tsayawa ki tambaye ni zaki shiga tambayana haka ina nan inda nake mana.
Munyi magana da ita nake fada mata tazo gidan anty Amina ta samay ni don Allah kada ta fadawa kowa ko ita akwai maganan da nake son muyi ne shiyasa nakirata.
Bata bata lokaci ba sai gata gidan dariya muka shiga yi mata tace amma anty Amina baki kyauta min ba yanzu ashe Rahama na gurin ki baki fada minn ba ?
Tace alkawari na dauka akai don haka babu yadda zan fada maki hakan kin ga na karya alkawari ko ?
Harara ta watsa min tace to yanzu ke may kike anan da kika bar dakin ki ?
Nace abinda kikaga inayi mana tace wallahi kin dai ji kunya Allah kuwa Rahama yanzu akan kishiya zaki bar dakin ki da mijin ki ?
Kin bar mutumi bawan Allah duk ya haukacewa mutane an rasa gane kan shi duk ya tsayar da aiyukan shi akan ki.
Nace yadai so ne amma ai bani kadai bace mace gare shi ke gara na bar mashi matan shi ko za a zauna lafiya yafi min.
Kin dai san daddy ba zai taba sakin ki ba batawa kan ki lokaci kawai kikeyi anan in zaki koma dakin ki ki koma tafi maki.
Anty Amina tace abinda nake dafada mata ke nan kullun wallahi tunda tazo gidan nan kishiyar may can kowa tashi ta fisheshi mana ba shike nan ba amma ita taki yarda.
Munyi magana dasu sosai amma basu shawo kaina ba daga karshe anty ke cewa dama kiran da mukai maki test muke son yi shine tace ke zaki iya koba abin yi yanzu dau dan duba min ita please ko maganan ku zaizo daya da nata.
Da sauri ta dago kai tana kallon inda nake tace ku fada min dan Allah may ke gudana ne wai ?
Yanzu dai dubata mugani please da sauri ta mike zuwa inda nake ta jawo hannuna ta dan rike kamar mai nazari can ta dago tace two months da kwanaki Rama ?
Na runtse idona a hankali ta jawoni da murna a jikin ta tace Allah mun gode ma yan bakin ciki kunyi kunya wallahi.
Bude bakin ki mu gani na bude mata duk wani abinda ya dace sai da tai min duk da nima na san dashi.
Yan zu may ye abin yi ta tambaya tana kallon anty Amina don taji may zatace da ita din .
Kunga wanan matsalan bai san dashi ba nace ba wanda yasani kuma dawowan shi daga chaina ne nasan na samu cikin nan don ga lissafina haka din ne.
Mun dauki lokaci tai muna sallama don dare yayi a lokacin ta tafi tun a hanya ta kira daddy din wanda ke zaune tare da Zulfa a falon shi.
Bayan sun gaisa ne take fada mai cewa daddy yanzu daga wurin Rahama nake tana kuma lafiya a inganttacen wuri.
Mikewa yayi ya ma manta a gaban Zulfa yake yake cewa tana garin nan ke nan tace tana nan daddy a gidan wata kawar mu take zaune.
Sunyi magana sosai sukai sallama yake cewa da ita gobe zai shigo ya samay ta yaji komai.
Ranan yayi barci kwanciyan hankali don yasan ban bata ba ke nan sai dai har lokacin anty tana bashi mamaki sosai.
Nayi kyau na kara murjewa dani dan dan cikin dake ajikina kyauna ya kara baiyyana duk da ba komai ne nake iya ci ba sosai.
Muna zaune da Anty Amina a falon ta mukaji an dana bell din gidan hakan yasa muka san anyi baki ke nan.
Ta tashi taje ta duba na jawo hijjab dina na saka hankalina yana gun tv ina canza Chanel sai kamshin turaren daddy ya daki hancina.
Da sauri na dago kaina mukai arba da shi yana tsaye saye da coth baki ya kura min ido baya ko kiftawa.
Inda Zarah take na kalla cikin bacin rai sai ta ware min hannayen ta alaman ina ruwan ta ita.
Bissimillah zauna mana Alhaji inji anty Amina take cewa dashi hakan ya samu wuri ya zauna suka fara gaisawa dashi.
Can ya juyo inda nake yace Rama yaya akayi kika zo nan bada sani ba kika zauna shiru nayi mashi kamar badani yake magana ba.
Yace bakiji may nake fadi bane halan dake shiru kowa yayi a falon can anty Amina ta mike ta shige tare da kiran Zarah tabi bayan ta.
Tashi yayi ya dawo inda nake zaune yana batun rugumay ni nace cikin wani irin murya dont dear touch me , kaje kaji da matan ka please ?
Murmushi yayi yace kina hauka ke nan kema kin shiga shirmay sauran ke nan tunda har kika bari shedan ya shiga zuciyar ki ya samu wurin zama.
Ba wani shedan sai gaskiya kayi min abinda suke so a zauna lafiya bazanyi sillar shiga hakkin kowa ba a rayuwana in wargaza mata farin cikin ta bayan irin halarcin da tai min a baya.
Ke kika san wanan amma ita wacce kiie son musguna min akanta bata ma san kinayi ba har yanzu.
Yin haka shi zai kara tabbatar da hasashen ta a kan ki harta dauka gaskiyane abinda take zargi gareki.
Ni ban taba zuwa gurin boka ko malami ba don na cutawa wani balle in kai ta ai mata sheri.
Wanan ba magana bane ki tashi mu koma gida don banga amfanin zaman ki ba anan yanzu.
Kaine baka gani ba ni kan nagani ba sai angani ba zaa ce ga aibuna kuma a gidan gida dai ne na bar masu abinsu na kuma bar masu mijin su a zauna lafiya.
Murmushi yayi ya mayar da abin ma wasa gareshi duk yadda yaso na sauka naki yarda haka ya tashi ya barni a gidan bai tsaya ba sai wurin Abban anty ya sheda mai halin da ake ciki dani.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,
62
Duk yadda daddy ya dauki abin da sauki sai yaga ya fara wuce lissafin shi don haka gidan Abban anty yaje ya fada mai komai washe gari da yamma sai gasu a gidan anty Amina tare.
Duk nauyi da kunyan Abban ne ya kama ni sosai dan zaman da mukayi dasu don sulhu sai na kama yi ma su kuka ina rokon Abban da suyi hakkuri su bar ni don Allah amma ni bazan koma gidan daddy ba kuma na barshi har abada.
Ran daddy yai matukar baci sosai Abba din ne yai abin manya yace dani to Rahama in banda abinki ai ba zamuyi maki dole ba ko ?
Ni da na dauka a matsayin uba nake gare ki a garin nan tunda a dalilin ya ta kika zo nan kuma ke din kin dauki ni tankar mahaifi a gurin ki.
Ashe abin ke ba haka yake ba gun ki tunda har zaki iya samun matsala ki ketare ni kizo wani wajen ki boye kin tayarwa mijin ki da hankali haka ?
Sai a tunane na yadda nake daukan ki yarinyar mai kaifin hankali na dauka ko a bayan raina bazaki taba watsar da iyalina ba ki guje mu.
Ko kin dauke ni mahaifin kishiyar ki ke nan kuma ba uba da nake ganin na zamo maki ba in baki sani ba yau ki sani ga mijin ki nan shi sheda ne.
Iyayyen ki don ni suka bada ke gun Yusufa batare da sun yi wani shakkan yin haka ba ga auren ku amma sai gashi matsala ya faru kin ketare ni kin zo wani guri na daban kin zauna.
Cikin kuka nace don Allah Abba ka yafe ni kayi hakkuri nayi kuskuren yin hakan da nayi a lokacin tunanen haka baizo min ba a raina.
Kuma a yadda anty ta nuna min Abba ko gurin ka na tafi ina ganin zata nuna min don ta nake zaune da kai.
Yace na fahince ki Rahama amma idan har kin dauke ni Uba ina son yanzu ki tashi ki koma gurina duk abinda zamuyi muyi shi a can din a gidana.
Haka kawai zaki min nasan kin dauke ni a matsayin mahaifi a gareki yanzu shiru nayi ina kuka a hankali.
Yace in banda abinki Rahama kin taba ganin inda akaiwa mutum dole idan kin ce kinayi sai na mayar dake idan kuma bakyayi babu dole ga zama ai.
Tunda sun kasa rike min ke akan amanan da muka basu basai su bani abina ba na rike ki amana ni don mahaifa basu gazawa da dan su ko yaya yake kuwa.
Wanan kasan da Abba ya tula min yasa na kasa ketare zancen shi na ce Abba kayafe ni na amince da nakoma gurin ka amma kuma ina tsoron abinda anty zata ce idan taji ina wurin ka kuma.
Wanan ma da akayi da yardan ta da amincewan ta tace na cuce ta balle yanzu taji cewa na koma hannun ka zata dauka ina son in mata wani sabon makirci ne kuma again.
Anty Amina tace ni a ganina da kikoma gidan Abba din da zama kiyi hakkuri ki koma dakin ki tunda Abba yazo da kan shi Rahama ko don condition din da kike ciki kina bukatan bedrest da kwanciyan hankali.
Da sauri daddy ya dago yana cewa bata da lafiya ne ko may tace to kusan hakane don tana dauke da lalura na karauwa a jikin ta a yadda na auna ta tana da bukatan samun hutu sosai don tana fama da stress tare da ita wanda nasan wanan tashin hankalin ne ke bara zana da ita.
Yace cikin wani murya na mamaki Rahama ciki ne tare da ke ban sani ba ko may ?
Tace dashi shidin ne da ita, Abba ka barta ta koma dakin ta kada ai fushin manya don Allah.
Murmushi Abba yayi yace kagani ko Allah ya azurta ku da alheri amma fitinan matar ka ya hana ku kwantar da hankalin ku, ku fahinci hakan gareta.
Abban yace Rahama na amsa da naam abba ?
Kiyi hakkuri tunda ga wanan lalurar ya gitta a tsakanin ku ki koma dakin ki ku reni cikin jikin ki da mijin ki.
Ki share komai akan Saade ni dai na haifi saade kin sani wanan halin da ta dauko ba nata bane aron shi tayi.
Don haka nasan zata sauko da yardan Allah don Addua bai bar komai ba ga bawa don haka may kikace kin amince zakibi mijin ki ko zaki koma gidana da zama ?
Shiru nayi shiko daddy duk ya kashe ni da ido yana son jin zabin da na yi a raina a gaban kowa.
Na bude bakina da kyat nace daddy tunda komawan shi kake so a gareni na amince zan koma dakina insha Allahu.
Yace Allah yai maki albarka Allah ya baki zuria masu albarka da zasuyi maki biyayya fiye da wanda kikewa iyayyen ki.
Wani kuka ne ya zomin ba kakautawa dole na mike na shiga daki na hado yan kaya na dama daga na jikina sai dogon rigan dana saka a hand bag dina don canzawa kawai.
Mukaiwa Anty Amina sallama Abba da daddy suna ta mata godiya muka bargidan sai da muka kai Abba din gida wanda har muka kai gida nasiha yake ta muna dukkan mu mun sauke shi yake cewa zai nemay ni nan da kwana biyu zai yi magana dani.
Tunda muka bar Abba nake ta kuka sai huci daddy keyi bai min magana ba mun dauki titin gidan mu naji ya miko hannun shi zuwa saman cikina naji ya shafa a hankali.
Yace a fili Allah na gode ma
Showing 258001 words to 261000 words out of 456145 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87 Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153