Ga hankalin mijin ki duk ya tashi shine yazo yake fada min ma wai jiya da yau baki fita da mota ba ?
Nace anty mota ai ba nawa bane kuma bana ubana bane don may zan kama amfani da kayan gori.
Gori kuma Rama wa yai maki gori kuma akan mota ban yi magana ba na juya na fita tabi yanayi na da kallo nan ta fahinci akwai magana.
Ina cire safa a kafana ya bankado kofan dakin ya shigo yana huci yace ashe baki da hankali ?
Duk motan dake gidan nan baki shiga ba sai motar lift zaki shigo don ki bata min suna ko may ?
In ma motar ki bata da lafiya ne baki magana a gyara maki ita sai ki kama shiga motar mutane da izinin wa zaki shiga motar wata ?
Nace ai banzo da mota daga gida ubana ba don haka banga abin da zai kai shiga motar makiya na ba ?
Wanda basu san darajan dan adam ba balle na aure ko jaki ubana bai dashi a gidan mu balle mota na tsaya matsayin da Allah ya aje ni.
Karya kike wallahi karya kike daga baya ke nan may yasa kike shiga da farko kina wasa dani wallahi in kin isa ki kara shiga motar wata ko wani ki gani ?
Nace bani ganin komai sai alheri don shi na saba gani dama ni dai bani iyawa wallahi nace banayi ko dole ne wai auren ?
Kin makara yarinya don kin shigo inda ba fita ki zauna nan kishi ya kashe ki gabanza.
Allah tsare ni da kishin abinda bai damu da damuwar wani ba wallahi.
Na juya na mike na shige bathroom dina na barshi nan wanka nayi nai alwala na fito zuwa sallah.
Fatima ta dawo daga inda suka tafi kitso da gajiye sai da muka gama komai muka shigo part din anty.
Daga dakin ta ta kirani naje tace samu wuri ki zauna na zauna tare da sauraren ta don inji may zatace dani.
Rama yaushe kika zama mara kunya ban sani ba ?
Ko abinda kikaga anayi ne kike kwaikwayo kin dauka abin alfanu ne yiwa miji rashin kunya haka ?
Banji dadin jin wanan halin gareki ba ban kuma san sanda kika fara hakan ba ma ?
Idan yana haukan shi ki kyaleshi mana yai tayi shi da kan shi ai zai dawo ya gane gaskiyan abinda yakeyi din.
Kuka ne yazo min ban iya magana ba har tayi tagama ban tanka mata na dade a zaune can namike nace da ita nagode na fita.
Washegari hamza driver nabi da zai kai yara ya sauke ni nace ya dawo shidda ya dauke ni.
Bayan kwana biyu da dare na shigo nace da anty zan je nai maganan tafiyan mu wurin daddy tace Allah yasa a dace na fita.
Yana zaune da matan shi na shigo da sallama na duk suka bini da ido gaidashi nayi ya amsa min a dakile faban su.
Nace dama magana nazo yi yace maganan baiyi anan ke nan ko Zulfa najin haka dama da alama zaman kawai take a tsakanin su.
Mikewa tayi ta dauki yarta tabar falon saura hindatu dake kan kare mai abu a kafan shi.
Na ce dama zancen tafiyan mu gidane zan samu break na two weeks shine nake son na tafi.
Kamar ba da daddy nake magana ba nai shiru shima shiru yayi yana kallon tv nagaji da zama namike yace naji sai nayi shawara.
Ban juyo ba na fice abina ina fita hindatu da gaban ta ya fadi ance abinda kakeyi sai kai tsanmanin shi kowa keyi.
Tace may zata je yi gida kuma yanzu yace ba maganan ki bane tace ayi hakkuri amma naga dai kamar ba abinda ya faru ne ai ?
Yace sai abu ya faru mutum ke zuwa gida don zata gun iyayyen ta shine wani zance kuma can.
Ya nuna mata bai son maganan don ba maganan ta bane wanan dole tai shiru don bai ba da fuskan ba dama shishigin tane yasa kowa ke ganin zaman dadi sukeyi.
Duk da dai abu ya hau kan shi amma ba irin yadda muke nufi din nan ba yana dan namijin kokari akan ta wani lokaci.
Sam naki sakin jikina da kowa a gidan sai yaran da kan dan jani da hira ko shi ba sosai ba kullun ina daki abina.
Ranan da zan karbi girki anty da kan ta ta kara yi min magana dole nai girki nakai mai sai dai ban tsaya ba .
Haka yasa yai tsanmanin da dare ma ba zan shigo ba don har goma da rabi muna zaune muna kallo da Fatima wanda ni karatuna nakeyi.
Sha daya saura yan min tina na shirya nai mata sai da safe nasan lokacin kila yayi barci ko.
Ban ko tsaya wani gyara ba ko dana shiga ya kashe wutan ko ina yashige na rufe kofa na nufi bedroom din shima wutan a kunne yake lokacin.
Can na koma bakin gado na makure tare da rufewa da hijjab dina a zatona yayi barci ne lokacin.
Ban dade da kwanciya ba naji ya mirgino zuwa inda nake kwance ya fara romacing din na ko gezau banyi ba kamar yana taba dutse yakeyi.
Naji yace humm ya fahinci zuciya na ya bushe sosoi a lokacin don duk wani weak poit din da yasa zai sani girgirza yabi ban motsa ba.
Yai kidan shi yai rawan shi shi kaidai har yagaji bai min magana ba nima hakan da safe duku duku na bar dakin ko wanka da sallah a dakina nayi na hada break fast nakai mai nabi yara muka bar gidan.
Sai yamma lis na dawo na samu gajiye har tagama abinci da nai sallah nakai na jera nafito ban zauna ba.
Yau ma haka na daure na tafi kamar jiya ba sauki ko kadan a kaina sai na Allah ya gama abinda zaiyi ya koma inda yake yake cewa yaushe zakuyi hutun?
Nace thursday din nan in Allah ya kaimu yace sai ki shirya sunday ku tafi kwana nawa zakiyi a can ?
Nace goma ko sati daya yace wai ko kina da hankali Rahama may zakije ki zauna gida kiyi har sati daya, ?
Saida na hade bakin ciki nace ganin iyayyena da yan uwana zanje nayi yace to ban yarda ba idan kwana hudu yayi maki sai ki shirya ku tafi din.
Banyi magana ba na gyara kwanciya na kawai ina adduan barci da safe na fice abina yana zaune yana lazumi.
Yabini da kallo kawai yana mamakin karfin hali haka irin nawa watau mata kowa da inda take da nata matsalan ke nan.
Wanan yarinyar karama tasan wai ta dakile namiji ita adole fushi take yi wawuyi kanki kikaiwa nina kwashi rabona ko ai.
Da kanki yarinya zaki dawo kamar yadda kika kawo kanki yanzu akai maki susa.
Tun ranan na fara shirina sai dana shirya tsab kafin ranan na danyiwa anty bayani sama sama sai dai ba komai ba.
Mun yi kitso har kumshi don tafiya kawai jiran gari ya waye mu dauki hanya ga yaran nason bina anty tace sai nice zanwa daddy magana amma na rasa yadda zan mai magana don basuyi hutu ba.
Hakana nai masu dabara nace daddy yace idan sunyi hutu zai kawo su mu dawo tare anty ma taban tsaraban da zamukai gida nai mata godiya.
Na dawo part dina ina cewa Fatima ta fito da kayan mu falo sai gashi ya shigo yabi jakar da Fatima ta dauko da kallo, fatima kan na ganin shi ta shige ciki.
Kudi ya miko min yace ga wanan ina ga zasu isheki ai har ku dawo nace akwai kudi a hannuna zasu isheni bai tsaya bin magana naba ya miko min kudin dari biyu ne zur yan dubu da kuma dari biyar.
Yacd nace Hamza ya shiya zaku samay shi a waje zaune yana jiran ku nace na gode a sanyayye.
Yace ku gaida mutanen gida kiyi min godiya wurin baba kafin mu hadu dashi.
Mun fito muka rufe kofa na nufi wurin anty nai mata sallama don naci arziki ba yaran suna makaranta.
Tace kun fito ko nace eh anty to idan kin je ina zaki sauka wurin mama laure ko kuwa nace anty wurin Inna ta dai zan sauka tace anya Rama bazaifi kyau ki sauka gida ba wanan karon ?
Nace anty kin san halin mama ba fasawa zatayi ba bari dai muyi nisa da nisa da ita a rabu cikin mutunci yafi tace shine kuma ai.
Tare muka fito da anty mun samu har an saka kayan a mota ko yana dan kakabewa ba anty ba koni nai mamaki ganin ACURA din daddy ce zamuyi tafiyan da ita ashe.
Mukai sallama da su anty Gajiye ma zata bimu taga gida su dawo da Hamza fatima ita ta shiga gaba ni da gajiye muna baya muka kama hanya.
Sha biyu daidai muna kauyen mu inda kowa yaga motar sai bin mu da kallon mamaki ake don ba, a san ko su waye ba cikin wanan tsaleliyar motar haka ?
Fadan mai gari yana makil da jama, a dagani wani sharia sukeyi a wurin zuwan mu ya dawo da hankalin su a kan mu.
Mun fito aka gane mune ga yara sun kewaye mu sai faman ihu da murnan ga Fatima ga anty sukeyi.
Ba karamin kaduwa nayi ba danaga irin tsaraban da daddy ya lodo muna a bayan motan shi don ban san da su ba saida na zo yanzu ake saukewa.
Nauyi da kunya ne ya kamani duk rashin mutuncin dana tsula masu gashi kuma ya bini da abin arziki kai gaskiya hindatu shu,umace wallahi don nasan ba banza ta barmu ba haka rashin fahinta na shiga tsakanin mu haka.
Don gaba daya gaskiya bakin daddy nake gani ina jin haushin shi haka kawai ba wai marin da yai min ba tun kan haka nake jin wanan yanayin a tare dani.
Abinda ban sani ba ashe shine aikin da akai muna ma daba duka ba so akayi gaba daya ma sakina akaso yayi ranan .
Sai abin ya tsaya iya mari kawai da nasha Allah baikai abin ga saki ba tsakanin mu don gaba daya lokacin haushina da takaicina yakeji.
Marin da yai min ne yadan ji sanyi a zuciyar shi sannu abin ya dan rage mashi yadda yake ji a kaina din.
Nima yadda yake ji haka nake ji idan na ganshi wani haushi da takaicin shi nake ji sai naji ma bani son ganin shi sam a raina.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA IDAN KIN KARANTA BAKI BIYA BA, , , ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA ALLAH YABI MUNA HAKKIN MU A KANKI DON ONLINE NOVEL NE WANAN, , , ,

54
Mun yi saurin barin uguwar nace ma mama Altine zan dawo tana ta zabga min addua muka bar gidan.
Har mutane sun fara taruwa a kofan gidan mu amma haka muka wuce bamu tsaya jin takaici ba sai ma Rukaiyya ke fadin mama bata taba fadan gaskiya.
Yanzu tasan Lawali baida gaskiya amma ta zage tana biyewa matar nan suke tijara.
Yanzu ai ta samu daidai da ita ba kamar yadda ta samu innan ki tana gasa mata kwakwa ba a baya ita wanan sunyi daidai don makirace sosai matar .
Murmushi kawai nai mata a raina nace ai sin gamu da sun dace sai suyi tayi yanzu.
Gidan Jatau muka nufa daga gidan mu tare da karin tsaraban da nazo masu dashi.
Tun a kofan gida muka hadu da shi yana ganin mu ya fara wagale baki ya kara tsufa sosai duk furfura ne ko ina fuskan shi har kan shi.
Yana fadin hajiya Rahama ashe an shigo garin namu sannun ku da zuwa nace malam jatau ya gida ya iyali yaune rana na farko da mukai magana ta arziki dashi.
Nace na taki sa, a dana samay ka a gida dama akwai maganan da nake son muyi da kai akan anty na ne.
Ya kara washe baki yace to to Allah yasa alheri ne nace in sha Allahu alherin ne idan ka yarda.
Dama ba wani abu bane so nake a samu dan injimin nika wa anty wanda zata dan rika samun kwabon kashi kaga yanzu ga yara sunyi yawa dole a dan kama ma wani wurin kaima ka huta.
Yaji dadin yadda na fada sai washe baki yakeyi yace to hakan na da kyau idan har zata iya ai yar uwar taki ce ba haguwa ko kana son taimaka mata bata iya tattali ba a rayuwan ta.
Nace in har ka yarda ba matsala sai a gwada agani ko Allah zai karba muna ta wanan hanyan .
Nace babu damuwa za, a gwada a gani idan zai karbu gareta yai min godiya nasa hannu na ciro dubu biyar na bashi nace ga wanan ayi hakkuri dashi hakana.
Sai ga Jatau da tsufan shi har yana dan rusunnamin wurin karban kudin yana ta zabga godiya.
Dama muna tsaye yaran gidan na leko mu har sun koma sun fadawa iyayyen su ga yar uwar Suwaiba ta birni can ta tsaya da baban mu a waje suna wani magana.
Nan dai suka fara sake magana a tsakar gida mu ana gwada muna birni mu da muka ga gwauna.
Sai gamu mun shigo da sallaman mu Rukkaiyya ta kwasa zata wuce su babu ko gaisuwa nace haba dai anty na.
Direct inda suke zaune na nufa tare da masu sallama suka amsa a gyatsire fuska babu walwala nace mun samay ku lafiya yaya yara ya gida ya kuma bayan rabo suka amsa da lafiya kalau sai dayan ce tace anzo lafiya ya mutanen wurin ku nace Alhamdullahi.
Na juya nabi Rukaiyya data fara tafiya don bata daukan wanan a gareta sai ga Suwaiba zanin jikin ta ma dai bai ko kalluwa tayo kan mu da murnan ta.
Inajin suna cewa an dai yi hasara wallahi muka rugumay juna da murna ta rasa inda zata sani don dadi.
Tace Rahama kece kika koma haka kamar baturiya aiko birnin ma ashe amsa ne don naga wasu yan birni da suka zo kwana ki gidan nan ko mu mun fisu dadin gani.
Ashe wai wata yar uwar kishiyarta tazo daga can shine take wanan haibaicin muna shiga dakin ta sai da gabana ya fadi don bazakace mutum mai raine ke kwana ciki ba haka wai kuma harda miji a hakan.
Godiya naiwa Allah a raina da ya rabani da wanan rayuwan na mutanen mu mace da kurciyar ta amma don kazanta da talauci takoma kamar tsohuwa.
Hakana muka zauna takawo muna ruwa cikin wani kofin silver duk ya dafe don tsufa.
Kowa yace bai sha na karba na kafa kai na ji wani mugun karni ya doki hancina haka na daure na hade zuciyana yana tashi.
Mun gaisa muka barke da hiran yaushe rabo a tsakanin mu mun dan jima a zaune nace Fatima miko min jakar nan ta miko min.
Turmi uku na fitar da kudi dubu uku sai sweet da sabulun wanki da omo nace Fatima mikawa matan can wanan kice su raba .
Rahama don may zaki ba su wanan himilin uban kayan haka dako mijin da ta aje su bai iya basu shi.
Ai harshi sai da taba yanzu har dubu biyar kamar na taushe shi na kwace naji sai son banza amma shi bai iyayiwa mutane hakan.
Nace haba dai Anty wanan fa shine sayen girma da mutnci a gareki ba don wani na ba dashi ba sai don ke din nan.
Haka zai sa su gane kin fisu har abada tunda har kina da wanda zai basu abu su karba a bangaren ki.
Hakane kuma inji Rukkaiya dake zuga zancen ita dai Suwaiba duk bakin ciki ya kashe ta akan an ba abokan zaman ta alheri.
Abinda basu taba yi ba sai gasu tare duk kan su sun zo yin godiya sai faman farin ciki suke suna ta zabga godiya da fatan alheri gareni da maigida.
Bayan tafiyan su na fara yiwa Suwaiba da Rukkaiyya bayanin abinda nake so dasu tare da masu fada akan su canza rayuwan su don banji dadin abin da na sama ba a gidan Suwaiba din.
Nace gobe gobe ta kwashe kayan ta zan turo a gyara mata dakin ta zanyi magana da mijin ta sai Rukkaiyya tace a dai gyara muna nima dakina ai ko daben kasa babu kin san auren nawa ba shiri akayi mama kuma wai bata son auren.
To Rahama nagaji da yawo hakana gashi duk babu sa,a na a gari ita mama kin san hakan ko a jikin ta bata damu ba wallahi.
Nace Rukkaiya sai hakkuri da iyayyen mu tun da sun riga sun haife mu tace yanzu ma da zamu fito bakiji abinda take fada min ba wai kada na bada kaina gun Rahama.
Yo Allah na tuba yaya zan rabu da yar uwata ko baki haka balle irin taimakon da kike muna ko bakizo ba ko yaushe aiken ki na saman hanya ana kawo muna duk Altine zata dawo.
Nace ni dai yanzu abinda nake so daku shi ne
Showing 228001 words to 231000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77 Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153