gurin yan uwanta tunda uban ya koresu a gidan shi.
Liman ne ya dakatar da zancen da aka dauko namu yake cewa haka ba kyau yan uwa ku daina don Allah.
An bude bayan buth aka fara fitar da kayan mu daga ciki ai take gulman fada ya koma kan kayan da muka zo dashi.
Liman yace masha Allahu alherin Allah ya sauka a gidan maigari ke nan abinda ake wa gudun zuciya ke nan yau gashi yar da ya saki uwar ta akanta ta zama alheri a gari.
Nan dai yaran maigari suka biyo bayan mu da kaya daga kofan zaure na biyu na tsaya ina sallama.
Wata mata nagani baka doguwa da ita ta amsa min sallama na sai ga inna ta fito daga dakin ta dauke da wani roba a hannun ta.
Tana ganin mu tace yaya bakin ki ne daga birni fa matar tace bakina amarya ban ko sheda su ba wallahi.
Inna cikin kawaici tace yar gurin ki ce diyar Audi dake birni da mai kuli kuli, matar cikin fara, a tace ikon Allah Rahama kune tafe sannun ku da zuwa ta shiga washe baki kamar ta taba sani na a baya.
Nan ta kwadawa wata kira Rahamu fito munyi bakuwa fa ga yar mu tazo yau sai ga mai suna Rahamu tafito daga dakin ta tace to daga ina yaya tace yar gurin Amarya ne mana dake birni tazo.
Suka shiga murna da ganin mu Inna ko ta basar kamar bata gan mu ba lokacin.
Dakin Inna suka kai mu nan kuma ake shiga muna da kayan mu cikin dakin nata na sheda dakin tane ganin kayan dakina na da aciki basuyu komai ba har wanan lokacin sabbi dasu kamar sabo.
Matar ta biyu ne takawo muna ruwa a kwanon sha mu sha sai ni kadai nasha yaraan sunki sha nasan akwai daga ke nan dasu.
Kayan mu kaf an shigo dasu gidan sai ga maigari ya shigo yana cewa asama ma bakon nan da yakawo yaran nan dan abin tabawa akace sai dai a sayo mai hura ai mai damu.
Hakan akayi harda mu mun sha huran don yaji kindarmo sosai a cikin shi sai gashi ya dawo yana cewa bakon yace zai tafi ke nan na fita nai mashi godiya yake fada min maigari ya bashi zabbi da kaji kyauta nace madallah an ko gode ya gaida su Anty ya kama hanya tafi abinshi na koma cikin gida abina.
Na samu yaran sun buge ga huran da suka sha har sun soma barci a inda suke zaune a takure na cire masu takalman su na gyara masu kwanciyar su.
Na fita zuwa sallah don lokaci yayi suna cewa wai ba, a kira sallah ba nace lokaci yayi ai nai alwala nai sallah nima na kwanta a gurin sai barci sai da aka kira sallah laasar na falka koshi don sabone dayin sallah a cikin lokacin ta sai kaji da zaran lokacin yayi kamar an tashe ka haka sallah yake ga wanda ya saba yinta akan lokacin ta.
Bayan na idar ne na fito zuwa gaida mutanen gidan daya bayan daya nake shiga dakunan su na gaidasu a cikin mutunci na dawo na samu yaran sun falka na kaisu sukai fitsari na rage masu kayan jikin su don su sha iska.
Lokacin inna tazo dakin muka gaisa da ita take tambaya na yaya wajen su hajiya Saaden suna lafiya dai ko nace lafiya kalau Inna.
Sai dan shiru nace Inna da alama dai zaman gidan nan kamar ba matsala nake gani ko ?
Tai murmushi tace gashi kin bada amsa da kanki bamu matsalan komai yarinyar yanzu ne ma zan iya ce maki nasan nayi aure ina da incin kaina babu zaman takura ko kadan.
Na dan hade rai jin tace nan yafi gidan mu ta lura dani tace ai gara na fadi gaskiya yarinya kina da wayon ki san zaman da nayi a gidan mahaifinki na takura a baya.
To nan din babu shi gaskiya kin ga idan nace maki akwai shi na dauki alhakin mutanen gidan nan.
Nace hakane kuma nan nake tambayan ta kanne na tace mahaufinki ya aiko da zan tare an dauke su amma dai sunan su tafi anjima kadan zaki gansu sunzo don anan suke cin abinci dare da rana.
Tunda can ba wani kula suke samu ba gurin uwar taku sai wahalan banza shiyasa ma shi malam yace su dinga zuwa nan ko yaushe suna karban abinci yanzu haka da kwanon su dare da rana a gidan kinga ko ina laifin hakan don ko hakan da aikai min ai ya wadatar ko ?
Nace hakane gaskiya Inna suka ban tausayi sosai nace suna karatu ko tace sunayi kin dai san yadda kararun kauye yake ne ai sai a hankali in ba irin ku da suka dage gayi ba din.
Nan dai muke ta hira jefi jefi ina mata hiran gidan su anty tace wai mata na birni ashe kullun cikin fitina haka ?
Ai namiji idan ba jarumi bane sai ya zabge ko yama tsiyace fitana fa ga kishiyoyi baida kyau ga addini halaka maigida yake yi irin hakan .
Na fara fitar da tsaraban da muka zo dashi tun Inna tana godiya har yakai tayi shiru ta kura min ido ina mata bayanin komai dala dala.
Na nuna mata buhun kayan danazo dasu nace ta tsinta wanda take so sauran sai nakaiwa su Rukaiyya.
Nan ne nake cewa niko sai banga Lawisa ba a gida da muka sauka naga kowa acikin su.
Inna tace baki da labari Lawisa tayi aure ne a dan yanayin mamaki nace Lawisa tayi aure Inna ?
Tace tayi aure a madadin ki gidan jatau kan mudin shi da maman mu ku taci shine hukuma ta tilsta mata bada yarta daya gareshi.
Na tausayawa Lawisa kwarai dajin wanan labarin abinka da dan uwa sai naji ba dadi daidai lokacin da inna take ta faman daga kaya tana cire wanda take so a gefe daya take cewa kina tausaya mata ai ke suka so gani cikin wanan yanayin.
Nace hakane kuma Allah aiba azzalumin kowa bane ya sama yana kallon halin kowa daya halitta ai.
Nan dai muka sha hira take cewa akwai yan mata a gidan suma ta zaba masu kala uku daga ciki nace ba matsala inna.
Tafita bawa kowa tsaraban shi take naji gidan ya kaure da murna suna zuba godiya nan suke shigowa daya bayan daya yi min godiya.
Maigari da matan sgi al, ajabi da farin ciki ya hana su ma magana sai godiya suke min kanne na sunzo nagane su mun dade muna hira dasu har dare suna furin mu ranan a nan suka kwana tare damu.
Maigari yasa aka yanka muna kaji akai miyan kuka aka burge shi cikin kukan mu kaci sosai don yayi mugun dadi.
Washegari kuma duk da Inna tai muna breakfast da indomei da mukazo dashi sai da mai gari yasa aka kawo muna kosai da masa da miya mukaci sosai naji dadi da yaran basu da kyakyamin abinci duk abinda naci suma sunacin shi.
Na shirya muka kwashi tsaraban mutanen gidan mu dana yan unguwar mu sai gidan mu.
Nan muka fara shiga na samu mama yadda na barta daurin zanin nan a gaba yai kazan kazan dashi na samu baba zai fita dama ni ya tsaya jira sai gani.
Bayan mun gaisa dashi ne yake tambaya lafiyan wacce nake furin ta nace duk suna lafiya gama yaran ta nan nazo dasu.
Yace yaya zancen aure kuma nai shiru can dai nace baba gaskiya aure ba yanzu ba don karatu nakeyi a can yanzu haka ma .
Yace ai yaga alama tun daga yanayin shigana ya fahinci hakan ya dan yi min nasiha mama sai kai da komo takeyi nakawo tsaraban su na bashi ya shiga saka muna albarka
Mama sai tsuki take tana zuba bakar magana cikin kashe murya yace fita batunta kada ki kulata halinta na nan bata sake komai ba dakika sani.
Shiyasa ma daga baya banga laifin uwarki ba dataki dawo min don halin laure sai ita
Taso ta daurre fuskan ta amma tunda taga tsaraban ta nan ta shiga washe baki tana cewa ikon Allah wai motsi yafi labewa ke nan harda mu tsaraba haka mai yawa.
Rukaiya da Suwaiba har sun shige cikin kayan su dana zo masu dashi ko nace zan shiga naga mama sai muzo muje mu gidan Lawisa.
Ina shega mama tace yar halas yanzu fa nake fada dake a zuciya na ina cewa kin samu uwar ki har kin share ni.
Nace wace ni nina isa mama na share ki na dai samu inna ne naji dadi jiya naso mu dawo nan ai mukwana sai hira ya kwashe mu har dare yai muna acan.
Na bata labarin zaman Inna a gidan maigari yadda take zaune lafiya agidan ga hadin kai da mutunta juna a tsakanin su.
Tace bana fada maki ba dama kinbi duk kin tayar da hankalinki ke ga mai uwa a gari.
Nan na mike na fara gyara mata gurin don duk gurun nata yai kura sosai a lokacin ba laifi don mutumin da ta sa a gidan yana da kula shi da matan shi da yaran su biyu.
Zuwan su Rukaiyya saubiyu sun samu ina aiki sai dana gama na shirya muka tafi gidan tare dasu.
Mama bata so ba amma babu yadda zatayi tunda yaran basu jin maganan ta na debi tsaraban da zan kai mata.
Muna shiga na hango ta da daure gaban zani kamar na uwarta tana girki a cikin rana.
Wani iri naji a raina ina cewa da nice a cikin wanan yanayin a cikin raina tana ganin mu tazo da murna ta tare mu.
Ina shiga dakin ta sai da
gabana ya fadi don babu komai a dakin kamar ba dakin budurwa ba.
Nan dai muka zauna ana hira sai faman kamay kamay takeyi nabata tsaraban ta tana ta godiya take cewa dama ta tara wanki bata da kudin sabulu yanzu ta samu tayi wankin ta hankali kwance idan ta samu mai diban mata ruwa.
Mun jima a gidan ta har yamma muna gurin ta sannan mukai mata sallama muka juyo zuwa gida tana ta min godiya kamar na kawo mata wani abu basu gajiya dajin labarin birni a bakina nima ban gajiya da basu labarin abubuwan birni dana gani a can.
Mun dawo nan gidan su na zauna zauna mukai ta hira dasu basu nuna min komai ba a yadda na zaci ganin canjin fuska a garesu.
Mama dai ne na ciki na ciki dani sai bayan sallah magariba nai masu sallama muka koma gidan mama Altine ranan a gidan ta muka kwana.
Can gidan maigari sai tabaya yakeyi cikin damuwa ko anyi muna wani abune muka koma gidan mu kuma inna tace babu komai dama nace zanje can kada babana yace ban kula shi ba.
Da safe na tashi nai muna abin karyawa mukaci muka koshi sai ga sakon maigari har gidan mama wai a kawo muna abin karyawa.
Mukai godiya naba dan sakon tukwaici yatafi yana jin dadin hakan nace yace inna ta bashi kwalin sabulu da omo yakawo min nan zan bawa makwata bai jima ba ya dawo duk makwabtan mu su da na aika masu dashi sai zuwa rana na koma gidan Inna ta.
Mun samu an aje muna abincin rana shinkafa da wake da mai dayaji akai muna, da rana munci shi sosai har yaran sai da nai mamakin su da sukaci shi haka da yawa.
Gaskiya ban samu maysaka ba garesu suna da dadin zuwa guri Nasir ne ma mai leke min ko ina muna tare dashi.
Naje gaida su mama hauwa gidan Garbati sunyi murnan ganina sosai nakai masu nasu tsaraban suna ta faman godiya, ban dade ba nai masu sallama na bar gidan na dan zagaya gurin dangin baba da na Inna ta nagaida su.
Munyi kwanakin da zamuyi cikin jin dadi ana gobe zamu koma ake ta faman hada muna tsaraba irin kayan kauye.
An soya muna gyada suya ruwa da mai bawa yaji gadan mai yawa yaji kayan kamshi da maggi, aya da gyada mai sugar, kayan miya na kauye naui naui ga galon din man shanu yasoyu sai kamshi yakeyi.
Nono da fura da gunban kunu dakan hannnu kishiyan Inna tai muna haka dai muka hada kayan tsaraban kauye mai yawa.
Ga kaji maigari yasa a soya muna yace akaiwa mijin anty ai mashi kuma godiya na ji matukar dadin hakan da akai min don wani tsaraban ma anan na barwa Inna shi.
Mama ta somowa anty mai aiki gajiye sunan ta, mijin ta yarasu bata taba haihuwa ba ana mata tayi tace zata tafi ta gwada.
Karfe sha biyun rana driver ya iso daukan mu na karaba da kaya daga cikin wanda nazo dashi na amfanina da kudi dubu biyar akaiwa lawisa naba kanina nace kada ma ya biya gurin mama dashi don nasan rashin imanin ta tana ina boye kudin ta hana mata su.
Muka kama hanya sai garin kano a na daga muna hannu raina duk ba dadin rabuwa da yan uwa babu yadda zanyi muka wuce suna kallona.
****** ********* ******
Mun sauka lafiya biyu ya dan gwauta muna gida aka shiga muna da kayan mu gida anty sai murna dawowan mu takeyi.
Tace kunje kauye kunciyewa inna kayan dadi ko nace mun dai cinyewa mijin ta dai don shine mai masaukin baki ai.
Wanka naiwa yaran nima nayi muka canza kayan jikin mu nakai gajiye dakin da zata zauna ba daki daya zamu zauna da ita ba.
Sai bayan mun hutane na fitar da tsaraban da mukazo dashi anty tace amma dai kun sasu sun kashe kudi gaskiya nace anty aikuma kun kashe naku akan su.
Tai godiya take cewa bari mu gwada ba wa yancan tsaraban ko zasu karba oho in ma basu karba mun dai basu ai komai ta diba taba farida takai masu part din su .
Babu wacce ta dawo dashi yadda muka zata hinduce ma tace ace idan akwai gyada a karo mata ta dade bataci gyada da sugar ba da soyayya.
Anty ta kara akai mata tai godiya tace sai sun shigo gaida yan tafiya kauye .
Sannu a hankali nafara koyawa gajiye yadda abubuwa suke yadda ake kuma amfani da komai don tare mukeyi da ita.
Sai bayan mun dawo da kwana hudu ne daddy yazo daga Abuja sun dai gaisa da yaran shi a waya tun cikin waya anty take fada mashi irin tsara ban da muka dawo dashi yace shima ta aje mai gyada yason ci da ayya.
Ranan da ya dawo yana manne da yaran shi suna bashi labarin kauye Nasir yana ta bashi labarin dokin da yagani gidan maigari harda yadda doki ke cin abinci sai da yaba uban labari kaf.
Monday muka shiga school don ranan muka koma samun Gajiye sai abubuwa suka dan yi min sauki don gaskiya tana da kokrin aiki.
Yo aiki ga mutumin kauye ai sai yaso jikin shi za, a ga kasawan shi gata tsabta kodon bata haihuwa ne oho.
Na dawo daga school ranan a gajeye hamza driver ya sauke ni ina fitowa ban san da mutane a haraban gidan ba gashi gyale na sa ba hijjab ba kafa na sai hardewa yake wani cikin wani.
Tunda na karyo kwana suka tsuro min ido banda daddy da hankalin shi ke ga wayan shi lokacin ina ganin magana sukayi a kaina sai lokacin naga yadan dago kai ya kalli inda nake tafe.
Nazo gap dasu zan shige na dan rusunna na gaidasu suka amsa min a cikin sakin fuska na shige abina.
Ina shiga Amirace ta fara ganina ta taso tana rugumay ni tana min oyoyo tare muka shige daki dasu bamu fito ba sai bayan sallah ishai don yanzu na dan samu sauki zuwan gajiye gidan.
Ko zanyi abu anty kance na huta kawai tunda ga gajiye a gidan ai kuma tana aikin ta baka ganin part din mu da datti duk da munfi sauran yan sauran part din yawa a gidan.
A daki na samu anty ta idar da sallah tana zaune ga jinior saman gado yana watsalniya da kafa shi gurin shi naje na daga shi sama ina mashi wasa duk da bai fara dariya ba a lokacin.
Anty tace dani wai Rama kin san may nace a, a anty juya gareta ina sauraren ta tace bashir ne fa ya matsa min a kanki.
Nace waye bashir kuma anty ?
Tace Bashir dai da kika sani ma na abokin daddy ku.
Haba kai don Allah don Allah Anty kibar zancen nan mana nifa ma zan bar gaida shi an fada mai ni yar iskace halan da zai wani ce yana so na can.
Mamaki kalamina ya bata yadda nai magana yarinta zalla a cikin sa kuma akan serious nake magana na.
Tace a, a basai kin ki gaida shi ba zan dai bashi hakkuri yafita batun ki kawai bashi ke nan ba nai fushi karshe ma na dauki yaron muka fice daga dakin ban dawo ba sai da zamu shiga kwana na dawo mata da yaron.
Ashe bayan fita na daddy ya shigo gurin ta don haka yake yi duk dare sai ya zagaya wurin wacce basu da girki yai masu sai da safe yakuma duba lafiyan
Showing 96001 words to 99000 words out of 456145 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33 Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153