halin yanzu.
Ya gama cin abincin shi na dauke kulolin a falin na fita dasu daga nan na shirya ni da dana muka dawo wurin shi.
A shirye nake dama da taron shi don haka ba mu samu wani matsala ba sai faman gumzar dayake kwasa kawai a lokacin saboda gamsuwan da yayi.
Washe gari har lokacin ban wani sake jikina ba don ina faman tunanen sabon fitinan da zai bullo muna muna zaman lafiyan kadaran kadaham da junan mu.
Dan kali da kwai na soya mai sai ferfesun kifi da nai mashi tare da hada mai abin sha zuwa rana kafin na gama hada abincin rana don kada yaji yunwa don idan yana kano ba aiki yake zuwa ba nan.
Ina son mai karatu ta sani cewa manufa wanan labarin kamar ishara ce a gare mu mata ba wai don nishadi bane kawai muke bin labarin a, a don dai isar da wani sako ne wanda ke dawainiya da alumma a yau.
Shi aure wani babban alamari ne a rayuwan mu bawai munauin shi bane don kawai burin mu don da yawan mu sai muna daukan aure kamar wani manufa ne na cin ma burin rayuwan mu.
Don haka nake son mai karatu da tafahinta duk da nasan ansani din amma zan kara tunatarwa akan hakan.
Aure mun san ibada ne don raya sunna ma, aikin Allah kamar yadda ya umurce mu damuyi shi don kawar da sha, awa akan mu.
Aure akan yi shi ne don son jin dadin zama tare sai dai kada mu manta da cewa aure zama ne nazo mu zauna zo mu saba .
A cikin wanan auren da mukeyi ne zai zaman to rabin fannin addinin mu yana a cikin shi don haka duk abinda zamu shuka mutabbatar da mun shuka alheri a cikin sa .
Don haka ya kamata musan cewa akwai wani babban alamari mai wahala a cikin aure.
Zaki iya fahintar cewa wasu ma auratan basu mu, amula a tsakanin su yadda addini ya shimfida munayin sa
Wasu ma auratan basu wa junan su biyayya domin basu ba wa junan su hakkin daya dace dasu sai ba muyi wa juna adalici a tsakani musanman mata masu kishiya.
Wanan kishin da muke sakawa aran mu da zaran mukaji za ai muna kishiya shike kawo wasu matsaloli a gidajen mu a yau ke da za, a sama a shirye amarya zata samay ki hakan ma amaryan da nata shirin yanzu take shigowa gidan.
Sai dai mu sani duk wace ta rike Allah bazata taba tabewa ba a rayuwan ta idan muka koyi cusa dabia ta jarunta hakkuri da juriya, bata tsigar cin mutunci ba ko yaudara ga abokan zaman mu don haka zai kawo gyaruwan a gida jen mu .
Amma ina dadin ke babba baki da kwanciyan hankali hakan ma amaryan babu shi ko kadan a tare da ita wanan zai sa maigida aikata abinda baida niyar aikatawa akan mu shifa hakkuri a rayuwa baibar komai ba a duniya.
Sai dai ba a son hakkuri yai yawa wanda zai iya cutar dake tun farko ke da aka sama zaki ja girman ki a gun amarya don ida baki bada kafa da nuna son kaiba babu yadda za, a samu kafar raina maki wayon ki a gidan ki.
Ba komai yasa na tsaya yin bayanin nan ba sai kawai don masu yi min magana ga yadda ya kamata novel din ya kasance aciki.
Muna bada labari ne ta inda ke uwargida ko amarya kike da matsala sai mu dan yi koyi idan zai yuyu mu gyara barnan da muke a gidajen mu tare da abokan zaman mu.
Dafatan za, a fahinci sako na bada kowa kuma nake wanan maganan ba sai dai don mu fahinci inda sakon yake nufa don kowa na da nashi illar daga mazan har matan a yau.
Manufa shine baii yuyuwa ace komai yazo yadda muke son ashi a ran mu dole tunda hanya ne na fadakarwa mu samu gyara da akasin shi a labarin.
Zaku ga a nan ba wai zama da kishiyann ne damuwa ba a,a kishin mu shine yanzui kadda kiga kishiya tana walwala ko kadan da mijin ki .
Idan kun lura ita Saadatu tana son shuka alheri amma kuma shedan ya shiga zuciyarta ya hanata barin ta ci riban abinda ta shuka ta kasa gane cewa tsayuwa daa kafun ta da imanin ta na farko akan Rahama shine zai kaita ga kyakyawan karshe a tsakan kowan su saboda zugin yan uwa da abokanai na barkatai da take dauka.

********* ********* *********
Bayan wata biyu sai abubuwa kara lalacewa yake muna ba wani jittuwa a tsakan kowa a gidan yanzu kowa tashi tafishe shi.
An kira masu shirin shiga camp dasu zo suyi register a inda ya dace haka yasa nabi umurnin daddy na cika da inda yake so nayi din.
Sai dai tunda na cika nake a cikin fargaba da tashin hankali don duk lokacin dana runtsa idanuna don na dan samu barci sai na samu kaina da tunanen irin fitinan da tafiya zai jawo a gidan gun matan daddy.
Babu yadda banyi da daddy ba akan ya barni a kano nai bautar kasa na anan amma yace ya riga da ya yanke hukunci ko a ranshi.
Ranan muna waya na sanar dashi da an kiramu wurin screning ana son ganin mu yace dani na shirya a gobe zai turo da Hamza ya dauke ni kuma nazo da Aisha da Atika idan zan zo.
Tunda mukai wanan maganan hankalina ya kara dagawa na rasa yadda zan tunkari anty da zancen zuwa na Abuja tunda tasan ko a kano zan iya yin shi.
Nasan tunda ansa acan daddy yake kamar hadin bakine mukayi dashi za, a dauka shi ke nan nida mijina amma kuma babu daman mu sake mutum yayi yadda ran shi ke so don gudun afkawa cikin tashin hankali da anyi ance.
Don haka da dare banyi barci ba na dukufa wurin rokon Allah daya jarabce ni da shiga cikin wanan rayuwan ya bani kwarin gwiwa tare da fitar dani da karfin mulkin shi.
Gashi daddy yace duk wani abin da nasan ina bukata na tabbatar da na dauko shi idan zan taho don idan munzo munzo ke nan da zama abinda ya fada min kenan da mukai wayan dashi.
Zuciya na tana fada min zamu samu matsala da anty kan wanan tafiyan da zanyi sai dai babu yadda na iya dole ya kama nayi shi din.
Tun a cikin darwn nan mun gama shirin mu don duk wani abinda ya dace mu dauka mun shirya shi yadda muke bukatan tafiya dashi din.
Na fito zuwa part din anty jiki ba karfi da kyat nake iya daga kafana na shiga dakin ta da sallama tai mamakin ganina da safe haka tunda ba school zan shiga ba.
Kamar yadda na saba gaida ita haka ma yau na gaida ita tace dani yau da wuri haka kika shigo nace eh anty dama nazo ne na fada maki jiya sako ya shigo min ana neman mu Abuja yau din nan don zuwa screening din shiga cam da zamuyi.
Tace tau wata sabuwar zance kuma?
A Abujan ne zakiyi screening din kuma Rama ?
Nace eh can suka tura muyi don kin san yanayin karatun nawa shiyasa akai musayan mu dana can ?
Tace ina ko zan sani in ba yanzu da kike fada min ba kuma yaune tafiyan ban sani ba Rama sai da kika shirya zan sani ?
Nace ban shirya ba anty shine nazo na fada maki don ki sani don da dare ne aka aiko muna da sakon na sani nima.
Tace yayi kyau sai dai zan gargade ki da abu daya zuwa biyu shine ki sani inma hada baki kukayi da mijin ki don kije can ki zauna zan sani ne Rama.
Kada kuma ki dauka wai zaki inda maigidan yake kice zaki tsiro da wani sabon sallo a zaman mu don bazan taba lamunce maki hakan ba abinda ya kaiki zakiyi ki dawo inda kowa yake zaune.
Nace insha Allahu anty kamar wata uwata ba kishiya ba take min magana tace daga karshe humm wai ni za aiwa loko bayan kun gama shirin shi dashi zakice wai jiya aka turo maki may kuke nufi dayin hakan da zakuyi muna wai ?
Nace anty nidai ban san wani magana ba bayan wanan kuma ba zan taba cin amanan ki ba a rayuwana kamar yadda nake fada maki kullun.
In ma zaki iya Rama aiga hanya nan don kin san halin kowa anan ai kila ma ni nawa mai sauki ne don zan iya lamuntar wani abin a kan ki.
Bata sake magana ba tabarni a zaune a inda nake sai da na mike don kaina nace zan je in shirya ke nan anty tace Allah ya tsare nace amin.
Ina dawowa dakina na kira Inna ta na sheda mata zancen tafiyan nawa, tace dani ita antyn naki yaya kukayi da ita akan zancen tafiyan nan dai na kwashe komai na fada mata.
Tace nasan za, a rina dama ai don za suyi zaton kun hada bakine ki samay shi a can su ku barsu a nan kano din.
Tace ni dai zan gargadeki da abu daya shine ki rike Allah ga duk alamuran ki don alamarin naku sai addua kawai saboda abin naku ya baci sai gyaran ubangiji.
Kada ki fidda rai da cewa bazaku taba dawowa daidai ba a tsakanin ku don wanan jerabawa ne kuke gani dake da su baki daya.
Ubangiji mai yin ikon shi a duk lokacin da yaso akan bawan shi ne idan ya tashi juye alamarin sai kin yi mamakin hakan a gare ku.
Idan kinyi la, akari da irin rayuwan da kukayi a baya da wanan baiwar Allah zakiga alheri ne tsantsan ta a tsakanin ku.
Nace Inna nikan sai nake ganin dama da wani manufa tai min hakan bawai din ta soni tsakani da Allah bane.
Tace a, a yarinya kada ki saurin manta halarcin da wanan baiwar Allah tai maki a baya can ba abin a manta dashi bane kai tsaye don harkan kishi ya hada ku.
Zau yiyu ubangiji yai maku hakane don ya gwada karfin imanin ku baki dayan ku zai yiyu ace kuma wani abune daga cikin hikimar ubangiji ya gwada ku a hakan.
Nace Inna ni wallahi duk na sare da halin wanan matar a yanzu kamar ba ita bace mukai zama na amana a baya tare da ita inajin ta kamar ita ta haifeni ma.
Yarinya kin taba ganin wani mutum da ya samu nasara a rayuwan shi batare da Allah ya jarabe shi ba a wani tsigar.
Kada ki mamaki a tsakanin ku dama akwai wata a kasan wanin ku ba mamaki wani laifi wanin ku yai ma Allah bai sani ba aka harabe ku da hakan a tsakanin ku saboda ku gane ba aiwa Allah shishigi ga alamarin shi.
Don haka dake da ita duk babu wanda yasan dalilin yin haka akan ku sai aita addua akan alamarin don Allah ya yafe muna.
Ko kuma ba hakan bane anyi gwajin imanin ku ne aga mai raunin imani daga cikin ku din .
Baji rasa ci da sha ba kina cikin daular ubangiji sai ki godewa Allah tunda wanan ne kawai taku matsalar.
Munyi sallama da Inna bayan ta kara min kwarin gwiwa akan tafiyan nawa nai mata sai mun isa zan kirata muyi magana ta fadawa baba maigari da tafiya yazo muna a bazata ne kuma dasu Aisha zan tafi can din.
Daga haka Hamza ya kwada muna sallama wai mu fito da kayan mu maigida yace kada muyi rana a hanyan mu.
Sai dana shirya na fitar da duk wani abin da zai lalace harda abinci duk nabawa gajiye shi na shiga sauran part din nai masu sallama na barsu da mamakin hakan nakoma na ssallami anty muka kama hanyan mu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU DON BA A YAFE BA SABODA ONLINE NOVEL NE......
68
Sai bayan tafiyan mu ne anty ta samu labarin ai harda su Aisha na tafi ranta yai matukar baci da jin hakan da tayi don sai take ganin na munafunce tane da hakan.
Ni kuma ina shakku da tsoron fada mata ne tace dama plan ne muka hada don kawai mu yaudare ta mu tafi Abujan.
Ta shiga kiran wayan tana fadawa su mama da yan uwa abinda take hasashen mun aikata ni da maigidan take cewa ai ba dole sai Abuja zan iya sevices ba akwai jahohi da dama a kasan.
Mama laraba kan da ta kirata fada tai mata tace ke Saade wai may ke damun kine haka da kike tsiro da matsala haka a rayuwan ki.
Yanzu koda ace ma ba akan wani dalili yatafi da ita can din ba ai abin farin cikine hakan a gareki.
Ina hankalin ki da tunanen ki suke shiga ne yanzu duk kin dauki kishin duniya da tashin hsnkali kin sakawa yar mutane akai.
Kiji tsoron haduwan ki da Allah fa akan wanan bakin kishin da kika sawa zuciyar ki yanzu.
Kin abin arziki kowa yans saka maki albarka ga hakan har wasu na son koyi da hali irin naki zaki bari shedan ya dinga rudin ki kuma ?
Ina ji maki tsoron ranan da yarinyar nan zata bijere maki akan irin biyayyan da take maki abin ba zai maki dadi ba don ko an kusa wallahi,
Kwanaki fa yaron nan naki ke fadawa mahaifin shi yadda kukayi akan dan wurin Rahama da Amira yanzu ke baki jin nauyi da kunyan haka.
Shekarun ki da ilimin ki basuyi maki rana ba ko kadan wallahi indai wanan hakin kika dauka.
Tace mama ba haka na bane ni bani son munafunci ne ga alamari tace ke dakata na fada maki gaskiya ba matar shi bace ya tafi da ita da yaje can yana hurda da wasu matan na banza fa kuna zube a gida dukkan ku hudun.
Jikin ta yai sanyi tace nagode mama tace ki godewa Allah Allah yasa kuma ni kadai kika fadawa wanan maganan kada ai maki dariya wallahi.
Sukai sallama ta hada da mata nasiha da lalashi tace tagode suka kashe wayan ranan tasha kuka sosai tana nazarin maganan mama din.
Tafe muke a motan tun muna dan hira jefi jefi har mukai shiru gaba dayan mu nikan sai tunanen magana ta da Inna ta na yau nake a raina.
Don ba karamin tasirin maganan yai min ba a zuciya na sai dai ina ganin a yadda muke din nan abu ne mai wuya mu shirya yadda take nufi din.
Mun isa abuja bayan karfe uku da yake Hamza ya san hanya bamu sha wani wahala ba don gidan da ya ce ya sake din ba wanda na sani bane a baya don yace wancan uguwar baida tsaro sosai.
Koda muka isa yana gida a lokacin yana dakon zuwan mu garin mun shiga gidan mun samay shi a falo zaune yana amfani da laptop din shi.
Ya dago kai a cikin murmushi yana muna sannu da zuwa ya mike ya nufo kofan da muke shigowa yana son karban dan shi da nake rugimay dashi a kafada na yana barci.
Nan Hamza dasu Aisha sukai ta shigo muna da kayan mu daga ciki yake cewa da Aisha kai kayan naku wancan dakin ya nuna mata dakin dake bangaren hagu ta nufa da kayan.
Bamu dade da zama ba sai ga hamza ya shigo da ya tsaya kakabe mota a waje yace barin zo mu fita ka samo maku abinda zakuci ko.
Tare suka fita lokacin ne nabi gidan da kallon mamaki muka zagaya gidane babba mai kyau yaji komai na zamani dakuna sun kai guda shidda a gidan wuri daban daban ga katon kitchen maigirma da komai a cikin shi zaka ce already akwai mace a cikin gidan ne dama.
Sun dawo da take away niki niki da drinks da kaji gassasu a cikin sa masu yawa sai kamshi ke tashi mukaci muka sha dama kafin su dawo munyi sallah a dakin da aka shiga muna da kaya.
Nan ida na idar da sallah na kira wayan anty don in sheda mata mun sauka lafiya sai dai wayan har ya gaji ya katse ba a dauka ba.
Maigidan yaso hamza ya huta amma yace ranan zai koma kano dole ya sallamay shi ya wuce ranan.
Sai bayan tafiyan Hamza ne daddy ya leko dakin da muke zaune yace zo mana Rahama nafito nabi bayan shi.
Yace naso ki duba tsarin gidan sai kiga yadda ya dace da tsarin ki shi dai wajcan dakin dana sa yaran su sa kayan ku shi zai zama nasu su biyu sai ke ki zabi wanda zai zama naki already ni nawa ga shi can daga karshen lungun barin dama daga ciki.
Nace to yau zamu zauna a nan don mun gaji zuwa gobe sai na duba idan na huta yace ba matsala ga hakan don kunyi tafiya.
Da dare ma sauran abincin da mukaci da rana ya rage amma sai da daddy yafita ta sawo muna dan abin tabawa.
Ranan nai barcin dadi kamar ace haka rayuwan zai dore muna daga mu sai shi a cikin kulawa da ya dace babu idon kowa a kan
Showing 276001 words to 279000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93 Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153