ta gyara min part har na anty takan gyara udan aiki yaiwa gajiye yawa.
Anty takan ce wai haka yan garin ku suke ne da saukin kai Rama duk wanda ka gani sai kaga yana da mutunci ji yarinyar nan kamar ba yar kishiyar inna ba komai tsakani da Allah takeyin shi.
Nace daga tarbiya ne anty amma ai akwai marasa mutuncin bamu dai hadu dasu bane kawai.

********* ********* *********
Daddy ya bugo waya next week zasu dawo insha Allahu haka ya kawo ba zama kowa na kokatin gurin gyara a lokacin.
Duk wani abinda hajiya mai gyaran harka tabani banyi wasa dashi ba na maida hankali a gurin yin sa.
Na kwashi yara saura kwana daya ya dawo mukaje gurin gyaran jiki mazan akai masu aski ni da Amira da fatima kuma aka wanke muna kai mukai kitso mai kyau don muna hutu a lokacin.
Sai da muka dawo ne anty taga abinda mukayi don tana barci muka fita gidan bata ma sani ba.
Ga kayan dana sayo masu na taron daddy taji dadin hakan soai da yama na shigo dakin da tsinken kitso da cumb nace ta zauna na gyara mata kan ta.
Don ni bayan kitso an gyara min jiki an min kumshi na sa lallen da mai gyaran harka taban a yatsuna.
Nai matukar kyau sosai har yaran ma anty tace dani kai Rama ni ina zan tsaya yin wani kitso kuma nace haba dai Anty don Allah dai ki bari ko shidda na kwashe maki .
Bataki ba da fada da komai nai mata kitso mai kyau haka yasa fuskanta ya fito da kyau bakin ta yana sheki sosai.
Na zauna kafin magariba na gyara mata yatsun kafan ta da sauran abubuwa tace dani Allah dai yai maki albarka har najini kamar bani ba wallahi ko.
Washe gari munyi aiki sosai irin gyaran part din daddy da girki itama hindatu tayi nata gyaran har girki ta shirya mai bayan mu ya bugo waya ai mai tuwo.
Da yamma suka iso garin take gida ya rude da jin dadin dawowan su lokacin.
Ina part dina da fatima Nasir yazo ya fada min dawowan shi sai da muka dan dauki lokaci na kwashi yaran da muka aha kwalliya mukaje taron shi.
Yana zaune a falon shi shida Bashir muka shigo gaba daya kallon shi ya dawo kan mu har sai da bashir din ya juya yaga may yake kallo haka ne.
Mun karaso muna mashi sannu da zuwa nakuma gaida bashir din suma yaran haka sun gaida abokin baban nasu.
Ina fadin akawo abinci ne sai ga hindatu tashigo dauke da kayan abinci tana ganin mu fara, ar fuskanta ya dauke.
Ta samu guri ta aje abincin tana fadin ga abinci kaci kai wanka ko zakaji dadin jikin ka .
Ina jin haka na mike ina cewa a huta gajiya daddy zamu mu gaida Anty Zulfa itama.
Yace ku kawo min tuwon ko ba ai min bane nace anyi maka daddy yace kawo min tun bashir bai tafi ba muci.
Tace wanan fa dana shirya ma ko may kake nufi da akawo ma wani kuma yaya zanyi da wanan din kuma ?
Yace ai bance ai min ba wanan ra, ayinkine hakan tuwo nace Saade tai min ai.
Yaya za, ayi wanda zaiyi girki daban may kawo tuwo davan kuma ?
Yace bisimillahi hindatu zaki fara kuma ko da dawon mutum bai huta ba zaki saka min bacin rai kuma ?
Tace may ye na bacin rai a nan tunda nice zan yi girki daka tafi ai dakin Saaden ka kwana ko ?
Yace idan hakane kwana nawa nai a gurin ta, ke banson fitina yadda nake so haka za, ayi kinji na fada maki gaskiya.
Wallahi wanan bai yuyuwa haka kawai kan wata can in bari ka danns min hakkina yace indai wanan shine danne hakki tona danne din .
Hakana tsara kuma hakan zanyi ke duk yadda akayi dake ba, a daidaine wai bafa gurin Rahama nace zan sauka ba balle kice zaki min fitina haka.
May ye banbancin Rahama da Saade karshe ma ai munafunci za, ayi ace wai ita Saaden ta yafewa wanan din girkin tunda kun riga da kun shirya.
Ke hindatu kin isheni wallahi ban son rashin hankali wallahi ko addini yabani daman zaben inda zan sauka amma nai haka don a zauna lafiya dai.
Muna fita part din Zulfa muka nufa nida yaran mun samay ta tare da maman ta da yarta a dakinta sun baza kaya sai yan dararakun su sukeyi.
Muka shiga da sallama suka amsa muna sun daure fuskan su a lokaci daya.
Muka gaida ita tare da mata sannu da zuwa ta amsa muna bamu tsaya ba muka fice abin mu.
Tun bamu karasa fitaba naji yarta na fadin kai Zulfa haka yarinyar nan ta koma ashe ?
Tace wallahi nima haka na gani, yar tace jita kamar ma itace tai tafiyan da miji ba ke ba wallahi.
Uwar tace Zulfa koma may ye yarinyar nan ki mata uzuri please tana dai dan kokarinta a kanki.
Yanzu fa ba wanda yazo gaida ke sai ita da yaran kin ga koma may ye ai dai tayi ko da kuwa na munafuncin kishiyace.
Tace gashi itace silar tafiyan ma gaba daya koba komai ki samu abinda kika bata ko ba mai yawa bane inji uwar tace aramawa kura aniyar ta.
Yar tace yaran fa tace ai dole ne inba haka ba tsiya zai shuka min ban ba yara shi komai ba kin san shi bai hada komai da yaran shi ba ai.
Mun koma gun anty tana kallon mu cikin sha, awa tace har kun dawo ko na zauna ina cewa ai har gurin anty Zulfa muke muka gaida ita.
Lalai Rama akwaiki da kalula wallahi ki dai yi a hankali wa yan nan da kike gani basu da tabas wallahi.
Nace ni don yaran kawai naje gaida ita don su saba da hakan don shi yaro ba ruwan shi ki san race nagane hakan ?
Kin yi hikima Rama na fahinci nufinki don yaro ba, a sashi ga zancen kishi yin hakan haukane da batan kai baka san may rike ma yaron ka ba wata rana in babu mutuwa akwai rabuwa mata mu kula don Allah da wanan kishiya bata iya yiwa dan ka komai sai in Allah ya nufa.
Ba,ace ta ka zure ba amma yadda Rahama ta shiga dasu sha tafito shima wani dan hikima na ne na gyaran zaman gida hakan.
Tace kin zauna abinci fa nace may girki takai mashi abinci ko anty shiyasa banyi batun kaiwa ba.
Tace to wata sabuwa ana dai drama a gidan nan wallahi kafin nai magana sai wayan daddy ya shigo mata yana cewa nace wa Rahama ta kawo min abinci mana naji shiru.
Tace dani kinji kuma wai akai may abincin nace dama nasan rigima zasu yi shiyasa muka basu guri ba dadi kullun yara suna ganin irin wanan fitinan haka.
Tace tashi muje da abinci muji may ke faruwa namike na dauko basket din da muka shirya kayan na fara fita dasu anty ma tabini da sauran drinks din da na riga na tofe su da ayan Allah ciki muka kai mai.
Muna shiga tana fitowa a fusace daga falon dagani anyi ba dadi a falon lokaci tace damu muna fukan banza kawai wallahi sai kun gane kun shiga hurumi a gidan nan.
Nikan na jera masu kayan abincin Bashir na ma anty sheri wai uwargida sarautar mata ke saade wai may ye sirin wanan abin ne haka ?
Tace Allah !
Ya ce naga gaskiya ai kan Allah ya barki da besty ki daga inda nake duke nace Amin.
Ina gamawa na mike na bar falon yabini da kallon sha, awa kai mutumin yaya haka kuma wai inji bashir ?
Tace kasan amarya ce fa gata yar shila banga laifin shi ba ai wata nawa rabon shi da ita haka ?
Bashir yace ikon Allah waike saade wata irin mace ce baki ko jin darr a ranki kan yarinyar nan haka wai ?
Tace na fada ma ai Allah ko baka gane ba har yanzu ne abin daga Allah ne fa.
Yanzu dai zuba muna abinci muci na baku guri ni dama an kwadaita min ne na tsaya ci kawai.
Yace a, a barta na zuba muna kada tace kuma bayan ta zai karye yanzu lalaba abina nake don nasan halin kayana sarai.
Shi ya mike ya bude sai kamshi ya daki hancin su yace no warder ka kore kayan shimkafa da miya don nasan shine dai abincin nasu.
Sunci sosai suna hira su uku sai da suka gama ne Bashir yai masu sallama ya tafi anty bata fito ba sai washe gari da safe ni na kwana da yaran a gurina ranan.
Washegari ma nina hads breakfast na hada komai nakai masu saida ta karya tafito ta samay mu zaune ina shirya yaran zasu islamiya don ba boko lokacin.
Nan muka shiga gaida ita ta amsa muna cikin fara,anta nake cewa da ita yanzu nake son wai da na hada maku fruits salad nakai maku gashi kuma kin fito.
Tace kai barshi kawai Rama ki huta kawai sai anjima ni zan ma kwanta ne yanzu bana jin dadi wallahi.
Subbahanallahi may kuma anty ko a dauko maganin ki ki fara sha kafin ki kwata ko ?
Tace kai Rama mutum na shan magani kulun abu jiya wa yau ni na barwa Allah sani ko ma may nene hakan nagaji wallahi Rama.
Mikewa nayi na shiga na hado mata magani tare da ruwa na kawo mata tasha sai dan wani lokaci takoma daki ta kwanta.
A raina nace wai kuwa anya ba jifa ne je damun wanan boyar Allah ba haka mace ba dama ta dan sake da mijin ta sai ciwo ya taso mata haka ?
Tunda ts shiga har muka gama abincin rana bata fito ba haka na daure nakai mata yana gida tare da yan uwan shi na samay shi a falon tun auren na da daddy sau yau naga Ibrahim.
Koda na shiga suna yan dararakun su yana ganina yasha toka na gaidasu na aje abincin ban tsaya ba don ba hijjab ko gyale a jikina a lokacin.
Tun shigowana naga kallon da daddy ya watso min nasha jinin jikina har nakai kofa mubarak ke cewa dani ina Saade ta shige ne baiganta ba tunda ya shigo gidan.
Nace ayya tana kwance bata jin dadin jikin ta ne shiyasa baka ganta ba ai duk suka ce Allah ya bata lafiya a gayar da ita.
Sai bayan la, asar lis daddy ya shigo part din namu inda ya samu dagani sai gajiye da fatima a lokacin mai part din na ciki ta tashi har na shafawa kafanta da tace yai mata nauyi magani.
Nafito daga kitchen ina saye da wando tie da purple da dan riga mai karani ya matukar matse min jikina komai na suran jikina a baiyyane yake din kayan sun matukar daukan jikina sosai.
Sai nai kicibis dashi ya shigo falon bai damu da wai Gajiye na nan ba ko fatima da yagani bakuwa yai wurina tare da kamoni a jikin shi Allah yasa ta hanya kitchen nake ba kusa dasu ba sai dai ai suna iya hango mu daga inda suke.
Ya rungumoni tare da matse ni a jikin shi yana fadin ke baki da hankaline ga maza zaki shigo falo ko dan hijjab baki saka ba dadin su gama kalle min wanan jikin da kike daukan hankalin mutane dashi.
Na dago na dan kalle shi cikin dan murmushi nace dashi ni ai ban san suna ciki ba ne kuma na riga da na shiga falon ko.
Nidai bana son hakana please nace to ai haka naga kowa na shiga ba rufe jiki yace ai kowa kikace kowa irin nashi suran daban ne, suma ai bada son raina suke wanan dabiar ba.
Nace na bari daddy ai min afuwan na yau please yace naki don sai na hukuntaki ga hakan ga wanan mara hankslin a falo ina ganin shi sai da ya kalle ki wallahi.
Nace ayi hakkuri yace naji ai ance matar na tuba bata laifi amma ni gaskiya an min gaskiya don haka ki kula .
Nagode nace ni dai so nake ya sake ni kada mai dakin ta fito ta samay mu a hakan taji zafi don kishi kishi ne.
Shiko yaki sake ni sai kokarin mu hada ido ni dashi yakeyi ina kawar da kaina kar abin yai muna nisa.
Na dai samu ya sakeni da kyat ya juya zuwa dakin anty ni kuma na gyara rigana daya squzeeing.
Mun kitchen naji gajiya tace Rahama kin dai shigo gidan nan da kafar dama maigidan nan naku banga macen da yake ji da ita ba haka a ran shi.
Don bai iya boye son shi gareki a gaban kowa wallahi sai dai sauran suyi hakkuri akan haka don ko ita uwar dakin namu tasan da hakan don ta leko tana ganin ku a haka naga ta koma da sauri ciki.
Na juyo gareta da sauri nace gaji don Allah anty ta fito yana rike dani tace tafito amma tana ganin ku ta juya ciki da sauri.
Nace subbahanallahi Gajiye shi na kewa gudu wallahi amma shi daddy ko a jikin shi ga hakan.
Ni yanzu yaya zan kalli anty don haka cin amana ne kamar nai mata yin hakan data gani.
Hakana na daure na ci gaba da aikin dake gabana sai dai zuciya na yana ci gaba da rashin dadi.
Daddy yana shiga dakin anty ya samay ta zaune a saman gado ta dukar da kan ta a kasa yace da ita kin tashi ke nan ashe ?
Tace na tashi kagama runguman naka ne da kake yi yace ruguma kuma rugumarwa kuma ?
Tace wanan ai rashin adalci ne yaya har cikin falona zakazo kana rugumar mace haka a gabana in zakuyi iskancin ku kuyi a bayan idona mana amma ba sai anzo nan ana ci min fuska ba haka ?
Yace cikin mamaki iskanci fa kikace Saade matar tawa dana rike ina mata warning ta shigo falo ga maza ba hijjab a jikin ta shine iskanci kuma ?
Ni dai ban son hakana gaskiya ayi duk abinda za, ayi a bayan idon na yafi min nace bani so daga yau kaji na fada ma gaskiya.
Saade kina ganin ni zanci amanan ki ne ko Rahama zataci amanan ki kike gani idan kin muna wanan zaton wallahi dukkan mu baki muna adalci ba gaskiya.
Tace ni dai nace ban so na fada ma yace idan baki son na riketa tana matsayin mata na sai ki raba auren kowa ya huta bashi ke nan ba.
Kallon mamaki yake mata sosai bai tsaya karasa maganan shi ba ya juya ya fice daga dakin rai bace.
Naga lokacin da ya fito hakan rai a bace ya fice daga part din baiko kalli inda nake ba yafice.
Ashe akwaita ke nan to ni may ye kuma laifina ga hakan don ai bani na rike shi ba shiyazo ya rugumay ni kuma na kwace kaina ai daga gareshi.
Ban yarda na shiga ba sai dai itama bata fito ba haka na daure na shiga ina fada mata an gaba abinci a dai bo mata ne nan ?
Tace fuska a daure barshi idan na tashi ci zan fito naci ai nace to wanka fa ko zaki ji dadin jikin ki ?
Rama don Allah dai ki barni please banajin son surutu yadda nake din nan bana jin dadi wallahi ko.
Nace Allah ya sauwaka na fice simi simi banji dadin yadda tai min ba amma yaya na iya ni na shigo ai cikin su.
Nikan ban koma ba nai zamana da yaran a falo sai da sukai barci naja Fatima muka koma part din mu ko saida safe ban tsaya nayi mata ba don ta san nima ai mutum ce ya kamata tai min uzuri ai tunda bani taga na rike shi ba.
Da safe ma dana tashi ban shiga gurin ta ba da wuri sai da rana ya dan yi sosai nashiga naje dakin ta nagaida ita.
Ta amsa min kadaram kada ham ban tsaya ba na juya na fita mun dan zauna nai hira da yaran tana jin mu suna ficewa muka bar part din ta din.
Tun da tace bata son surutu may zan tsaya yi har laifin nawa yafi wanda take tsanmanin nayi ta kara min wani.
Ban fito ba muna ciki ni da Fatima kallo take niko ina resch dina sai dai raina ba dadi har lokacin.
Da dare naja Fatima muka nufi part din tana zaune a falon ta muka gaida ita tace Fatima kina gidan ashe ?
Tai murmushi tace ina nan hajiya yaya jikin mun baki guri ne kada mu damay ki kina son hutu shiyasa baki gan mu ba.
Tace OK,
Ta fahinci magana karamar yarinya tai mata tadago kai ta kalleni taga ina magana a hankali da jinior yana kada kai shima yaron alaman amsa min yakeyi.
Muna ta hiran mu da yaran ta mayar da hankalinta ga wayan ta muma sha,anin mu muketayi.
Sai wani dan lokaci na mike
Showing 210001 words to 213000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71 Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153