mu.
Washegari ban yarda a sayo abin karyawa ba ni nafita da kaina muka hada abin karyawa tunda safe ya fita gidan yace na duba abinda nake bukata sai muyi waya dashi a sayo muna.
Bayan fitan shi nai wanka na shirya nafito don duba gidan da kyau kafin in fita na kara kiran layin anty sai da wayan ya dauki lokaci sannan aka daga cikin murya mara dadin yanayi tai min sallama na fara gaida ita ta amsa min ba daidadi nace jiya na kira in fada maki mun sauka lafiya baki kusa ina gani na fada mata hakan.
Tace ina daga falo wayan nawa yana daki ne nace yaya yaran duk da ita da mukai tafiya bata tambayi lafiyan nawa yaron ba.
Tace suna lafiya nace dama na kira ne mu gaisa tace ta gode ina kokarin kashe wayan naji tace dama ashe harda su Aisha ne zaki tafiyan ban sani ba ?
Na dan yi shiru can dai nace eh don kin san ai dole inzo da wanda zai kama min yaro tunda kamf zan shiga kuma ba a zuwa da yaro.
Tace amma ai ya kamata na san da hakan ba wai naji daga sama ba kin tafi dasu nace ayi hakkuri anty nayi kuskure ta tabe bakin ta kamar ina a gaban ta tace wanan kuma matsalarki ce hakan ai don ban da daraja a idanun ki yanzu.
Tunda kina ganin mun zama daya abinda nake sallo dashi kema dashi kikeyi yanzu miji ko ?
Haba dai anty don Allah ki bar wanan magana bai dace ba kuskure ne nayi don Allah kiyi hakkuri please.
Sai naji ta kashe waya tana tsuki na kalli wayan nace nikan dai na shiga uku da anty mata ko may nayi banyi daidai ba a rayuwan ta nifa naje sallaman ta amma bata tsaya munyi maganan kirki ba da ita tashiga gasa min magana.
Bamu zauna ba ranan muka shiga gyara gida daki na mun gyara mun gyara gidan ko ina don har Atika dake jigila da baba idan yai barci tana fitowa ta kama muna wani aikin muyi tare da ita.
Gidan ya dauki kyali ga kamahin girki na tashi mai nuna alaman mace ta shigo gidan ke nan a ranan, don gidan dake da mace a ciki daban yake da inda babu mace cikin sa.
Daddy ya dawo gida da yamma ya samu gidan ya canza kala komai a gyara shi yadda ya dace ayi shi a inda mace take gida sabanin da babu mace a cikin sa tunda ya tare a gidan.
Nai mashi sannu da zuwa ya zauna a daya daga kujerun falon yana nuna gajiya a tare dashi ya mike kafafuwan shi ya mayar da kan shi bayan makatin kujera tare da lumshe idanuwan shi yana shakan kamshin girkin dake tashi.
A hankali na tako dauke da cup da goran ruwa mara sanyi sosai a hannuna na duka a hankali na aje cup din da goran ruwan.
Takalman dake kafan shi na fara cire mai sai ya dago kanshi daya sagale ga kujeran ya bude idanun shi a hankali tare da sauke su a kaina.
Ta kalma na cire tare da zare mai safan dake a kafan shi sai naji ya sauke ajiyan zuciya nace sannu da dawowa daddy ya aiki ya hanya ?
Alhamdullahi yace dani na dauki cup din ja tsiyaya mai ruwa na mika mashi ya karba tare da kwankwadewa ina rike da goran ruwan a hannuna har lokacin.
Nace dashi akara zubawa ne ?
Yace No I, am ok nagode ya sauke ajiyan zuciya nace idan ka huta ruwan wanka yana jiran ka a bayi sai yace ok nagode.
Bai dade ba ya mike ya shiga dakin shi ko da na bi bayan shi yana tsaye a tsakiyan dakin yana bin dakin da kallon yadda yasha gyara haka.
Na karaso ina cewa dashi ko na taimaka mane da cire kayan daddy naga kamar yau kasha aiki sosai ?
Ya sauke murmushi a fuskan shi yace ai kullun haka nake da wanan aikin kin san abinda mutum ke nema baya gajiya da yin shi.
Na taimaka mai da cire kayan ya shiga bayi ni kuma nafita zuwa karasa aiyuka na dake gabana a lokacin kada dare yayi ban gama ba.
Koda yafito yana saye da rigar jallabiya na maza mai dogon hannu na tsaya daga ga gefen shi nace daddy abincin ranan kafa yana nan.
Ya juyo yana kallo na tare da kokarin nade hanayen rigar nashi dogon rigar bubu ne a jikina har kasa kayan sun min kyau sosai ajikina, yace ai da baku sa min ba tunda bana dawowa sai yamma lis haka.
Yau ma don kuna gidan yasa na dawo don na huta hakana, yace yau dai kin wuni ke nan a cikin aiki wanan gyara haka ai yai maki yawa gaskiya.
Nasa Kabiru ya samo maki yar aiki da zata dinga taimaka maki da aiyukan gida sai ki samu hutawa haka wa ranki don Allah.
Murmushi nayi nace godiya nake daddyn mu sai dai tai min gyaran gida da sauran aiki amma banda girki gaskiya don ni tun a kan Saliha na sasuda da zancen yan aiki a raina.
Na kawar da zancen da cewa dashi kunyi waya da Hamza jiya ya isa lafiya ko ?
Yace wallahi ban samu kiran shi ba sai gashi shi ya kirani yana fada min ya isa da karfe goma sha daya na dare.
Nace maza dai basu damu da tafiyan dare ba su nikan ina zan iya tafiya a cikin dare haka na ?
Yace antyn ki ma ta kirani dazun da yamman nan ina hanya nace Allah sarki suna lafiya ko nayi kewan su Nasir wallahi jiya jiyan nan.
Yace suma ai dole suyi kewan ku anty ki dai ce ke fadan da ta saba dani wai may nake nufi da tafiyan dana shirya maki ?
Da sauri na dago ina kalon shi don son jin amsan daya bata din?
Yace nace da ita ai ba wurina kika zo aikin ki ya kawo ki kai Zulfa ce dai ma nake ganin batai min wani korafi ba akan hakan sosai don ta basar da maganan ita.
Nace a sanyaye nima ta kirani tai min korafi wai nazo da Aisha da Atika ban fada mata zanzo dasu ba.
Yace to may take nufi da ba za, a zo dasu ba watake son ya kama maki yaron ko idan an barsu a can duba maki su zatayi ?
Nace sai hakkuri alamari amma ai yanzu da sauki don ta rage wani abin ai yana tafiya yace kadama ta rage ita zai dama ai.
Yace ni zan karasa masallaci can kasa kada a fara sallah badani ba don wurin akwai nisa da nan kadan nai mashi adawo lafiya ya fice.
Na kwalawa Aisha kira ta amsa tafito dauke da baba a hannun ta nace don Allah aje wanan sarkin kiuyan ki sa muna turaren wuta kamshi ya dauki gidan.
Daga haka na wuce zuwa dakin dana gyara a matsayin nawa na fara shirin yin sallah don lokaci ya gaba to sosai na magariba.

********* ********* *********
Ranan monday na shirya zuwa camp ban tafi da baba maigidan ne ma da kan shi ya sauke ni inda na samu har dalibai ire iren mu sun fara taruwa a wurin sosai.
Bai tafi ba sai da yai min komai ya tabbatar banda matsala yai min sallama ya tafi yake cewa idan na gama na kirashi yazo ya dauke ni tunda ban san gari ba anan.
Har yamma muna wurin muna tashi na kira daddy don na samu ni har angama min komai nawa yanzu posting zan jira fitowan shi.
Daddy ya iso muka kama hanya sai gida a yadda nai tunanen zan samu yaron ya jigaita sai na samay shi hankali a kwance don dama ya saba da su Aisha ko ga madara da idan yai kuka zata bashi yasha.
Nima ranan nagaji sosai ban tsaya ba nafara tafiya ne naji Aisha tace dani Anty an fa kawo yar aikin dazun da kika fita.
Da sauri na juyo nace da ita tou har an kawo ta tana ina tace tana dakin mu tare da Atika nace bari nai wanka idan nai sallah sai na fito mu gaisa da ita.
Na shige ban zauna ba na fada ban daki na watsa ruwa a jikina ina fitowa wanka ne waya na ya dauki kara na karasa da sauri na dauka kada ya tsunke.
Gajiye ce ke kirana a lokacin don haka nai murmushi muka shiga gaisawa na tambaye ta mijin ta tace dani yana lafiya tace wallahi hajiya gidan sai ya koma ba dadi da baku nan .
Kun tafi kun barni ni kadai sai matan gidan masu ji da kan su babu dadi wallahi hajiya.
Nace kai Gajiye baga anty nan ba ki dinga shiga kuna dan gaisawa mana ai zaki ji dan saukin kadaicin naki.
Tace wa ni hajiya don Allah rufa min asiri matar dake zargina may zan mata nayi fari a gurin ta ko ke ai hakkurin ki ne yasa kuke tare har yanzu.
Nace to yaya zanyi Gajiye ai binta ya zama min dole kada nazama butulu gareta nice fa mai laifi ni da na aure mata mijin ta yanzu.
Kinga kuwa ai ba zan yarda ace a kaina aka samu matsala ba haka da ita sai dai tai tayi wata rana zata gane gaskiya da kan ta.
Tace humm hajiya Rahama jiya fa bayan tafiyan ku bakiga haukan da akasha gidan nan ba malam musa da kanshi ke fada min yaga anata gungu gungu a gidan yasan kuma akan tafiyan naki ne.
Nace ai yanzu kan su ake ji ni kan Allah yai min gyadan dogo na samu na dan tsere na kwana biyu sai suci kan su kuma yanzu ai.
Mun dan dauki lokaci muna hira bayan mun gama na kashe wayan ne na tayar da sallah don nasan an fara sallah a wani wurin don yanayin sallah garin ba daya ba da namu can kano.
Sai da nagama komai nafito falo jin nafito sai ga su Aisha da Atika da yar aikin mu ashe yarinyar gwari ce yar budurwa zata kai Aisha ko ta girmayta sai dai gajera ne ba a gane shekarun ta sosai.
Ta zube kasa tana gaida ni na amsa mata tare da tambayan ta anzo lafiya tace lafiya ma nace yaya sunan ki tace Helen take amma ana kiran ta da Lami ne nace yayi.
Nace da ita don Allah ina son ki rike ni amana kamar yadda muma zamu zauna dake amana anan tace yes ma.
Nace aikin ki a nan shine zaki dinga muna shara da wanke wanke da sauran yan aiyuka amma banda girki tace ok ma nagode.
Nan dai tana batin wurin daddy ya dawo daga masallaci ya zauna anan falo inda ya samay ni a zaune.
Yana cewa na dauko mai system din shi a daki na mike naje na dauko mai na kawo mai na samu ya zauna a gaban abinci zai fara cin don mun shirya maikomai dama.
Kai a gaskiya sai ince dole ne wasu mata suke kishi don zama da miji ke kadai akwai dadi don ban san haka ba sai yanzu da muke zaune daga ni sai daddy da yarana kawai sai yadda naso dashi ya koma mun kamar wani narkake dashi sai yadda nake so a gidan .
Ai ko ba komai dai na morewa rayuwana na kwana biyu ga hakan kafin na koma ga turke na mai cabo cikin zama da kishiyoyi.
Ranan muna zaune da dare baba yana gefen shi yana aiki sai ga wayan shi na ringin sai kusan zai katse ne ya dauka ashe hindatu ce takirashi.
Jin muryan yaron dake wasa mai kama da kuka a kusa dashi yasa tana daukan waya tace dashi indai cutane ai sai ka matsa don cin amana mu ba aje damu ba sai a dauki wace ake ganin tafi mu daraja don son kai kawai.
You are very stupid yace da ita abinda ya jawo hankalin mu ke nan na dago kai da sauri ina kallon shi yace don rashin mutunci sai ki kira wayana kina min maganan banza don rashin hankali nazo da ita ke ma ai sai kizo din mara hankali kawai.
Ido na tsura mai dana fahinci da wata daga cikin matan shine yake waya sai na kawar da kaina gefe daya ina duba tv dake aiki a falon.
Ya gama yaja tsuki bai min magana ba nima ban yi ba nasan dai maganan dayace bai wuce akaina ake mai korafi ba don jin abinda ya fadi.
Satin mu biyu daddy ya shirya ya tafi kano ranan da ya sauka sai da akai fitina tsakanin Zulfa da hindatu kan rabon abinda yaje dashi.
Itako anty na dama jiran shi take da ta karbi girki ba komai tai magana a kan shi ba sai zance na data nuna bacin ran ta akan dauke ni da yayi ya tafi dani Abuja da sunan wai na tafi aiki .
Ranan dai sunyi ba dadi inda yace da ita yanzu ke bakiji kunya ba ace wai ke , ke wanan korafin don rashin godiyan Allah gareki.
Tace may ye na rashin godiyan Allah din ga haka kishiya fa ka dauka kake tare da ita ka bari a nan wai ni tsuhuwa ko may kake nufi dayin hakan ?
Nasan da yardan ka don ka cuta min ka bata kwarin gwiwan zuwa Abuja don yin bautar kasa may nene ba ayi a kano da akeyin shi a Abuja kawai.
Yace ke Saade na kaishi din sai may kema tunda Rahama ta tafi kema sai ki shirya aiki tafi ko tunda ta zama maki abin gasa yanzu.
Nan dai ya mata kaca kaca kin san halin maza akan abinda suke so ba a taba gane kan su sai su borewa mutum.
Ba anty kadai ba kusan kowa yai mai wanan korafin dan tafiya na Abuja yace suma sai su shirya suje bautar kasan sai a zauna lafiya .
Ita Zulfa diploma tayi ita ko hindatu NCE ne da ita ta tsaya a nan sai anty da tare sukai bautan kasan su dashi a lokaci daya.
Wanan borewan da yayi dole sukai shiru da zancen amma yasha kara agun magabata amsa daya yake basu shi bautar kasa Rahama taje yi a can dole sai ai shiru ba bakin magana kuma don kowa yasan da bautar kasan da akeyi.
Kwanan shi goma sha biyu ya dawo garin inda ya samu na shiryawa dawowan nashi kamar zan tari wani bako ta ko ina na shirya mai.
Ranan kamar ba gun wasu matan daddy yafito ba cab don bamu ragawa junan mu ba sai da muka bar juna don kan mu waahegari ma bai barni ba sai daya debi rabon shi a gare ni.
Na hada mai break fast mai dadi yaci ya fita ban fito ba na kwanta don akwai gajiya sosai a tare dani sai sha biyu da rabi na falka nai wanka na shirya na fiti falo ko ina tsab helen ta gyara shi ba wani makusa a gidan.
Bayan na karya ne nace Atika ta dauki min waya na ina budewa naga sakon da aka turo min na posting din mu da akayi.
Inda aka turani babban asibitin dake garin Abuja don aiki dasu naji dadi sosai da gakan don nasan zan karu sosai ga wanan ci gaban dana samu.
Da murna na kira daddy ina fada mashi inda aka turani bautar kasan abinda ban sani ba daddy ne ashe ya shiga yafita na samu aka turani wurin.
Jin yadda nake farin ciki bayan mun gama wayan ya kalli wayan nashi yai murmushi yace Allah sarki waban yarinyar akwai sauran kurciya a kanta dai har yanzu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU DON BA, A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , , , ,
69
Bayan komai nawa na bautan kasan ya kammala nagama daga MBBS zuwa housemanship dina wanda komai a cikin gata akai min shi shine sai kuma ga posting ya biyo baya inda aka tura ne asibiti gashi kuma maigidan ya matukar tausaya min ga hakan.
Don yasan ba wani gata ke gare ni ba ta ko ina iyayyena basu tare a guri daya ban tare da mahaifina haka ma yan uwan haihuwa na muke da su.
Matar da nake jin sauki a gunta ta dauke ni kamar kowa nawa yanzu kishi yasa mun raba hannun riga da ita .
Ya zama wajibi ya tallafawa rayuwan wanan yarinyar don sun tauye ta shida Saade a rayuwan ta.
Ni kaina na san an an min gata don sai jefi jefi nake fita zuwa camp a lokacin don execuse a wurin dake nuna ni matar aure ce mai karamin goyo tare dani.
Komai yanzu idan akwai kudi zai sai wa mutum gata a wurin jama, a don ni kaina na san an gwada min galihu so sai a wanan fannin.
Mun yi waya da Zarah take fada min suma sun gama har anyi posting fin su ko tana a cikin kano bata fita ba.
Bayan mun dan taba hira na dan bata labarin sabon rayuwan da nake ciki tai dariya tace ai maza sun fi mu wayo Rahama gaskiya daddy yana son ki
Showing 279001 words to 282000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94 Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153