Bataji dadi ba na samu su Zarah ina fada masu hajiyan harka tace may kikace ke sai nake fada masu Zarah da Fati sukace kinyi daidai wallahi.
Bata zuwa yar iska mara mutunci kawai gasa mata kwakwanta ga hannu sai ta raina kan ta a gidan nan.
Wai harda fadin da ke tashigo tana ganin tagama dashi take zaton harda ke sai ta juya ki.
Aisha da fatiman sister din shi dake gefe don isowan su ke nan garin suna cin abinci sukace karya take ko a can ma kwasa sukayi dashi bakuga sun dawo maku a bazata ba daga shan amarcin da ya gudu nan yayi a kano.
Aisha tace wallahi ina ga watsatsar yarinya yai karo da ita don mun je gidan mun samu suna fitina dashi da alama dai amarya fanko ce sai dai maneji kawai.
Ai kaji abinda akewa gudu inji Fati yanzu tazo zataiwa mutane rawan kai a gida ita a dole ga yar iska ko?
Wuri ta samu ai daya gwada mata ita ba komai bane bata da kima da daraja da ta shiga hankalin ta da kowa.
Ai kinsan mazan yanzu ba kowa ya damu da wanan ba sai kiga sun share har ma su so fifita ta banza akan na kwarai akan ta sai su rufe idanuwan su duk da sun san watsatsace.
Basu san maganan Allah baya tashi ba akan zina ko tai haifa masu ko a samu jika hakana sai anyi daya biyun a garesu.
Nace ai yasani don data shiga gonar Amira ta fada mai a gaban shi sukai yi .
Da Amiran Aishan shi ke tambaya nace da ita fa cewa yarinyar tayi tafi karfin ta don da ubanta take kwana ta tashi ita.
Sai dakin ya dauki salati hajiyan harka tace dama ido ya bude sai fatiman daddy tace wani amsa aka bata to nace Amira kuma cewa tayi ko ita ai mace ce sai taje ta auri ubanta ta zauna kishi da uwarta ba komai bane.
Dariya suka sa kai yaran yanzu sai kace koya masu magana akeyi nace wallahi ni kaina sai da naji kunya a wurin ai.
Amira bataji nauyin uban ba tace da ita kuma don kin kwana da daddy nina sa ba bakon abu bane a wuein ki tunda da abokan Nasir yara kanana kike kwana kafin daddy din.
Dakin ya kara kwashewa da szbon dariya bandani sai Aisha tace don Allah ji wanan irin magana zata sa yara su fitsare muna a gaban mu.
Hajiyan harka tace ai yaron yau ka barshi kawai inda ka gan shi kinga ta karbewa uwarta fada ke nan ya zama nata don kin san dai ita Rahama bazata iya fadin hakan ba a gaban shi.
Shiyasa ake cewa kasada ne shiga gidan dake da yara yan mata in har zaka shiga to shigo da salama a zauna lafiya amma in har kace zaka taba masu uwa kaiko naka ya samay ka a gidan.
Kai shi da yara kayi da uwar su nace ai ni Amira ta ban mamaki data rufe ido ta gasa mata zance haka ko Nasir don ina mai tsawa ne shima nasan da yanzu sun kwasa dashi ko tuni tunda rawan kan ta har ga yaran kullun cikin kai karan su take a gaban shi.
Aisha tace takama ka ta in dai kan yaran shi ne don yanzu na sabanta yake mata nan gaba sai ta rena kan ta gareshi indai yaya ne.
Mikewa nayi tsaye ina cewa nifa sam bata gabana yanzu ko kadan don na fahinci kurciya na diban ta.
In bashi ba zata kalli idona tace wai dani ta shigo da badon tsoron Allah ba ai tun ranan zata zama bazawara.
Hajiyan harka tace na rabaki in ke baki mayar da ita ba indai yaran yanzu ne ita zata mayar dake don yaron yau baijin kunya tubbuke icce har sayen shi a gida.
Daga uwar har diyan ta jefa tsanar su a gurin maigida komai sai its ta zama mai juya gida yadda suke so.
Nace wanan dai tana da niya yadda na gan ta da halayen ta don fitsaran ta yayi yawa sosai wallahi.
Fita nayi daga dakin na barsu suna ci gaba da zancen ina shigowa dauke da wani tire na zubo sayyayen nama a ciki naji Fati na fadin .
Kin sai ai yaran sokoto nan suna kadagi da iya iskanci haka suke dama su da kishin hauka kan kishi sai su kashe mutum kishin da uwa da diya ake yin sa da yan uwan ta baki daya.
Ai da a garin sune da kunga abu wallahi don zakuga inda kishin hauka yake ba sanayya ko kadan koda kuwa yan uwa ne.
Nace dako sun raina kan su wallahi da na gwada masu waye Rahama sun sanni ke kyalewa fa mutum yake ba wai tsoro ba.
Zarah tace kaiyya Rahama na rabaki kishin da ake hadawa da asiri shine kishin balai bakiji tace saida ta shirya maku ta shigo ba tasan abinda ta takane inkiji hakan ai.
Nace indai hakane muje zuwa ni ga Allah na dogara ba da mutum ba sai mu zuba ta gani ai ni da kaina zan zauna na kai karan ta ga Allah.
Ba sai naje gun wani ba don abinda zanyi shi wanda taje wurin shi zaiyi Allah zan fadawa yai muna maganin ta..
Nace da mutane kuci nama don Allah bari a kawo maku abin sha ku dan sha kafin ku shirya don lokacin tafiya holl ya kusa.
Aisha tace yanzu kin hana min amarya zuwa ta taka nata rawan kafin nabada amsa Zarah tace ba inda zata wallahi bafa komai bane take son zuwa don kawai ansan itama matar gidan ne yanzu.
Shine fa kawai in bashiba may ye na nacewa da sai ta tafi ance ba ayi dakai kace kai sai anyi dole ta tsaya gareshi shi da ya dauko ta tayi.
Ashe maganan bai kare ba don ta fadawa iyayyen ta suka kirashi akan maganan don may ana buki a gidan ita zamu ware ta a gefe.
Wanan ai an nuna mata kiyayya ne da tsana tunda itama matar gida ce dole a dama da ita ina shiri a dakin mama Altine sai gashi har dakin ya biyoni kin san namiji wani lokaci kamar baida wayo yake.
Sun gaisa da mama yake cewa dani zarah na zaune don Allah Rahama kubar yarinyar nan ta tafi bana son yawan korafi wallahi.
Caraf Zarah tace wallahi idan taje muko sai mun muzanta ta don bamu gaiyyace taba a harkan mu kawai taje muna da rawan kai ko ta saka muna fitina ta watsa muna taro tunda bata da hankali.
Yace haba tunda tana so ku barta mana ta tafi ba shike nan na juyo nace ba dai harkana ba kan ta bari idan nata ya tashi idan ta ganni duk abinda taga dama tai min.
Mama tace kai itama dai yar nan ance ba ayi dakai dole ne yaran nan nada gaskiyan su fa fitina ne ba a so tayi da yara balle su da take ganin sa,oin tane tunda ta shigo da rawan kai haka ba kama kai kagama ganin gudun mutanen da ka sama.
Ai ba a mulki da karfin dole sai an lalaba akanci gari bada karfin tsiya ba yadda tazo masu.
Yace to shike nan ya fice ta sake samun shi wai ra shirya ya bata motar da zata da ita nata yai karama a wurin.
Yace ke sunce basu bukatan zuwan ki zuwan dole ne ko lahira ake rabo a wuein mai abu yace baya bukatar ka wurin ba sai kayi hakkuri ba.
Aiko nan ta tubure mashi har da son zagin shi wai dama ashe shi mijin tace ne bai iya gidan shi ba ya dauko ta ashe mace tafi karfin shi bata sani ba.
Suna cikin wanan rikicin ne sai ga Zulfa take tambayan may ya faru itace ke fada mata sai Zulfa tace da ita kama kanki da Rahama wallahi.
Ba irin su akewa a zauna lafiya da ace kin iya bita da kinfi kowa jin dadin ta amma yanzu tunda kikaga haka kama kan ki kawai da ita don duk abinda kike ji Rahama da kike gani tafiki iya shi wallahi.
Nan fa ta shiga fada wallahi ita danine mu zuba in karatu nake takama itama tana dashi dariya Zulfa tayi tace a hakan kama kanki wallahi Rahama tafiki iskan ci shiru shirun mutum mugu ne.
Ke ma in ba hauka ba may ya kaiki shiga harkan Rahama ki zauna lafiya ai kun kulan da kikace ke nan a gida nan da ita.
Hindatu tashigo ta gan su tana sake magana tai mata wani kallon banza tace wanan kuma fa haka ?
Shi dai yana zaune bai bar abinda yakeyi ba bai kuma bita kan su ba nice na shigo karshe da yarana har Nasir munyi kyau sosai damu.
Jin muryan Anty yasa ahi dago kai yana dariya yace kai kai kai my princess kece haka yau ta haye jikin uban nata sauran duk suka rufe shi ko kallon inda take zaune banyi ba tana zaune sai harara take waysa muna nace ke ba yar iska bace a raina.
Daddy banga ka shirya ba ko kai zamu bari gadin gidan ne da dukiyoyin mu don har su mama da kowa watsewa zamuyi mu.
Yace nikan ina nan sai Zulfa tace da yar amarya shi ba tare zasu zauna ke nan a gidan tunda bata zuwa ai.
Hindatu tace da zulfa din kai maman hanif taje ina kuma don Allah ki bar wanan zancen mana haka wanan ai rashin fahinta ne.
Sai yarinyar tace tunda ni ba mutum bace ba ko in dai bukine ai ba yau nake zuwa ba balle ace za ai min maganan banza a kan wanan din wani irin bukine ban gani ba a rayuwana.
Eh kin gani kan wuein bin yara kanana asha gara ba dai don matsayi ba wanan kan ba irin ku ke zuwan shi ba.
Kafin tai magana nace oya ku karbi kudin ku mu tafi kada mu makara sai ranan ashe ta fara ganin yarana a gidan don su ba su ma san da ita ba a gidan.
Hankalinta na kan abinda uban keyi da yaran sai ga yan matan suma sun shigo amsan kudin kari ihisan tace daddy mukan sai dubu dubu ko ?
Nan suka baibaye shi suna abinda yasaba dasu yama fita batun mu a wirin tsoki ta buga ta fice daga falon sai kowa ya kwashe da dariya ta juyo tana fadin dariyan ku zai koma kuka soon mu zuba daku a gidan nan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,
104

Buki yayi buki don an cika an min kara sosai a wurin zakace ko Aisha yar cikina ne nake bukinta.
Anci ansha an raba gift don angon yayi kokari shima sosai zan iya cewa a gaskiya Aisha tayi dace da mijin aure mai mutunci ga addini a tare dashi.
Mun dawo gida a gajiye kowa ya nufi wurin kwanciyar sa masu yin wanka da sallah suka je yi.
A falona muka baza kolin mu nan muka dasa wani sabon hira a wurin sai biyu da wani abu kowan mu ya samu wurin kwanciya don an gaji.
Washe gari kuma da aiki muka tashi gidan don akwai walima ga daurin aure ranan kan yan uwan mu sunzo maza da mata sai da suka tuna min da rayuwar kauye.
Ayi dauri aure a massalacin uguwar mu bayan an fito sallah azahar anci an sha karfe hudu aka fara shirin walima daga shi za, a kai amarya dakin ta.
Biyar da rabi aka tashi walima sai ga daddy ya shigo har part dina yace ina Aisha amarya nace dashi tana ciki.
Ki shirya ta yanzu zamu kaita gidan ta ni da mama Altine da matar maigari nace dashi da sauri daddy yanzu yace an daura aure may zata zauna maki yi a gida nabaku minti goma ku fito min da ita yanzu.
Dole haka muka shirya ta tana kuka nima kukan nakeyi mama Altine ta rike suka fice zuwa part din daddy din inda daga can zasu wuce da ita gidan mijin ta.
Ina zaune aka aiko wai nazo na samu harsu hindatu da zulfa a falon na samu wuri na rakube a kasa bashir na min ba, a ban amsa shi ba sai murmushi raina ba daddi ko kadan sabo da rabuwa akwai daci gare shi duk da a gari daya muke dai.
Ya soma da addua bayan ya gama yace to Aisha yau dai zaki fada a sabon rayuwa duk da yake dai banda wani shakku akan rayuwan ki sai dai ki sani zaman gida ba daya yake da gidan miji ba.
Yi nayi bari na bari da kika ji ana fada to shine aure aure wani bangare ne maigirma cikin bautar ubangijin mu.
Don haka ki zama mai biyayya da sanin ya kamata ki gina rayuwan gidan ki da zurian da zaki samu idan Allah ya kawo su.
Da zaki yi koyi da rayuwan yarki da kika zauna da ita zan iya cewa zaki iya zama da kowa a duniyan nan .
Don kin dai ganni da yar uwar ki duk zaman ki a gidan nan damu bazaki ce ga rana daya da kikaji wani sabanin daya taba shiga tsakanina da ita.
Kinga ashe idan kiyi kwatan kwacin halaiyar ta zance zaki zamo MARICIN KAN DUTSE fitar ka sai an daure.
Dariya suka saka a falon Bashir yace sunan kaunar tawa ke nan ashe daddy yace sunan ta ke na a gare ni.
Anyi baki anyi fari a gidan nan sai idan ka jefota a ciki take saka kan ta abinda bai shafeta ba koda ta gani bata taba saka kanta a cikin sa.
Ga abokan zaman ta nan a gidan nan idan akwai ranan da tazo min da wani korafi a kan su dukkan su.
Don haka yanzu kema zaki dora a inda ta tsaya don muna fatan har ki dara ta ga naki halaiyar da zakiyi a gidan mijin naki.
Kuka take sharba a hankali shi kuma yaci gaba da magana yana fadin Zulfa da hindatu ga Aisha zata tafi gidan mijin ta yau ina fatan idan akwai laifin data taba maku zaku yafe mata.
Sai ya juya gun Aisha din yana fadin Aisha ga yannen ki nan da kika zauna dasu ki toke su gafara bisa kan zama ko akwai wani sabanin da ya shiga tsakanin ki dasu su yafe maki.
Zulfa ne tace Aisha kan ai mu fuka ba Rahama ba zamuyi missing din ta a gidan nan don Aisha ai yarinyar zamace gaskiya.
Idan tana wuri dan ka baida matsala zaka iya fita hankalin ka a kwance ba wani damuwa gareka ko aikine ka saka ta baka taba jin bacin rai a wurin ta.
Mama Altine tace haka ake son dama ka zauna wuri ranan barin ka aji bakin ciki ba ana Allah Allah dakai ka tafi.
Aisha ta mike har gaban Zulfa tace anty don Allah ki yafe min idan akwai abinda nai maki a zamana daku a gidan nan.
Tace Aisha nikan baki min komai ba in ma kin min na yafe maki har ga Allah taje gun Hindatu itama tace ta yafe mata itama din tace ta yafe mata.
Zata koma ta zauna yace ga yarki nan baki roke taba sai ta nufoni tana zuwa tafada a jikina a take ita kuka nima kukan nakeyi.
Cikin kuka take fadin Anty don Allah ki yafe min nace Aisha ni baki mun komai ba na yafe maki.
Sai ta nufi daddy daidai kafan shi ta duka tana rusa kuka tare da rokon shi gafara cikin dauri yace Aisha na yafe maki Allah yabada zaman lafiya.
Sai ku tashi mu tafi mama yace wa su mama Altine da mama Abu kishiyar Inna ta.
Nan suka fita suka bar mu shi da bashir a gaba suna baya zaune su sai gidan mijin ta.
Aisha yau ta tafi ta barni nida yara da kewan ta don zan iya cewa duk haihuwan da nakeyi Aisha ce tafini sanin zafin wahalan dawainiya da yaran iyakana dasu shan nono ko wani abin can na daban.
Nasan ba niba har yaran sai suji kewar rashin ta a tare damu a gidan haka na mike na barsu nan zaune a na hira na nufi part dina.
Kowan mu yayi kewar rabuwa da junan shi da dan uwa a ranan don duk abinda nakeyi ina dai yine kawai a ranan har dare.
Washe gari baki suka fara tafiya garuruwan su da sannu duk gida ya watse aka bar mu mu kaida yadda muke.
Amira raguwa ce don haka yanzu kusan Atika ce takoma jan ragaman part din nawa don ni kaina bana son ma na matsawa yar marainiyar Allah da damuwa kada Allah ya kamani da laifi.

********* ********* *********
Saida na huta na koma girki na sai dai abinda na kula dashi shine Niima bata taran ranan girkin ta koda yaushe idan daddy yana gida tana manne a falon wurin shi koda kuwa aiki yake shi.
Na dawo aiki sai da nai wanka na
Showing 426001 words to 429000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143 Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153