kin fita kin barni na dan samu barci wanan maganin dana sha jiya bai barni nayi barci ba sai fitsarin da nake yi.
Nace dama haka mutumin mai magani yace min idan maganin ya karbi mutum zai dinga fitsare cutar dake a jikin shi.
Tace jiya kan nasha bauli ba kakatawa a gareni Rama har sai da naji tsoro sosai.
Amma wanan maganan da ki kayi yanzu ya sa hankalina ya kwanta sosai da jin bayanin hakan.
Take cewa ni masu fitinan nan na kullun suka tayar dani daga barci na da na keyi.
Cikin mamaki na juyo gareta nake tambaya nace fitina kuma akayi a gidan ne anty ?
Tace akan ki ba ai kema kin san cewa da duk ku kai tafiya sai anyi fitina saboda ke a gidan nan.
Nace a sanyaye ni kuma anty ?
Tace ke mana Rama kin san su zasu iya saka ido akan mutum amma shi mutum bai damuwa da abin da suke ciki da miji ko yaushe.
Tai tsuki tana cewa sunce idan kunyi tafiya sai ya kashe maki makuddan kudi masu yawa da baya kashewa mata shi.
Tace bari Rama yau naji abin mamaki sosai a gidan nan gurin mutanen nan ashe ba karamin kudi matan nan suke karba gun mutumin nan ba haka.
Yau da Allah ya kama su kinji yadda yake masu fallasa ai sai da sukayi dana sani yace daga yau idan ba gaba daya zai ba da abuba ba zai sake ba ko wace mace kudi ba komai lalurar da tazo mai dashi a gurin shi.
Ajiyan zuciya na sauke nace anty zato zunubi su a ganin su gun daddy na samu wanan kudin haka nai sayayya dasu ko may ?
Tace in ma a gunshi kika karba Rama ina ruwan su da hakan ne wai su udan sun fita dashi wayan san abinda sukeyi a can din.
Yanzu ai ya basu amsa don yace kin mai daidai don haka yake son gani idan yabawa mace kudi yasan inda suka shiga ba gobe sai anzo tambayan shi ba alhalin bai san may ake da makudan kudi hakan ba masu yawa .
Wai Rama kiji matan nan fa, da kuma namiji munafuki wai ashe har wani kudi yake basu na sayan kayan need din su da bai ba mu anan.
Nace cikin mamaki kamar ya anty tace wai na sayan pad da kayan makeup ko da may ye ma don ni takaici ya hana na tsaya na saurare su ma na dawo nan abina don dashi dasu duk haushi suka bani.
Tace ni dama nasan karya ne in bashi ba a ina suke samun wanan kudin da sukewa mutane karya haka dashi ?
Anty kiyi hakkuri akan wanda kike dashi mai hakkuri yana tare da Allah ai da baki da amanan su ai gashi yau kowa yaji may suke ciki kuma ai sun wa kan su in sheri ne don kowa yaji may suke ciki yanzu ai.
Wai ma don ya mayar dani van san ciwon kaina ba Rama sai gashi wai yazo min da maganan su nai banza dashi ya karaci zamqn shi ya ban guri don ni banga abinda zai fada min ba kuma na yarda dashi.
Na mike na cewa anty bari na shiga naga mutane na nadan watsa ruwa na fito sherin su dai a kansu zai kare ai.
Ina fita na shiga part dina na samu su Fatima zaune suna kallo suna ganina sukai min oyoyo da gani na.
Tambayan su nake ko sunci abinci suke cewa dani sun dafa sunci don yanzu suna girki abinda suke so a waje na.
Ban tsaya ba na shige dakina na shiga wanka na fito sallah aka fara na shiga yi.
Ban daga daga wurin ba har sai da na idar da sallah nai shafa,i da wutiri na mike fatima na kira nace ta fitar da kayan na gani nan muka baje komai na kwashi tsaraba na da anty da sauran na yaran na shiga wurin anty da su.
Tana daki anan na zube kayan falo na samay ta a cikin daki ta idar tana addua na shiga gun ta.
Ta shafa take cewa har kin fito ne Rama nace eh anty dama tsaraban da na sayo ne na kawo maki ki gani idan sunyi maki.
Ban da na yara har da kuma ni Rama abin ai yayi yawa dai ko nace haba anty yawa kuma fa akan ki abu zai min yawa anty ?
Aiko da na zama butulu gare ki anty aduniya akwai abinda zan maki wanda zan iya rama abinda ki kai min a duniyan nan ?
Kai haba dai ki daina saka wanan a ran ki mana, Rama ai hakan hukuncin Allah ne ba yina bane.
Ni fata na yanzu shine Allah yabaki naki rabon a gidan nan nima naga jinin ki a cikin gidan nan kamar kowa.
A cikin raina na karba mata da amin amma a fili murmushi kawai nai mata nace kai haba anty muje kiga kayan a falo kada mu bata maki guri nan.
Tana fitowa taga kayan take cewa kai kai kai Rama wanan kayan haka duk a lagos kika samo su haka waya na daga na kira Fatima nake cewa duk su kwaso sauran kayan su kawowa anty ta gani.
Nai mamaki danaga tana jidan kayan kitchen din da nazo dasu sai bayan ta gama zabe tana ta yabawa da kyaun kayan haka .
Take cewa kin san ina da amare har biyu shiyasa na zaba masu ba sai munje saya waje ba daga baya.
Amare a ina kuma anty tace gajiye da Fatima mana Rama ai dole nice uwar amaren dai ina ce.
Shiru nayi mamaki ya rufe ni na hali irin na anty ko ni da Fatima take guna banyi wanan tunanen ba haka.
Amma saboda salihanci irin na anty sai gashi ta ita tayi wanan dabara ganin nayi shiru naji tana fadin Rama kin fasa abinda kaiwa wani a duniya shine rabonka a lahira walau sheran ko hairan don haka don Allah ki barni na samu wanan ladan na alheri dana sawa raina.
Wanan shine kadai abinda mutum zaiyiwa wani mai bukata na kasa dashi ya tsira ga ubangijin shi.
Don haka gobe zan baki kudin kayan ki sauran list din abinda nake bukata garesu kuma akan su duk kece zaki sawo Rama na saya a gurin ki wanan alkawari ne naiwa raina hakan.
Shiru nayi duk imani da tausayin ta ya kamani sosai sai tunane nake wai ita wata irin mutum ce a duniyan nan cikin mata ?
Bata fita ko ina tana gida anty time tana bautan Allah da auren ta haka kuma abinta ban taba ganin ya rufe mata ido ba ita a rayuwan ta.
Sai naji tana ta faman yaba kyawon les din da na sayo muna tace kuma kayan yara sun matukar burge ta a rayuwan ta.
Muna cikin fira sai ga maigidan ya shigo fuskan shi a daure murtuk dashi dagani har wanan lokacin ranshi a bace yake mai.
Gaishe shi muke yi daya bayan daya yana amsawa kamar baya son amsawan a lokacin.
Tambayan ko kayan may ye wanqn haka yayi take cewa kayan da Rama ta saro a lagos ne mana.
Inda nake ya juya yana cewa ke har yaushe kika samu sayan wa yan nan kayan haka cikin mamaki ?
Nake cewa dashi da muka tafi da matar Adebayo ne ta kaini na sayo su a can.
Yana tafiya yake cewa kada fa ki ce zaki fara shiga Dubai wanan abin dana gani haka fa ?
Dariya duk wanda ke falon yasa saboda maganan shi sai anty ke cewa aiko bataje ba sai tai oda kuma su shigo mata yanzu akwai hanyar bussines ai a cikin sauki masu yawa.
Ya har falon mukaci gaba da harkokin mu sai dare na koma ni da su Fatima part dina gan kwanta ba karatu na shiga yi ina nazari saukina abinda na koyo da muka tafi chaina dashi ne akayi bana garin.
Washe gari ban tsaya ba na loda kaya a mota na fice gidan Allah ya taimakeni tun a mosque da mukaje sallah nai ciniki sosai an kwashe lace din dana fito dasu ranan gaba daya har ana nema don kyaun su.
Na dawo gida nagaji mukai kicibis da Zulfa yarta na wasa a haraban filin gidan ina ganin ta na ja burki sai da aka dauke yarinyar na karasa inda nake aje mota na.
Na fito ganin Zulfa duk da nine na fito unguwa ya kamata tai min sannu da zuwa a lokacin amma na san bazan samu hakan ba a gareta na daure na gaida ita da gida.
Maimakon ta amsa min sai cewa tayi amma tukin naki Rahama ya zama na ganganci zaki shigo kin san akwai yara a gidan zaki kwaso haka a guje nikan ki rufa min asiri kada ki mayar dani baya please ?
Mu koma dani dake ba maishi a gidan mun zama daya ke nan a hakan don Allah ki rufa min asiri please.
Mamaki ne ko takaici ya rufe ni na tsaya rugumay da takardu a hannuna ina kallon ta nace haba anty mai yai zafi haka kuma da wanan maganan haka ?
Aiko da ban taba haihuwa ba nasan zafin yaron don ina da imani a zuciya ban ga dalilin da zan dauki alhakin karamar yarinya irin baby ba haka ?
Daga can bayan mu naji ance damu aiko jaririya ce sai a kashe akan kishi tunda mutum na bakin ciki da diyan mutane tunda shi bai haifa ba saboda hassada.
In haihuwa banza ne ai mace ta haifi nata mugani mana amma sai kai ai kokarin salwantar ma da wanda Allah ya baka kuma saboda bakin hassada.
Murmushi nayi nace sai dai ku sani ni baniwa Allah garaje akan abinda ya boye da haihuwa da rashin shi duk ikone na ubangiji ni ko a hakan da nake nagodewa Allah na kuma ko yaushe ina cikin gode mai ga irin ni,imar da yai min wanda kowa bai taba zaton haka ba a gare ni.
Zama mace ta hudu a wurin mijin irin daddy aiko ba hahuwa alhamdullahi don babu abinda na nema na rasa sai dai nagodewa Allah na a hakan.
Tunda mijina bai taba banbatani da masu diya agidan ba kuma rasgin haihuwa ba wai ya damay shi bane don ina juya cikin ku ashe ko Alhamdullahi tunda daidai nake ga kason kowa ko ban haifa ba an haifa min kuma ina da iko yadda naso dasu.
Ban tsaya jin amsan su ba na shige abina na barsu nan suna ta faman haushi kamar mahaukatan karnu ka.
Zan shiga naji hindatu na fadi lalai yarinyar nan wuyan ki ya isa yanka ashe don kina ganin kamar kin kai kowa ne a gidan yanzu.
Na juyo nace har akwai may wata kama na kwarai ne can na daban ana ko kuwa taron cushe inda za, a bar mutum yayi zabe ai ba mai zaben ku cikin gidan nan kuma kun san da haka sai dai ku godewa Allah abin ya zama na sadaka ne gaba daya.
Na shige abina na barsu nan kamar ran su zai fita wurin jifana da bakar magana ni dai banji ba balle naji zafi suko sunji nawa dana fada masu.
Don basu taba zaton nasan cewa ba shine ya nemay su da aure ba bashi su akayi ya aura a dole.
Sunji matukar haushin wanan kalamin harda cewa wai a bari maigidan ya dawo ai dole ne a zauna dashi.
Har dare ina jiran kira banji komai ba kuma ban ma fito hira ba fun anty don damuwan da ya kamani kan wanan yawan gorin da suke min na rashin haihuwan da banyi ba kuma ban fadawa anty abinda ya faru ba tsakanina dasu.
Washe gari cikin kuka nake fadawa Zarah irin gori da habaicin da suke min idan magana ya hadani dasu.
Hakkuri ta bani tace kada nasa zancen a raina don Allah bai mata da ko wani bawan shi ba sai take cewa dani na samu miyar kuka koda yaushe na zauna na shashi sosai don yana sa mace samun haihuwa idan bata haihuwa.
Tun wanan ranan zan hada kuka yaji daddawa da kayan yaji na zauna na shashi sosai.
Kuma ina hadawa da bissimillah kafa dari daya da goma sha uku na shafawa kasan marana.
Sai kusan bayan sati daya ranan daddy ya shigo ina zaune saman sallaya muka gaisa yake cewa dani Rahama idan zaki shigo gida ki daina gudu da mota haka don gujewa kaddara.
To daddy nace dashi insha Allah bazan yi godu ba har ya fara tafiya sai naji yace amma kuma nai mamaki don ban san lokacin da kika fara tukin ganganci ba haka ?
Na ce cikin murmushi daddy ni bani gudu kaima ka sani ka kuma sheda hakan gare ni ai sai dai zan kara tsarewa insha Allahu.
Ya ke cewa dani matar Adibayo tace a fada min kayana zuwa tuesday zasu shigo hannuna insha Allahu.
Nace ai min godiya wurin ta sosai yake cewa yana gani wani sati zai wuce zuwa Bangkok akwai taron da zasuyi acan din.
Nace amma ba dadewa zakayi ba ko daddy naso kafin kai tafiyan asan matsaya akan Gajiye da Fatima yace haka nake planing nima kafin dai na tafi hakan za, ayi insha Allahu don shawara ne mai kyau wanan.


Kuyi hakkuri da wanan da kyat na samu na dan rubuta maku shi don har yanzu ina jin jikina wallahi nagode kwarai da kulawan ku gareni yan uwa wanda na bata ma rai ga jina shiru suyi hakkuri don Allah dani halin jiki da jine hakan nagode da fatan zaku fahince ni yan uwa.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON ONLINE NOVEL NE BA A YAFE BA , , ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA KEDA ALLAH YAR UWA DON ONLINE NOVEL NE, , ,
58

Daddy bai bar garin ba sai da ya tabbatar da komai ya ian kama akan zancen auren Fatima da hamza gajiye da maigadin gidan shi.
Har dukiyan aure sai da ya biya tare da duk wani abinda ya dace ayi a kan aure na fannin maza yabar garin.
Wanan karon daddy bai tafi dako wace mace ba shi kadai yai tafiyan shi batare da ya tayawa kowa ba gashi s n sa rai cewa ,
Daya daga cikin su ne za, ai wanan tafiyan da ita zuwa waje don haka kowa a cikin shirin tafiya take amma sai ganin shi kawai sukayi yazo sallaman su akan zai tafi.
Yakawo kudi yabawa kowa wanda zatai amfani dashi bayan kayan abincin da ya sayo muna, masu yawa ko wani part aka shiga dashi equally,
Da ganin irin wanan tafiya tafiya ce mai muhinmanci a gare shi zai tafi ya dauki lokaci acan har sai ya gama shige da ficen abin da ya kaishi kasan zai dawo gida Nigeria.
Gashi yanzu bakin kishi ya jawo wa kowa hasara yai tafiya shi kadai suna kallon ba wacce ya tafi da ita.
Sana,a ta nake da karatu ba wasa Allah kuma ya taimake ni ina samu sosai a wanan fanni,
Ba karamin haushi da takaicina matan daddy ke ji ba saboda wanan tafiya din da akayi bada su ba.
Daga karshe sai ga shi ranan Saturday tunda safe sun tayar damu da fitina a tsakanin su akan fadan yar wurin hindatu wai ta dauki baby sai ta yar da ita daga hannun ta, da gangan .
Allah ne ya kama su don suna tsaye suna magana a waje kan tafiyan daddy din ita hindatu ke cewa da ita wanan ai sheri ne da makirci kawai irin namaza don ya ga bada ita zai tafi ba.
Suna cikin wanan gulman ne sai ihisan ta dauki baby din daga hannun uwarta tana wasa da ita daga gefe.
Sai kawai ta sake ta a kasa ta fadi cikin wasa maimakon uwar tai mata magana sai tana dariya ga har bakin yarinya ya fashe tana tsala ihu ita ko zulfa taji haushi takaiwa Ihisan bugu sosai take fitina ya fara a tsakanin su don kowa bai kawar da ido ga danshi.
Fada sosai suke wanda wanan halin ba abin mamaki bane a tsakanin su tonon asiri suke cikin daga murya na fito don raka yara na samay su a hakan su gajiye da sauran yan aiki na daga dayan barin suna sauraren su.
Kukan da yarinyar keyi ga bakin ta da hanci najini a gurin da ta bugu yasa na kasa wucesu nace da uwar ki duba wanan yarinyar anty bakiga jini yadda yake zuba mata ba ne ?
Ta mayar da kallon ta ga yarinyar jini ne sosai yake zuba da sauri na karasa gurin na bude bakin yarinyar take hankalin kowa ya tashi nace da fatima yi sauri dauko min kada a first aids box .
Abin ba dadi yadda nake cusa kada a bakin yarinyar ina fitar mata da jini a cikin sa ashe harshen yarinyar ne ya hakori yai mugun datse shi yake fitar da jini.
Da kyat na samu jinin ya tsaya nace maza ta kaita asibiti a duba ta zaifi don ai mata alluran T,T .
Showing 243001 words to 246000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82 Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153