waje don sai nake ganin wanan ciwon nata ne ke son dawo mata kuma.
Subbahanallahi Allah dai yasa ba shi bane don bani son wanan mugun cutan yace kagab ta nan Alhaji dama zuwan da muka taba yi lagos ta sayo mata wani maganin gargajiye shi tai amfani dashi tun lokacin ya lafa.
Yanzu kuma ai Rahama batayi karan banin zuwa bata wani magani ba kuma can tunda ta riga ta zarga ta inji hajiyan daddy ke fadin hakan.
Alhajin yace haba saboda may ai tsakani da Allah ta ke mata taimako ai bai gajiya ga bawa idan ya tashi yi.
Nace ai a lagos ne mun shiga kasuwa naga maimaganin yana talla nai mai magana yabani yanzu ma ban gane wurin ai don an dade.
Allah dai ya bata lafiya inji Alhaji ya fadi cikin damuwa da abin sai hajiyan tace dama ina son ganin ku gashi Allah ya kawo ku yau.
Tace ba komai bane sai zancen sauran matan ka akan aiki da yar uwar su keyi su ka hana su korafi yai yawa daga iyayyen su don Allah suma ka sama masu aikin a bar wanan zancen hakana inda hali.
Yace hajiya ni banaki bane ai tun farko idan baki manta ba sai da na basu baki sukace Sana,a za suyi su naba kowa jari don uin sanaan don dama ni ba aikin nake so ba gare su.
Hajiya macr mai hankali da sanin ya kamata ake bari ta fita aiki ba wacce zata fita ba kimtsi ba sanin ya kamata ba don nasan kan aikin nan zamu iya samun matsala dasu watarana.
Tace na daice ka sama masu aikin kowa ya huta don uwar ita hindu har waya ta bugo min tana son yi min tijara ranan.
Don haka kaji abinda na fada ma yace itama bani na sama mata ba ai don haka kowan su ya gwada saan shi ya nemawa kan shi don ni yanzu ban ma san ta idan zan fita neman wani aiki ba can.
Kada ki manta da halinsu hajiya sai na samo kuma suce ai bashi suke so ba zan daibawa kowa baki ta fara idan ta samu din shike nan ko ?
Ni dai ina duke ban dago kaina ba a inda nake ina sauraren su ban jima ba namike nace zan je na gaida Abban anty dasu Zarah.
Sai dare muka dawo gidan a gajiye na dawo din haka ko wurin anty ban samu shiga ba ranan mukai wanka bayan munci abinci sai barci.
Ranan jajibur ma ba sauki a gidan fitina ne akan wai an yanka sa sai yabawa maigadi mijin Gajiye kafafuna da kai don ya san raba shi gareshi fitina ne.
Aiko suka ce dawa Allah ya hada su bada shi ba don gajiye na yar uwana zai masu haka aiba su kadai bane mabukata akwai masu so da yawa a gari .
Shine ya kawo masu fitina akayi kaca kaca a tsakanin su nikan ban fito ba sai labari nake ji don muna ciki muna aikin sallah saboda su Aisha bazasu iya min yadda nake so ba idan na barsu.
Sai da mama Laraba ta shigo gidan ba shiri ta tsawata masu suka daina wanan fitinan da suka sa a ran su.
Bayan tagama dasu ne ta shigo wurin mu take cewa jiya na shiga barka ance kin shigo baki samay ni ba ai nace eh mama tace harda tsaraba haka maiyawa Rahama mun gode Allah ya raya maki yan diyan ki ya tsare muna su nace amin mama don yanzu mun saba saboda dan zaman da mukayi da ita.
Na dibar mata nama mai yawa nace taje ta kara don ya yanka masu sa ita da sauran yan uwanta taita godiya tana cewa ke gashi kin bani naman da saboda kai da kafa wasu ke ta masifa a gidan.
Na dai yi dan murmushi kawai tare da tambayanta su anty Fatima yar ta yar Farida tace suna can uguwar su mai nisa shiyasa bata ganin mutane ai yanzu tunda suka koma can din.
Tace bari ta shiga taga jikin anty nai mata sai anjima ta tafi ta dan jima wurinta suna hira kan matsalolin gidan ta tafi daga baya.
Washe gari sallah muka tashi mun gama aiyukan mu don tun dare muka hada komai shiyasa muka samu saukin aiki ranan sallah.
Daddy ya shigo da kanshi har part din nawa yana saye cikin wani shadda gezena sai maiko take faman yi fara tare da yaran shi maza yayi don fita sallah idi.
Ya samu na shirya yaran ya dauki haidar bayan mun gaisa mun mashi barka da sallah.
Suka fice gidan aiko yana fita da yaran ya samu Nasir da jinior na jiran shi ya fito saiga hindatu ta rako wata kaunarta da aka aiko gunta.
Ta ce lalaima don bata san da kayan ba sai yau da ta gani a jikin su munafunci dai baya karewa a gidan nan su diya matan sai a kaisu a bola a yar mu gani.
Bai kulata ba ja yaran shi suka fice don kada su makara basu samu sallah idin ba a ranan.
Dun kai awa biyu a waje ashe saida ya biya dasu gidan mahaifanshi da wasu yan uwa yai masu barka da sallah ya dawo gida.
Part din anty ya fara shiga yai mata barka da sallah tana ganin haidar a kafadan shi yai barci tace a, a babana daga massalacin kuma kai barci ta mika hannu ya miko matashi ta shinfide shi a wurinta.
Ya dan jima ya fito ya shiga wurin Zulfa da hindatu nice ta karshen zuwa ya dubani nai mai barka da sallah ina tambayan yaran yace haidar yayi barci suna gurin uwar su ta shimfide shi can.
Naji dadin jin haka don alama ya nuna ba karamin saukowa anty tayi ba sosai ya dan zauna kamar yadda ya zauna suka gausa da kowa ya fito.
Haka akaita aikin sallah ban sha wahala ba don ga gajiye da Aisha da helen da Atika su ne karfin aiki sai fama da wayan mutane nakeyi masuyi min barka da sallah.
Sai wani lokaci aka kawo min yaran Amira tai masu wanka wai sun bata jikin su da maikon nama.
Muna cikin magana naji hayaniya ya kaure wai ashe kan girki ne hindatu tace ita zatai girki ranan zulfa tace bata isa ba ai can suke zaune da miji don haka ba ruwanta da girkin kano.
Sun jima suna fitina shiya shiga tsakanin su ya raba fitinan yace baza tayi ba dani da ita ba maigirki a garin nan sai idan mun koma can don haka bai son wani fitina kuma.
Tai masifa babu kunya gajiye na mayar min nace babu gwani ke nan a garesu don basu bar kan su ba ma balle wani shetin daine aka kullawa a tare.
Dare yayi na shiga gun anty na gaida ita sai na samu ta kwanta naga wata yar dattijuwa tazo wai gwagon ta ne muka gaisa da ita na karasa gun anty nace anty yaya dai tace dan nama biyu fa naci shine jikin nawa ya koma min ba dadi wallahi.
Nai mata sannu na dan dade a wurin ta nai mata Allah ya sauwaka na tafi don yara saboda na bar haidar baiyi barci ba a lokacin.
Washe gari sai dana karya naje gaida ta tana zaune a kasa ga cup din tea a gaban ta bata sha ba sai sanyi yakeyi .
Nace anty kisha mana kada yai sanyi tace bari Rama bana jin dadin komai jikin nan nawa sam ba dadi wallahi da kyat na samu tasha tasha magani.
Na jima na barta don ta dan huta na wuce wurin daddy na gaidashi suna tare da Zulfa na gaidasu a tare ya amsa min itama dai ba laifi ta dan amsa a dakile.
Yake cewa dani yana son mu shiga gurin su baba kafin mu koma sai dai bai san lokaci ba amma mu zauna a shiri dai.
Naji dadin jin hakan nai mai sallama na fita daga wurin su din na zagaya inda su Aisha ke aiki a gurin gajiye na dan zauna tare dasu.
Yinin ranan dai haka naji bana jin farin ciki a tare dani haka dai nake daurewa ban yi magana ba da kowa.
Zarah ta shigo mun dade muna hira shiya mantar dani komai da nake ciki a gidan mun sha hira ta tafi.
Da dare na leka anty ban dade ba na dawo don kaina yana min ciwo a lokacin na kwanta sai barci ya dauke ni har suka gama suma suka shigo suka kwanta.
Can cikin dare naji ana dukan kofana da karfi na falka kusan tare muka fito falon da Aisha dake barci a dakin su.
Nace waye yace bude Rahama nine na bude da sauri don jin muryan daddy da nayi ina budewa nace daddy lafiya dai ko a wanan lokacin.
Yace Saade ce jikin ya tsananta mata sosai ina son muje asibiti yanzu da sauri na koma na dauko hijjab dina don dan rigar barci ne a jikina dama.
Na bi bayan shi da sauri muka nufi dakin tun a kofa kanajin kugin ta tana nishi ina shiga naga halin da take ciki take jikina ya mutu don abin ba kyau .
Nai mata sannu ta dago kai da kyat tace dani Rahama kin tashi kinga jikin ya tashi kuma again tun da safe haka nake yanzu ne ya zama worst haka kuma.
Nai mata sannu ta karba tace dani Rahama don Allah ki ta hakkuri da diyan ki gasu nan zan bar maki amana a hannunki da fatan zaki yafe min.
Hawaye suka zubo min nace haba dai anty don Allah ki bar wanan magana duk zafin ciwo ne daddy yace ku kamata muje gun mota da sauri.
Dagota da zamuyi sai ta rike min hannuwa na gam tana son yin magana ba baki kuma gareta bayan maganan da tayi din.
Innalillahi kawai nake kira nace daddy kama muna ita don Allah daddy ka yafe ma anty don tana cikin wani stage yanzu mawuyaci ya juyo da sauri yana kallon mu ya karaso ya rike ta kafin wani lokaci tafara dan shakuwa tana murmushi ga magana abakinta amma baya fita batafi minti biyu ba Allah ya karbi abinshi.
Salatin da na saka ne yasa shi kara razana ya ruvumay ta ajikin shi yana fadin Saade na yafe maki na dan taba hannun tanaji ina ba motsi rai yai halinshi a saukake ta cika a dakin ta.
Wani iri kuka ne yazo min da ban san na iya irin shi ba ma nace yau nawa ya samay ni anty kin tafi kin barni da babban nauyi a kaina haka ni Rahama na shiga ukku.
Tsawa daddy ya daka min yace ke bari kuka mana kila dogon suma tayi nace ba suma bane daddy she has gone salati ya fara yana fadin yanzu Saade kin tafi kin barmu da yaran nan ke nan.
Ai take wuri ya rude da kuka na tashin hankali amma har wani lokaci har wasu makwabta sun shigo gidan.
Sai dai daga Zulfa har hindatu babu wacce ta leko sai da asuba ya kula da hakan don mu a wutin gawar nata muka kwana har safe.
Yaje ya dinga dukan kofan su da karfi yace to sai ku fito marasa imani ita nata ya kare sai ku jira naku kuna jinabinda ya samay ni amma mugun hali ya hana ku fitowa tun dare.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,
84
Kafin gari ya karasa wayewa gidan mu ya cika da jama,a yan uwa da abokan arziki sun cika gidan don anyi sanarwa a massalataiya anji.
Mama Altine da wasu daga cikin iyayye na sun iso tunda safen nan don asubanci sukayo don su samu zanaidar ta.
Muna zaune cikin tausayi da tashin hankali kakai mata komai daya dace aiwa mamaci aka dauko anty muna ji muna gani za a kaita gidan ta na gaskiya gida ya sake rudewa da kuka.
Yaran suna manne dani suna kuka aka fice da ita zuwa gidan gaskiya inda kowa dole ya halarce shi idan lokaci yayi.
Nidai har aka wuce da ita banga giccin daya daga cikin matan daddy ba a wurin aka wuce da ita mutane akabita da adduan alheri tare da fatan dacewa da rahaman ubangiji.
Rigan barcin dake a jikina dashi na wuni ranan sai hijjab din dana saka gashi duk inda nasa kafana yara suna biye dani.
Mutane basu da tsoron Allah don ranan yan uwanta suka fara wani shawara can akan abin duniya.
Dakina nake zaune washe gari ranan su Inna sunzo da kishiyoyinta da wasu yan uwa na da suka zo muna gaisuwa.
Kuka nake sosai cikin tashin hankali suna lalashina da kyat na bude baki nace Zarah dole ne nai kuka .
Zarah anty ta tafi ta barni da babban nauyi a kaina zarah yaya zanyi da wanan nauyin haka dole ne nai kuka anty ta wuce tabar mu a daidai lokacin da muke bukatan ta a tare da mu.
Tace haba Rahama kiyi imani mana duk mai rai yana tare da wanan balle yaran nan tun tana a raye kusan kece komai nasu sunan ta haife su ne kawai ita.
Kin san halin su sun san naki matsala daya ce ita wanan yarinyar da keda akidar kishi a zuciyar ta amma nasan itama zata sauko idan girma ya kara shigan ta.
Kuka nake sosai har su inna suka saka baki da sauran mutanen dake dakin da kyat na dan tsagaita kukan nawa da nake yi.
Ranan da akai uku kuma ranan abin ya dawo muna sabo don anyi kuka sosai na rashin wanan boyar Allah mai mutunci da karamci a tare da ita.
Ta samu sheda na alheri a gun mutane wanda kowa ke fatan samu ga jama,a a bayan shi.
Sai dai matsala daya shine irin yadda yan uwan anty suka nuna zalaman su a fili don muna ji muna gani suka shiga yanyana kayan da ta bari cikin rashin tunanen ta bar baya a duniya.
Ba wanda yai tunanen cewa akwai yara ta bari dama daddy ya gargade mu akan mu sa masu ido ga duk wani abinda zasuyi ga dan zaman su damu a rabu lafiya.
Shiyan na bari don bakin cikin yadda suke harkokin su a cikin nuna rashin da sukayi sun manta da anfi bukatan ganin mai kaya bisa ga abinda ta bari a duniya.
Idan kaga daddy zaiba mutum tausayi don ya ramay yai baki ya koma wani silent dashi gwanin ban tausayi.
Sai da zasu tafi ne wata sister din anty ta samay shi wai tana son ta dauki Amira ta zauna a wurin ta yai dan murmushi yace asiya sai dai kuyi hakkuri amma Amira tare da yan uwan ta zata zauna.
Don ni banda akidar barin diyana a wani wurin don haka ai hakkuri da wanan zancen kawai a barta a cikin yan uwanta.
Sun danyi magana akan wasu kaya nata yace yanzu shi ba wanan ke a gaban shi ba adaiyi hakkuri har nan gaba idan an natsu.
Su tafi don basu so haka ba sun so daukan ita Amira din ta zauna a wurin su amma fir yaki yarda da tsarin su.
Mama Altine da wanan gwagon nata suka bari a dakin anty kowa ya watse ubangiji yasa anty ta huta Allah yasa Aljannan fiddausi ne makomar ta acan itakan ta tafi da sheda mai kyau da kowa ke fatan samu ga jama, a.
Sai gidan ya koma shiru an barmu mu kadai yasu yasun mu yaran suka ce su ba zasu kwana a part din ba a wurina suka dawo har Amira din.
Ba a daina zuwa muna gaisuwa ba don mutane suna shigowa jefi jefi kwanan ta biyar da rasuwa nace da yaran su shirya muje muyiwa Abba mahaifinta gaisuwa a gidan shi.
Mota biyu muka tafi dashi har mama dasu gajiye duk muka tafi gaida Abba din yaji dadin zuwan mu yai mata addua tare da fatan Allah yasa albarka ga abinda ta bari a duniya.
Nan yai mun nasiha mai ratsa jiki sosai yake fada min girma da nauyi da kuma dadin dake ga rikon maraya in anyi hakkuri yace abin akwai wuya sai an daure gaskiya.
Kuka nake ina sauraren shi daga karshe ya juya kan yaran suma yai masu nasiha tare da ja masu kunne kan jita jita da biyayya.
Mun shiga cikin gidan suma mun masu gaisuwa muka fito don su ko ajikin su sai harkokin su kawai suke a gidan kamar ba abinda ya samay su ma.
Mun tafi gidan iyayyen daddy daga can su ma sun muna yadda ya dace babba yayi sun kuma kara jajan ta muna kan mutuwan.
Alhaji yace danj tau Rahama sai dai mu kara baki hakkuri don yanzu wani nauyi ne maigirma ya samay ki rikon maraya sai kayi hakkuri.
Don shi uban nasu yace tare zasu koma dake har ita wanan din don muso ta zauna nan wurin mu amna yace can yake son ta koma don karatu don haka aita hakkuri dakowa ma don zaki ta ganin abubuwa harda ma wanda baki taba tsanmani ba.
Kuka nake yi yai min nasiha haka ma ita hajiyan shi bamu dade ba muka dawo gida don mutanen da ke shigowa yin gaisuwa.
Don su wa
Showing 342001 words to 345000 words out of 456145 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115 Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153