shiga gulmanta ke nan a tsakanin mu.
Idan kuma dayan tazo a zauna da ita a zagi wacce bata kusa kunga hakan bai muna ba gaskiya ko yaran mu dake sauraren mu kullun zasu fara zargin mu muna fukaine ko su ma su koyi zama irin na annaminanci a rayuwan su.
Don haka don Allah mu sahircewa junan mu mu kama mutuncin kan mu mu zauna lafiya a tsakanin mu zama na amana son juna da karuwa sai kuga komay ya tafi sannu a hankali a tsakanin mu.
Amma fa ni shawara ne nake baku ba wai nace lalai sai hakan ya gudana ba don kowa da ra, ayinshi a tare dashi.
Hmmm maganan ki ai gaskiyace Rahama don baki fadi karya ba ga zancen ki tundai ni da za a kaiwa amaryan part dina mu zauna tare aiko kunga akwai matsala ke nan.
Babu wani matsala ga hakan idan kin iya kama kanki da bakin ki gare ta kika ja girman ki sai kiga kinyi power a wurin ta.
Hmm ai na yarda da ake cewa ba wayewa bane wayo dan kauye da kuke ganin su sun fimu tashin birni wayon tsiya.
Na dago ina dariya nace abin kuma sheri ne haka anty daga shawara kuma.
Tace wallahi Rahama duk sunan mun girmay ki ne kawai amma wallahi duk Rahama kin fimu wayo Allah ko.
Ki duba shawaran bada kudin nan da yai muna in badon ke ba ni ina zanyi wanan tunanen ma yanzu kuma gashi kinzo mina da wani babban shawara wanda duk maganar ki gaskiya ce a cikin sa.
Sai bango ya tsage kadangare ke shiga kafarsa ai idan muna kama kan mu, muna abin mu in matuarity wa zai kawo muna raini a gidan nan.
Mun dauki lokaci muna hiran mu duk dai akan matsalan rayuwan zaman gidan daddy ne da yadda za a dora dashi.
Kwasan ba zato sai ganin daddy mukayi a falon kowan mu ya baje sai kwasan dariya muke yi a falon.
Kallon mamaki, muka bishi dashi har ya kataso cikin falon shima sai bin mu yake da kallo yana mamakin kasancewar mu a wuri daya haka.
Sannu da zuwa muke mashi hankalin shi na kan yan yaran dake zaune a gefen mu suna shan lollipop ko kallon shi Antyna bata yi ba zakace ko wata babbace ita irin yadda ta share uban nata.
Ya karasa gunta yana fadin yau kuma wani sabon sallo kuka dauko ne a gidan haka yakai hannu ya dan taba yar wirin hindatu yana kiran sunanta sai ya juya gun ta zulfa ya lakaci fuskan ta ya dauki anty yana kiran sunan ta tare da ce beta yana fadin my Saade ke nan .
Sai yarinyar takama bultsewa tana son ya sauke ta tana fadin umm, umm ummm yace da ita kai my Saade badai kema kin iya fushi ba ko ?
Ba wanda yai mashi magana bayan gaisuwa sai da yaga yarinyar bata yarda ne ya direta tare da cewa ai ke zaki biyo ni sai Zulfa tace tunda an saba bin bayan ka ba.
Dama ai kunfi kusa ta hannun damarka ce din da sauri hundatu tace da ita haba dai kuma.
Yana sauke yarinyar yake cewa ina sauran yaran ne suke bashi amsa da suna school basu dawo ba tukun.
Ya juya zai fara tafiya sai naji hindatu na cewa dashi amaryan fa tana can ne ya dan juyo yana cewa tana part din ta mana.
To sundundun ke nan haka ashigo kamar munafuka kuma ba ko sallama asan da zuwan ta gidan shiru nayi nasa dama mai hali baya barin halinsa ai.
Abu ne mai wuya su bar hslin nan don ya zama masu jiki ko don kowa da kalar nata kishin a rayuwan ta.
Bai dade da fita ba suma suka watse kowa ya koma part din shi da zama don dama zaman na ranan ne kawai aka dan yi shi .
Ni dai ban sake bin ta kan shi ba dama akwai gajiya a jikina tare da yarana muka kwashi barcin mu na rana sallah kawai na tashi nayi na koma na kwanta abina sai shidda da yaran suka dawo gida na tashi.
Mun dan zauna dasu har bayan magariba ina idar da sallah na fara shirin fita don zuwa duty Aisha na tsaye tare dani tana fada min cewa jiya ma da kyat ta samu daddy yai barci nake cewa sai yayi hakkuri uwarshi ba mai zaman gida bace anytime.
Daddy ya shigo dakin a daidai lokacin da nake magana ina saka rigan aikina daya tsaya min daidai saman kayan dake jikina.
Sannu yaran suka fara mai ban juyo inda yake ba saida na gama na juyo yana duke rike da hannun daddy karami suna magana.
May ke faruwa ne kuma Rahama naga kowa ya shiga gun amarya ke baki shiga ganin ta ba mana tun dazun.
Wani kallo na jefa mai daga inda nake tsaye tare da cewa wa ni daddy wani komawa baya kuma zai kama ni da tazo ta sama a gida bata nemay ni ba sai nice zan je gunta haba dai abin nawa bai kai can ba ai.
Murmushi yayi yana dan girgiza kan shi tare da fadin bakuwar ku ce fa shine kuma wani matsala can daban.
Nace bakuwar ka dai daddy may ye hadina da ita ni kuma da zata zama bakuwa don Allah dai abar ma zancen.
Yace hmmm Rahama Rahama wani lokaci sai kiyi wani abin takar ba ke ba wallahi may ye na komawa baya don kinje kun gaisa kawai da ita.
Nace to yar gidan sarakai ko to talaucin nawa ni baikai can ba tukun na kai hannu na dauki hand bag dina yake fadin wai ina zakine kuma ?
Nace wurin aiki night duty na shiga week din nan na fara ok abin yakai har ki fara baki fada min ba ban sani ba kuma.
Nake cewa kamar ya ban fada ma ba tunda kasan dai aikina ne hakan banda choice akan wani abu kuma.
Na dago alaman zan fara tafiya yake cewa dani Rahama sai na dakata shiru yayi tare da kura min idanuwan shi a kaina.
Nima din kallon nasa nakeyi sai dai ba zan iya jurewa ba na dukar da kaina yace kada ki bullo min da wani sabon halin da ban sanki da shi ba a baya akan kawai na kara aure.
Naga dai ba wannan ne karo na farko dana kawo maki kishiya ba a gidan nan ko yarinyar dabaki ko santa ba, baki san waye ita ba kike son ki kirkiro wani fitina a kan ta kuma.
Nace fita akan kayi aure zanyi fitina ko may niba mata na sama a gida ba ni har ina da bakin magana ni da akai maka dole a kaina ba da son ran ka ba.
Yace ok haka kikace ko nace dashi ai haka din ne ni har wani kadari ne dani gare ka dama matar cushe ba wani power ne da ita ba sai hakkuri don haka duk matan ka ni ba wacce nake kishi ina dai zaman abinda aka dauko ni yi ne kawai .
Kuma ina fatan Allah ya bani ikon cinye nawa kalar jerabawan na rikon marayun da ya hau kaina da karantana.
Yace haka kika ce dai ko ?
Dama ai hakan ne daddy yace no warder naga baki taba kishina ai a rayuwan ki sai dai masu kaunana suyi.
Nai murmushin dole duk da raina a bace yake nace, Daddy nayi kishin hauka na zama wa a gurin ka aiko dana ji kunya kishin mijin da yake na mamajo kullun aure.
Wani sabon suna na samu ke nan kuma a gidan dama tun dawona dana samay ku haka a wuri daya nasha jinin jikina kan akwai abinda ake kulla min a wurin kuma.
Gashi kuma yanzu na gani da idanuwa na tun ba a kwana ba kin nuna a zahiri don ban sanki da saurin sarewa ba irin haka ?
Ban iya magana ba sai duban time din da nayi alaman zai sa na makara ya fara tafiya yana fadin dama mata ba a shedan ku ai na gaskanta hakan yanzu.
Indai akan kishiya ce har kai min mumunar fassara ba damu inda saniyar gaba tasha ruwa kona baya a nan zata sha itama.
Bai juyo ba ya sa kai ya fice daga dakin na sauke ajiyan zuciya nabi bayan shi tare da yara da sukai min rakiya kamar wacce zatai tafiya ba duty zan tafi ba a lokacin.
Ban yafi ba sai da nai masu abinda na saba gaba dayan su har manyan nabawa kowa abinda ya sauwaka a hannuna daga can na hango daddy yana fitowa daga part din amarya da sauri na kawar da kaina daga ganin shi na tayar da mota na bar gidan.
Ashe bayan tafiyana yake tambayan yaran na tafi ne suka ce yanzu na fice daga gidan ai.
Bai tsaya ba ya barsu ya shige wurin shi kai tsaye tare da turo kofan shi ya rufe suma shigewa sukayi wurin mu tare da rufo kofan part din.

********* ********* *********
Washegari a gajiye na shigo gidan ban daki na fada nai wanka tare da cire kayan aikin da na dawo dasu na aje a inda muke tara kaysn wanki na na kullun.
Abinci Amira ta kawo min ta zauna tana zuba min ni kuma ina shiryawa hira muke da ita a kan Jinior muna kwasan dariya sai ga Aisha ta shigo dakin.
Tace mummy dazun ai naga amaryan daddy a waje tayiwa kawayen ta rakiya mummy baki ganta bane fa wata, , , ,
Haba Aisha don Allah rabani da zancen ban haushi ko ma yaya take ai haka yaga abinshi ya dauko ko wa kan sa namiji ina ruwan shi da wani siffa idan ya tashi son mace.
Wai ni mummy may yasa daddy yin aure ne kuma sai fa da Za,id yai min magana kan auren nan da daddy ya kara ranan, cewa da wanda zata aura din.
Nace may kikace dashi ke tace cewa nayi dashi ina ruwan sa bana son yana mun irin wanan maganan again don ba abinda ya shafi rayuwan mu bane.
Nace kinyi daidai Amira don da da haja sai yakai ga fada maki maganan da rayuwan ki zai kai ga baci .
Tace ai ban daukan wanan raini ne mace ta dinga bari mijin ta ko saurinta na zancen yan gidan su a gaban ta tana kyaleshi watarana abinda zai fada sai yafi wanda ya fara fada mata da farko.
Nace kai ashe yar tawa tayi girma da wayone haka lalai daddy nada gaskiyan shi dayace aure zai maki .
Tace kai mummy auren may can kuma don shi yana son aure shine ni zai ce ai min nifa masters nake son na yi fa idan ma na gama.
Ke rufawa kanki asiri da wani karatu can kya karasa a dakin mijin ki idan kunyi aure in kuma kin haihu to shike nan kuma sai a zauna raino.
Da sauri ta fado min a jiki tana rufe min baki tana cewa kai haba haba mummy tana dan jijiga min jikina.
Uban ne ya shigo muryan shi mukaji yana cewa ke ke ya haka kuma uwar taki ce kuma kikewa haka kuma ku ba kwa girma ne wai ?
Da sauri ta daga min a jiki tana dan turo baki tace daddy mummy ce fa nice nai magana da cewa mutum bai awasa da dan shi ne ni haka nake da diyana.
Ke fice min da wanan shirmayn banzan naku don Allah zanga maman ki ne da sauri suka fice daga dakin.
Ya karaso inda nake zaune bakin gado yana kokatin tungumoni a jikin shi da sauri na dago ina kallon shi cikin mamaki nace amma dai kasan hakan bai dace ba don bani ce dakai ba.
Sai akace don ba ke ce dani ba kada na taba ki kuma ko ?
Kara kai hannun shi yayi yana kokarin lalabana da sauri na kauce tare da mikewa tsaye ina fadin mutum da amarya tsaleliya ya dawo yana taba tsohuwa kuma ?
Sai naji yaja tsuki tare da juyawa zuwa bakin mirrro dina ya tsaya yana fadin ina son mu hadu idan anyi sallah a falo na Allah ya kaimu nace dashi kawai.
Ya fara tafiya ina bin shi da kallon yadda duk mood din shi ya canza daga yin magana kan amaryan ta shi.
Sai na fahinci da akwai matsala duk yadda akayi bisama idan anyi la, akari da yadda suka dawo batare da sunyi sati dayan da sukace zasuyi ba a kano.
Wanda nasan sun zauna can ne dama don ya samu hutu da yar amaryan shi kada ya dawo nan a damay su sai kuma gasu ba sukai satin ba sun shigo.
Yana fita na dan leka yaran na dawo na samu wuri na kwanta sai barci ban falka ba sai da Amira ta shigo ta tayar dani.
A Lokacin har karfe uku saura da sauri namike nai sallah na gyara jikina sai ga wayan daddy ya shigo min ina dauka yake cewa dani wai may kike jira har yanzu muna ta jiran ki.
Nace gani tafe ai tsab na shirya sai kamshi nake na nufi falon nashi inda na samu duk suna zaune a falon nice kawai ban shigo ba.
Nashiga da sallamana abinda ya fara tarona shine yarinyar da na hango zaune gap da daddy a saman kujera daya dashi wanda ba kasa fai muke irin wanan zaman ba indai za ai irin wanan zaman.
Maimakon na zauna saman kujera sai na koma daga bayan kujera naja na tsaya tare da cewa gani naji kace kana nema na ?
Yace zauna mana baki ganin kowa a zaune ne nace dashi eh to na dai gan su a zaune sai dai zaman ne naga kamar babu tsari yau gare shi don kasan ba haka muka saba zama ba ai.
Ya dan yi murmushi tare da daukan remote ya rage vollume din tv dake aiki a looacin ya ce da yarinyar ke Ni,ima koma wurin yan uwanki ki zauna.
Sai taunan chewgun take yi kas kas ta dago kai da sauri ta dan kalli inda nake tsaye kamar zatai magana sai ta mike ta nufo gefen da zulfa take ta zauna.
Na samu dayan kujeran na zauna a kai may karatu kada kiga laifina nayi hakane don saurin yankewa fitsaran da naga yarinyar tana shirin muna shine dalilin danai amfani da wannan hikimar na fahintar dashi yakuma gane bazan zauna ba a yadda suke zaune din nan.
Yace damu ok dama na kiraku ne don na gabatar maku da Ni,ima a matsayin sabuwar abokiyar zaman ku a gidan nan.
Ya juya gunta yana fadin Ni,ima ga mata na da nake aure nake kuma tare dasu kuma uwayen diyana a gidan nan.
Wanan itace zulfa itace ta maye gurbin uwargidana da Allah yaiwa rasuwa sai kuma ta biyun itace hindatu ya nuna ta yace wanan kuma itace kike biwa watau Rahama ke nan.
Sai ta dago kai tana min wani irin kallo tana tauna chewagun tare da wani mayde bakin ta a yatsune fuska.
Ya juya gare mu yana cewa wanan itace Ni,ima da na auro na kara a acikin ku da fatan zan samu zaman lafiya a tsakanin ku.
Babba ya rike girman shi haka ma karami ya rike nashi a matsayin karami Ni,ima da fatan zaki zamo mai biyayya a garesu a zauna lafiya.
Sai may muryan yarinyar naji tana cewa idan sun so a zauna lafiya may zai hana sai dai bazan yarda da saka ido ko shishigi ba a rayuwana.
Na dago ina kallon yadda take magana tana wani har da idanuwan ta baki na magana hanci na magana ido yana magana nace tau, , , ,
Tana fadin haka sai ta mike ta bar falon yana kiranta ko juyowa batayi ba ta shige abinta.
Gaba daya muka bishi da kallo don kowa yaga abinda ya dauko wanan karon a gidan kuma a zahiri watau fitsara ya shigo muna kuma again.
Zulface ta kawar da shirun da falon yayi da fadin tau dada yanzu sai yaya kuma ka daiga abinda ka kwaso kuma wannan karon.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,

103
Ba shi ba da ya dauko ko mi dake wurin munji kunyan abinda yarinyar tayi mashi a gaban mu don mijinka daraja ke gare shi a idon ka da kima.
Amma sai ga wata a gaban mu ta zubar da wanan darajan nasa da kima da mutunci da muke gani a gaban mu.
Hindatu ne tai karfin halin karawa da cewa eh gaskiya yau kuwa mun gaskanta yarinya ka dauko wa kan ka don nishadi tunda mun ga irin kalanta ta tun yanzu.
Mikewa nayi tsaye tare da cewa da su Allah ya bamu alheri na barsu a zaune har lokacin bai iya cewa uffan ba.
Ina shiga na zauna falo don duk yaran suna zaune a falo hira suke jana dashi amma na kasa basu amsa sosai sai Amira ce ta dan maida hankalinta a gareni tana cewa mummy halan anyi wani abune
Showing 420001 words to 423000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141 Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153