nakeyin abina tun mama nacewa wai Innata tana sa ina masu jagwalgwale har ta gaji ta sa ido ranan girkin inna ta idan na dawo tallah da wuri kafin naje diban ruwa zan tsaya na taya ta aikin girki da gyaran gida.
Haka yasa yanzu ban sha wani wahala ba a gidan auren nawa da na tsinci kaina a ciki da rana tsaka.
Yau da yake ba fita hira yakeyi ba sai gashi ya dawo gurina tunda magariba, anan yai sallolin shi kofan daki inda yasa nai mashi shimfida.
Nakawo mai abinci na koma daki na zauna ina ciki naji ya kirani yana cewa fito mana Amarya ki barni kuma ni kadai a waje ina maki gadin kofa.
Haka yasa na fito daga ciki na samu gefen tabarman da yake zaune na zauna can dan nisa kadan dashi.
Ya soma cin abinci koda na fito yace wai ke waya koya maki girki haka ne yar karama dake amma kin iya girki haka.
Nace Lah inna ta ce ai nice ke mata girki idan ina gida, yace kai amma gaskiya ta kyauta min sosai.
Yaushe rabon da na dinga cin girki haka acan acan mai dadi a gidan nan ?
Cikin shirmay yara nace kai haba Alhaji ga mama hausatu ga mama hauwa ga kuma yar barayan ka duk kace baka cin girki mai dadi ?.
Yace ai sunayi amma nakin yafi dadi ne Amarya da ina da lafiya ai wanan girkin da kika iya da na more ma hannun ki .
Don ance yadda mace ke aikin ta ko mai nata haka ake samun shi nace to kila magi ne basu sakawa kamar yadda nake sakawa a nawa ?
Murmushi kawai naga yayi min yace to ke naga bakici komai ba mana ko har kinci naki ne ?
Sai da na dan tabe baki can nake cewa nifa ko a gida tuwo bawai ya damay ni bane nafi son naci shimkafa komai rashin dadin shi ko abu mai dan ruwa.
Shiyasa ma mama takan ta fada da inna ta wai itace take koya min rashin cin tuwo gani diyar tallakawa dani sai karya.
Nace kuma fa Alhaji babu laifin Inna a ciki nice dai bana so idan an matsa min naci sai na amaye shi kaf.
Yace ikon Allah abin naki halita ne ke nan nace haka naji Inna ta tana fadi shiyasa koda zanyi auren nan maganan inna ta ko yaushe shine kada nai sakaci da kunnu don shine abincina.
Yace to ashe sai na dinga sawo maki shimkafa kawai kina sarafawa kina ci ko ?. Nace a, a kada ka wahal da kanka ai na saba da hakan don ni abinci bai damay ni ba.
Yace ashe shiyasa man shanun da na sayo maku ke naki kamar ba, a amfani dashi tunda baki cin tuwo ?
Muna cikin haka dashi sai ga mama tashigo gaidashi tace a, a ango da amarya ake hira ashe Sabuwa na bayan ta tafe.
Sai ji mukayi tace ai abinda yakeyi ke nan yana biye mata kullun jiya wa yau abu yaki ci yaki cinyewa an kwaso muna mai farar kafa tana batun mayar damu marayun dole.
Haba Sabuwa may yakawo wanan magana haka kuma a gurin nan wanan yar cikin taki ne zaki tsaya yiwa wanan magana haka ?
Tace Allah ya raba yata da wanan bakin jaraba na wanan yarinya dubaki gani don tsaban rashin kunya wai zaune take shimfida daya da Alhaji adole ita wai ga mace ?
To yin haka laifine kuma mace da mijinta ana raba su zama ga shimfida daya tunda anriga da anzama daya ko ?
Dama yaya kune masu daurewa karya gidi ai take gani kamar ta kai mace ?
Kai yauko ga wata magana ga sabuwa uku gareki uke ke gareta to mayye banbanci a nan.
Ya dakatar da ita da cewa yanzun dai may ya kawo ki nan din don ina fama da kaina ban son fita ?
Tace dama zuwa nayi naima yaya jiki sai na samu kana ma a cikin raha ne ashe kai ?
Yace eh kin san ina gurin da ake kwantar min da hankali kamar yadda nake bukata ko yaushe.
Ai naga alama sai ayi a sannu don kaji dokan likita idan da son samune ma kabar gurin yarinyar nan har ka samu lafiya don nasan kana ganin ta ba kyaleta zakayi hakana ba ?
Yace shi likitan ne yaba da dokan na kauracewa iyalina din ?
Kada na basu kulawan da ya dace dasu sai na nisance su ko ?
Kadai yi a hankali don ko banza ita a ganiyar kurciyar ta take yanzu tunda jarababban yarinya ce ta na iya saka yin abinda bashi ba ?
Yace kamar yadda kika sani yin dole shekaran jiya ko kika tashi kashe ni ke nan ?
Idan ban kashe ka ba ai wanan mai ido tsakiyar kai zata kashe ka ita.
Ta juya ta wuce abinta yace sakariyan banza kawai mara hankali da tunane.
Nan mama dake sauraren su tun zuwan su ta nisa tace kai halin sabuwa sai ita kullun ba a girma.
Yace ina girma ga sabuwa anan bakin kishin yarinyar da bata ma san tanayi ba yana batun kashe ta don ita kanta kawai ta sani a duniya.
Sai lokacin nace mama ina batun zuwa gaida ke da wuni sai gaki kuma kin shigo yanzu tace to na hutar dake ai nazo duba jikin maigidan ne dama.
Yace jiki Alhamdullahi da sauki sosai yanzun ma nake batun shan magani na da likita ya ba ni ai.
Tace to amma malam a tsaya ga na likita kawai ba a dan gwadawa dana gargajiya agani kuma ko a dace.
Yadda aka fita dakai a gidan nan fa shekaran jiya ya tayar wa kowa da hankali sosai.
Yace ai ina kan gwadawa ke ma kin sani al,amarin ciwo ne yanzu idan ya kama sai a hankali fitan shi.
Ta nisa tare da cewa haka ne kuma Allah dai ya kawo sauki kawai za, a ce .
Ta juyo inda nake na dukar da kaina ina wasa da kafana dana ke kadawa a hankali, take cewa to mu kwan lafiya Amarya.
Nace mama Allah ya bamu alheri tace amin ta juya tafice tare da rufo min kofan shigowa sashen nawa.
Yace bari na koma daga ciki sai ki samu ki shige da kayan nan ciki ko ?
Nan ya mike da kyat zuwa cikin daki ni kuma naci gaba da kawar da kayan da yai amfani dasu a gurin.
Haka a dadafe yai kwanakin da zaiyi a daki na ya koma gurin sauran matan shi can.
Ranan naji shakat a raina don nan yake zaune duk wanda yazo gaishe shi ciki zai shigo su gaisa dashi.
Haka yasa na kasa sake jikina a gurin nawa don yawan manyan mutanen kauyen mu da ke shigowa gaida shi.
Shi ko na lura yana jin dadin azo a samay shi a gurin nawa da yake acan acan ko yaushe a cikin gyara da kamshi.
Don ina manejin dan kayan kamshi da anty ta turo min dashi daga birni saboda mama altine ta kashe lokaci gurin yi min bayani a kan kamshin dakin mace.
A ranan da ya koma dakin mama washe gari sai ga Iyyaye na sun samu labarin rashin lafiyan nashi sunzo gaida shi.
Ina dakina ban san shigowan su ba ashe har sun dan jima da shigo sai mama Altine ne ne kewa ni banga diyata ba fa ?
Lokacin mama ta tura a kirani ana fada min na taso da murna na nazo dakin inda suke da zuwa ina ganin su maimakon nai murna sai kawai na fashe da kuka kawai.
A, a ashe da mun san haka zakiyi muna da bamu zo ba sai dai mu tsaya daga kofa mu gaidashi mu koma.
Da kyat suka samu nai shiru mama altine tace ashe har yanzun yar tawa bata daina wanan tabaran nata ba ?
In banda haukanki ai sai a dauka ko wani mugun hali ake maki gaki kinyi kyaunki bulbul dake daki ya karbe ki.
Na kara shigewa jikin mama altine ina cewa wallahi mama nayi fushi ace idan ita Inna ta taki zuwa ta dubani har dake mama bazaki zo ki gan ni ba sai kace nai maku wani laifi ?
Yanzun baga mutanen gidan ku masu kirki da karamci suna kula dake ba duk halin da kike ciki fa muna da labari.
Mama altine da dayan makwabciyar mune kawai suka bini zuwa dakina ita Inna ta taki zuwa nan ta zauna dakin mama hausatu har su fito daga guri na su tafi.
Narasa irin taron da zan masu don murna nace mama ni nama rasa may zan baku wallahi tace, ba mu ruwa ya wadatar damu tunda munsha a dakin yar uwarki amma zamu sha naki.
Ruwan randan kasa na da yai matukar sanyi har naso bayan randan ke bayarwa don sanyi.
Na debo masu suka kinkima sosai nan muka kara gaisawa dasu suna ta yaba kyaun dakin danayi.
Nace mama yaya wajen anty na kuna da labarin ta ko ?
Tace Anty ki Alhamdullahi don ta samu lafiya sosai har naji tana cewa tana son zuwa ta duba mu ma nan.
Nai murna kwarai dajin wai antyna zata zo garin duba mu mun jima da su mama muna dan hira sukace zasu koma sai ga yarona habibb da leda wai Alhaji yace abawa bakin da sukazo suyi hakkuri.
Ban tsaya duba ko may ke cikin ledan ba na mikawa makwabciyar mu ledan sukace ashe mu dawainiya muka kawo maku kuma mu da mukazo duba lafiyan maigidan.
Kafin su barni su kara jamin kunne nayi hankali da Sabuwa da diyan ta a gidan don gujewa makircin su.
Ban sani ba ashe bayan tafiyan su fitina ya tashi tsakanin Alhaji da Sabuwa wai don may zai ba su mamana leda da abuba ciki ?
Wa nafi da zai fifita uwaye na akan su ai itama matan gidan su suna zuwa gaidashi amma bai taba basu komai ba sai ni za , abawa iyayyena.
Da kyat aka samu wutan ya mutu bayan kakausan kashedin da yai mata yana hurta sai ya sake ta wanan karon.
Jin kalman saki yasa ta ja bakin ta tai shiru tasan tunda ya furta hakan zai aikata ne don bai taba hurta mata kalma na saki ba a duk rikicin da sukeyi tsakanin su.
Sai gashi yau akaina yana furta mata cewa ta ishe shi da fitina a gida ai itama wasu ta samu a gidan kuma ba abinda bai mata ba lokacin da take ganiyar amarcinta har zuwa yanzu.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,


IDAN KIN BIYA KIKA BAWA WACCE BATA BIYA BA ALLAHNA GANIN KI DON AMANA NE A GARE KI YAR UWA, , ,

10
Sannu sannu sai gashi lokaci yana ja a wanan lokacin duk wani dan matashin yaro dake gidan idan dare yayi muma shiyana muna karatu, wanda suke jin dadin hakqn anan zamuyi ta shirmay har dare kowaya watse.
Bayani nake masu sosai yadda zasu fahinta gakaratun da suke dan tsinta a gurina.
Wani lokaci kuma novel zan samu mai dadi da ma,ana da koyar da wani abinda ya shafi fannin rayuwan dan adam.
Zan dafa abinci na zuba a babban tire nan zamu taru muna ci muna hira muna dariya abin dai na kurciya zallah kawai.
Har zuwa wanan lokacin zama na da maigidan kamar kullun ne ya kan yi iya bakin kokarin shi don yaga yadda zai yi ya dan samu gamsuwa.
Sai dai hakan bai yuyu ba a gare shi don da alama matsalar shi tana nan mai bai gushe daga gare shi ba.
Don idan yaso ya kai gare ni sai naji yana zufa yana wani irin kugi mai fitar da wani sauti na ban tausayi.
Ni kaina nakan matukar jin tausayin shi idan ya shiga wanan halin don haka zai wayi gari ya wuni a wahalce dashi dashi.
Na fara fahintar wasu abubuwa duk da dai wayo na baikai na fahinta ba a lokacin amma sai nake fahintar ba gani kadai hakan ke faruwa ba har ga sauran matan shi musanman ma dai sabuwa.
Idan ya kwana a dakin ta zanga ya tashi wani lokaci ba dadi har aka fara dan rade radi a gidan abinka da gidan yawa.
Ranan mama da kanta take bugun cikina akan zancen take cewa dani wai amarya kuna dai biyewa wa maigidan yaki natsuwa har ta samu lafiya komai ya zama daidai ko ?
Nace mama na daina zama ne idan yana daki kike nufi?
Ta kama baki tace wane ni da fadar haka amarya rufa min asiri tace ni dama cewa nayi kawai ki dan kaurace mai ga shimfida irin ki dan rika ba da lokaci din nan .
Kin san shi namiji kullun a bukace yake da mace ba ruwan su da lafiyan su koda hakan kuwa zai masu illa ne.
Nace mama kina dai nufi idan yana daki na fito waje na barshi ya huta ya samu hutu sosai ko.
Nan dai ta gane shirmay na bai bari na fahince ta sai ta fito min fili tai min bayanin komai a baiyyane.
Cikin canza fuska nake ce mata gaskiya mama ni Alhaji bai taba nuna min wanan abin ba a tsakani na dashi sai mutunci kawai.
Kan ta ya daure ba don ta yarda ba don tasan hakan ma ba zai faru ba koda kuwa ace ni ba yarinya bace yaya zan zauna har wanan lokacin.
Karshe dai sai cewa tayi dani ki daiyi a hankali kinji kada ki yarda ace an samu wani matsala a kan ki kinji ya ta.
Nace to mama nagode Insha Allahu zan kula kamar yadda kikace din.
Sai gurin karima sarakuwan tane ranan take kara fayyace min yawan hasashen da ake mun a gidan kan lafiyan Alhaji.
Muna hanyan makarata ne take fada min komai tare da jamin kunne akan na kara kulawa sosai.
Tun ranan ban yarda ko dan tabanin da yake ya samu relief din da yake yi na daina bari yanzu.
Har abin ya fara dan damun shi da yai min magana ban boye mai komai ba na fara kuka ina fada mai abinda akace ina yi mai.
Ya gane anja min kunne ne akan haka yasa ya daina kada ya jamin bakin jini ga iyalin shi don su a ganin su nice ban bari ya samu sauki.
Ranan dakin mama hauwa yake ciwo ya murtuke shi a cikin dare aka kwasa sai asibiti.
Nan suka fara fahintar cewa ciwon ne dai bai bar jikin shi ba ba yadda suke hasashe bane.
Koda aka dawo dashi gida wanan karon andai dawo ne amma yana matukar jin jikin shi sosai.
Don yakai idan zaiyi fitsari ma kusan zakaji yadda yake faman nishi da kugi kafin fitsari yazo mai.
Wasa wasa ciwo sai gaba gaba yake mai ya ramay yai baki sai dan wuya takai ma yanzu bai fita kamar yadda yakeyi a baya.
Cikin haka ne ranan aka aiko babana yai faduwan mashi a hanyan shi na dawowa daga kasuwan kauye da yake zuwa.
Alhaji ya samu labari don haka yana dakin sabuwa yasa a kirani nazo na dan rusunna daga kofan dakin nata don ban yarda na shiga daga ciki ba don ta cikin dakn zaune a lokacin.
Yake cewa dani yanzu nake jin labarin abinda ya faru da mahaifin ki jiya shiyasa na kira ki.
Ki shirya sai zuwa ta rakaki ki dubo shi amma kada ku wuce goma ku dawo gida.
Nace na gode cikin murana wanan ne karo na biyu bayan aure na da naje gaida mahaifana.
Na farko tare dashi muka tafi ban ko kai minti talatin ba baba ya matsa min nafito muka koma gida.
Sai wanan daya bani bako mu tafi da zuwaira na dubo jikin mahaifina ko shi nasan don baya jin dadi ne da tare zamu tafi dashi.
Tsab na shirya cikin katon hijjab sai nikaf dana dora akai duk d dare ne amma na saka nikaf din na tare fuskana da shi.
Har mu uku muka tafi don Aisha ta biyo mu da taga zamu fita tare da zuwaira din.
Da sallama muka shiga gidan a tsakar gida muka samay su suna shan iska tare da baba.
Nan muka durkusa muka gaida su tare da mai yaya jikin shi da Allah ya sauwaka ya tsare gaba.
Sai can yake cewa wai Rahama ke ce ai ban gane kiba ikon Allah ya kuke ya gidan duk kuna lafiya ?
Yaya shi maigidan naku da na sa jikin dafatan ya samu sauki ko don ance jikin nasa ba dadi kuma ?
Bayan mun gama gaisawa da baba ne da tambayoyin da ya jero min na juya inda mama take tayi tsit tare da kura min ido.
Ko may take kallo hakana ban sani ba daga jikina na daiga duk da dare ta kura min idanuwan ta a kaina.
Nace mama mun samay ku lafiya yaya gida ashe baba kuma wani kaddarane ya samay shi haka?
A cikin basarwa take amsa min gaisuwa na a tsatsaye na gaida Inna ta dake zaune a gefe tana motsa kunu mai zafi data dama ina ga na baba ne.
Can na mike na leka dakin mama gurin su Lawisa suma ba wani karban arziki ne na samu a gurin su ba.
Na fito na shiga dakin Inna ta na samu kannena zaune suna dan hiran su, suna gani na suka
Showing 36001 words to 39000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13 Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153