mama laraba take kula dani sosai ita kuma Attu tana dawainiya da jariri da kan ta.
Naji dadin kasancewan su tare damu sosai don ba karamin kula suke bamu ba dagani har baby din yadda ya dace ayi a aladan hausawa.
Duk da ba sabo nayi da mutane ba sosai amma suna shigowa jefi jefi yin barka zaman bariki ke nan wani ko don ya shigo yaga yanayin gidan ka zai shigo tunda daman shiga ya samu gare su gashi kuma na aika masu da haihuwan dama.
Saboda haihuwan da nayi yasa daddy yai kwana biyu sai ya juyo Abuja ranan da zai dawo kwatsam ya fadawa anty cewa zai tafi da Nasir da jinior Abuja don akwai makarantan da yai masu register a can tare kuma da ihisan zasu tafi.
Take tace dashi bata yarda da hakan ba yace ba yardan ki nake nema ba umurni na bayar a shirya su in da abinda za a shirya masu su tafi.
Take ranta ya baci taso saka tsauri sai da taga ba gudu ba ja da bayane ta nemi hajiyan shi da kuka take fada mashi zancen tafiya da yaran da yazo mata dashi.
Hajiya tace haba Saade ina shi ya haifi ditan shi kuma ba wai ya dauke su daga gareki bane gaba daya karatu ingantattace yake nema masu.
Wai may yasa kuke hakane please kin fa san inda za, a kaisu ba wai wuri bane na mugunta ina kin san halin Rahama akan yaran ki in banda so da kauna ba wani abu a tsakanin su.
Yarinyar da tun bata mallaki hankalinta ba take a hannun ki don yanzu kishi ya hada ku tare idon ki zai rufe har ki manta da irin amanan da ke tsakanin ki da yarinyar nan.
Yanzu ne baki kaunar hurdan ki da wanan yarinyar ko may ?
Ko har kin manta da irin mutinci da yardan dake tsakanin ki da wanan yarinyar a baya yanzu zaki rufe ido ki nuna baki san halin wanan yarinyar ba ?
Ko har kin manta saboda kishi yardane fa yasa har kika amince kika zabo ta da tazo ta rike maki zurian ki koda bayan ki kika aminta da ta zauna da mijin ki don yarda da tarbiya da kika bata da hannun ki ?
Wanda har muke ganin a lokacin hakan bai dace ba sai bayan shigowan ta muka gane cewa bakiwa kan ku zaben tumun dare ba.
Sai yanzu ne kuma zaki dawo ki nunawa mutane cewa alharin da kika shuka dama bada zuciya daya kika aikata hakan ba da wata manufa kika aikata hakan gare ku ?
Sai kuka yazowa anty tace hajiya da wata manufa kuma fa kikace tace eh man da wata manufa mana in bashi ba may ya rufe maki ido haka har kika manta da makomar ku ga Allah.
Yarinya na faman binki kina ta zubar da mutuncin ki da kimar ki ga idon yarinya don ma kin samu yar albarka da tasan ciwon kanta da yar zamani ce da bata san halarci ba may kike zaton zai faru a tsakanin ku.
Yaro yau ko kaika haifeshi yaya ka kare dashi balle an baka aman shi riko idan zakiwa kan ki fada kiwa kan ki ki kama mutuncin ki zaifi maki alheri kin ji na fada maki.
Anty sai kuka take sharba don nasihan hajiya yai matukar shiganta sosai sai dai har lokacin gani take anci amanan ta.
Daddy yana gama shirin shi sallama kawai yai mata ya kwashi yaranta Amira kawai ya bar mata don ta taimakawa uwarta da wani abin.
Kuma yasan cewa zuwanta a halin yanzu wani sabon fitina zata kara haddasawa a tsakani wanda zaita kawo rikici a tsakanin mu ko yaushe.

********* ********* *********
Muna zaune sai ganin su mukayi ya iso da yaran kowa yayi mamakin ganin su sai dai ni da dama ya fadawa cewa yaran zasu dawo nan da karatun su.
Su mama sun dauka hutu sukazo sai da suka gansu da jakkunan kayan su ne suka fahinci da akwai magana.
Ihisan taki sake jikin ta sai shan toka yarinyar keyi duk wanda yai magana a hasale zata bashi amsa.
Ashe ba karamin rikici akayi ba da yaje ya dauko yarinyar a gurin uwar ta sai da mahaifin hindatu yazo yasa baki ya wuto da yarinyar din.
Ina dakina kwance daddy ya shigo dakin idanuwan shi a kan mu ya dan rankwafo inda nake yace barka da arziki nace barkan mu daddy kuna lafiya ya baby din yake kuma ?
Na juya inda yaron yake kwance a cikin showel nace gashinan kwance gurin yaron ya duka ya dauko shi ya dade dashi yana mashi addua kafin ya aje shi yana fadin Alah ya raya muna Aliyu haidar acikin amincin shi.
Na lumshe ido nasan sunan da yaron yaci ke nan in ban manta ba sunan mahaifin anty ke nan ya sakawa yaron ni dai amin nace tare da fatan Allah yasa yaron ya biyo asalin mai sunan na gaskiya sahabi kuma suriki ga mazon rahama.
Ya dago bayan ya aje yaron yace dani ga yaran nan sunzo ke nan anan zasu zauna sai hutu zasu dinga zuwa gun uwayen su suna ganin su.
Nace Allah ya taya mu riko yace dani amin sai ayi hakkuri duk da kin saba dasu yanzu akwai dan canji ga baya sai an kai zuciya nesa ga wasu abubu na su.
Nace ba komai in sha Allahu zaa kiyayye da yardan ubangiji da ai na kowa ne bana mutum guda bane dama.
Yace ya gode yafice daga dakin nafito falo don in basu masaukin da zasu zauna saboda akwai baki a gidan.
Dakin da suka taba zama nan na sake ba su Nasir sunji dadin hakan sosai don na fahinci suna son dakin tun lokacin da nace dasu shine daidai da samari kofan shigowa su kuma suna ganin sun kai samari din yanzu.
Ihisan ce da nace ta zauna da su Aisha ta kawo min gardama wai ba zata zauna da su ba do bata zama da yan aiki.
Nace to kiyi hakkuri ku zauna idan su mama sun koma sai ki kama daki daya daga cikin dakunan bashi ke nan ba duk da nasan tai karama da zama daki ita kadai .
Aiko tace ita bata san haka ba sai dai na bata nata dakin ko ta zauna a falo nan mama ta saka baki tai cikin ta da fada har uban ya fito ya samu ana wanan rikicin haka.
Yake tambayan may ye mama ta fada mai komai dake faruwa yace idan hakane su su Aisha su koma daki daya da helen sai a gyara mata wancan din da helen ke ciki.
Duk da raina ya baci sai ban nuna komai ba ga haka nasa suka gyara mata takoma ciki aka zauna lafiya duk da nasan yaran zasu takura zama da kafira a daki daya.
Washe gari da safebayan nai wanka na shirya ina zaune ina cin abinci mama na daga gefe na tana gyaran wani ganye a roba da zata hada muna na kunun kanwa tace dani.
Rahama nace naam mama tare da dago kaina tace abinda nake so dake shine kikara hakkuri akan zaman yaran nan a tare dake.
Musanman ma wanan yarinyar da kike gani tunda kikaga ta fara tsiyataku irin haka tasha hudubar shedan sosai a kan ki ne.
Don haka don Allah Rahama na rokeki da kikai zuciyar ki nisa akan zaman yaran nan dake don wani babban rikici ne ya dauko maki kuma anan.
Kin san maza su basu gane haka sai in abu ya faru dasu ne hankalin kan kawo wuta cewa sunyi kuskure wani ma ko ya gane bai gyarawa don suna takama iko a hannun su yake.
Nace in sha Allahu mama zan fake don nima na fahinci yarinyar tazo da wani manufa akaina tun zuwan ta na lura da hakan gareta.
Tun da aka gyarawa yarinyar daki bata fitowa falo sai idan ta fito cin abinci tana gamawa kuma zata koma daki ta zauna ita kadai.
Ban damu ba sai harkokina na suna nake don ban tsaya binta kanta ba tukun nakama shaanina kawai muka barta yadda ta ware kanta gare mu.
Monday ya kaisu makaranta nai arziki harda Atika ya hada ya mayar can duk ko da tsadan makarantan amma yai min wanan karar haka.
Shiyasa nake son daddy sosai wurin irin wanan halin nashi na karanci ga dan kowa don nima haka yai min a baya.
Saura kwana uku suna Zarah da maigyaran harka suka iso Abuja da tarin abin arzikin su washe gari basu zauna ba suka fara shirye shiryen abinda zasuyi na sunan komai da yakamata ace anty ce tai min sai ga abokan arziki sunyi tsaye sun fitar dani kunya da taimakon Faiza kawata komai ya kammala masu don su ba wai sanin garin sukayi ba.
Da yamma yan suna daga kano suka iso yan kauyen mu da kuma yan uwan daddy maza da mata gida ya cika da baki tako ina jama, a ne a gidan.
Nai mamaki yadda mutane sukazo min haka Suwaibana bata samu zuwa ba don ance tana jinyar mijinta Jatau baida lafiya sosai.
Ta ban tausayi yadda ake min labarin suna fama a can gashi basu da mai taimaka masu duk da yake a kwance ya tsuke bakin aljihun shi tam bai sayen ko magani dashi suna matukar wahala sosai.
Nace da Rukkaiya shine aka rasa wanda zai bugo waya ya fada min halin da take ciki ga yara ga lalurar miji da wani zataji kuma ?
Ranan suna daddy ya baiyanawa jama, a sunan yaro Aliyu sai ranan suna anty Zulfau ta iso tare da wasu yan uwanta su hudu.
Ta girgiza kwarai da ganin irin daular duniyan da muke ciki a zaune take mood din ta ya sauya tun kan ma ta shiga gidan.
Abokan tafiyan ta na kara zugata wai dankari kune aka bari ashe a can kuna gafin gida ga inda arziki yake nan jibge.
An mayar daku wa yanda basu iya cin duniya ba ke nan an kawo wace ta iya ci an ajeta ana itace matar gaban mota an mayar daku tsofi da karfi da yaji.
Naji isowar su amma sai banga sun shigo gidan ba nake tambaya akecewa suna waje tukun basu shigo ciki ko.
Can sai gasu sun shigo ina saye cikin wani dogon rigan din kin Dubai da gyalen shi iri daya masu ruwan kore da milki a jikin su.
Sannu da zuwa nake masu a take yadda suka amsa min a wullakance sai na fahinci da akwai magana a tare dasu.
Nan dai aka cika su da abin motsa baki kala kala a gaban su sai faman bin gidan da kallo sukeyi suna mayde baki.
Can buki yayi buki a kace ana nema na a waje nafito lokacin na sauya kayan dake jikina zuwa wani hadaden lece maron colour.
Nace ance ana magana dani ko wake nema na Zulfa tace dani nice nace gani anty kina son wani abune ko may ?
Tace eh k dakin maigidan nake nema dama nace to sai
tambayan yai min wani banbarakwai nace sai dai a rofe kofan nashi yake don jama, a.
Tace to aban key din nace a, a anty ga dai daki can na gyara maku don zuwan ku shida kan shi ya rufe kofan da zaifita don jama, a da sukai yawa a gidan.
Tace ban gane ba may kike nufi nace ba komai sai dai ki bari idan ya dawo sai ya bude maki ki shiga ko ?
Tace ikon Allah dakin mijin ma Rahama hanani shiga zakiyi ko may ikon naki da mulkin har ya kai can ban sani ba ashe ?
Nai murmushi babu bacin rai nace ban kai can ba amma sai dai kiyi hakkuri don Allah don key yana a hannun shi ya fita dashi.
Ta juyo fuuu ta wuce dakin da suka sauka sai bin mu da idanuwa mutane ke yi don anji may muke a wurin.
Gun mama taje da fadan ta sai da suka gama sauraren ta mama Rakiya tace da ita haba Zulfa may yakaiki wanan maganan kuma haka a bainar jama, a keda kikazo abin arziki kuma ?
Ki bari mana idan mijin naku ya dawo sai ki tafi amma ko nice yanzu ya rufe kofan shi bazan baki key ba tunda baa nan kike zaune ba tare damu.
Tace kuma wai su mama sun goya mata baya ai mata cin mutunci nan dai suka taru sukai mata fada ashe komawanta daki takira shi a waya ta kwashi karya da gaskiya ta fada mai.
Anci an sha anyi shagali harda walima akayi wa, azi wa mata aka dan raba abinda aka sayowa jama, a a wurin.
Yan asibitin mu sun min kara sosai don sunzo wurin sunan harda wanda ma ban zaci zasu zo wurin ba sun zo tayani murna sun kuma koma da abin arziki a hannun su.
Sai dare ya dawo gida lokacin yan gari sun rage sai mu da bakin mu yasu yasun mu muka rage a gidan.
Muna dakina dasu Zarah mun baje sai hiran sunan mukeyi sai ga ihisan wai nazo daddy yana kirana.
Na saka hijjab dina na fita don nasan daddy yana dakin shi a lokacin ban kawo komai a raina ba nai sallama na shiga dakin sai ganin Zulfa nayi a zaune cikin rashi damuwa nace da ita ashe kina nan anty ya gajiya.
Sai naji bata amsa min ba na gaidashi da dawowa ya amsa min tare da cewa wai may ke faruwa ne yanzu Zulfa ta samay ni da wani zance koma ince tun ina can ta buga min waya lokacin muna meeting ban jiba sosai.
Cikin mamaki na juya gareta ina cewa may akayi kuma ban fahinta ba ni yace dakata Rahama don na kawo ki nan ke kadai bashi zai jawo kiwa matana cin mutunci ba abainan jama, a haka daga tambaya sai ki rufe ido ki dinga gaya mata maganan banza haka a bainar jama, a.
Kin fita ne ko a tsaanin ki ke kadai keda gidan ne da wata bata da ikon zuwa tayi yadda ranta ke so a gidan.
Yaushe kika fara halin rashin mutunci irin haka ban sani ba kada na karajin qanan halin a gida don bazan lamunta a wullakanta min mata na ba ko kadan kin sani.
Idanuwa na rutse a hankali na mayar da hawayen dake son zubo min a lokacin don ba zan yarda kishi taga bacin raina na bukatan ta ya biya.
Nace ayi hakkuri duk da ban san abinda nayi ba amma tayi hakkuri don ni tazo garin nan bazan so tace nai mata wani abin bacin rai ba .
Ina fadan haka ban tsaya ba na juya na bar dakin raina a bace a daki nake mayarwa Zarah abinda ya faru tace dama shi ya kawo ta taga ta bata maki sha, ani ba komai hakan bai samu ba ta hadaki da miji yaci maki mutunci a gabanta.
Nace ba komai ta dauki bashi in dai ban cuce ta ba bata barin garin nan Allah bai tona mata asiri ba ai a gaban shi.
Washe gari ban bi ta kansu ba an hada abin karyawa wanda wasu masuyi na kudi nabawa aikin yi har abinci su suka kawo muna ban fito ba sai rana nafito na gaisa da mutane har ita din Zulfa saida na leka dakin da suke na gaida ita da bakin ta.
Sai wani kallon banza suke min anty na bata zo ba amma taimin aike na abinda zata bamu wanda kayan baby ne da nawa masu kyau da tsada ta aiko muna dashi tace tunda yaro yaci sunan mahaifinta Aliyu.
Sai washe gari yan suna suka shiga kasuwa da gari bayan sun huta sunyo sayayya sosai a kasuwan.
Sun dawo suka fara shirin tafiya tun basu tafi ba na fara kewan su a gidan sako sosai na shiryawa iyayyena da yan uwa na da basu samu zuwa ba misanman ma Suwaiba na dake cikin wani hali na ban tausayi.
Sun shirya tsab da safe zasu wuce ina kallon yadda Zulfa ke nuna min ita fa matace kuma tana da iko da gidan mijin ta sau yadda taso.
Ban kula ba ban damu ba daga ita har mijin daya share ni a gaban bakina duk da banda Zarah da maigyaran harka ba wanda yasan halin da nake ciki a gidan.
Zaune muke muna hiran mu a dakina duk da dare yayi har wasu sun fara barci a gidan sai sama sama muka dinga jin hayaniya na tashi.
Bamu damu damu saurara ba da farko sai dai da muke jin muryan daddy yana tashi muka kashe kunnuwan mu wurin saurare.
Fada ne sosai tsakanin daddy da Zulfa ke tashi yana fadin wallahi idan har baki fito min da kayana ba sai ran ki yai matukar baci.
Ko allura na bai taba bacewa ba a gidan nan sai yanzu zan nemi abu in rasa shi nidawa ke dakin bayan nidake ke kwana a ciki.
Daga inda hajiyan harka take kishingide ta mike zaune tana cewa lalai Rahama kin cika yar halak wallahi.
Fadane fa ake a gidan nan nace matsalar suce hajiya ni ba abinda ya damay ni da sha, anin su su suka sani.
Muryan mama Laraba yasa muka kara saurarawa tace bakiji ne Zulfa tun farko dakika zo may muka fada
Showing 303001 words to 306000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102 Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153