abinda bai dace ba aiko.
Don may bazai yi magana ba yaga abinda bai yi mai dede ba a rayuwan shi tace ai yanzu sai kaje kabashi wanda yai mai daidai amma babu inda Lawisa zata sai ya zube mata kudin auren budurwa.
Washe gari tun da safe suka amsa kiran maigari da yai masu sun samu har Jatau ya hallara a kofan gidan maigari.
Suna zuwa aka fara magana kansu maigari yana tambayan baasin da yasa mama ta tura a dauko mata yarta daga gidan mijin ta bayan an gama magana.
Mama ta kwashe cin mutuncin da Jatau yazo har gida yai masu tun dasafe tace wanan dalilin yasa ta rike yarta sama ai kudin bazawara ya biya bana budurwa ba.
Maigari yace malam Jatau may yasa ka aikata hakan ya gyara zaman shi yace wa maigari an samu kuskure a nan amma ayi hakkuri don shi gaskiya yana son matar shi don haka adaiyi hakkuri.
Nan mama ta kafe kan yarta bazara koma ba sai ya zube kudin da ake zubewa budurwa da kayan aure ko ya sakar mata yarta.
Jatau dai ya fahinci idan yai wasa wanan matar tafishi balai zai tashi a tutar babu.
Nan dai ya shiga kamay kamay yana bada hakkuri akan a dai yi hakkuri a bashi matar shi.
Amma mana ta kafe kan sai ya biya su kudin auren budurwa har aka watse a gurin ba akai ga matsayan zancen ba.
Sula dawo gida kowa na cicika gashi shi Jatau yaji dadin dan kwanan da yai da Lawisa duk da yadda yake ikirarin ya samay ta din amma son ta ya shiga ran shi lokaci daya.
Haka ya koma kamar karamin mahaukaci ranan har takai iyalin shi sun fahinci ya fada tarkon karamar yarinya da ya jajibo masu a gida lokacin.
Nan suka fara sake mai habaici irin na tsufin mata da suka san kan mata shiko bai bi ta kan su ba don ba batun su yake yi ba yana batun yarinyar dan ya sharaf.
Da yamma ya shirya yazo gurin mama don su sulhuta dashi amma babu magana mai dadi mama tana a kan bakan ta na sai ya biya sauran kudin auren budurwa zata yarda yarta ta koma gidan shi.
Tabarshi nan tsugunne takaicin ta duk ya rufeta badon yana son yarta ba don ya samu gurin sauke manyan ta shi da ba abin da zai hana yai mata rashin mutum ci amma babu yadda ya iya dole yabi ta yadda take so ya samu matar shi ta koma dakin ta.
Ita ko mama tana ganin ya fara saukowa ta sa a ranta sai tai mai mugun yaga sun kwashi rabon su sai ta lalashi lawisa ta koma don ko banza hakan yafi mata zama gida ai.
Da dabara mama ta fara koyawa Lawisa irin hikimar ta na kwatan abu a gurin miji da sauran dabaran zaman da zatayi a gidan Jatau ta zauna lafiya.
Mutanen gari sun saka mama a gaba da tsegumi amma ita ko a jikin ta hakan bai taba damun ta ba kanta kawai ta sani.
Har yaran nata suka fara fahintar halin uwarsu don sun fahinci kudine kawai a gaban ta lokacin ba damuwan su ba nan suka fara mata tijara ta kasa gane masu baki dayan su don sun hada kansu gareta.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA HAKKIN AMANA YA NA KANKI YAR UWA, ,
21

Sai misalin karfe biyu na rana anty ta falka daga nauyayen barcin da take yi lokacin.
A hankali ta bude idanuwanta da sukai mata nauyi muryanta a kasalance ta motsa bakinta da kyat tana fadin tare da bin mu ida muke zaune jugun jungun dakin ni da ma.
Rama sannun ku ko jikin har yakai an kwantar dani ko wallahi bana jin dadin jikin nawa kwata kwata.
Da sauri na mike daga inda nake zaune na kura mata ido ban ko kwakwaran motsi a lokacin.
Nake cewa sannu anty yaya jikin naki mama ma ta mike da sauri ta karaso inda muke tana mata sannu da jiki.
A hankali ta daga idonta ta kalli ledan drip din da ake kara mata tace har ruwa aka saka min ashe.
Nace yaya jikin karo na biyu ta daure ta kakaro murmushi wanda ya zama mata dabia hakan.
Tace Alhamdullahi Rama sannu da kokari kinji tajuya gurin mama tace mama sannu na hanaki hutawa ko ?
Mama tace Allah dai ya baki lafiya kin ji nace mama bari na kira likitan yace idan ta tashi a kira shi na mike ina kai kofan dakin aka turo kofan.
Mijin tane yashigo dakin da wasu leda a hannun shi na magani da fruits na karbi ledan mama tana mashi sannu da zuwa yake cewa ashe ta falka.
Heart beat yaya jikin naki tai mashi murmushi tace Alhamdullahi dear ashe kana kusa bakin gadon ya karasa ya zauna.
Tare da dan tausa muryan shi gareta suna magana yanayin shi a cikin damuwa yake sosai a lokacin na juya da sauri nafice zuwa fadawa likita ta tashi.
Bai tsaya likitan tare muka shigo dashi dakin nan ya samu suna magana yakarasa kusa da ita yana tambayan ta yadda take ji yanzu.
Bayan an rubutun da yayi na dan lokaci ya mikawa mijin nata takardan yace aje a sayo wanan magani a gwada mata a gani.
Likita yace za, a cire drip sai a bata abinci ta ci kafin a kawo wanan maganin da ya rubuta mata.
Tare suka fita sai ga wata nurse ta shigo dakin ta gaida mu nan ta fara cire mata ruwan dake jikinta tabar canular a hannunta tana mata sannu.
Ruwa na bata ta wanke baki tare da dan gyara zama nake tambayan ta azuba abinci ko na hada mata shayi ta sha ne ?
Tace tea zata sha kadan ko hanjinta zai dan warware mata don bata jin dadin komai a lokacin yadda tace haka ne mata tea mai zafi da kauri na hada mata.
Sai gashi ta dan fara zufa tace na bare mata lemo tasha sosai ta zauna tasha lemon da nake barewa ina bata sanka sanka tana sha a hankali.
Ranan dai haka muka wuni faman laluran asibiti don tace akai yaran daga school gidan sister din ta, sai a lokacin nake tunane ashe anty nada yan uwa a garin.
Ni dan zamana da ita ban ji tana magana akan yan uwanta ba ko da na rana daya ne amma sai gashi naji tana cewa akai mata yaran ta can gurin yar uwarta.
Haka dai na bar wanan mamaren a cikin zuciyana ni kadai naci gaba da abinda ke gabana lokacin.
Haka mukai ta fama da ita don taji jiki sosai abin tausayawa idan mutum ya ga halinda take ciki a lokacin.
Kwanan ta uku aka bamu sallama muka dawo gida don yanzu ba fever ba kuma dizzynes a tare da ita.
A hankali take lalaba rayuwanta inda duk wani motsin da zatayi idanuwan mu yana a kan alamarinta don likita yace tana bukatan hutu da kulawa sosai.
Wanan dalilin yasa muka mayar da hankalin mu akan komai da zatayi in ba wanka da kewaya ba babu abinda muke bari tayi a rayuwan ta.
Sai gashi cikin yan kwanaki ta gyagije sosai baka cewa itace tai ciwo haka a yan kwanakin da ya shige.
Har ta kwata asibiti ta dawo gida ni dai banga daya daga cikin abokan zaman ta ta leko taba da sunan sannu.
Abin ya bani mamaki matuka don ashe kishi harda ciwo anayi akai ashe kishi yana birni kauye hauka suke yi da sunan kishi.
Ranan da dare ta kirani take sheda min gobe monday zan fara fita zuwa training din data fada min.
Nace anty baza, a bari idan kin kara jin sauki ba sai na fara tace a, a haba aiko yanzu Alhamdullahi ai na samu lafiya sosai ni ko wanan adduan da kullun kike min ne waya sani.
Don ko da yaushe itace may cewa dani Rama ai min adduan nan mana na sha da sauri zan mike naje na samo ruwa nai mata tasha tana lumshe idanuwanta.

****** ********* ******
Tun da safe na shirya don tare da yara da zasu makaranta zamu tafi saida nayi duk wani aikin daya dace ace nayi a part din kafin na fita na shigo dakin anty cikin shirina .
Ta bani wani takarda da zan kai furin mukai sallama dasu na fita gabana sai faduwa yake don ban san may zan je na sama ba a gurin.
Makarantar yaran muka fara sauke su sai ya wuce dani zuwa inda zamu tafi mun dan taba tafiya mai dan nisa bayan mun sauke su sai gamu a wani bakin get an rubuta NANA TRAINING CENTER da manyan haruffa.
Nan ya saukeni tare da yin min sallama sai shidda zai dawo na yamma ya dauke ni kamar yadda anty ta umurce shi.
A hankali nake tafe sai mata nake gani manya da yara nau,i nau,i, kowa tana harkan gaban ta a gurin.
Wata yarinya nagani tafe da saurinta har ta dan wuce ni nai mata sallama nace don Allah office din shuga nake nema.
Da hannu ta nuna min ta wuce da saurin ta gurin na nufa amma office din a rufe yake lokacin.
Nakoma gefe na rakube a guri daya ina aukin raraba idanuwana gurin kallon masu shige da fice a gurin kowa sai harkan gaban ta takeyi.
Can naga wata mota tashigo har kofan office din da nake tsaye sai ga wata yar matashiyar mata tafito daga cikin motar rike da handbag din ta tana kokarin gyara gyalen ta.
Sai da tazo gap dani zata shige nai mata ina kwana ta juyo tana kallon na tare da amsa min har ta juya zata shige sai kuma ta waigo ta dan tsaya tace amma ke newa ce a gurin nan ko nace mata eh.
Dan kallona tayi sama da kasa tace ok ra sa kai tashige office din kai tsaye.
Sai bayan yan mintina wata ta leko tace ance ki shigo ina shiga ba laifi don gurin ya hadu sosai tace kece daga gurin anty Sa, ade ko ?
Nace nice hajiya take cewa yanzu ta bugo min waya amma na dauka ai ko wata babbace ke ashe karama ce.
Idan son samune da zaki iya sai mu jefa ki guri biyu kiyi training din mugani ko ?
Nace zan iya insha Allahu wanan matar dake tsaye ta kalla bayan ta gama dan rubutu a wani file tare da kallon takardun dana mika mata dana shigo.
Tace ki bita zatai maki bayanin komai idan kun fita nace nagode tace ba matsala muka fice muka barta aciki tana rubuce rubucen ta.
Matar da aka hada mu bayan mun fita tace kingane may ye sunan ki nace Rahama Aliyu tace zan fara kaiki ajin koyon zaman gida da sauran aiyuka idan mun gama sai mu koma fannin kwalliya da ado ko yaya kika gani ?
Nace nagode anty tare muka shiga na samu mata a zaune wasu harda cikin su wasu kuma dai gasunan.
Ta nuna min guri na zauna tai indroducing dina ga sauran mata ba bata lokaci aka fara normal activities din da suke yi gurin.
Sannu a hankali na fara fahintar abinda ake nuna muna na na kuma fahinci anty ta kawo ni ne don na fahinci duniya sosai kafin na shigeta.
Zama da iyali ne akai darasi a ranan kowa taba da hankali tana sauraren bayanin da akeyi a gurin.
Ana gamawa wasu suka fice wasu kuma suka tsaya aka fara darasin ado da kwalliya na jiki dana gida.
Haka muka wuni ana fahintar damu abubuwan karuwan duniya a gurin dan har tafiya da nau,in magana sai da na fahinta akwai sallon yin shi.
Sai biyar saura aka fito nan naga wasu masu training na shigowa matar tace na shiga tunda ba, azo daukana ba.
Fanin girke girke ne nan kuma aka shiga sabin darasi har shugaban gurin tana shigowa yin bayani abin gwanin ban sha,awa dashi.
Fitowan mu yayi daidai da zuwa Hamza driver na shige muka nufi gida da murna na.
Irin sallaman da aka koya muna yau da shi na shigo gidan cikin tausa murya harda dan tafiyan da aka nuna muna ya dace mace ta dinga yi.
Suna ganin haka suka saka min dariya anty dake zaune a kasa tace da kyau kaunata aiki ya fara ke nan.
Nai dariya na gaidasu da tambayan lafiyan jikin ta ban zauna ba na shiga na kwabe na dora muna girkin dare.
Sai bayan magariba nagama nashiga nai wanka tare da dauro alwala nai sallah.
Tun wanan ranan sai ya kasance banda lokaci kai ko kadan don busy nake koda yaushe haka ya rage min duk wani sauran kunci da tunanen gida dake cikin raina.
Sosai na mayar da hankalina ga training din dake bamu sai gashi tun ba aje ko ina ba na fahin rayuwa zan iya yin komai in a gentle maner.
Hakan yasa anty taji matukar dadi a ranta ko yaushe tana min kallon sha, awa sosai don jina take kamar blood sister din ta har cikin ranta.
Banda matsalan komai tare dani don komai nake so yanzu zata saya min shi ba bata lokaci haka yasa ma ko ina son abu ban nunawa a gabanta.
Ko abin yan mata tagani yanzu zatace wanan abin ya dace da Rama na bari na saya mata shi.
Mama Altine kance Rahama zaki ko iya shan ruwan garin mu idan munje.
Nace kai haba mama a ina natashi da bazan sha ruwan kauyen mu ba ni wacece mama?
Kwana biyu bana ganin mijin su kila don bani zama ne yasa bamu haduwa ban sani ba.
Na koma wata saliha dani don ko matan gidan na iya shegen su bana kula tsabgan ko kadan sai na mayar dasu wasu binan can.
An yi bukin yaye mu na course din wats biyu danayi a Nana traning center anty bata samu zuwa ba sai mama da yara ta tura sukazo min.
Alhamdullahi abinda akaje nema an samu don na sake gaba daya na koma Rahama ta ta birni komai nawa ya sake gashi makerin kyawona ya gama kera min hallitana na cika na zama budurwa a lokaci daya ko don sauyin abincin dana samu ne yanzu ba irin wanda muke ci a kauye ba nai saurin wanan girman haka ?
Sati daya da gama training dina addimition dina ya fito na jorna da BUK nan na fara zuwa makaranta ban samu wani wahala ba don yanzu kan mage ya ya waye sosai.
Ranan na dawo da yamna lis a gajiye nake banga anty a falon ta ba yadda na saba samun ta tana dan zama ana hira.
Sai da na shiga gurin mu na aje kayana nafito zuwa dakin ta a kwance na samay ta nace anty lafiya dai ko ?
Tace da sauki yau ina dan jin jikin ne Rama amma ba wai wani can ba da yamman nan ne ai na, dan ji ba daidai ba.
Na dan tsaya tsaye ina nazarinta a gurin sai dai ban fahinci komai ba na juya na fita zuwa kitchen.
Abinci na hada muna don baci akeyi ba sai nayi dan kadan nagama na shige dakina wanka nayi na fito zuwa gurin anty na samu ta tashi tayi sallah tana zaune a gurin ta ishishire kafata tana ganin na shigo ta mayar da hankalinta gare ni tana fadin har kin kammala ne Rama ?
Eh anty na bata amsa ina nufin gadon dakin dake yamutse a lokacin na fara gyarawa tace ai dama kin barshi har da safe ki gyara nace bari dai a gyara kiji dadin kwanci ai.
Fira muke ina dan kawar da kayan da nagani barbaje a dakin take cewa dani ya kamata fa idan kunyi hutu ki dan leko gida hakana.
Kada muyu rashin hankali yau fa kin kai wata biyar a garin nan babu wani labarin gida kada ace ko an sace ki ne ai.
Dariya nayi nace haba dai ina zasu zaci haka tunda sun san da mama muke nan din ai bazata bar dukiyanta can ba ta gudu.
Innan ki nake tunane wallahi nakan so a dan aika mata da dan wani abu sai dai gurin nakune da wuyan zuwa wallahi sai in mutum zan tayar yatafi can din.
Anty ai zan tafi da zaran anyi hutu na dubo su nima hankalina yana gurin inna wallahi ga rayuwa yanzu kowa kan shi ya sani.
Amira ce ta shigo dakin tana kwala min kira wai nazo ga Nasir zai bata min waya na ya dauka yana game dashi.
Amira bari ya gama sai na baki ke ma kiyi game din dashi a, a Rama jeki karbi wayan ki bana so ana ba yaro waya ni.
Ba wasa a fuskanta don haka na bar abinda nakeyi naje gurin yaran a cikin hikima na karbi waya na zauna muna game din dasu har zuwa dare sukayi barci.
Bayan na gyara wa kowan su kwanciya ne na rufo kofan dakin zuwa dakin anty ta canza yanayin zaman ta yanzu zuwa jingina jikin ta da bakin gadon ta.
Anty baki
Showing 69001 words to 72000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24 Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153