Fita yayi daga dakin don i zuwa yanzu ya fahinci mata da ksidin su ya zama mai dole ya mike ya kara gyara gidan shi da kan shi ba sai an hankaltan dashi ba .
Bayan fitan shi ya biya gidan Raliya nan ya samu ta tafi bai kirata ba ya share ta don ya fahinci komai yanzu.
Motar da na saya a can ya shigo don haka sabon tsegumi ya taso a gidan kuma don takanas ta kano Raliya tazo har gidan ganin motan da idon ta.
Matar da zatai zuwa goma garin bata shigo gida ba amma sai gashi ranan da na fita girki yake cewa da Zulfa da zata karba kada tayi girki Raliya zata shigo garin.
Tashigo da yamma sai gata gidan bamu ma san may ya kawo ta ba lokacin muna falo har yaran ina saye cikin shadda maron colour yasha aiki tun daga sama har kasan rigan don zanin ma an mashi aiki na dan je gidan wata nurse din mu da muke shiri da ita ta haihu ranan aikai suna shine muka leka ni da zulfa dasu Aisha.
Tana shigowa muna fsli suna cin kayan bukin da muka dawo dashi tana ganin ko wani cas a cikin kwalliya kamar zamu buki sai ta daure fuskan ta.
Kaina na duke ina karanta sako a wayana sai ji nayi yaran na mata sannu da zuwa ban dago kai ba son na shagala da karatun abinda nake karantawa.
Idon ta akainaa don tun dawowa na bamu hadu da ita ba dama sai yau din nan da ta samay mu a hakan zaune ana ta hira.
Sai da ta kusa zaunawa ne ma na dan dago kai na ga ashe itace muna hada ido naga tai saurin kawar da kanta banji komai a raina ba irin yadda a baya nakan ji gaba na ya fadi idan na gan ta tashigo.
Nace au sannu da zuwa tace yau ta zauna banga sun gaisa da Zulfa ba ban kuma kula ba sai maga wayana yana kara na dauka Doctor Fati ce tazo ashe tana tambayana ina gida ne nace eh.
Ban ko kashe wayan ba sai gasu sun shigo gidan tun a kofa tace one family ke nan doctor kune nan gaba daya da iyalinki kuna harka.
Kai lalai in dai wanan kwallitan kukewa ogo zaku ko rikita shi ya daina fita kun gan ku kuwa kamar wasu da zasu dinner dare.
Mukai dariya nace kai doctor fati ke dai akwaiki da zolaya kwalliya kan ai sai baiga kallo gamu har hudu a jere ras sai wacce ya zaba.
Zulfa tace kai doctor fati kamar kin san dama ina son ganin ki wallahi tace to ai gani tace wanan lace din da mukai magana yana nan na cire maki shi ihu tasa tace da gaske antyn mu ?
Tace bake kikace kalar kike so ba ban sayar ba yana nan a aje maki naso idan zata fita ta kai maki a wurin aiki ne.
Tace aiko nagode wallahi kin san kuwa har neman shi naje zulfa tace banace zan cire km aki shi ba dama ai kyau alkawari cikawa.
Tace dama mota nazo gani naganta ma a waje gashi can su dear na kallo da ogan naku don muna shigowa ya dawo shi ma tace muje naga kayan kafin a zabe su.
Mikewa mukayi nan muka bar ta zaune tare da yara muka shige abin mu mun jima a dakin sai gamu mun fito da kayan da ta zaba a leda.
Har kofa muka raka ta can muka gansu tsaye suna kuskus a tsakanin su bamu kula su ba muka gaida mijin doctor fati dake jiran ta suka tafi muka juya zuwa cikin gida.
Muna shiga Zulfa ke fadin wanan fa gulma tazo yi dama an tsegunta mata zancen motar ki shine tazo gani nace ita ya shafa wanan kuma.
Tace bari ki gani yanzu zuwa gobe zakiji sabon rikici ya barke tace wa hindatu ai bata taba bari boni yai barci ita wurin kullin sheri.
Ba wanda ya zauna falon cikin mu kowa dakin shi ya nufa don yamma yayi a lokacin can na samu su Aisha suna gwada wasu dogayen rigunan da na zabar masu cikin kayan da suka shigo.
Carab na anshe rigar hannun Aisha nace kema kin san tun can na fada maki wanan diyana na sayowa helen kuma jiya akai min waya wai taki zama gun da take tace wurina zata dawo.
Aisha ta fara fadin don Allah dai mumm ki bar min wallahi ina son rigan nan tun can nace ai sai da nace dake ki zaba kikaki yanzu ki zo ki dauke mata shi.
Kuma ma iyakarki da wanan rigar Aisha a gida kawai don bai fita maki waje kinga tsagar shi yana da yawa a baya sosai.
Sai ta turo baki nace ashe baki son cikin wanca da na sayo muna mu biyar masu tsadan nan bakiga na dauko su nan ba.
Da sauri ta miko min rigar tana fadin wallahi nikan wacan din nake so a bar mata wanan din na fasa son shi.
Atika ne kawai nake ganin dogon rigar nan baiyiwa sai Amira tace ida bai mata ba sai abar min don Allah mum na dauki riganunan ina dubawa sai na jefawa Atila dake kusa dani karamin kuma yana da kyau sai duk yara sukayo kan ta wai zasu kwace ta fado min tana fadin anty boye min don Allah sai duk suka danne ni wai zasu kwace rigan mun shagala muna ta ihuce ihucen mu a dakin ya shigo duk yaran na saman kaina suna son kwace rigar a hannu na don wani lokaci haka mukanyi wanan wasan dasu.
Muryan shi mukaji yana fadin kai wanan wasan fa haka zaku jin mata ciwo ne ko may duk suka daga suna numfashi nima dai dariya nake masu nace kyalesu Atika duk wanda ya kwace maki sai na hada maki da nashi ki hada biyu.
Suka fice daya bayan daya daga dakin don ganin shi ya shigo dakin sai bayan sun gama fita daga dakin ne yake cewa dani kin shige cikin yara kuna mugun wasa haka kamar wata karamar yarinya dake.
Nace ina kokarin jawo dan kwalina daya cire dama may nake ba yarinyar ba kaine dai baka gani yanzu don kaga na tsufa maka.
Baki ya dan mayde yace ni zan tafi magariba ya gabato sai dai da safe ke nan don Allah kisa Nasir ya rufe gida idan tara yayi.
Nace za a rufe ai insha Allahu har ya fara tafiya yace dazun Raliya ta shigo tace wai duk baku tare ta ba daga ke har Zulfa may yasa zakuyi mata haka Rahama ?
Nace ikon Allah so take na goya ta ko may ta shigo nai mata sannu da zuwa da yaya hanya may kuma take so nai mata bayan wanan.
Yace har ma kun gaishe ta ashe nace wallahi na gaida ita da zuwa shigowan doctor Fatima ma yasa muka barta falon muka shiga dakin anty ganin kayan da akazo dasu.
Yace to ni yanzu ma ina shiri ta bugo tana fada wai tazo matana sun mata wullakanci a gidana.
Nace shiya kawota dama tsegumin in bashi ba ai naga har tazo ta koma bata shigowa gidan nan.
Yace ni zan tafi nace sai da safe har yakai kofa nace gobe in Allah ya kaimu fa Su Amira zasu tafi sayen form din Jam sai dai dana yace wallahi shi bai son yin karatu a kasan nan.
Ya juyo yana kallona tare da fadin sai ina zai tafi baida hankali ne killa kamar Nasir zan sake shi kadai zuwa wani kasa karatu .
Baiji da kyau bane idan baiyi ba sai ya zauna gida ba gashi ga gidan yai ta zama mana nace haba daddy yarona fa yanzu yakai big boy ne fa.
Tsuki yaja ta sake ce min sai da safe yana tafiya yake fadin idan na dawo na samu bai tafi ba sai na bata mashi rai gobe..
Nace ba a ko bata mai rai tare zamu je ya cika a zauna lafiya gobe din yace ato dadai yafi maku sauki kan.
Da kyat na lalashi Nasir da ya bari muje ya cika ya bi umurmin daddy isan ya fara yi a na daga baya sai ka tafi inda kake so lokacin ka dan girma.
Zulfa ta shigo ta samay shi yana cika yana batsewa ta samuna baki na samu da kyat na shawo kan shi da nasiha da komai ya yarda dani.
Tare din muka tafi dasu suka cika form din don dole Nasir din ya cika saboda ubam yace ba zai kaishi waje karatu ba yanzu sai ida ya kara girma.
Koda ya dawo gidan bamu nan mu fita lokacin ashe da wuri ya dawo gidan ba yadda ya saba hantsewa ba idan yana can.
Sai da na shiga na dan huta na fito zuwa wuri shi na samay shi kwance rigingine ba barci yakeyi ba daga kofa na tsaya nake cewa dashi .
Ina kwana ya dan juyo yana cewa dani har kun dawo nace eh munyi sakkone don mu samu da wuri da rana zan tafi aiki ne in Allah ya kaimu anjima.
Har na juya zan fita nace ashe yau da wuri kadawo haka yace eh nadawo bakin hana a barni na huta ba kowa sai zargina yake wai nina saya maki mota.
Nace Ya Subbahanallah kuma dai shikuma aka kulla yanzu kuma nace dole suce haka don ina yar matsiyata ko ita da ta sai nata kwanaki wa yai magana ko don ni yanzu na saya shine abin magana don ba a son agan ni da karuwa ko ?
Bai dai yi magana ba ns juya na fita raina a bace nace wai may matan nan ke nufi dani ne kodan ya kasance ban iya karyan duniya ba ni da watace aiko da sun sha haushi wallahi don da komai na gani saya zanyi na shigo dashi gidan.
Allah bai dora min irin wanan rayuwan na kwasan banza da wofi ba shiyasa har suka samu daman zargina idan sun ga nayi abu.
Kwantawa nayi har na fara barci sai ga Aisha tazo wai inzo daddy yana kirana a falon shi take ce min naga Amarya ma tazo duk suna falin zaune nace tau.
Sai da na dan bata lokaci na fito falon na samay su zaune suna jiran fitowan nawa na karso da sallama na na samu wuri na zauna kowa sai cika take tana batsewa a cikin su.
Yace yauwa kun hadu ko dama ba komai yasa nace kuzo nan ba sai maganan motar Rahama da kuka gani kuke zargin ko nine nan na saya matashi da kudina na munafunce ku.
Da sauri na dago kaina nace motar tawa ake zargi kuma hannu ya daga min alamar nai shiru na barshi ya gama sai na kada kai kawai tare da gyara zamana.
Yace yanzu gaku ga ta kuji daga bakinta idan nine na saya mata ko na taimaka mata da koda kwandala ga sayen motar nan da tayi.
Kafin nai magana sai zulfa tace haba haba dai yaya ai wanan maganan ma haka bai dace ba koda kaine ma ka saya mata motar ai ba laifi bane balle Rahama ai ba wacce za a zarga bane yanzu don an ganta da wani abu a cikin mu.
Duk mu nan fa mun san aikin Rahama ban ga dalilin da zai sa mu dorawa kan mu wahala bayan mun an zata iya sayen abin da ma yafi wanan din.
Humm umm inji Hindatu ina ruwan karere kina nufin ke nan yanzu Rahama tafi aji ko may kike nufi da maganan ta.
In ma bata fi mu aji ba ai yanzu dai kunji ba shi ya saya mata mota ba don haka ya kamata ku bawa kan ku lafiya muyi fatan muma Allah ya bamu abin yiwa kan mu.
Haba sai ko sukai cikin ta da masifa ni may zance tun da Allah yai min gata an karba min zancen sai naji Raliya na fadin wa za aiwa burgan aiki ko wa akafi aji ni wallahi kar nake kallon mace don nasan wanan plan din ba yau ba kada ku mai damu kananan yara mana .
A raina nace zaki gane shayi ruwa madam don zan gwada maki na fiki iya bariki in shi kike takama.


To yan uwa kun bani mamaki sosai wallahi kunce sai na bace ban fada maku uzurina yanzu kuma na fada maku amma hakan baiyi ba saida na samu marasa hakkuri da basu yarda da kaddara ba suna sake min magana yadda ran su ke so.
Idan kuna ganin maganan da kukai ta fadi a gamay dani shine adalcin zama ko kuma zaku iya sani yi dole sai ku matsa kuyi tayi .
Masu cewa ba zasu sake shiga group dina na ba matsala guban wani zuman wani sai Allah ya kawo masu hakkuri dani da yadda nake dama ko yanzu ina tare dasu sun dade suna hakkuri da rayuwa don sun san ba ni nai kaina ba nima yar adam ce kamar kowa acikin ku.
Yadda kuke da uzuri haka nake da uzuri nima amma masu hankali a cikin mu sun san da hakan.
Masu fadin kudi suka biya don na zauna ba hutu naita rubata masu labari akan dari uku sunyi kuskure zan iya mutum kudin shi yaje inda za, a dadada mashi ran shi.
Ni ina can ina neman waya don na faranta maku rai ku kuna nan kuna ta aibanta ni don rashin hakkuri da son kai irin na wasu.
Ina mai karaba wanda suka fahinci matsala na hakkuri ba kullun ne zaku dinga jina ba haka zan ta maneji har sauki yazo muna da fatan zaku fahince ni yan uwa nagode


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , , ,
92

Ubangiji Allah ya jikan anty yai mata rahama yasa ta huta yasa aljannan fidausi ne makomarta.
Wanan mata bazan taba mantawa da ita ba a rayuwana duk wani rudin shedan da ya shiga a tsakanin mu lokacin dan zaman da mukayi a rayuwan ta bana taba jin zafin ta ko haushin ta.
Saboda irin rayuwan da ta gina ma rayuwana a baya wanda har tawa mutuwar tazo ba zan daina amfana da abin da tai min ba.
Shiyasa har gobe ina jin jinin ta kamar duk abinda nai masu ban masu wanda ita tai min ha sai dai na kwatanta kawai iya yina.
Don abin da yasa nakewa mai karatu wanan bayan shine tun da suka fara cecekucen su zauna nake cikin kamala da sanin ciwon kai tankar ba dani ake wanan badakalar ba.
Wanda yadda nake zaune cikin natsu ya jawo daddy mai da hankalin shi a kaina yana kallon yadda nake zaune ba abinda ya damay ni sai ma jan ajin da nake tankar ba da ni ake zancen ba.
Don ban biyewa haukan kishi nai wani dogon hayaniya yadda ya tsamaci zanyi ba da farko.
Wanan kuma zaki iya tuna training din da anty ta fara kaini na koyon zaman duniya tun farkon zuwa na wurin ta.
Banga amfanin shi ba sai yanzu da girma yazo min na san ciwon kaina nake amfani da irin darasin da na koya a wurin.
Watau mace ta zamo kamila mai jan aji da natsuwa ba ko yaushe a cikin hayaniya ba da watsar da kai.
Raliya da yake mai ilimi ce ta san duniya sai yadda na mayar dasu wasu bi can ya bata mata rai don kishin yanayi na da jan aji ya tsone mata ido.
Bata taba sanin na koma classic lady ba sai dan ganin da tai min din nan sau biyu baya dawowa na yasa ta gane cewa akwai aji sosai a gareni.
Don na waye nasan duniya na san ciwon kaina komai nawa a natse nake aiwatar dashi ba kamar sauran ba.
Take wani zafin kishina ya rufe mata zuciyar ta gashi taga akaina ake fitina amma sai waya nake kallo ina dan murmushi can na nisa nake cewa iya kar maganan ke na dama don ni zan tafi na shirya ina da theater da karfe hudu da zanyi.
Na mike tsaye daga inda nake zaune na juya gun hindatu na ce Hindatu idan kina ganin komai daddy ne ke maki a rayuwa har kike zargin haka take muna muna kina hada dan karamin banga a gida don tayar da hankalin mutane to aiki babba na gaban ki kuwa don zaki tabbata cikin wanan halin.
Ina fadin haka na juya na fara tafiya ina fadin Allah ya bamu alheri anty Zulfa don Allah ki bar bata bakin ki hakana.
Don wanan bazata taba daina halin ta na sheri ba tana tauye rayuwan ta dana wasu ni yanzu banda lokacin bata wa wurin kallon abinda wata keyi naci gaban ta.
Aiko ta shiga bakin ta don har na shiga daki na rufe tana faman surfa ruwan balain data saba yi bata ko gajiya ita da fitina shiyasa take kullun cikin bakin rai.
Sai bayan na dawo ne da dare Amira ke fada min ai dazun fada kuma ya sarke a tsakanin Raliya da Hindatu kafin ta bar gidan.
Kai Allah dai ya sauwaka ita wai bata tunanen yanzu yarta ta girma ne tana ganin abinda takeyi gashi gidan wani zata wata rana.
Aisha dake shimfide baba tace ai ihisan din ce tai mata magana shine har ta
Showing 375001 words to 378000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126 Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153