kece gaba gaba ?
Tana shiga ta takani sai da na danyi kara takuma juyo tana cewa dani may ye haka kuma zaki cika mu da ihu ke kuma ?
Nace malama amma dau kinji kin takani aiko da wanan takalman naki yanzu.
Hindatu ban fa son hauka wallahi zan bata maki rai yanzun nan a wurin nan.
Suka zauna ya figi mota sai sababi yakeyi ran shi a bace yake fada inda yake shiga ba nan yake fita ba.
Mun kai gidan kowa ya fito ta tsaya a baya itama Zulfa ta koma kusa dashi tare da mika mai yarta ya karba.
Mutanen gidan na falo hardasu mama laraba da suka shigo gaida shi nan muka shigo duk kallo ya koma a kan mu .
Aisha tace yau tafi da gidan ka akai muna rangas wazamu kalla a nan uwar gida ko may bi mata ko yar uku mai gumban uku koko amarya mai batun hankali zamu kalla.
Kowa taimai kirarin shi don haka aka washe suna muna sannu da zuwa nan suka samu kujera suka haye.
A kasa na zauna naga zaman su haka baiwa hajiya dadi ba don ta tsuke fuskanta ba fara, ar da takeyi da farko na ganin mu.
Daya bayan daya muke gaida su inda su ko sukace ina wunin ku cikin jam,i muna tambayan ya maijiki ?
Nace Allah yasa ciwo kaffara ns yace amin Rahama ashe kinje gida ne kwanan nan bamu bada tsaraba ba sai gashi an kawo muna mai yawa haka ?
Nai murmushi na dukar da kaina yace Alhaji karami baka kyauta min matarka zata ganin gida baka fada muna ba.
Dana sani aida nai aike garesu don mutanen na sa mutinci da sanin ya kamata gaskiya.
Naji dadi sosai ga yabon da akaiwa iyayyena a gaban kowa ko ba komai an karama min iyayyena kowa naji tunda bani kadai bace a wurin ai.
Sai hiran su suke zubawa ina zaune daidai kafan Anty, a takure na kasa sakin jikina dakowa a wurin .
Can dai na sa hannu a cikin handbag dina naciro goran zuman da dan wurin garbati ya bani tsaraba da zan dawo har galon daya shine na ciko gora dashi na kawo wa Alhajin daddy kada nazo hannu sake naji kunya don ban san abinda sauran suka dauko mai ba.
A hankali na mike daga inda nake zaune na karasa kusa dashi na tsugun na nace Baba ga zuma asha magani dashi.
Gaba daya aka mayar da kallo gare ni yace tare da dan yun kurowa kai yar nan ubangiji Allah ya albarkace ki da zuria masu albarka.
Nagode nagode kinji Allah ya saka maki da mafificin alheri hajiya tace Allah yasa mai kyaune gashi muna ta yawon neman zuman da baida hadi dama an gode Allah ya rufa asiri.
Daga inda daddy yake zaune yace wanan tafiyan na Rahama dai ne ke nan don gashi tasha addua muna zaune.
Yanzu ai babu zuma mai kyau sai dai hadi ko inji Zulfa nace wanan mai kyaune baida hadi ko kadan.
Da wuya a samu zuma mai kyau sosai yanzu sai sunyi mashi surki nan kuma aka shiga hiran zuma din.
Can nace ai zuman dake da kyau ba bace yake ba har ma idan mutum bai yarda da kyaun shi ba zaka iya zuba shi a kasa ka gwada shi.
Idan baida kyau kasa zai tsose shi ne a take idan kuma mai kyaune haka zai tsaya a saman kasa baya tsotse shi.
Kaji wani hikima kuma na mutane yanzu sai kuma a gane gaskiya a hakan inji daddy nace mu haka mukeyi a wajan mu.
Don Allah dear ku tashi mu tafi dare ya soma ana ta faman hira tunda munyi abinda ya kawo mu din inji hindatu data suka tana cika tana batsewa.
Yace gaki ga hanya ai idan kin gaji ne don ba mahaifin ki akazo gayarwa ba zaki bude baki ki fadi hakan.
Alhaji yace a, a ku tashi ku tafi ai na gode da zuwan ku Alhamdullahi kuma ai na samu lafiya ko .
Bai tashi ba duk da mahaifin shi yai mai magana sai zuwa can mama laraba tace Alhaji karami kwashi matan ka kuje gida hakana don dare ya soma yi.
Ya amsa da to mama muna nan dai a zaune bai tashi muma ba mai ikon tashi a cikin mu.
Sai shadaya da rabi mukai masu sallama muka dawo gida a hanya yace da anty Saade wanan kaunar taki fa kada ta amshe maki fada gurin Alhaji fa ?
Tace ai ba matsala komai Rama zatayi ai na alheri ne ga kowa sai wanda bai san da hakan ba gare ta.
Neman suna ne don a san da ita take hakan ai abinda mutum yayi badon Allah ba don yabo ai baida, , ,
Will you keep quiet my friend ke zaman ki ke nan hassada da bakin ciki a rayuwan ki duk abinda wani yayi idan bake bace ba daidai bane ?
Dama shi dan bakin ciki ai haka yake kan shi kawai ya sani bai san wani ba inji Zulfa dake da takaicin Hindatu din a ranta.
Kai ku bar wanan maganan haka please ba a zaman arziki kullun sai tsiya hakan baida wani amfani wallahi anty ce ke wanan maganan.
Har muka shiga gida kowa na kule da dan uwan shi a rai ni dai ana tsayawa na bude gefen da nake na fice na basu guri.
Har na fara tafiya naji daddy na fadin Rahama ki hado min tea don shi kawai zan iya sha in kwanta yanzu.
Kamar yaya ta hado ma tea kuma kasan dai koda kai tafiya ban fita girkina ba ka tafi.
Hindatu ban fa son wanan haukan naki nace ta hado min tae tunda baki da hankali ke baki san Allah ba.
Nan fitana ya kaule masu anty tace dani wuce mu shige ki hado mai tea din kada dare yayi fadan su ba mai karewa bane su.
Ban bata lokaci ba ina shiga na wurgat da jakata na fada dakin abinda amaryan baba na tabani takuma hada ni da Allah nai amfani dashi na dauko na nufi bathroom na aiwatar kamar yadda tace min nayi.
Daga nan na fito na nufi kitchen na fara hada mai tea din daya bukata take naji na fara hadewa jikina yana bani abin akwai shi da ma, ana.
Koda nakai mai tea din yana wanka na aje mai na tafi nima na kimtsa jikina na dawo.
Kafin na gama komai naji na hade kamar wata chewgun dani ga wani irin desire da nake ji duk kasala ya rufe ni nasan wanda nasha ne ya fara aiki a jikina shima.
Yana zaune yana shan tea na shigo dakin yace kin rufe kofan na amsa da eh na samu wuri na zauna.
Bai juyo ba bai kuma dago kai ba yace to yaya kuka bar mutanen gidan nace suna lafiya suna gaida ku.
Yace shi baba maigari harda dawainiya haka yaiwa Nasir wanan babban rago haka ?
Nacd Nasir dama mutumin shi ne bai samu doki ba ya samu rago ai yace hakane wata rana ai zai iya bashi dokin ma inda halin hakan don duk wanda ya baka kadan akwai ranan da zai baka babba ai.
Yana gamawa ya hawo gadon yana cewa kin fadawa anty ki zancen ginan da akewa baba ne nace ban fada mata ba tukun.
Yace wani amsa kika shirya bata don kin san zataji ko tagani ranan da duk mama Altine tazo garin nan.
Shiru nayi don nasan maganan shi gaskiya ne yace sai ki ce da ita kudin kine tun tuni kike tarawa kikai aikin dashi.
Nace dashi nagode na lumshe idanuwana don sai godiya nakewa Allah da ban fada mata komai ba tun farko tunda nagane bai son asan shine ya gyara muna ko may yasa oho.
Kamar ya karanci zuciyana sai naji yace bana son abinda zai kawo bacin ran wani daga cikin ku ne.
Kuma ya kamata a taimaka masu duk da nasan ina da amsa ga kowan su don ba wanda banyiwa shigen hakan ba daga cikin su.
Gori da habaici irin naku na mata ne ban so ga alheri idan nayi shiyasa ban son yawan surutu haka.
Daga haka ya rungumoni nan wasa ya canza sallon shi ranan daddy ba karamin jirkita ni yayi ba don kamar ya zauce min ya koma a ranan da kyar na samu ya barni na huta.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE DON BA A YAFE BA ONLINE NOVEL NE, , ,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YAR UWA DON CIN AMANAN ALKAWARI DON KIN SAN ONLINE NOVEL NE, , , ,
56
Washegari nafito shar dani cikin dogon rigar material kayan sun matukar karban jikina sosai.
Nayi kyau dani kaina na sani don na bata lokaci wurin shiryawa na samu an hada breakfast dan fruit na hada mai da ferfesu.
Nakai mai har lokacin daddy yana kwance bai tashi ba na shiga na hada mai riwan wanka a bathroom.
Inda yake kwance saman gado yana barci na nufa na zauna a bakin gado nafara ja mashi dan yatsun kafan shi a hankali.
Da kyat ya bude idanuwan shi ya sauke su a kaina nace daddy ka tashi kaje ka duba yadda baba ya kwana don naga ko jiya yana dan jin jikin nan nashi.
Ya gyara kwanciya gami da mika yace dani da safe haka Rama ?
Daddy tara fa ya kusa yanzu ai gara kaje ka duba shi don hakane kawai yanzu tsakanin mu dasu.
Murmushi yayi ya jawo ni zuwa jikin shi yace kwalliyan nan naki ya burgine sosai Rama.
Nace nagode daddy Rama ban san godiyan da zan maki ba a daren jiya kin mantar dani duk wani tarin matsalolin dake a cikin rayuwana.
Kunya naji na noke kaina kasa yace Iam telling you the true kina sani a farinciki ko yaushe wanda ni ban san dalilin shi ba Rama ?
Na dan yi kokarin raba jikina da nashi sai naji ya kara matse ni yace da ace zan san wake gyara min babby na haka ko yaushe zan iya yi mata kyauta a rayuwana.
Nagane so yake ya gane may ye sirin nawa sai nace cikkin dariya daddy ka godewa Allah don shine yai min hallitta na hawainiya kila mai canza kama ko wani lokaci.
Rama ya fadi a kasalance na amsa a hankali yace bana so kina fushi dani kina min rowan farin cikina a kan ki.
Baki san irin halin da kika jefa daddy naki ba yan kwanakin da suka shige ko kin saka ziciya a cikin garari a gidan nan ?
Bana so kina daukan zafi haka dani bake ba duk wanda ke a karkashi bana son ya bata ran shi a kaina ko kadan.
Wanan dalilin yasa nabarki kije gida har tsawon kwana hudu don ki samu ki huce ko zan samu kwanciyan hankali.
Bana so ina fadi mutum yana fadi nakan ji zafin hakan a raina sosai gashi harkin hasalani nakai ga taba lafiya jikin ki wanda ko yaushe nakan kalli hannuna dana daga na mare ki da shi a matsayin bai min adalci ba ko kadan.
Kara lafewa nayi a jikin shi nace daddy ni yar kace daka raina da hannun ka kuma yanzu ina a matsayin matarka don haka kana da ikon daukan ko wani irin hukunci ai a kaina don ka cancanci yin hakan a gareni.
Idan babba bai nuna matsayin shi na babba a na kasa dashi ai ko yauahe karami baya sanin yai laifi don haka nima ina mai baka hakkuri da kayafe min duk abinda nai maka a lokacin.
Sai dai ba yina bane don a lokacin wani irin yanayi nake ji a kan ka daddy ina jin zafin ka ina jin takaicin ka fiye da kima raina yana matukar baci sosai koda kuwa sunan ka naji an ambata min.
Sai naga ya dago ya kalleni kadan ya mayar da kaina a saman kirjin shi ya sauke ajiyan zuciya bai yi magana ba sai dai ina jin yadda kirjin nashi ke halbawa sosai can naji ya sauke ajiyan zuciya.
Yace, Rama akwai matsala a wani wuri don abinda kike ji nima din shi nake ji sosai a raina akan ki sai da nayi kokari na sa ai min rokon Allah don na dan samu sauki don gaskiya koda zamu zauna a hakan ba zan iya rabuwa dake ba a rayuwana.
Yace na kuma ji dadin fada min sirin zuciyar ki da kikayi don haka shine zama na tsakani da Allah halinku ne na mata shiyasa ko yaushe bani zama ban saka an min sauka ba akan iyalina dani kaina don neman kariya daga fititinu masu haddasa fita a tsakanin ko da yaushe.
Rama ina son ki nima nasani wanda hakan yakai ban iya boye hakan a gaban kowa duk yadda naso na boye irin yadda nake jinki a raina ba zan iya hakan ba a gareni.
Don haka ki kara hakkuri akan wanda kike dashi ki zama mai juriya akan komai ki kawar da idanuwan ki akan kowa a gidan nan.
Nidai ke zama daku nakuma san halin kowace daga cikin ku ance kowa da halin shi ake zama dashi ai.
Kin min abin da yasa raina jin dadi a daren jiya kin gwadawa duk wanda ke guri ke yarinya ce mai tarbiya da sanin yakamata.
Ba komai ba sai daraja min iyayyena da kikayi a gaban kowa wanda nasan ko a bayan mu zasuyi magana a kan hakan da kikayi nakin zama aaaman kujera suna sama su ma.
Don haka shine girmama iyayye da daraja su wanda matan yanzu basu san barin haka a gare su wani sakaci bane maigirma sun dauki yin hakan garesu a matsayin wayewa ne.
Kin ba Alhaji zuma wanda har yasa ba Alhajin ba har hajiya saida taji dadin hakan da kikai masu nagode Rama Saade ce kadai a cikin ku takewa mahaifana haka a baya yanzu kuma naga ta daina hakan itama.
Amma ance shi alheri ko sau daya kaiwa mutum bazai taba mantawa da shi ba a rayuwan shi.
Nai murmushi nace daddy kakanina ne fa kuma iyayye na don may nai masu alherin don su saka min albarka har zakai min godiyan yin hakan da nayi albarkan su fa nake nema nima ?
Murmushi yayi yace dani ai kin samu kuwa Rahama don Alhaji ya saka maki kwado kwado.
Daddy tashi kai wanka ruwa yana jiran ka a ciki tun dazun yace bakya so na kara shakan kamahin matana naji dadi ne bayan kwana biyu an hana ni jin dadi da abata.
Murmushi nayi na zare jikina daga nashi na mike ina cewa Allah ya kaican yana hanaka jin dadin abinda kake so ai.
Bayan yai wanka ne ya karya bai tsaya ba ya dauki key zuwa ganin Alhajin nashi har mota na raka shi saida ya fice gidan na juya zan shiga ciki.
Hindatu ce a tsaye ta dafa bangon gina tana min kallon harara ko ajikina nace a raina sai dai ruwan idon ki ya tsiyayye.
Ban bi ta nata ba na shige abina na barta a wurin ta bini harda zagi ni dai na shige abina.
A can part din anty na shige har lokacin bata fito ba na juya zuwa daki nawa part din.
Ban dade da shiga ba sai ga gajeye ra shigo wurina tana cewa dani hajiya Rahama dama ina jiran ki huta ne muyi magana dake.
Nace gajiye lafiya dai ko ?
Tace dani bakomai sai zance na da maigadi gashi ya matsa min yana ganin nice tare da ku yaji har yau ba wani zance akan maganan mu.
Na nisa nace hakane ai baki ma san wani abu ba wani sabon zance tsakanin Fatima da Hamza driver.
Tace ashe kin sani Hajiya nace wanan tafiyan da mukayi ne na fahinci akwai matsala a tsakanin su.
Nace ni yanzu Gajiye ba wai naki hakan bane kinga ga naki zancen ya shafe ni kin dai san halin matan gidan nan cewa zasuyi munga wuein ci munzo mun tare wa mutane haka a gida gaba dayan mu
Wanan kan zasu fada don fada don basu raina magana su nace ni indai haka bai zama matsala ga maigidan da uwar dakin mu ai suje suyi ta fada kawai.
Yanzu ki bari idan daddy ya natsu zan fito mashi da maganan ai muji may zai fada akai don ayita ta kare .
Tace bari ta koma kada uwar dakin mu ta falka bata kusa tana fita na koma na kwanta don a gajiye nake a lokacin sosai.

********* ********* *********
Ya shiga gida da sallama ya samu daddy da hajiya zaune suna karyawa tana bashi abinci, a hankali ya shigo da sallaman shi duk suka bishi da kallo don bai saba shigo masu wanan lokacin ba hakan.
Sun zauna da shi suka gaisa yake tambayan yadda mahaifin nashi ya kwana da jikin shi hajiya tace da sauki sai dai cikin dare jikin ya dan motsa mai Allah ya taimake mu zumar da wanan yarinyar takawo muna yana nan shi muka samu mukai amfani dashi Alhamdullahi sai ya samu sauki yai barci sosai sai yanzu ya falka shine
Showing 237001 words to 240000 words out of 456145 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80 Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84Chapter 85Chapter 86Chapter 87Chapter 88Chapter 89Chapter 90Chapter 91Chapter 92Chapter 93Chapter 94Chapter 95Chapter 96Chapter 97Chapter 98Chapter 99Chapter 100Chapter 101Chapter 102Chapter 103Chapter 104Chapter 105Chapter 106Chapter 107Chapter 108Chapter 109Chapter 110Chapter 111Chapter 112Chapter 113Chapter 114Chapter 115Chapter 116Chapter 117Chapter 118Chapter 119Chapter 120Chapter 121Chapter 122Chapter 123Chapter 124Chapter 125Chapter 126Chapter 127Chapter 128Chapter 129Chapter 130Chapter 131Chapter 132Chapter 133Chapter 134Chapter 135Chapter 136Chapter 137Chapter 138Chapter 139Chapter 140Chapter 141Chapter 142Chapter 143Chapter 144Chapter 145Chapter 146Chapter 147Chapter 148Chapter 149Chapter 150Chapter 151Chapter 152Chapter 153